Skip to content
Part 45 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

“Gara da kika zo Zee… Tun ɗazu muke ta fama ya ƙi cin komai… Kuma Doctor ya ce ya ci wani abu…”

Asad ya faɗi yana maida wayar da ya kira Labeeb aljihunshi. Gefen gadon Mamdud Zainab ta zauna. Ta fi mintina biyu ba ta ce komai ba, tana kallon yadda gaba ɗaya ya fita daga hayyacin shi. 

Ba ta yarda da muryarta ba saboda kukan da take ji za ta iya somawa a kowanne lokaci. A raunane Mamdud ya ce, 

“Sallah da ake bina na samu na rama… Sai yanzun na idar…”

“Da ka bari ka ƙara samun sauƙi tukunna…”

“In kuma don in yi sallar na farka fa?”

Ya buƙata yana tsare Zainab da idanuwanshi, ba ya son yadda suke mishi, ba komai hakan ke ƙara mishi ba sai ƙaunar su, baisan abinda fitowar gaskiya zai yi ba. 

Amma yana tsoro, rashin Arif na mishi wani irin ciwo. 

“Ka daina… Bana so kana wannan maganar… Yaya Anees kana jinshi ko?”

Zainab ta faɗi hawaye na cika mata idanuwa. Jin sun yi shiru ya sa ta haɗiye kukanta. 

“Ni dai ka ci wani abu… In haɗa maka tea? Me za ka ci?”

Sanin halin Zainab ya sa Mamdud faɗin, 

“Tea ya yi…”

Kafin Zainab ta ce wani abu Asad ya sauka ya ɗauki mug da cokali. Haɗa wa Mamdud ɗin tea ya yi mai kauri ya miƙa wa Zainab ta riƙe, hannun shi mai lafiyar ya miƙa wa Asad ya kama yana ɗan taimaka mishi ya kishingida. 

Tukunna zainab ta bashi mug ɗin, a hankali yake kurɓar tea ɗin yana jinshi kamar toka a cikin bakinshi. Sam baya jin sha ko cin komai. Kawai ba zai iya rigimar Zainab ba ne a yadda yake jinshi. 

Shiru suka yi, kowa da kalar tunanin da yake yi a ranshi. Babu mai magana ko ƙarfin halin hira. Gara ma Asad da suke chatting da Mardi. Ya rasa me ya sa shaƙuwarsu ta fi ta da. 

Tun ranar walimar Dawud suka yi wata irin shaƙuwa ta ban mamaki. Komai baya mishi daɗi, dauriya kawai yake, yakan samu nutsuwa in suna hira da ita. Ko don ita kaɗai take fahimtar irin abinda yake ji kan Zulfa ne ya kasa ganewa. 

Ta san ka so abinda ba za ka samu ba, ta san ciwon abin, ta fi kowa gane yanayin abinda yake ji tunda ya faru da ita. Magariba da aka kira ne ya sa su miƙewa suka yi alwala. 

Dutsen da Anees ya samo wa Mamdud ya yi taimama da shi ya miƙa mishi, ya tsaya ya yi ya ja gadon yana juya shi yanda zai fuskanci gabas kamar yadda suka yi mishi ɗazu tunda babu dama ya motsa ƙafarshi. 

Tukunna suka fita zuwa masallaci suka bar shi da Zainab da ta fito daga banɗaki bayan ta ɗauro alwala. Sallah ta yi, ta idar tana zaune kan dardumar tana wa Arif addu’a ta ji wayarta na ringing. 

Sai da ta idar lokacin har ta yanke tukunna ta janyo jakarta ta ɗauko wayar, buɗewa ta yi taga wanda ya kira, kiranshi tayi. Ringing ɗin farko ya ɗaga 

“Kin barni da kewarki… Wayar ma sai kin min yanga za ki ɗauka?”

Ɗan murmushi ta yi. 

“Yi hakuri… Sallah nake shi ya sa… Kewa ba kai kaɗai kake yinta ba…”

“Hmm… Da kin jira ni Friday mu zo tare.. Duka jibi ne fa kika rufe idanuwanki.”

Jin wata sabuwar rigimar Ishaq yake nema ya sa ta faɗin, 

“Ya ka dawo daga aiki? Ya gajiya?”

“Gajiya gata nan… Gidan babu daɗi da ba kya nan…”

“Ba gani ba muna waya.”

“Haka za ki ce ko? Ya jikin Mamdud ɗin?”

“Da sauƙi, Alhamdulillah.”

“Ma sha Allah… Allah ya ƙara sauƙi ya tsare gaba. Zan ɗan yi aiki kaɗan…Za mu yi waya anjima. Ki kula min da ku… I love you.”

“Love you more… Kuma ni kaɗai ce ka ƙi ka yarda.”

Tana jin dariyarshi ta cikin wayar. 

“In ya fito sai ki daina min musu ai.”

Ya faɗi, sai da yai kissing ɗinta ta cikin wayar kafin ya kashe. Sauke numfashi ta yi tana jin kewarshi sosai, sai dai in ba ta zo ta ga Mamdud ba ba za ta taɓa samun nutsuwa ba. 

Labeeb ne ya shigo da sallama. Da fara’a Zainab ta amsa shi, Mamdud kam da ido ya bi shi zuciyarshi na dokawa da ƙarfin gaske. Duk yadda yake son su san komai don ya huta yana tsoron abinda hakan zai musu.

Sai da Labeeb ya zauna tukunna ya amsa sannu da zuwan da Zainab tai mishi. Yana ɗorawa da, 

“Ya hanya? Ina Ishaq ɗin?”

“Alhamdulillah… Shi bai zo ba ai… Sai Friday ya ce. Aiki ya mishi yawa ba za su barshi ya…”

Katse ta labeeb yai da faɗin, 

“What? Shi ne yabarki kika taho ke kaɗai? Bari in kira shi…”

Waya ta ga yana shirin ɗaukowa daga aljihunshi. 

“Ba ni kaɗai ba fa… Ƙaninshi da yake Nile uni ya sa ya rakoni… Kuma ni ce na ce sai na taho… Yaya ko ni kaɗai zan iya zuwa fa… Ina Abuja ina kaduna?”

Idanuwa Labeeb ya kafa mata, da gaskiyarta duka awa nawa ne, ko ita kaɗai za ta iya zuwa. Ya kamata yasan ta girma yanzun. Ba yarinya bace ƙarama da take buƙatar kulawarshi ko da yaushe kamar da. 

Sai dai har abada a idanuwanshi da zuciyarshi Zainab ba za ta taɓa girma ba. 

“Nasan za ki iya zuwa… Bana so ki zo ke kaɗai ɗin ne…”

Murmushi Zainab ta yi. Wannan gardamar ba za ta iya winning ba. Don haka tai shiru kawai. Su Asad suka shigo. Kujera kowa ya ja yana samun waje ya zauna. Idanuwa Mamdud ya kafa w Labeeb da ke fassara ‘In ba za ka fara magana ba zan yi.’

Sosai Labeeb ya gyara zamanshi yana maida numfashi kamar mai shirin kokawa da abinda zai fito daga bakinshi. Gaba ɗaya ya wani hargitse. Mamdud na kallonshi har lokacin. 

Ya kasa daina mamakin zuciya irin ta Labeeb da yake son raba wahalar kowa, Shaiɗan da hassada su suka sa shi kasa ganin waye Labeeb sai yanzun da yake jin lokaci ya ƙure mishi. 

Hannunshi ya kai ya dafe ƙirjinshi inda zuciyarshi ke ciwo kamar ya buɗe ƙirjin ya fito da ita ya huta, amma yasan abu ne da ba zai yiwu ba. Muryar Labeeb ta katse mishi tunanin da yake yi. 

“Ina son faɗa muku wani abu ne… Sai dai ina tsoron yadda za ku ɗauke shi…”

Ya ce yana ƙin yarda ya haɗa idanuwa da kowa a cikinsu. Matso da kafet ɗinta Zainab ta yi ta zauna saitin Labeeb ɗin. Cikin sanyin murya ta ce, 

“Ba sai ka faɗa mana ba in ba ka so Yaya.”

Girgiza mata kai ya yi, abu ne da ya zata ya binne shi har abada, sai yanzun yake jin girman laifukanshi da tarin zunuban da baisan ko ya soma wanke kwatarsu ba. In har yana jin nauyin buɗe su a gaban su Asad. 

A gaban ‘yan uwanshi da yake jin komin munin laifukanshi ba za su guje shi ba. Ya zai ji in aka bayyana sirrikanshi da abinda yake ɓoyewa a idanuwan dukkan mutanen duniya? Da wanne ido zai kalli Ubangijin shi? 

Numfashi yake ja yana fitarwa da sauri-sauri saboda wani irin tsoro da ya kamashi. Sam bai shirya wa kwanciyar kabari ba, babu abinda ke dawo mishi sai ɗan girman inda aka karkata aka saka Arif, aka bi da tukwane da ƙasa aka rufe ko ina ruf. 

Wata irin zufa ke fito mishi, dafa shi ya ji an yi ana girgizawa. 

“Yaya… Breathe… Don Allah ka bar maganar nan… Ba sai mun ji ba.”

Asad ke faɗi cikin tashin hankali ganin yadda Labeeb ɗin ya birkice lokaci ɗaya. Da ƙyar ya samu ya saita numfashin shi kafin ya soma magana. 

“Ina da wata rayuwa da ba ku san da ita ba a baya… Kafin aurena da Zafira… Kafin aurena da Ateefa… Na ɗauka komai zai zamana a ɓoye… Komai ba zai taɓa fitowa ba… Wannan ranar ba za ta zo min ba. 

In za ku kula inba don…don Arif ba bana so ‘yar aiki na kwana a gida ko da bana nan… Na fi so ku kwana ku kaɗai …”

Shiru ya yi yana maida numfashi, yana jin yadda gaba ɗaya hankalinsu yake a kanshi. Yadda ɗakin yai wani shiru, muryarshi kawai ke tashi, kafin ya ci gaba da faɗin, 

“Bazan tuna exact shekaruna ba… Abinda ba zai mantu ba shi ne ‘yar aikin da ke shigo min ɗaki da wuƙa a hannunta… She is so big… Babba sosai… Tana taɓa ni… Har ƙasan zuciyata na san bai kamata ba… Bana so… Ko da yaushe… Tun bansan me take ba har na fara sani… Tun bana ganewa har na fara ganewa… Ina jin yadda na canza a can ƙasan zuciyata. 

Sai dai bansan ya zan tsayar da canjin ba… Kasancewata cikin mata kala kala bai taimaka min ba… Na wa kaina alƙawari wata ba za ta sake min abinda ‘yar aikin nan ta min ba… Ni ne zan yi… I will be in control. 

Abubuwa sun min yawa sosai… Sosai abubuwa suka yi min yawa… A nan ku ne… Kula da ku… Mummy da Dady basa nan… Tunanin kar abinda ya same ni ya same ku… Acan kuma ni ne da wata rayuwar ta daban…ni ne da bin mata kala-kala…kullum babu hutu cikin kaina….”

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Yayaa…”

Zainab ta ƙarasa wasu hawaye na zubo mata, duk wannan ya riƙe shi kaɗai, basu sani ba. Girgiza mata kai Labeeb ya yi, ba ya son su ce komai sai ya gama, da dukkan ƙarfin gwiwar da yake da shi yake faɗa musu abinda yake faɗa musu. 

“Nasan kuna buƙatata… Kuna buƙatar kulawa da tarbiyya… Sai dai ni ban san me nake buƙata ba… Ban sani ba… In na rasa yadda zan yi da ku… Ko ina tunanin bana cike muku gurbin Mummy da Dady… Mata nake bi… Mata su ke mantar dani duk wata damuwa kafin in fara shan syrup… Kafin ƙwayoyi da suka zame min jiki. 

Ban taɓa sha a cikin gida ba… Ban taɓa bari ko da wasa kun san wata rayuwa banda wadda nake nuna muku ba… Ina buƙatar ku kasance masu nagarta… Bana son abinda zai taɓaku… Bana son lalacewata ta same ku…”

Dafe kanshi Asad ya yi cikin hannuwanshi yana son in mafarki yake ya farka, ba zai yiwu ace Labeeb shi kaɗai ya ɗauki waɗannan abubuwan ba, shi kaɗai bai taɓa rabawa da su ba. Bayan duk wahalar su akanshi take. 

Anees kam cike da mamaki da al’ajabi yake kallon Labeeb yana son haɗa rayuwar wannan sabon Labeeb ɗin da yake ji da kuma ta yayanshi amma sam ya kasa. Kanshi ya kulle. 

“Ko abokai banda su… Kowanne aboki kuɗi yake so a wajena.. Kowanne aboki so yake in mishi hanya ya shiga film… Kowanne aboki so yake ya ji wani abu game da ni da zai yi wa mutane kuri da shi. 

Kula da ku shi ne kawai abinda nake yi a rayuwata da nake jin daɗinshi… Matan.. Ƙwayoyin… Giyar… Babu abinda nake ji dai-dai saboda ina jin zunubansu na tarar min… Kafin Mamdud ya shigo rayuwata…”

Labeeb ya ƙarasa yana ɗago kanshi ya sauke idanuwanshi akan Mamdud da ya sa hannunshi mai lafiyar yana goge hawayen da suka tarar mishi cikin idanuwa. Ya rasa abinda ya kamata ya ji, abubuwan sun mishi yawa. 

“Haɗuwa da Mamdud ya sa ni jin kamar haske ne ya shigo rayuwata ta ɓangaren da babu komai sai duhu. A rana ɗaya na ji na samu aboki… Ina buƙatar wani ya san ni … Asalin ni…mai muni da mai kyau… Dukana. 

Mamdud ya sa rayuwa ta min sauƙi… Ya sa in na tafi na barku bana tunanin wani abu zai same ku… A hankali ya tashi daga abokina zuwa ɗan uwan da zan iya faɗa wa komai da ke faruwa da ni.  

Kuskure na farko da na yi… Buɗe wa Mamdud gurbatacciyar rayuwata… Shi ya fara saninta duka… Bansan ya akai ba… But ina jin har ƙasan zuciyata duk wani zunubi na shan kayan maye ko neman mata da Mamdud ya yi ina da kaso. 

Ni ne sila… Ni na ja shi…sai dai wallahi ba da niyyar ya yi kalar abinda nake yi ba…kawai ina son wani ya fahimta ne…wallahi Mamdud ba da niyyar ɓata maka rayuwa ba… Ba haka bane nufi na…”

Labeeb yake faɗi muryarshi na sarkewa saboda laifukanshi da yake ji suna sake danne shi, saboda kukan da Mamdud yake yi, inda shi hawayen ke zubo wa ƙila da ya samu sauƙin abinda yake ji a halin yanzun. 

Sosai kukan Mamdud yake tsananta da maganganun Labeeb ɗin. Yana da na sanin hassadar da ya bari ta yi tasiri a zuciyarshi, yadda yake tunanin Labeeb ya samu komai na rayuwa bayan ba haka bane ba. 

Yana tare da Labeeb a ko da yaushe, kafin ya kashe wa kanshi dubu biyar ya kashe musu hamsin. Kuɗinshi basu dame shi ba, ɗaukakar da yake da ita ba ta gabanshi. Rayuwa yake lalube mai inganci da bai samu ba a lokacin. Tallaba yake buƙata daga wajen Mamdud ɗin da ya kasa bashi. 

Hawayen Asad su suka fara zuba, ya ɗauka ya gama sanin tashin hankali sai yanzun da sam ya kasa fahimtar yadda za a yi mutum ɗaya ya riƙe wannan abin a ranshi shi kaɗai. Zainab ma sosai take kuka. 

Hannun Labeeb Anees ya zo kamawa don ya bashi comfort ko yaya ne, Labeeb ya janye yana girgiza mishi kai, baya buƙatar komai daga wajen su sai ya gama. In ya so ko me za su yi sai su yi. 

“Aure na da Zafira shi ne sanadin barin neman matana… Like bansan me ya faru ba… Kawai na san bazan iya komawa zina ba…dauɗarta nake gani sosai bayan nasan menene aure… Ƙarya nake in na ce yadda Mamdud yake yi da rayuwar shi ba ya damuna. 

Sai dai banda bakin da zan hana shi… Waye ni to? Yaushe na gyaru da har zan mishi wa’azi? Wa ya nuna mishi kalar rayuwar nan? Zulfa ta san ina neman mata… Ita ta matsa min da In yi aure don tana ganin zan bari. 

Sai dai bata san ina shaye-shaye ba… Ba don in ta sani za ta yi min wani kallo ba… Sai don zuciyata ba ta jure ganin damuwa a idanuwanta… Kamar rayuwa ba ta min wahala sai ga Ateefa…kallo ɗaya… Kallo ɗaya nai mata nasan akwai damuwa. 

Ƙaddara kallon mu kawai take… Sai kuma ta haɗu da Mamdud…”

Katse shi Mamdud ya yi yana goge hawayen da ke zubar mishi kafin ya ce, 

“Baisan duk idan na kalle shi bana ganin komai ba sai mutumin da yake da abinda ni banda shi ba, ba kuma zan taɓa samu ba… Baisan tare muke a kullum ba amma burina bai wuce yadda zan yi wani abu da zan fishi ba. 

Me butulun zuciyata take saƙa min banda hassada ga mutumin da bai min komai ba sai alkhairi… Ranar birthday na ce ranar farko da nake jin kamar na tsani Labeeb. 

Saboda na yi tunanin shi ya sa yarinyar da na fara haɗa shimfiɗa da ita samun wani abu a lemo na sha… Bayan ranar na ga me Labeeb yake so, in lalata rayuwata kamar yadda tashi ta lalace. 

Asalina ya sani ƙyamatar duk wata rayuwa irin ta Labeeb da yake yi a wajen gidanku nake… Rana ɗaya hakan ya rugujemin… Rana ɗaya burina na ƙin kusantar zina ya sauya. 

Hakan ba zai zama dalilin da zan ci gaba da neman mata da shaye- shaye ba… Sai na buɗe wa shaiɗan zuciyata ya zauna… Wannan ba laifin Labeeb ba ne…lalacewata zaɓina ne… Kamar yadda tashi ma zaɓin shi ce. 

Dukkan mu ba mu da dalilin da za mu kare kanmu a gaban Allah… Sai dai kana da tarin alkhairai da za su danne laifukanka. Bani da komai sai hassada Labeeb… Da me zan je lahirata?”

Ya ƙarasa wani gunjin kuka na ƙwace mishi, Asad… Anees… Zainab sun zama ‘yan kallo yau, yayyensu guda biyu suke kallo cike da baƙunta. Suna mamakin yadda duk wannan tashin hankalin ya sirrantu daga sanin su. 

Sai lokacin wasu siraran hawaye suka zubo wa Labeeb, sam hassadar Mamdud ba ta dame shi ba. Dole ya yi mishi ita. Wanne alkhairi yai mishi da ya wuce ja mishi lalacewa. 

Muryar shi a dakushe Labeeb ya ci gaba da faɗin, 

“Ina acting a films da dama… Plot na soyayya kala-kala…sai ƙaddara tai min plot na daban… Buɗe idanuwa nayii na ji duk numfashin da zan ja akwai Ateefa a cikin shi. 

Sosai ƙaddara ke kallon mu muna ta haukan mu… Da dubban matan da suke cikin rayuwata… Sai ƙaddara ta haɗa ni soyayya da yarinya ɗaya da Mamdud… Shi ne kuskure na biyu. 

Da na bar Ateefa ta zaɓa a tsakanin mu… Shi ne kuskure na… Ƙarya nake in na ce da minti ɗaya na yi da na sani… Ina sonta sosai wallahi… Ina son Ateefa…”

Hannuwa Labeeb ya sa yana dafe fuskarshi, zafin hawayenshi na sauka cikin tafukan hannunshi. Kafin ya ja numfashi ya fitar da shi yana buɗe fuskarshi. 

“Soyayyar Ateefa ta haɗa mu faɗan da ba ku san da shi ba da Mamdud… Nasan na mishi laifi… Amma na ɗauka ba za mu jima ba zai yafe min… Kullum fatana da addu’ata kenan… ‘Yan uwa ba sa riƙe junansu na lokaci mai yawa…haka nake faɗa wa kaina. 

Zai haƙura yabar min Ateefa… Bayan ni na kasa haƙura in bar mishi ita…”

“Me yasa ba za ka faɗa musu abubuwan da nai maka ba?”

Mamdud ya buƙata yana jin ina ma ace zai iya sakkowa daga kan gadon don ya haɗa idanuwa da Labeeb sosai, ya ga shi ɗin wanne iri ne a cikin mutane. Jin Labeeb ya yi shiru ya ce, 

“Zainab ba zai faɗa muku ba… Yayanku zuciyarshi ba irin ta mutane ba ce ba… Saboda baya so ku tsane ni… Ba zai faɗa muku na bi duk wata hanya da zan iya tunani ba don na hana auren shi da Ateefa. 

Ba zai faɗa muku da na ga na kasa na yanke alaƙ da shi ba… Ni yakamata in biya shi alkhairin da ya yi min…babu kunya a cikin idanuwana na ce ya biyani kula da harkokin shi da na yi. 

Da kaina na ciri adadin kuɗin da nake da buƙata na barshi… Kiran shi… Text ɗinshi…babu wanda nake amsawa… Sai dai me… Ina binku… Ina magana da ku bayan na tsani ɗan uwanku. 

Wace irin gurɓatacciyar zuciya nake da ita? Ta yaya zan raina wa kaina hankali in ce ina son ku shi kuma na tsane shi? Ƙarya nake idan na ce bana kewar lokutan da muka tafiyar tare da shi. 

Ƙwayoyi da cocaine ɗin da ya dinga ƙoƙarin hana ni sha su suka zame min abokai… Tun kuna min maganar don Labeeb ya yi aure nima na bar muku gida har kuka haƙura.

Har raina nufin in bar dukkan rayuwar ku na yi… Na kasa… Na kasa barin ku wallahi… Arif… “

“Ya Rabb…”

Shi ne abinda Zainab ta iya faɗa tana haɗe kanta da gwiwarta, kuka ne take ji da ba shi da sauti saboda daga zuciyarta yake fitowa da wani irin ciwo.

“Banda kowa a duniya… Banda kowa sai ku ɗin dai da nake son bari… Bansan ina zani ba a cikin duniya… ‘Yan uwa nake nema kamar in siye su da raina… Ku kaɗai ne… Ku kaɗai ne ba kwa kallona da ƙyamata bayan kunsan asalina… Ku kaɗai kuka karɓeni ni kuma nai muku butulci…”

Da sauri Asad ya tashi daga inda yake yana komawa gefen gadon Mamdud ɗin ya zauna, kanshi ya ɗora kan cikin Mamdud ɗin yana wani irin kuka da ko a rasuwar Arif bai yi irin shi ba. 

Baisan ta yaya za su soma faɗa wa Mamdud ba zai ga jininshi ba a duniya, bai san yadda za su cike mishi gurbin abinda ya rasa da wanda ba zai taɓa samu ba. Duk idan aka yi maganar ‘yan uwantaka ta jini a gaban Mamdud sai ya ji wani iri. 

Saboda baya son ya tuna cewa shi ɗin akwai wani banbanci a tsakanin su, a tashi yarintar ya ɗauka ƙaunar da suke mishi za ta mantar da shi. Tarin dukiya ba zai siyi iyaye ba komin lalacewar su. 

Tarin dukiya da ƙauna ba za su taɓa cike gurbin ‘yan uwantaka ta jini ba komin gurɓacewarta. Akwai tarin hikima da ba kowa zai iya fahimta ba. Shi kanshi Labeeb ba wani abu yake wa kuka ba sai wannan ɗin. 

Kafin ya kasa faɗa ya yi saurin cewa, 

“Cikin zulfa… Cikin Zulfa ba nawa ba ne… Na Mamdud ne…”

Wani shiru ne ya ziyarci ɗakin. Banda ƙarar agogon da ke aiki yana nuna cewar a iya wajensu komai yake tsaye. Rayuwa na ci gaba da tafiya a wani wajajen. 

Ɗagowa Asad ya yi daga jikin Mamdud yana kallon shi cike da wani baƙon yanayi, ya kasa haɗawa ko da wasa yadda aka yi cikin Zulfa ya zama na Mamdud balle har zuciyarshi ta yarda. 

Anees kuwa idanuwanshi kan Labeeb suke, yana son ya faɗa mishi cewa kuskure ne wannan karon. Yana son ya faɗa mishi wani mummunan wasa ne da bai kamata yai musu shi ba. 

Wannan wace irin ƙaddara ce? Shi ne abu na farko da ya fara zuwa zuciyar zainab kafin wani yanayi da ta kasa fassarawa ya lulluɓeta. Tana jin yadda idanuwanta suke mata zafi saboda kukan da take yi. Kanta har sarawa yake yi.

Sam Mamdud bai yi ƙoƙarin goge hawayen da suke zubar mishi ba, ya ƙyale su su ci gaba da zuba saboda baisan ranar dainawar su ba. Ta ina zai fara? Kukan rashin Arif? Ko kuma na rasa su? Ya bar zuciyarshi ta fara daga inda ta ga zai fi mata sauƙi. 

Cikin kuka ya ce, 

“Ina karantar tsanata a fuskokin ku ba don na ga laifunku ba… Butulcina ba zai yafu ba… Ban cancanci tausayinku ba… Don Allah ina roƙonku… Ku fita daga ɗakin nan… Ku barni iya abinda nai muku… Iya rashin ku ya ishe ni har ƙarshen rayuwata… Bazan iya jure jin yadda kuka tsane ni ba… Wallahi bazan iya ba… Ku yi haƙuri… Kar ku faɗa min…”

Ya ƙarasa yana wani irin kuka mai cin rai. Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo wa Labeeb. Cikin ɓacin rai yake kallon Mamdud 

“Saboda me ka ce min raping ɗinta ka yi? Saboda me?…me ya sa ba za ka ce min ƙaddara ba ce? Me yasa ba ka faɗa min ba ma ka cikin hayyacinka ba? Balle kasan abinda kake yi?”

Labeeb ya ƙarasa maganar wasu sabbin hawayen na zubar mishi. Shi ma cikin kukan ya amsa Labeeb ɗin, 

“Saboda na san za ka yi min uzuri! Saboda ban cancanci hakan ba! Saboda ina son ka ji zafin abinda nai maka ka tsane ni kamar yadda ya kamata ka yi!”

Hannu Labeeb ya sa yana goge fuskarshi duk da sabbin hawayen da yake ji suna zubar mishi. A ƙufule ya ce, 

“Kar ka faɗa min abinda ya kamata in ji ko in yi Mamdud Ibrahim Maska…”

Wata dariya da ta juye zuwa kuka Mamdud ya yi. 

“Mamdud Ibrahim Maska ko? Don bana cikin hayyacina ba zai zama uzurina na ɓata rayuwar yarinyar da na ɗauka a matsayin ƙanwa ba… Sanin bana cikin hayyacina ba zai sa ta yafe min ba… Yaushe za ka soma tsanata ne wai? Ba ka ga su Asad sun fara ba ne?

Me kuma zan yi? Ko sai ka riƙe ɗana na cikin Zulfa a hannunka tukunna za ka gane abinda na yi muku?!”

“Cikin ya fita! Ya zube!”

Sosai Mamdud yake kallonshi kafin wata dariya ta kubce mishi. Sosai yake dariyar da duk wanda zai ji yasan ba ta lafiya bace ba. 

“Ba zai canza abinda na yi ba! Ba zai canza ɓata mata rayuwa da na yi ba…”

Su dukkansu kallon Mamdud suke yi, sosai suke kallonshi suna wani irin kuka. Zubewar cikin Zulfa shi kuwa ya canza komai. 

“Kun gani ko.. Don Allah kar ku faɗa min…ku tafi ku barni kawai…”

Mamdud ya ƙarasa cikin kuka ganin ya kasa fahimtar kalar kallon da suke mishi suna wannan kukan, shi ya kamata ya yi kukan rasa su. Shi ya kamata ya yi irin kukan da suke yi. 

“Sai ka saba… Ko itace ka sa ka kore ni kana ajiyewa sai na dawo wallahi… Na rasa Arif Yaya Mamdud… Kar ka sani binne wani ɗan uwan nawa bayan yana da rayuwarshi… Ni ban tsane ka ba… Bansan yadda zan tsane ka ba. 

Faɗanku da Yaya bai dame ni ba…kun fi kusa… Ni dai ba inda za ni…”

Asad ya faɗi yana share hawaye. Jinjina kai Anees yayi yana ɗorawa da, 

“Ba ma zama a tare da juna lokacin da komai yake dai-dai. Muna zama ne in komai ya hargitse…muna riƙe da hannun junanmu yadda ko mene ne in ya wuce muna nan tsaye ba tare da ya kayar da mu ba. 

In kana tunanin don ƙaddara irin wannan ta faru da kai za mu tafi ka yi kuskure…”

Kukan Mamdud ne ya sake tsananta, yana jin zuciyarshi kamar za ta fito, yana da yaƙinin ko ‘yan uwan da suka haɗa jini da su ba za su so shi kamar yadda su Asad suke sonshi ba. 

“Ba ku haɗa jini da ni ba…”

Miƙewa Zainab ta yi, kafin su san me yake faruwa ta ɗauki mug ɗin da Mamdud ya sha tea da shi ta haɗa shi da bango ta fasa, abinda ya rage a hannunta ta yi amfani da shi tana yanka tafin hannunta. 

Su duka tashin hankali ya sa sun kasa nufarta, kujerar Labeeb ta sa ɗayan hannunta tana ja baya da shi akai, ba ka sanin kana da ƙarfi sai ranka ya ɓaci. Tsaye ta yi kan Mamdud, hannunta ta dunƙule tana ba jinin dake zuba damar fitowa sosai yana zuba kan cikin Mamdud yana fallatsa har jikin Asad da ke kallonta cikin tashin hankali.

Wani irin kuka take yi 

“Sa hannu ka tarba Yaya Mamdud… Jini kake buƙata irin namu ya yi yawo a jikinka kafin ka yarda da ƙaunar mu ko? Ka tarba! In sha za ka yi in tarawa za ka yi a wani waje a kira likitoci su saka maka shi sai a yi! Ƙila za ka daina mana gorin cewar ba mu isa mu so ka yadda muke sonka ba saboda ba bu jininmu a jikinka. 

Kasan abinda kuke sha… Kaɗan ya rage na fara… Yaya Asad ne kaɗai ya sani saboda haukana da yarintata na zaton zai sa in daina jin rashin Mummy. 

Me yasa za ka shigo rayuwarmu in kasan ba za ka bari mu so ka ba? Me ya sa za ka dinga min duk wani abu da ya kamata Dady yai min? 

Me ya sa kiranka kawai zan yi za ka zo ka ji damuwata… Me ya sa bakinka zai kira ni sister in ba za ka bari in so ka ba?!”

Kuka yake yana kallon jinin Zainab da ke zuba a jikinshi cikin tashin hankali, zuciyarshi na gab da fitowa saboda dokawar da take yi, tashin hankalin mutuwar arif ne kawai zai kai mishi wannan da yake gani. 

Yana kuka yake faɗin, 

“Na daina… Ibnalillahi wa inna ilaihir raji’un…Zainab na daina…bakina ba zai sake furta jini ba…”

Kallonshi take tana ganin alƙawarin da yai mata duk da bai furta ba. Ba za ta bar Labeeb ya ɗauki nauyin faɗa wa Mamdud ba zai samu haihuwa ba. Don yau ne rana ta ƙarshe da su dukkansu za su dinga ɗaukar nauyi su kaɗai. Daga 

Labeeb ɗin har Mamdud… Tare za a raba kowa ya ɗauka.

“Doctor ya ce ba za ka samu haihuwa ba… Ƙaryar banza ce tun da Allah ne yake kyautar shi.”

Kallon Zainab da ke janye hannunta da ke ɗigar jini Mamdud yake kamar yaren Swahili ta yi mishi maimakon Hausar da ta yi. Kukan shi ya ji ya yi tsaye cik. Muryarshi kamar ba tashi ba ya ce, 

“Me take cewa?”

Yana kallon Labeeb da ya kau da kanshi gefe kafin ya kalli Asad da ke kusa da shi da ya rufe fuskarshi da tafukan hannunshi yana kuka har jikinshi ke ɓari. Anees ya kalla da cikin sabon tashin hankali ya ce, 

“Haka Doctor ya ce, sa’adda ka yi hatsari wai ba za ka sake haihuwa ba…”

“Oh…”

Mamdud ya faɗi yana jin wani abu ya rufe da wata irin ƙara a zuciyarshi. Burinshi ne na ƙarshe ya ɓace ɓat daga zuciyarshi kafin ƙwaƙwalwarshi ta fara yawo. Ƙwanshi ɗaya kenan a duniya. Shi ne ƙaddara ta gifta mishi akan Zulfa. 

Ƙarshen burin ganin jininshi ne ya zube. Hannunshi ya ɗora kan cikinshi inda jinin Zainab ya zubo yana ɗago da tafin hannunshi zuwa dubanshi. Yana ganin yadda jininta ya yi mishi fenti. 

Sam baya buƙatarshi kafin ya samu ƙauna ta gaskiya. Ya san ƙauna ta gaskiya akan Arif… Shi ne kawai Allah ya jarabta da yi wa soyayyar da yake jin ‘ya’yan shi ne kawai zai iya yi wa irinta. 

Wataƙila wannan shi ne hukuncin shi, wataƙila wannan ƙaddarar ita ce silar samun rahmarshi. 

“Godiya ga Allah a cikin ko wanne hali…”

Mamdud ya faɗi can ƙasan maƙoshi, kafin ya soma jero, 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Yana yi wasu hawaye masu ciwo na zubo mishi. Su dukkansu ɗauka suka yi, a tare suke farawa su dire suna kuka, da yarda cewa Allah ne kaɗai zai kawo musu ɗauki. Da imanin cewa sauƙi na tare da wanda bai saki ambaton Allah a lokacin da ya fi buƙatar taimakon shi ba.

Jan kujera Anees ya yi yana haɗeta da gadon Mamdud ɗin, hannunshi da yake kallo kamar zai ga canjin rubutun da ƙaddara ta yi mishi a ciki ya kamo yana dumtsewa. Yana son nuna mishi suna tare da shi a cikin rashin shi. 

Hannun Zainab da ba ciwo Labeeb ya kama yana zagayawa da su suka zauna ta ɗayan gefen Mamdud ɗin. Sannan ya kama hannunta mai ciwon yana kallon girman yankan da ke jiki. 

Hawayen da suka zubo mishi sun hana shi magana. Ɗayan hannunshi na riƙe da na Zainab ɗayan na kan kafaɗar Mamdud. Anees ɗayan hannunshi da baya cikin na Mamdud ya kai ya kama na Asad ya riƙe dam. 

Duk yadda rayuwa za ta gwara su, ko wace kalar ƙaddara kan musu sauƙin ɗauka saboda sun gane ƙarfin da Allah ya basu na ɗaukar ƙaddarar duk da ya ɗora musu na tare da ƙaunar junansu. 

Kuka suke na abinda ya faru, kuka suke na abinda suka rasa. Kuka suke na yarda da ƙaddara, kuka suke na jiran sakamakon da yake zuwa ga waɗanda suka rungumi ƙaddararsu da hannuwa biyu.

***** 

Bai koma gida ba sai wajen goma saura na dare ranar. A falon ƙasa ya samu Ateefa da ta miƙe jin shigowar shi tana ƙarasawa ta yi hugging ɗinshi. Yanayin yadda ta riƙe shi kamar zai gudu ya sa shi yin mamaki. 

“Tee lafiya dai ko?”

Sake shigewa tai jikinshi. 

“Babu komai… Ka daɗe sosai.”

Sauke numfashi ya yi. 

“Ban kula dare yayi ba…Afuwan ban kira ba kuma.”

Ba ta ce komai ba, ta ɗan yi jim tana jin ɗuminshi, yanayin muryarshi da yake a dakushe yai mata wani iri. A hankali ta ɗago daga jikinshi. Hannunshi ta kama, bai yi musu ba ya bi ta suka hau sama. 

Ba ta tsaya da su a ko ina ba sai dining area ɗin, kujera ya ja ya zauna. Wata irin gajiya yake ji da ko magana baya son yi, yana kallonta ta zuba mishi abinci. Plate ɗin ya ja gabanshi tana miƙo mishi cokali. 

Sama-sama ya ci abincin ba don yana jin yunwa ba, ya sha ruwa. 

“Har ka yi me?”

Ɗan yatsina fuska ya yi. 

“Bana jin yunwa… Bana jin daɗin komai ne… Kwanciya kawai nake son yi. “

Fuskarshi take kallo da take a kumbure. Kafin ta miƙe tana ba shi hannunta da ya kama yana miƙewa shi ma. Bedroom ɗinsu suka nufa, nan ta barshi a tsaye ta shiga ta haɗa mishi ruwan wanka ta fito da towel ta miƙa mishi tukunna ta fice ta koma dining area ɗin tana haɗa kayan da ya ɓata ta sauka kitchen da su. 

Sa’addmda ta koma kayan bacci ta ɗauko mishi ta feshe mishi su da turaruka ta ajiye akan gadon, kafin ta sake kayan jikinta zuwa na bacci ita ma. Da ya fito wankan ma bai ce mata komai ba, ta kula baya son magana. 

Kayan shi ya saka ya hau kan gadon ya kwanta. Ko ta ina yake jin yadda awannin nan da suka wuce suka fama mishi ciwukan da yake ɗauke da su shekara da shekaru. A ko ina na zuciyarshi yake jin zafi da raɗaɗin da suke mishi. 

A Wani fannin kuma yana jin kamar ya sauke wani ƙaton nauyi ne da ya jima yana ɗauke da shi. Yana jin yadda ƙannen shi suka karɓi El-labeeb da El-Maska. Yadda ya raba Rayuwar shi ta baya tare da su ba tare da sun ƙyamace shi ba. 

Yadda suka fahimci ƙaddarar da bai da iko akan faruwarta. Zuciyarshi na mishi nauyi duk idan yanayin fuskar Mamdud da halin da yake ciki suka gifta mishi. Zai miƙa duk dukiyar da ya mallaka in har hakan na nufin Mamdud zai samu haihuwa. 

Sai dai yana da yaƙinin addu’a za ta iya canza ƙaddarar Mamdud. Allah mai rahma ne ga bayinsa. Musamman masu yarda da dukkan fuskar da ƙaddara ta zo musu da ita. Mai kyau ko mai muni. 

Ateefa da ta hawo kan gadon ta katse mishi tunanin shi. Wutar ɗakin ta kai hannu ta kashe musu tana kunna ta gefen gadon marar haske. Sai da ta ja abin rufa ta soma rufe Labeeb tukunna ta rufe kanta tana jan jiki ta kwanta. 

Hannun shi ya kai ya lalubi nata yana riƙewa cikin nashi. Sannan ya matsa yana ɗora kanshi kan pillow ɗinta, gyarawa ta yi yadda zai kwanta sosai. 

“Bana jin daɗi… Komai ciwo yake min.”

Goshinta ta haɗa da nashi tana jin hucin numfashin shi akan fuskarta. 

“Komai zai wuce… In sha Allah. Allah baya ɗora mana abinda ba za mu iya ba… Yakan ɗora mana ƙaddara don ya gwada ƙarfin Imaninmu ne.”

Lumshe idanuwanshi Labeeb ya yi yana buɗe su, maganganunta na zama a zuciyarshi. 

“Bansan ya Mamdud yake ji ba… Sai dai tunanin bazan taɓa samun yara ba kawai na sa in ji numfashina na shirin ɗaukewa…”

Sake matse hannunshi Ateefa ta yi cikin nata, tana neman kalaman da za ta yi amfani da su. 

“Ka yarda ba komai ba ne a rayuwa yake da alkhairi ko? Haka ma yara a rayuwar wasu… Allah ya ga ba za su zame musu alkhairi ba shi ya sa bai basu ba. 

Hakan baya nufin addu’ar su ba za ta juya zuwa wani abu mai kyau a duniyar su ba…”

Duk yanayin da yake ji sai da murmushi ya ƙwace mishi. 

“Tee kin iya kalamai masu nutsar da mutum…”

Turo baki ta yi, ta yi ƙasa da murya sosai. 

“Ba wani nan… Ni ban ma san me nake faɗa ba. Kawai bana son ganinka cikin damuwa ne…”

Sumbatarta ya yi, shi ma baya son jinshi cikin damuwa. Sai dai damuwa na ɗaya daga cikin abubuwan da rayuwa ta ƙunsa, babu wani farin ciki da yake dawwamamme kamar yadda babu damuwar da take dawwamammiya. 

Sosai yake buƙatar Ateefar shi. Yake buƙatar ko na ‘yan mintina ne ya manta damuwar da yake ciki, soyayyarta na fifita mishi ciwukan da ke mishi zafi. Don haka ba ta gaza wajen taya shi raya daren cikin nishaɗi da ƙaunar juna ba. 

<< Rayuwarmu 44Rayuwarmu 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.