Skip to content
Part 13 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!” Malam Haruna ya maimaita har sau uku yana duban Maryam gami da sauraron bayanan Inno.

Shiru ya ɗan yi yana nazari, kafin kuma ya dubi Inno.

“Shakka babu wannan ba na asibiti bane.”

“Yanzu me kake ganin za’a yi Malam?” Fadin Hajiya Hafsatu cike da jimami, sauran mutan gidan duk basu nan da yawa an tafi jeran ɗakin Amarya don a ranar za’a kai ta gidanta.

“Akwai inda zamu je da Maryam, ke Fatima ki shirya muje tare. Ai za ki tuna Malam Kabiru ko?”

Inno ta ɗan yi jim, kafin can ta ɗago kai tana duban mijinta.

“Shi dai abokin Baba?”

Ya gyaɗa kai da murmushi.

“Shi dai, wurinsa zamu je. Inada labarin unguwar da suka koma ba tun yau ba, sai dai Allah bai sa zan je ba sai yanzun.”

Inno ta gyaɗa kai, kunya ya ɗan kamata.

“Yanzu Malam ba zai ce don larura ta same mu bane muka tuna da shi? Gaba daya nauyi ya kamani.”

“Banda abinki Fatima, ai kamawa take. Kuma Allah ne bai yi za ku je din ba sai yanzu.” Cewar Hajiya Hafsatu.

Murmushi kawai Malam ya yi yana duban Maryam wacce kanta ke a ƙasa, ita kadai ta san azabar da take ji a kirjinta. Ta wayi gari ba dangi ga shafewar tunani. Sai kuma ga jarrabawar rashin ji da magana. Me za ta yi banda ta godewa Mahalicci ya da Ya ƙageta kuma Yake sane da dukkan wani hali da zata shiga?

Tun tana kallonsu har ta gaji ta sunkuyar da kai kasancewar bata san me suke cewa ba.

Koda Malam ya kwatantawa Alhaji Lawwali wurin da yake nufin kai Maryam. Nan da nan ya ganeshi.

“Ah, to ai ta kwana gidan sauki nima. Kamar Kaka yake a wurin surukina Huzaifa.”

Mamaki ya kama su, sai kuma abin ya yi musu daɗi a karshe aka ajiye magana sai an kai Amarya zuwa gobe sai a je wurin Malam Kabiru.

*****

A daren aka kai Amarya hankali sai ya koma ga Maryam. Gaba daya taron ya ficewa Inno da su Humaira daga rai. Humaira da kyar take samu ta ci abinci sai Inno ta lalaɓata.

Washegari kuwa tun karfe goma suka yi shirin tafiya. Sai dai bisa ga shawarar da Alhaji Lawwali ya bayar, kada a soma zuwa da Maryam har sai Malam da Inno sun je sun gaidashi daga nan su yi mishi bayani. Sosai sun ji dadin shawarar wannan ta sanya suka shirya suka kama hanya.

*****

Malam na zaune a tsakar gidansa an shimfiɗa masa tabarma yana karatun Alkur’ani. Sallamar Baharu ɗaya daga cikin yaran Almajiransa ne ya katseshi. Ya amsa sallamarsa ya ci gaba da karatun har ya kai aya.

“Ya akai Baharu?”

Cike da ladabi ya amsa.

“Kana da baƙi ne a waje.” Bai ji wani mamaki sosai ba kasancewar ya saba samun baƙi kala-kala. Kai ya gyaɗa.

“Toh, gani nan zuwa.”

Ganin Baharu bai motsa ba ne ya sanyashi dubansa.

“Maza ne da mace.”

Malam ya ce.

“Ikon Allah, toh ina zuwa.”

Ya buɗe murya ya yi kiran Gwaggo Kubra. Ta fito daga kofar cikin gidan. Dattijuwa ce sai dai ta fi shi kwari sosai don ya girmeta. Umarni ya ba ta kan ta kawo tabarma. Ba musu ta juya ciki ta dawo, Baharu ya shimfiɗa, ya fice ya yi kiransu.

Shekaru fiye da ashirin kenan, dama tasan za’a yi hakan, abu ne mai matukar wuya Malam Kabiru ya ganesu farat ɗaya, don ma dai idanun akwai kwari har a lokacin.

Bayan zamansu suka gaisa, ya fi gane surukinsa Alhaji Lawwali. Ganin haka Malam Haruna ya ɗan matsa kaɗan.

“Malam ba ka shaida mu ba ko?”

Malam Kabiru ya ƙara dubansu sai dai dagaske bai gane ba. Kafin ma ya ba da amsa Malam Haruna ya ɗora ta hanyar nuni da Inno.

“Wannan Fatima ce diyar Malam Zakari Dambatta.”

“Allah Mai Iko! Dama suna nan? Ina suka koma? Allahu Waheed.”

Yana maganar a ɗan rikice, Malam ne ya kwantar da kai ya mishi bayani a nutse. Salati ya yi sannan ya dora da fadin.

“Muna roƙon Allah Ya bayyanamana su, Ya sa su na kyakkyawan hannu.”

Duk aka amsa da Amin. Karshe ya umarci Inno da shiga cikin gidan, ya kuma sanya a kawowa su Alhaji Lawwali ruwa. Anan ne yake jin dangantarsu da Alhaji Lawwali, ya yi addu’a sosai suka ci gaba da hirar jimamin rashin su Malam Zakari. Sai bayan sun kammala shan ruwa da furar da ya tilasta musu sha sannan Malam ya soma bayanin takamaiman abinda ya kawosu. Tun daga zuwan Maryam na farko Kauyen Cinnaku har zuwa yanzun da ta samu matsala.

Cike da tausayawa Malam Kabiru ya hau girgiza kai.

“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ai wato muna cikin wani irin zamani ne da mutane ba sa tsoron Allah. Yanzu a kashe mutum ma a yar da gawar a titi ba komai bane. Allah Ya kyauta, Allah Ya bata lafiya, Ya gafartamata. Ina son ganinta.”

“Mun bar ta a gida, dama mun ce zamu zo ne mu soma yi maka bayani tukunna.”

“Ba komai, kar ku damu. Da yau da gobe duk ɗaya ne in Sha Allah zamu yi nasara.”

Suka amsa, sai da suka kara ɗan ta6a jira kafin su yi sallama Inno wacce ta samu tarba mai kyau a gidan ta fito ta kara yin godiya ga Malam. Ya bata hakurin rashin su Malam ya kuma yi fatan Allah Ya bayyanamusu su.

*****

Kwance yake Hanan na gefensa tana bacci, shi kuwa idanunsa ƙurr a kan fuskarta, so yake ya ga abinda ya  ɗauki hankalinsa game da ita. Don kyau Hanan kyakkyawa ce, hakanan tana da diri daidai gwargwado kuma ta iya sarrafa mutum a shimfiɗa. Matsalarta uku ne zuwa. Ta fiye naci da kuma yarda da soyayya. Hakanan ko nawa za ka damƙamata sai ta nuna zalamarta akan kuɗi ga kishi da ta ɗarsawa zuciyarta nashi. Murmushin gefen kumatu ya yi. Yasan ta haɗu da aiki.

A jikinta ta ji ana kallonta wannnan ya sa ta buɗe idanun. Ya bita da lallausan murmushi wanda ya ƙara kashemaka jiki, miƙewa ta yi ta nufi hanyar banɗaki. Sai da ta wanke baki kamar yanda ya sharaɗanta mata, baya son kowane irin wari ne mara kyau. Dole ta sanya ta ke kiyayewa. Bayan ta fito ya buɗemata hannunsa ta kuwa hau gadon ga fada jikinsa ya matse.

“I love You.” Ya ji ta furta, yamutse fuska ya yi gami da ɗago kai.

“Ban hanaki ba?”

Ya ƙarashe yana jan gashin dokin da ke kanta. Ta kuramishi idanu wasu kwalla suka cika nata idanun.

“Ba zan iyaba Fu’ad, dagaske nake sonka. Aurenka nake son yi.”

Ita kanta ba ta san sadda kalmar ta suɓuce daga bakinta ba, me kuwa zai yi banda dariya, tun tana biyemishi tana murmushi har ya ba ta haushi ta haɗe girar sama da ta ƙasa.

“Aure fa kika ce? Are you out of your senses?”

“No! Kawai ina sonka, kuma I mean it! Tun haduwarmu ta farko nake maka son aure, ba na biyan muradina ba. Muna komai irin na aure, me zai hana ka aure ni? Tun haduwarmu na kama kaina daga kula dukkan wani da nake kulawa ya zama kai kaɗai ne yanzu nawa. Soyayya ce ta janyo nayi hakan, kar ka ƙi aurena Fu’ad. Please ka aureni.”

Tun soma maganarta ya zubamata idanu yana kallonta. Har ga Allah kallon wacce ta sha kwaya yake mata wannan ta sanya ya shiga bankaɗa ƙarƙashin pillow da ta kwanta kafin ya sauka ya hau laluba jakarta. Ganin haka ta biyoshi a baya ta fisge jakar.

“Me kake nema?”

Ya ɗan haɗe gira.

“Abinda kika sha, saboda kina magana kamar wacce ta sha kwaya ne. Ni kuma iyakata sigari, bana mu’amala da masu shan sama da ita kin gane ko?”

Ta tabbatar ya mugun rainamata wayo, sai dai ta daure ta zauna gefensa gami da dafa cinyarsa tana kallonsa tsakar ido, shima kallonta yake ba tare da ya ji komai ba.

“Ba abinda na sha, ban sha komai ba Fu’ad, a hayyacina nake. Ni Hanan ina maka son aure.”

Ya yarda yanzun dagaske take, ba kuma ita ce farkon nuna wannan rashin hankalin gareshi ba. Wannan ta sanya shi tamke fuska.

“Ku mata rashin wayewarku kenan, daga an ɗan shafaku shikenan sai ku susuce ku soma roƙon rayuwa da mutum har abada. Look, idan kina son mu’amalarmu ta ɗaure, kar ki ƙara kawomin batun Love ballantana kuma aure. Wannan shine gargaɗi na karshe da zan miki. Bana so ba kuma kaunar hakan. Besides, waye zai auri YAR BARIKI? Please kar ki ƙara maganar.”

Daga nan ya mike ya ja Towel ya shigewarsa banɗaki. Kanta ke wani irin sarawa, wa zai auri ƴar Bariki? Wannan kalma ta fi komai sukar zuciyarta. Miƙewa ta yi a haukace ta suturta jikinta don daga ita sai vest da wando three-quarter. Abayarta ta dora ta dauki dukkan abin bukatarta tana kuka da sheshsheƙa ta bar ɗakin. Ko bayan fitowarsa ya ga wayam, dama an saba hakan sai dai yau shi kansa yasan kalamansa sun fi na koyaushe zafi da muni. A karan kansa sai yake jin bai kyauta ba sai dai kuma ba yanda ya iya, shi bai iya bin mace yana ban baki ba akan wata bukatarsa.

*****

Ya tsani kwanan cikin asibitin, a wani ɓangare akwai wata irin rayuwa wacce ba kowa ke iya tsallake mata ba. Ba kuma sai kana mazaunin cikinta bane, a’a, wasu matan ba ka iya tsallakewa tarkonsu. Shakka babu ko ina akwai nagari da kuma mugu. To shi kam zai ce ya haɗu da mata wane ashirin waɗanda ke mishi tayin kansu, daga ƴanmatan har matan aure. Wannan yana daga dalilan da ya sanya baya son keɓancewa a wurin da jama’a suka yawaita ko suka san shi. Dole ce ta sanyashi kama ɗaki a hotel din kafin kammaluwar ginin da ya ɗauko a gidansa.

Ɗaki na goma sha uku yake a Bristol Hotel, kasancewar shiru ne ɗakin, yana shirin tafiya wurin aiki, wannan ta ba shi damar tsinkayar ƴar hayaniyar da ke tashi a ɗaki na goma sha huɗu.

Ya yi mamakin maganganu da dama da suke fitowa daga bakin mazauna ɗakin. Mamaki yana kara kasheshi ta yanda tsoron Allah Ya yi ƙaranci a wurin ƴan adam. Bariki ma ba’a ɗauketa komai ba. Sam bai ji tausayin budurwar ba, koma me saurayin ya faɗi daidai ne, da ita kuma mai hankali ce da ta yiwa kanta faɗa.

A nutse ya kammala shirinsa, ya karasa ga abincin da aka kawomishi ya ɗan tattaɓa, kewar Ummansa na damunsa. Hakan yasa ya shiga nemanta a waya. Sun gaisa take tambayar batun karatun su Amira.

Murmushi ya yi.

“Ba fa matsala Umma, Uncle Hashim ya ce kawai nayi kokarin yin magana da mai makarantarsu ta nan, a bada hakuri a kuma san abinda ya kamata a yi, amman a hannunsa zasu karasa.”

“Toh hakan ma ya yi kyau. Mun gode Allah. Yanzu kana ina ne?”

Ya ɗan rausaya idanu a ɗakin.

“Ina hotel.”

Bata ce komai ba sanin da tayi tun a baya ya tsani kwanan cikin asibiti kuma ta yarda da dalilansa.

“Toh Allah Ya tsare. Ashe abinda ka yiwa Hajiya Salma kenan? Kaga Adam bana son rashin ta ido. Wannan ba tarbiyyata ba ce.”

Ya dafe kai, kenan labari ya zo gareta.  Sosai take mishi nasiha cikin tattausan murya mai sanya nutsuwa.

“Na gode Umma, ki yi hakuri ba za ki ƙara kamani da laifi makamancin wannan ba in Sha Allah.”

Da murmushi ta amsa.

“Alhamdulillah, na gode nima Allah Ya yi maka albarka, Ya tsaremin kai a duk inda za ka shiga.”

Da wani nishadi ya ce ameen sannan suka yi sallama.

Kayyakin bukata ya dauka hannunsa ya saƙale white coat dinsa ya fito daga  ɗakin. Hakan ya yi daidai da fitowar Fu’ad daga nashi ɗakin, ya shirya tsaf cikin wando three quarter blue da baƙar t-shirt sai face cap dinsa wacce ake wa laƙabi da hana sallah.

Ido hudu suka yi da juna sa’ilin da kowannensu ke murzawa ɗakin mukulli. Adam ya ji wata irin faɗuwar gaba, kada dai yaronnan ne ke kwana da mace?

‘Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!’  Ya furta a ƙasa ransa, a fili kuwa ɗauke kai ya yi kamar bai ganshi ba ya juya abinsa. A bangaren Fu’ad kuwa bai yi mamakin ganin Adam anan ba sai dai bai zargeshi da aikata irin aikinsa ba. Asalima sai ya ji nauyin ganin da ya yi mishi, koda dama ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yake. Gani ya yi idan ya tafi zai kufce mishi ba lallai ya san inda zai sameshi ba kuma yana so su yi magana wannan ta sanya ya yi azamar shan gabansa. Adam ya ɗago kai fuska a murtuke yana dubansa. Kallon ma alamar tambaya ce ba bukatar sai an furta.

“Kayi hakuri, na tsayar da kai. Sai dai roƙo ne zan yi gareka.”

Ya ƙarashe a marairaice yana jin ba daɗi.  Abin ma sai ya so ba Adam dariya, bai ta6a ganin inda ake yakice mutum yana mannewa ma kamar dole,  ya dubi agogon hannunsa.

“Zan je wurin aiki, na yi latti yanzu. Na dauka nan kake kwana ai.”

Sai kunya ta ɗan rufeshi, ya yi ta maza yana shafa sumarsa.

“Yeah, nan na kwana.”

“Ok, sai na dawo kenan.” Daga haka ya giftashi ya wuce.

*****

Daga inda take tsaye tana hango Joshua suna neman yin cacar baki da wata baiwar Allah da bata gane ko wacece ba.

“Joshua!” Ta kwala mishi kira tana daga saman balcony.

Kusan a tare suka juyo, sai dai sam ba ta gane fuskar ba. Joshua ya ƙarasa da saurinsa.

“Yes Ma.”

Tana ƙarewa matar da ke tsaye kikam kallo ta ce

“What’s happening? Who is that woman?”

Ya girgiza kai.

“I dont know her oo, this is her third time for coming here. She wants to meet you, she said you know who she is. She is very stubborn.”

Ta ƙura idanu tana duban matar, can dai ta ce.

“Let her in.”

“Ok.” Daga nan ta juya zuwa ciki, ya juya ga matar ya bata umarnin ta shiga. Sai da ta watsamasa kallon raini shima ya kauda kai yana muzurai, ya yi gaba ta bi bayansa zuwa falo.

Daidai sadda Salma ta sauko zuwa kasa har lokacin tana mamakin ko wacece wannan.

Tana karasowa ta ɗago kai tana dubanta da murmushi. Gaban Salma ya faɗi.

“Hajiya Salma.”

Gaban Salma ya fadi, ta ji miyan bakinta ya kafe da daure ta hadiye tashin hankalinta ta tamke fuska.

 “Me ya kawoki gidana? Wa ya nunamaki?”

Ta yi wata dariya kafin ta ce.

“Kina tunanin ba zamu taɓa nemanki ba? Ko kin manta yarjejeniyar da ke tsakaninmu na yi miki tuni?”

Ɗabas ta zauna saman kujera ba tare da ta shirya ba. Ta dubeta lokacin da gumi ke tsastsafo mata.

“Inace mun kashe magana da ke?”

Halima ta yamutse fuska, ta shafi shafaffan hancinta.

“Ke Salma, wallahi daga ke har Hayat ku fita idona! Ki kama kanki tun ban fasa kwai kowa ya ji ba! Gwara miki iccen kabari sau dubu a kaina! Ki kiyayeni Salma!”

Salma ta maze.

“Me kike nufi? Me kike bukata kuma Halima banda abinda akai ya wuce shekaru sama da ashirin?”

Wata harara Halima ta wurgamata tana mai girgiza ƙafa.

“Kinsan me? Ba wurinki na zo ba ma wallahi, dauki waya ki min kiran Hayatu.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 12Rumfar Kara 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×