Kamar ɗan yaro haka Dawud yake zaune ya ɗora kanshi kan kafaɗar Abba. Yau buƙatar kulawa yake fiye da yadda zai misalta. Sai sauke ajiyar zuciya yake saboda kukan da ya sha.
Sai yau yake jin yau kukan rashin Ummi da Sajda. Yai kukan duk abinda ya faru da shi, sai yau yake jin kamar hawayen shi duk da ya zubda sun fito tare da duk wata damuwa da ya daɗe yana riƙewa.
Tayyab na zaune kan kujera da murmushi a fuskarshi. Ya kasa yarda su ne a haka yau, abin na mishi kamar mafarki tun ɗazu, sai da ya ga Zulfa ta fito daga ɗaki ita ma fuskarta ɗauke da murmushi.
“Yunwa nake ji… Yaya Tayyab ina Mami wai?”
Ɗan yamutsa fuska Tayyab ya yi, ya ga shigarta ciki ɗazu, amma suna nan bai kula da ko ta fito ba, ɗago kai Dawud ya yi daga kafaɗar Abba zai yi magana kenan Mami ta shigo da sallama ita da Khateeb.
“Mami da kanki… Maimakon ki bari in je in ɗauko shi?”
Cewar Tayyab, hararar shi Mami ta yi.
“In ba kwa nan wa yake ɗauko min shi?”
“Na yi shiru.”
Tayyab ya faɗi yana sa hannu ya rufe bakin shi. Dariya Zulfa ta yi tana ƙarasawa ta zauna a gefenshi. Khateeb kuwa takalmanshi ya cire ya ruga da gudu yana faɗawa jikin Dawud.
“Don… Ka siya min irin jakar Ahmad… Mai Power Rangers ne. Yana da kyau kuma.”
Riƙo shi Dawud ya yi.
“Ni ai banga irin jakar ba.”
“Da ka ce jakar Power Rangers fa…”
Murmushi Dawud ya yi. Bai san ta yadda zai fara wa Khateeb bayani kan Abba ba. Zai barshi sai nan gaba tukunna in ya ƙara hankali zai fahimta sosai.
“To zan ce… Ka je ka cire uniform ka ci abinci.”
Sumbatar dawud ɗin ya yi a kunci tukunna ya sauka daga jikinshi yana tafiya wajen Mami da ta kama hannunshi tana faɗin,
“Kai ba za ka tashi ka tafi gidanka ba ko? Sai yamma ta yi?”
Shagwaɓe fuska Dawud ya yi.
“Shikenan yanzun Mami ni bazan zo in zauna ba sai ai ta korata?”
“Ai yanzun ba gidan ku bane nan… Ko mami?”
Cewar Tayyab da Dawud yake harara. Dariya Mami ta yi tana ɗaga mishi kai, kafin ta wuce da Khateeb ciki. Abba kallon su yake da yanayin ƙaunar su da yake karanta a fuskokin su.
Zuciyarshi na karyewa. Har abada ba zai taɓa iya samun kalaman da zai yi amfani da su wajen gode wa Mami ba. Yadda ta riƙe su Dawud yana jin ko shi da kanshi iya abinda zai musu kenan.
Shi kanshi yasan ya kamata ya tafi gida, amma sam zuciyarshi bata son yin nisa da Abba. Gani yake kamar da ya bar gidan komai zai ruguje.
“Ka tafi gida… Babu inda zan je… Ina nan Dawud…in sha Allah.”
Abba ya faɗi a tausashe. Da tsananin mamaki Dawud yake kallon shi, idanuwan shi cike da alamun tambaya. Ɗan murmushi Abba ya yi.
“Lokaci baya canza ƙaunar gaskiya… Dan na jima bana nan baya nufin na manta yanayin abubuwa a tattare da ku. Har yanzun yadda kake yi da fuska in kana tsoron rushewar wani abu bai canza ba.
Yadda kake da fuska in kana mamaki yana nan… Ina iya karantarka ko da ba ka yi magana ba… Hakan bai ɓace min ba.”
Kai kawai Dawud ya iya ɗagawa don yana jin in yai magana hawaye za su zubo mishi. Yau kam kamar baida control akan su haka yake ji. Abu kaɗan ke taɓa zuciyarshi.
“Yaya karka fara…”
Zulfa ta faɗi muryarta na rawa. Don kalaman Abba sun sa jikinta yin sanyi. Babu wanda zai taɓa fahimtar ƙaunar da ke tsakanin iyaye da ‘ya’ yansu. Kamar yadda ‘ya’ ya ba za su taɓa biyan iyaye ƙaunarsu ta shekara ɗaya ba. Girmanta mai yawa ne.
Ɗan dafe kai kawai yayi yana miƙewa. Sai da ya haɗiye wani abu da ya yi mishi tsaye tukunna ya ce,
“Na tafi…”
Kafin ya ƙarasa Tayyab ya ce,
“Sai da safe”
“O. M. G Tayyab to sai na dawo… Ka ji min yaron nan. Duk dama kun gaji da ni…so kuke in bar muku gidan ba?”
Dariya Tayyab yake yi, don baya son ya karanci kewarshin da yake yi. Sai ma jiya da ya yi wani mugun mafarki ya tashi ya fito daga ɗakinshi zuwa na Dawud ɗin kamar yadda ya saba ya tuna baya gidan.
Sai kan gadon shi ya hau ya kwanta har gari ya waye. Yasan zai jima bai saba da rashin kwanan shi a gidan ba. Rayuwa kenan, kullum da canjin da zata zo maka da shi, na ci gaba ko akasin hakan.
“Abba na tafi.”
Dawud ya faɗi.
“Allah ya sanya albarka ya kai ka lafiya. Ka gaishe da ita.”
A kunyace ya ɗan ɗaga kai yana tsayar da idanuwanshi akan Zulfa.
“Kinsan kirana za ki yi kawai in kina buƙatar wani abu ko?”
“Komai lafiya yanzun Yaya… Ka nutsar da zuciyarka ta samu hutu don Allah…Mami na tare da ni…ga Ya Tayyab… Ga Abba.”
A sanyaye ya amsa da,
“Ni kuma fa?”
“Kai fiye da su yaya… Fiye da kowa”
Ɗan murmushi ya yi, yana jin ƙaunar ƙanwar tashi har ranshi. Ba don Yumna ba babu inda za shi don kasancewa tare da su na sa shi nutsuwa ta daban. Da ƙyar ya ja ƙafarshi zuwa ƙofa.
Miƙewa Tayyab ya yi yana rakashi har wajen motarshi.
“Ina tunanin Zulfa ta koma makaranta gobe in Allah ya kai mu.”
“Tayyab ka barta sai Monday in Allah ya bamu aron rai… Sannan ta ƙara hutawa.”
Ɗan jim ya yi.
“Allah ya kaimu Monday ɗin… Mun yi kewarka sosai.”
Murmushi yayi.
“Ba za ku gane yadda nai kewarku ba… Mintina ashirin ɗin da ke tsakanin mu jinsu nake da nisan gaske.”
Sauke numfashi Tayyab yayi.
“Haka rayuwar za ta ci gaba da tafiya ko Yaya? Canji ko da yaushe?”
“Canji ko da yaushe Tayyab… Sai dai a cikin kowanne in ka duba akwai alkhairi da ci gaba…”
“Hakane… Asr na yi… Hirar mu ba za ta ƙare ba… Sai mun yi waya.”
“Ka kula da su sosai… Ka kirani in kuna buƙatata.”
Murmushi kawai Tayyab ya yi, yasan Dawud ya riga da ya saba. Nutsuwar zuciyarshi na tare da kula da su. Babu abinda zai taɓa canza hakan. Tsaye ya yi har sai da ya ga fitar motar Dawud ɗin daga cikin gidan tukunna.
*****
Yana parking ɗin motar shi da gudu ya ƙarasa cikin gida kamar yaro, a tsakiyar falon ya yi sallama idanuwanshi na neman Yumna da ta juyo tana mishi kallo cike da alamun tambayar ko lafiya.
Ƙarasawa ya yi ya zagaya hannuwanshi akan ƙugunta ya ɗagata sama tare da jujjuya su a cikin falon. Dam ta riƙe wuyanshi tana ihu.
“Wayyoo… Wallahi karka faɗo da ni… Ka sauke ni…”
Dariya yake yi sosai yana girgiza mata kai tare da ci gaba da juya su.
“Abba ya dawo… Abban mu Yumna…”
Ɗan ware idanuwa take tana son fahimtar abinda Dawud ɗin ke cewa, sauko da ita ya yi tana maida numfashi, kafin ta ce wani abu ya rungumeta tsam a jikinshi.
Dariya yake sosai kamar wanda aka yi watalbishiri da zuwa Makka. Farin cikin shi ya sa ta farin ciki duk da bata fahimci ko na menene ba. Yau ne karo na farko da ta ji sautin dariyarshi. Duk da ta kan ga fara’arshi.
Amma dariya irin wannan ba ta taɓa ganin yana yinta ba, hannuwanta ta zagaya tana riƙe shi sosai.
“Ban taɓa jin dariyarka ba.”
Daƙuna fuska ya ɗan yi yana tunanin bai taɓa dariya a gabanta ba kenan. Hakan kawai yasa wata dariyar kubce mishi. Zame jikinta ta yi daga nashi tana kallon fuskarshi sosai.
Hannuwanta takai tana tallabar fuskarshi, kyau yai mata na ban mamaki da farin ciki shimfiɗe a fuskarshi.
“Ba ka taɓa yin kyau irin na yau ba…”
Murmushi ya yi sosai.
“Duk da haka bazan kaiki ba…”
Girgiza mishi kai ta yi, ya sa ɗan yatsanshi ɗaya kan laɓɓanta yana faɗin,
“Bana son gardama… Kin fi ni kyau… Ni nake ganar mana haka…Ra’ayinmu kika ji a bakina…”
Murmushi ta yi.
“Babu wanda ya kai mijina kyau.”
Ja mata hanci yayi hakan ya sa ta sakin fuskarshi tana ture hannunshi
“Sallah fa zan yi…”
Kai ya ɗan ɗaga yana sakinta don shi ya tsaya a hanya ya yi Sallah abinshi. Bedroom ta nufa, baya jin yadda yake jinshi ɗin nan zai iya zama. Ya kula duk idan ta yi sallah takan yi karatun Ƙur’ani.
Sake fita ya yi ya yo cefane, aikam har ya dawo ba ta sakko ba don haka ya shiga kitchen ɗin. Nishaɗi yake ji na daban, ya ɗauka ya manta yadda ake jin farin ciki irin na yau.
Girki abu ne da yake jin daɗin yi tare da Ummi tun suna gidansu. Sai ya zamar mishi ɗaya daga cikin abubuwan da yake son yi in yana cikin damuwa ko farin ciki
Cefanen yake gyarawa, fuskarshi ɗauke da murmushi.
“Ummi ina kewarki sosai wallahi… Bana jin daɗi da ba za ki ga matata ba… Bana jin daɗi da ba ki ga yadda muka zama ba… Sai dai ina samun nutsuwa duk idan na tuna addu’ar mu na samunki a kullum.
Akwai alƙawarin ki da zan cika… Abba ya dawo amma zan ƙara ba shi lokaci don ina tsoron sake rasa shi…”
Ɗan ɗaga kafaɗa ya yi.
“Rayuwa cike take da abubuwan tsoro Ummi… Hutu na ga wanda ya rasu ya samu rahma… Na san za ki ce in yi sadaka don Gode wa Allah da yau ɗin nan.
Zan yi idan na sake fita… Mami ma tana samu mu yi sosai… Tana rage min kewarki…”
Ta jima tsaye bakin kitchen ɗin tana jinshi yana magana shi kaɗai, jin ya yi shiru yasa ta matsa tana rungume shi ta baya.
“Me kake yi? Da wa kake magana?”
Shiru ya yi har sai da tai zaton ba zai amsa ta ba tukunna ya ce,
“Ummi… Banda hankali ko?”
Girgiza mishi kai ta yi.
“Ina yi nima… Nasan ba ta jina… Amma yana bani nutsuwa ta daban in damuwa ta min yawa… Cikin kaina nake jin kamar muryata na ba ni haƙuri.”
Murmushi ya yi, yanajin dadin yanda ta fahimci abinda yake ji game da magana da Ummi. Sakin shi ta yi tana miƙa hannu za ta karɓi wuƙar da ke hannunshi ya janye.
“Ki taya ni hira… Ki barni in yi girkina.”
Ware idanuwa ta yi.
“Ka rufa min asiri… In wani ya shigo ya ga kana girki fa?”
Tsayawa yayi yana kallonta
“Sai me don wani ya shigo? In ke aka samu kina yi fa?”
“Ni ai matar gidan ce… Dama girki aikina ne.”
“Haka nima kula da ke aikina ne… Taya ki hidimar gida na ɗaya daga cikin hakan. Ban damu don wani ya zo ya samu ina wanke-wanke ko girki ko taya ki shara ba.
Gara ki fara sabawa… Ina da ra’ayin taya matata kowanne irin aiki. Tunda addini bai haramta min hakan ba.”
Ganin rigima cike da idanuwanshi ya sa ta yin murmushi.
“Ni dai ban yarda ba… Ba na so… Ka fito min daga kitchen in yi girkina. Beside me maka iya dafawa?”
Ɗaga mata gira ya yi duka biyun. Har yanzun kunyarshi ba ta gama sakinta ba, ba kuma ta jin zai taɓa daina yi mata kwarjini. Sai dai ba za ta bari kunyarshi ta hana ta nuna mishi son da take mishi ba.
Ganin ta yi shiru tana murmushi ya sa shi sauke numfashi ya juya ya ci gaba da yanka kayan miyar da yake yi tun da fari, kazar da ta ga yasa a tukunya ta ɗauka ta ɗauraye ta kunna gas ta dora.
“Bani labari…”
Ya buƙata, jingina bayanta ta yi da kantar kitchen ɗin.
“Wanne irin labari?”
Ɗan ɗaga kafaɗa ya yi.
“Mai daɗi…”
Tare suka ci gaba da girkin tana ba shi labarin rayuwar boarding school. Yana mata dariyarshi da ta samu waje tai zaune a zuciyarta.
****
Ya kai mintina goma tsaye a bakin ƙofar ya kasa samun ƙarfin shiga cikin gidan shi. Ba don komai ba sai don ya tsani ɓata wa Ateefa rai. Baya son abinda zai yi hurting ɗinta ko kaɗan.
Sanin gaskiya sai ya fi taɓata akan sanin cewa cikin Zulfa nashi ne. Yasan Ateefar shi. Bai da wani Zaɓi ne da ya wuce yi mata ƙaryar. Da ƙyar ya iya buɗe ƙofar ya shiga da sallama. Yana jin yadda muryarshi ta fito a sanyaye.
Steps ɗin da zai saukar da shi cikin falon ya taka guda uku. Hango Ateefa ya yi can tsakiyar falon zaune ƙasa kan kafet, ta hade kanta da gwiwa. Jikinta sanye da hijab.
Yawo yake da idanuwanshi, takalmanta kansu a tsakiyar falon suke gefe da gefe. Hakan ya tuna mishi cire nashi takalman kafin a hankali ya soma jan ƙafafuwa zuwa cikin falon sosai kamar wanda aka ɗora wa kayan nauyi.
Mukullan mota ya gani can gefe guda a ajiye, hakan ya sa zuciyarshi dokawa. Girgiza kai yake yana maida numfashi. Kar ace Ateefa binshi ta yi, kar ace ta ji gaskiyar da ya kamata ta fito daga bakinshi.
Ƙarasawa ya yi ya zauna yana fuskantarta, hannunshi ya kai ya dafa kafaɗarta.
“Tee…Ateefa…”
Ya kira yana haɗiye wani abu da ya tsaya mishi a maƙoshi saboda tunanin ciwon da take ji a zuciyarta, ciwon da shi ne sanadin shi. Ɗagowa ta yi, fuskarta har ta yi ja, idanuwanta sun kumbura saboda kukan da ta ci.
Muryarta a dakushe ta ce,
“Ba tun yanzun ya kamata ka aure ta ba… Matarka ta farko kuskure ce… Ni kaina kuskure ce. El-labeeb… Zulfa ya kamata ta zama abokiyar rayuwarka…”
Katse ta ya yi da sauri.
“Zafira mistake ce… Na sani… Ke zaɓina ce Tee… Don Allah karki hukunta ni da tunanin aurenki kuskure ne… Karki ce haka…”
Wasu hawaye masu zafi ne suka zubo mata.
“Saboda me za ka yi min ƙarya? Saboda me za ka ce cikinka ne bayan ba naka ba ne?
Ko da yake ma, me yasa zan tambaya… Ka iya kallon idanuwan Mummy dana Dady. Duk ƙaunarka da ƙannenka ka zaɓi su tsaneka… Ka kalli dukkan idanuwansu bakinka ya furta musu ƙarya.
Wace ce ni da zan tsammaci gaskiya daga wajenka… Sai mene ne ƙarya kuma a zaman mu? Soyayyar da kake min?”
Tunda ta soma magana yake girgiza mata kai, shi kaɗai yasan zafin da maganganunta suke mishi, sai dai zai barta ta faɗi son ranta tunda shi ma ya yi mata nashi son ran.
“Kareta nake yi… Bansan me ya kamata in yi ba… Bazan iya bari wani abu ya taɓata ba…”
Ya faɗi a raunane. Wani kuka ne ya ƙwace wa Ateefa, tana jin zuciyarta kamar ana ƙona mata ita da wuta saboda zafin da take mata har a ko ina na jikinta. Kamota ya yi ta ture hannunshi tana janye jikinta.
“Ka ƙyaleni! Ka ƙyaleni kawai…”
Sake kamota ya yi, sai dai wannan karon kukan da take ya tsananta, hakan yasa ba ta da ƙarfin ture shi, kwantar da ita ya yi akan cinyarshi yana ɗora nashi kan a jikinta.
“Ki yi haƙuri… Don Allah ki yi hakuri… Wallahi ina sonki… Babu abinda zai canza hakan…”
“Kana son Zulfa…”
Ta Faɗi cikin kuka.
“Ina sonku ku dukkanku.. Ina inajin jinina ne yake yawo a jikin Zulfa… Yarona ne a cikinki Tee… Na miki laifi… Na miki laifuka a satukan nan…wallahi na daɗe a ƙofar gida ina tsoron shigowa….don Allah ki yi haƙurii…”
Kuka take, ba ta san yadda za ta daina son labeeb ba, sai dai tana tsoron matsayin tata soyayyar a wajen shi.
“Da ka faɗa min gaskiya…”
Muryarshi a dakushe har lokacin kanshi na kwance a jikinta.
“Za ki fahimce ni? Ki ɗago ki kalli idona ki ce in da na tambayeki kafin in yi abinda na yi za ki yarda… Ba Za mu yi faɗa ba… Za ki tsaya a gefe dukkan ‘yan gidanmu suna tsanata na wani lokaci ba za ki ce komai ba… Ki ɗago ki kalleni ki ce ina da wani zaɓi banda ƙaryar da na yi miki…”
Sake maƙalewa ta yi a jikinshi tana wani irin kuka. Ba za ta taɓa yarda ya ɗauki cikin da b S nashi ba, ba kuma za ta iya jure kallon kowa na ɗora mishi laifin da bai yi ba, ba ta damu da son kare ‘yar uwarshi da yake yi ba. Wannan matsalar shi ce.
Matsalarta shi ne kariyarshi, ita ce farko a wajenta fiye da komai, ta tsani yadda zuciyarta ta yarda da cewar baida wani zaɓi da ya wuce yai mata ƙaryar duk da hakan bai canza cewa ya mata ƙarya ba.
Jin ta yi shiru yasa shi faɗin
“Ki yi haƙuri …ban ce wannan ita ce ƙarya ta ƙarshe da za ta shiga tsakaninmu ba… Na miki alƙawari zan faɗa miki gaskiyar ko mene ne a lokacin da ya da ce… Zan kuma ba ki haƙuri… Zan yi ta baki haƙuri har sai kin haƙura saboda rayuwarmu ta jima da haɗuwa waje ɗaya.
Da yarona a jikinki ko babu. Zuciyarmu ta gauraya. Bazan barki ki kubce min ba. Mutuwa kaɗai ce za ta rabamu…Mutuwa kawai.”
Ajiyar zuciya kawai ta ke saukewa, kalamanshi na shigarta.
“A shirye kake ka rasani da yaron mu saboda Zulfa…”
Runtsa idanuwanshi ya yi.
“Tunanin hakan na min ciwo ta yadda ba za ki fahimta ba har yanzun Tee… Ke ce komai nawa… Bansan ta yaya za ki gane hakan ba… Rayuwata za ta samu damuwa idan babu ke…”
Ba ƙin yarda da hakan ne ba ta yi ba, kishi ne yake cinta.
“Haka ka ce… Bazan taɓa kai matsayin zulfa a wajenka ba…”
Ɗagata ya yi, sannan ya sa hannunshi ya ɗago ta daga jikinshi, fuskarta ya tallaba yana saka idanuwanshi cikin nata tare da kamo hannunta ɗaya ya ɗora akan zuciyarshi.
“Tunda taganki bata samu nutsuwa ba saida ta mallake ki… Kin zauna daram a ciki… Fitarki na nufin za ta daina bugawa. Tare da ke take numfashi Ateefa.
Ta yaya zan miki bayani yadda za ki gane? Ke da Zulfa ba za ku taɓa zama ɗaya a wajena ba. Matsayin ku daban ne… Hakan baya nufin baki da muhimmanci a wajena.
Duka rayuwata zan iya miƙawa saboda ‘yan uwana… Kinsan hakan tun kafin ki aureni… Ke kuma kina cikin Rayuwata…”
Kai ta ɗan ɗaga mishi, sai yanzun ta fahimta, ba muhimmanci Zulfa ta fita a wajen Labeeb ba, ba son Zulfa ya fi yi a kanta ba. Matsayin su ne daban daban. In aka zo tsakanin su zai iya komai saboda ita. In aka zo kan Zulfa zai iya haƙura da jin daɗin rayuwa in har hakan na nufin sauƙi a wajenta.
Amma da duk bugun zuciyarshi haɗe yake da soyayyarta, tana ganin gaskiyar hakan cikin idanuwanshi. Ganin yadda fuskarta ta yi wata irin nutsuwa ya sa shi faɗin,
“Laifina zai yafu? Ki faɗa min ya zan gyara abinda na yi?”
Ya ƙarasa maganar yana goge mata fuskarta da hannuwanshi, son shi take ji a ko ina na jikinta. Bata taɓa tunanin zai yiwu ka so mutum da yawa har haka ba sai akan Labeeb.
Ko cikin bacci za ta rantse ƙwaƙwalwarta bata manta yadda zuciyarta take sonshi. Tun abin na bata mamaki har ya daina.
“Ya wuce… Ka auri zulfa…”
Ta faɗi maganar na fitowa daga kan harshenta tana ƙona mata harshe saboda zafinta, sai dai tasan hankalin ta ba zai taɓa kwanciya ba in ba auren Zulfa ya yi ba.
“Cikin sati mai kamawa…”
Runtsa idanuwanta ta yi tana karanto duk addu’ar da ta zo kanta saboda wani irin kishi da ya taso yake neman lulluɓeta. Sumbatarta da labeeb yayi ya sa ta buɗe idanuwanta.
“Ina sonki… Ina sonki sosai.”
Da ƙyar ta iya amsa shi da faɗin,
“Ina sonka nima…fiye da yadda zan iya faɗa maka… Ina kishin soyayyata za ta haɗu da ta Zulfa a zuciyarka…”
Ɗan guntun murmushi ya yi, kishin Ateefa daban ne, zai yi ƙarya in ya ce baya jin daɗin yadda take kishin shi.
“Ba zan haɗa soyayyarki da ta kowa ba… Saboda babu wadda zan so kamar ki… Soyayyarki daban take a zuciyata Tee. Sai dai in so kowa kala daban.”
Lumshe idanuwanta ta yi tana bude su cikin fuskarshi.
“Sonka ne raunina El-Maska…sonka ya yi min yawa… Ka daina ƙara min wani.”
Ta ƙarasa cikin sanyin murya, murmushi ya yi yana jin yadda zuciyar shi ta samu nutsuwa. Miƙewa ya yi tsaye yana kama hannunta ya ɗago da ita, janta yayi suka hau sama zuwa bedroom ɗinsu. Zaunar da ita ya yi gefen gadon.
Cikin nutsuwa ya faɗa mata komai, yadda yasan da cikin Zulfa har zuwa yau ɗin. Ba ta ce komai ba sai hawaye da suke zubar mata, ta samu miji da ke ƙaunarta amma bakowa bane yake dace da ‘yan uwa masu son su kamar Labeeb.
Ƙaunar da ke tsakanin shi da family ɗinshi gaba ɗaya tana bata mamaki, tana kuma jin yadda har abada ba zata taɓa samun irinta ba. Miƙewa Labeeb ya yi. Da kanshi ya shiga banɗaki ya haɗa mata ruwa ya fito.
“Dubi yadda kika ɓata min fuskarki da kuka… Hawaye baya maki wahala ke kam.”
Shagwaɓe fuska ta yi.
“Sonka ne yake fito da su.”
Space ɗin da ke tsakanin su ya haɗe, tana jin numfashin shi kan fuskarta.
“Yadda kike sona yana min daɗi… Yadda kike nuna min yana saka ni farin ciki…”
Idanuwanta ta zuba mishi, har yanzun akwai rama a cikin nashi idon.
“Wanka zan yi…”
Ta Faɗi ganin yadda yake kallonta, sauke numfashi ya yi yana ɗan ɗaga mata kai kafin ta raɓa shi ta wuce. Gefen gado ya koma ya zauna yana maida numfashi kamar wanda ya sha gudu.
In Ateefa na tare da shi ƙwarin gwiwar da yake ji daban ce. Har ya samu ƙarfin fuskantar su Zainab anjima. Kwanciya yayi kan gadon ƙafafuwanshi na ƙasa. Wayarshi ya zaro daga aljihu ya duba ya ga ko biyar ba ta yi ba. Ya ajiyeta kan gadon. Baisan lokacin da bacci ya ɗauke shi ba.
Ko da Ateefa ta fito ta ganshi ya yi bacci tausayinshi ne ya kamata, rashin nutsuwa ya hana mishi bacci kwana biyu. Shiryawa ta gama yi cikin riga da zani na atamfa simple style, haka ma ɗaurin ɗankwalin da ta yi, powder kawai ta shafa wa fuskarta.
Ita ɗin ba ma’abociyar kwalliya mai yawa bace ba, takan ƙoƙarta farkon auren su da Labeeb ɗin, wani lokaci hannu yake sawa ya goge mata janbakin duk da ta sa ya ce ta fi mishi kyau a haka. Sai ta bar wahalar da kanta.
Gefenshi ta kwanta ba don tana jin bacci ba, ta sa hannu ta ɗauki wayarshi, bata taɓa nuna mishi tana jin kishin sunan Zulfa ne passwords ɗinshi na komai ba, ba za ta manta satinsu uku da aure ba.
*****
Zaune yake kan kujera yana danne-danne a jikin system ɗinshi a falonsu na sama. Ta fito daga ɗaki ta samu waje gefenshi ta zauna.
“Baka tura min hotunan wajen walimar ba… Ka ce an tura maka a wayarka kafin a kawo Album ɗin…”
Wayar ya ɗauka tana gefenshi ajiye ya miƙa mata tare da faɗin,
“Ke ce ba ki tuna min ba… Na manta… Ungo ki tura.”
Karɓar wayar ta yi, ya ci gaba da danne-dannen da yake a jikin system ɗin. Swiping ta yi ta ga akwai key a jiki.
“Buɗe min…”
Ta faɗi tana miƙa mishi wayar, ba tare da ya ɗago kanshi daga abinda yake ba ya ce
“Rubuta Zulfa…. Zai buɗe.”
Wani abu ta ji ya tamke a ƙirjinta.
“Zulfa ba cousin ɗinka bace?”
“Yep…duk abinda kike son buɗewa nawa in kinsa zulfa bai buɗe ba ki sa zulfa1 ko zulfa2.”
Yadda yake maganar ba tare da wata damuwa ba ya sa ta danne abinda take ji.
“Me yasa Zulfa a ko ina?”
Ɗagowa ya yi da alama yana son nazarin fuskarta.
“Kawai…”
Ya amsa yana ɗan ɗaga mata kafaɗa ba ta sake ɗaga maganar ba.
*****
Har zuwa yau ba ta sake ɗaga mishi maganar ba, buɗe key ɗin tayi tana shiga gallery ɗinshi tana kallon hotuna. Ba ta taɓa wuce hotuna da videos ba. Tana girmama yadda ba ta da shamaki da wayarshi.
Tasan za ta iya buɗe text ɗinshi bai damu ba, yakan ce babu wani sauran sirri a tsakanin su. Su kwanta waje ɗaya, su tashi waje ɗaya. Saboda me wayarsu za ta zama sirri. Ta zaɓi ta bar mishi abinshi ne don gudun ɓacin rai.
Ba ta so ta buɗe ta ga hirarsu da Zulfa da tasan dole ma ta ɓata mata rai. Kira ne ya shigo wayar, kafin ta saka ta a silent har Labeeb ya motsa. Asad ne, ɗagawa ta yi.
“Sai ka tasar min miji yana bacci?”
“Oh Anty… Auren nan fa mu ma yinshi za mu yi a daina mana gorin soyayya.”
Asad ya faɗi daga ɗayan ɓangaren. ‘Yar dariya ta yi.
“Kice mishi su Zee Zee sun iso yanzun nan… Tana ma tare da mu.”
Ganin Labeeb ya miƙe zaune yana miƙa ya sa ta faɗin,
“Ya ma tashi Asad… Bari in bashi.”
“No ki faɗa mishi kawai….sai anjima Anty.”
Sallama tai mishi tana sauke wayar daga kunnenta. Kallonta Labeeb ya yi a kasalance don jikinshi ya mutu, kamar marar lafiya haka yake jinshi ya kuma san baccin yammar da yayi ne.
“Na gaji sosai…bansan bacci ya ɗauke ni ba…”
“Na san ka gaji… Ga yamma ta yi shi ya sa na kasa tashinka… Asad ne ya ce Zainab ta zo.”
Sai da ya ji kanshi ya sara, miƙewa ya yi bai ce mata komai ba ya shiga banɗaki. Wanka ya yi tukunna ya ɗan ji ƙarfin jikinshi. Alwala ya yi kafin ya fito don ko bai duba agogo ba yasan magrib ta gabato.
Sa’adda ya fito Ateefa ta ɗauko mishi kayan da zai sa. Har turare ta fesa mishi a jiki, sakewa ya yi tukunna ya fita zuwa ɓangarenta.
“Me za ka ci kafin ka dawo?”
Ta buƙata don tasan fita zai yi. Shagwaɓe mata fuska ya yi.
“Mene ne kuma?”
Ta buƙata, kawai ware idanuwanshi ya yi yana turo mata laɓɓanshi da suka ƙara mishi kyau.
“Me na yi kuma? Daga na tambayi me za ka ci?”
“Ba wani ɗan hug… Fita fa zan yi…”
‘Yar dariya ta yi tana takowa inda yake, hugging ɗinshi ta yi.
“Shikenan?”
Lumshe idanuwa ya yi yana ɗan ɗaga mata kai. Sosai yake buƙatar hug ɗin, zamewa ya yi daga jikinta ya sumbace ta kafin ya ce,
“Ki dafa ko me yai miki zan ci… Sai na dawo.”
“A dawo lafiya… Ka kula da kanka.”
“In sha Allah… Ki kula min da ku… Ina sonki sosai… Kin san haka ko?”
Kai ta ɗaga mishi, sai da ya sake Sumbatarta kafin ya fita. Murmushi kawai ta yi tana gode wa Allah da miji irin Labeeb. Ba lallai bane ya yi wa kowacce mace… Amma ita ɗin shi yai mata.
Masha Allah