Skip to content
Part 14 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Kamar ta yi magana sai ta fasa ta mike.

“Ina za ki kuma?”

Fuska a murtuke ta amsa.

“Ai kinsan dai ba zan gudu ba Halima tunda gidana ne ba tashi sama zan yi ba. Wayata zan je ɗaukowa.”

Dariyar rainin wayo ta yi.

“Ai fa, masu gida. A dai bi a hankali don abin aro bai rufe katara. Wataran kwaɓa za ta yi ruwa ko nace tana dab da yi muddin ba’a yi ta da wajewa ba. Atoh!”

Salma ba ta tankamata ba ta nufi sama da sauri-sauri. Halima ta bi bayanta da kallo ta yi wata dariya gami da kwafa tana bin kowane kusurwa na falon da kallo. Wani tafkeken hoto na Fu’ad ta gani. Ta yi wani murmushi gami da faɗin.

“Ɗan mu ya girma kenan!”

A can kuwa Salma na shiga ɗaki ta dau wayarta saman gado. Hannunta har rawa yake ta kira lambar Hayat sai dai har ta gama ƙararta bai ɗaga ba. Sai da ta kira kusan sau uku ana huɗu ya ɗaga.

“Ya akai Darling, ina duba patient ne.”

Ta numfasa dakyar tana haki da kallon kofar shigowa ɗakin ta katseshi.

“Akwai matsala Hayat! Ka zo gida yanzu. Halima Badar ce ta zo.”

“Wace haka?” Ya fadi a mamakince don har ga Allah bai ganeta ba. 

“Idan ka zo za ka ganta kuma ka tuna ko wacece. Yanzu na fi buƙatar zuwanka. Rashin zuwanka matsala ce babba garemu.” 

Har yanzun dai bai gane ba saidai tunda ya ji muryar Salmar ya san ba abu ne na wasa ba. Wannan ta sanya ya amsa mata yana zuwa kawai suka yi sallama. 

*****

Kallonta yake yana nazarin inda ya san fuskar.

‘Allah Mai iko.’ Ya furta a ransa don ya san kawai kama ce, banda haka babu abinda ya haɗa biyun balle ya ce abu ɗaya suke. 

“Yauwa ita ce Maryamar.”

Furucin Malam Haruna ya katse tunaninsa. Ya jinjina kai.

“Allah Sarki, In Sha Allah zan taimakamata. Sai dai fa inaga za ta zauna anan idan ba damuwa mu ga yanda Allah zai yi.”

“Eh toh, amman mu ai zamu koma can Ƙauye.”

Malam Haruna ya faɗi da ɗan nauyi. 

“Haba Haruna, ai an zama ɗaya. Yanda nake kallon su Hashimu kaima haka nake ganinka matsayin ɗana. Don haka ku ɗauka kun bar Maryam a gida ba a baƙon wuri ba.”

Inno da Malam suka ji dadi.

“Mun gode sosai Allah Yabar zumunci.”

“Sai dai Malam kana ganin Humaira za ta amince ta zauna wurinmu?”

Fadin Inno sa’ilin da Malam Kabiru ya mike ya shiga cikin gidan. 

Girgiza kai Malam ya yi. Ai ba zai yiwu ba, dole ne dama mu hakura da zaman Humaira a wurinmu. Nan din dai za ta zo har mu ga abinda hali ya yi. Ita ce kusan bakin Maryam yanzu tunda ita ce za ta kula da ita. Yau da gobe sai Allah, duk da muna fatan alheri, amman naka sai naka.”

Inno ta goyi bayan maganar mijinta sai dai ta ji ranta ya sosu. Ciwon rabuwa da Maryam da Humaira take ji sosai. Yanzu Allah kaɗai Yasan tsawon lokacin da zasu ɗauka ba su tare tunda dai Allah kaɗai zai ba Maryam lafiya ba wani ba. Fatan dacewa kawai suke yi. 

Bayan dawowar Malam ya miƙawa Maryam zuba ya mata alamar ta sha. Ba musu ta yi amfani da cokalin ta sha da Bismillah a zuciyarta. Ya Mata alamar ta ƙara, nan ma ƙarawar ta yi. Har sai da ta sha sau uku kafin ya karɓa ya ajiye. Malam Haruna ya mishi batun kawo Humaira. Har a zuciyarsa dama ya so hakan sai dai kar su ga kamar zai rabasu da ƴa da uwa ne. 

“Hakan ma ya yi daidai ai, babu matsala. Allah dai Ya yi mana jagora.”

Suka amsa da Amin gami da jaddada godiya. 

“Tana iya karanta hausar ajami?”

Har suna haɗa baki wurin cewa eh. Dukkansu wannan dabarar ba ta zo musu ba. Da tuni sun yi mata bayanin komai a takarda. Kai tsaye Malam Kabiru ya dauki takarda da tawada ya rubuta mata dukkan bayanan da ya kamata ta sani. Daga batun dawowarta gidansa da zama ita da Humaira da kuma aikin da zai soma yi mata na addu’a. 

Maryam ta karɓi takardar ta shiga karatu, tun ma kafin ta ƙarasa ta shiga zubar kwallah. Shikenan zata rabu da mutanen da take yiwa kallon iyayenta? Ta ɗago kai ta dubesu, Inno ma hawayen take fitarwa tana mata alama da ta yi hakuri da hannu. Gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta dubi Malam Kabiru ta gyada masa kai. 

Jikinsa ya ɗan kara sanyi da kamannin da yake ƙara gani a fuskarta. Shi dinma gyada mata kai ya yi. Ganin kamar tana so ta yi magana ne ya miƙa mata takarda da tawada kusa da ita sannan ya dubesu.

“Ina jin tana son faɗar wani abun, ga takarda nan ta rubutamuku. Bari na dauro alwala lokacin sallar la’asar ya taho.” 

Suka amsa, tunda ta soma rubutun ba ta ɗago ba har sai bayan ta kammala. 

Fuskarta faca-faca da ruwan hawaye ta miƙawa Malam takardar. Inno kukanta ya tsananta ganin wai yau mai magana ce ta koma kurmar dole. 

“Babu abinda zan ce gareku sai godiya da kuma addu’ar Allah Ya biyaku da alherinSa. Na gode sosai, kun riƙeni tamkar ku kuka haifeni hakazalika kuna iyakar kokarinku wurin yimin maganin matsalata. Sai dai ku sani, na yarda haka Allah Ya ƙaddara min na yi rayuwa na kuma ƙare rayuwata ba tare da nasan cikakken asalina ba. Ku yi hakuri ku kyaleni na zauna a wurinku har zuwa sadda Allah zai Yayemin ko mene. Na yi imanin wataran sai labari. Kar ku rabani da ku, ku nake yiwa kallon iyayena.”

Malam ya karasa karantawa a raunane, Maryam dai kuka take sosa itama. Ya daure ya juya bayan takardar ya maida mata amsa. Hakuri sosai ya bata gami da mata nuni da cewar su masu kaunarta ne, ta yi hakuri ta rungumi kaddararta da hannu bibbiyu wataran sai labari. Ba da son ransu zasu rabu da ita ba saidai hakan zai fiye mata alheri. Wato samun saukinta. 

Ta karanta ta share hawayenta tana ɗan murmushi duk domin kwantar musu da hankali.

“Kema kukan ya isa, hakuri za’a yi kada ki ƙara raunanata.” Fadin Malam Haruna. A dole Inno ta share hawayenta sai dai a ƙasan ranta  tasan za ta yi kewar Maryam sosai domin kuwa ta dauketa a matsayin ɗiyarta ta cikinta. 

*****

A gefen Malam Kabiru ba abinda ya ɓoyewa iyalinsa game da Maryam,sun tausayamata karshe suka nuna ba wani abu da zamanta tare da su.

Da wannan Inno ta zauna suka shiga cikin gidan, ɗakin su Bilkisu na baya anan Maryam ta zauna, shi kuwa Malam Haruna ya koma ya taho da Humaira da Jamila. Humaira na ganin Mamanta, ta faɗa jikinta ta yi lamo, kunya  ta hana Maryam janta zuwa jiki. Ta ƙara yin ƙasa da kanta. 

“Ah, wannan kyakkyawar ai sai ta kwace min mijin. To ba zata saɓu ba, bari na zo na yi mata bille a fuska.” Faɗin Gwaggo da wasa. Inno da da su Yaha wacce ke zama a gidan suka yi dariya. 

“A’a dai Gwaggo, ya karaya tun da wuri haka? Ai kya bari zama ya miƙa mu ga kamun ludayinta. Idan dagasken ta kwace to sai a jinjina mata.”

Nan ma dariyar ce, ganin haka Humaira ta mike zaune tana mirza idanu amma bata ce uffan ba. Bayan an ɗan yi raha, Inno ta lallaɓa Humaira ta ce nan za ta ci gaba da zama har Allah Ya ba mahaifiyarta lafiya. Ba musu ta ce toh, ta gwammace ta zauna da Mamanta anan akan ta bi su zuwa Kauyen Cinnaku ta bar Mahaifiyarta ba tare da sanin halin da take ciki ba, zaman ma ba zai mata dadi ba. Mafarkinta ya koma na samun saukin Mamarta, ya tashi daga na karatun boko don ko tunawa da shi ba ta yi.

*****

A waje ya yi parking motarsa don ba ya jin zai ɗau lokaci a gidan kasancewar yana da aiki a asibiti. Bayan sun gaisa da Joshua ya shige ciki ransa a ɓace, ji yake yau zai iya zagin Salma da ta katse mishi aiki kawai saboda wata can Halima da bai san da zamanta ba. Babu sallama ya bude kofar falon ya sa kai. 

“Salma ya akai?”

Da yake Salmar ce ke kallon saitin kofa,ita kuwa Halima tana jin muryarsa sa ta juyo gaba ɗayanta ta kasheshi da murmushi tana taunar cingam abinta. 

“Dr Hayatu Bello, rai kan ga rai?”

Ta ina zai mance fuskarnan? Bai isa ba! Nan da na zafin da ya ɗauko ya sauka ya koma fargaba da ɓacin rai. Ya ƙaraso a dake gami da zama kusa da matarsa yana duban Halima. 

“Me kuma kike nema a wurin nan? Me ya kawoki?”

Wata dariya Halima ta sheƙe da shi. 

“Wannan shi ne wata sabuwa kenan! Ai garin masoya ba ya nisa, da ba ku nemi inda nake ba ni ganinan na nema. To wai duk mene ya Kawo sauyi a fuskarku? Saboda Halima? Ban yi zaton ganin wannan razanin a saman fuskokinku ba kodayake tsoron allura ta tono garma kuke. Don ba laifi naga ɗan namu ya girma.”

Ta ƙarashe gami da ƙara duban hoton Fu’ad. Suka dubi hoton suma kamar ranar suka soma ganinsa. 

“Wai me kike so? Ki fadamin naji, ko nawa ne zan biyaki! Amman zuwanku gidannan kin sani babban hatsari ne!”

Hayat ya faɗi a harzuƙe. Ta tamke fuska ta koma a Halima Badar sak wacce suka yiwa farin sani a baya.

“Kai Hayat! Runtse ido ba makanta bane! Sannan idan maye ya manta uwar ɗa ba ta manta ba. Har Ni za ku gwadawa Bariki? Kun ɗauka na mutu ai ban rayu ba saboda kun sa yaranku sun cinnawa gidana wuta.”

Tayi wata dariya kafin ta rangwaɗa kai.

“Mugunta ita ce halina, wanda kuma ya yi nufin yinta shi ne abokina wallahi! Don haka ku sani kun taɓo tsuliyar dodo! Halima ba za ta kyaleku ba ta shigo rayuwarku kenan.”

Hayat da Salma suka dubi juna, Salma ba bakin magana sai gumi, Hayat ne ya kara yin ta maza gami da sassauta matsar da ya yiwa wuyanta da necktie. 

“Abin bai yi zafin haka ba, ki faɗa me kike so?”

Ta gyara zama sosai tana fuskantarsu. An zo inda take muradin a zo. Kallonsu take ɗaya bayan ɗaya, su kam dama kamar kwayar idanunsu za ta faɗo tsabar kallonta. 

“Abu ne mai sauki. Gida nake so dankarere nima koda kuwa bai kai wannan ba. Sannan ina bukatar kudaden da zan bude shago da su nima na dinga juyawa ko zan kama kafar Tsohuwar Matar Late Alhaji Haisam Zakariyya.”

Ta ƙarasa zancen da shaƙiyanci tana jefawa Salma wani irin kallo. 

“Ba zai yiwu ba!” Faɗin Hayat yana muzurai. Salma ta yi saurin damƙe hannunsa ta tari zancen. 

“Za ki samu, zamu ba ki matukar za ki rufamana asiri Halima.”

Ta sheƙe da dariya gami da turo ɗauri gaban goshi. 

“Haba Hayat, ya da saurin yanke hukunci? Ka manta kai ɗan karere ne ba ɗan na gada ba? Ba don shekarun da na kwashe a Saudiya ba da tuni na zo anyi ta an ƙare saboda ba uban da ya ginamin gidana a cikinku balle ku sa yaranku su ƙonemin shi. A zatonku i yanzu bana duniyar ko? To wallahi ko zan mutu sai dai ayi mutuwar kasko da ni da ku!”

“Ke Halima!” Ya mike tsaye a fusace, Salma ma ta miƙe ita  kuwa sai ta kwantar da kai jikin kujera tana dubansa tana dariya. 

“Dukana za ka yi? To Bismillah Hayat, shege ka fasa.”

“Please no.” Faɗin Salma tana rike hannunsa. Ba da son ransa ba ya koma mazauninsa. 

“Shikenan, za’a ba ki.” Ya furta yana huci. 

Ta mike tsaye bayan ta ajiye lambar wayarta. 

“Muddin bakwa so ɗanmu ya sanni kuma ya san komai daga wurina toh ya dace ku gaggauta cika alƙawari. Wallahi wallahi bani da mutunci bani da kirki! Kai Hayat ka fi kowa sani tunda tare muke a baya. Idan kuwa ku ka ce za ku nunan ku ƴan birni ne, zan nunamaku nima shegiyar ƙauye ce!”

Daga nan ta yi hanyar waje sai ta dawo baya tana murmushi da dubansu. 

“Idan ba kwa kaunar ƙara ganina a nan, kuna gudun haɗuwarmu da Fu’ad. Ku gaggauta cikamin alƙawari sai a zauna lafiya.”

Daga haka ta fita tana rausaya jiki. Hayat ya bugu tebur.

“Wai meyasa ba ki bari na kakkaryata bane?”

“Saboda ba shi ne mafita ba, ka manta me ta ce? Mutuwar kasko za’a yi muddin muka yi wani yunkurin don haka dole mu yi hakuri mu ba ta abinda ta buƙata.”

Hayat bai so ba, ko kwandala ba ya son ya ga anyi asarar ta a banza don a cewarsa Halima banza ce. Ya ja tsaki ya fi a kirga karshe ya lallaɓa ya koma bakin aiki. 

*****

Sallamarsu ce ta ɗau hankalin jama’ar dake ɗakin. 

“Oyoyo ƴan biyuna.” Cewar Yaha tana duban Amir da Amira wacce ke riƙe da Jidda. Tare suke gaba ɗaya har Hashim da ya tsaya gaisawa da Kakansa da Anti Khalisat. Mami kaɗai suka bari a gida. Tun shigowarsu Humaira ta saki baki tana kallonsu. Ƴan gayu da su tubarakAllah. Zama suka yi suna gaida Gwaggo Kubra da Yaha.  

Can kuma Shuraim da Anti Khalisat suka shigo. Zama suka yi aka gaggaisa. 

Idanun Anti Khalisat ya sauka saman na Humaira.

“Ina ku ka samo ƴar budurwa?” 

Kunya ta ɗan kama Humaira hakan yasa ta gaidata. Ta amsa fuska a dan sake. 

“Kyakkyawa kuwa sai dai ba ta kama kafar My Amira ba.” Fadin Shuraim da zolaya akai dariya. Amira ta saci kallonsa ta wurga masa harara, dama tun a hanya ya addabeta kusan kullum abu ɗaya. 

“Kai ware can! Ina da haɗi? Ai yanzu nima nayi ƴar budurwa tunda ita wannan mai baƙi kamar daddawa guduna take. Ba aro ba ɗani kuma.”

Faɗin Gwaggo tana duban Amira ta sauke maganar akan Anti Khalisat. Ai kuwa aka sanya dariya. 

“O’o Gwaggo daga ganin Sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi? Kya bari kiga kamun ludayinta ko?”

Faɗin Yaha tana dariya. 

“Ba komai Gwaggo, Ni Amira ta isheni tunda dai an hakura an barmin ita. Ba zamu yi aron wannan din ba.” Anti Khalisat ta furta tana dariya. Sun saba ƴar wasa da Gwaggo kamar ba suruka ba. Shigowar Hashim ne ya sa yaran miƙewa su fita, ganin haka Humaira ta gaida Hashim ta fice itama zuwa wurin Mamarta. 

“Wannan fa daga ina?” Hashim ya nemi ba’asi. 

Tiryan-tiryan Yaha ta shiga bata labarin abinda ta sani game da Maryam, sosai suka tausayamata. Suka yi addu’ar samun saukinta. 

“To ita yarinyar haka za ta zauna ba karatu?” Faɗin Hashim. 

“Gaskiya dai nima ban goyi bayan zamanta haka ba, kuma nasan tana zuwa makaranta a can.” Anti Khalisat ta furta. 

“Um um anya kuwa tana zuwa, don naji kafin su Innon wata yar uwarta Jamila tana kuka tana cewa shikenan ita kadai za ta soma makaranta banda Humaira, Innon na cewa tayi hakuri. Bana jin suna makaranta.” Fadin Gwaggo Kubra. Hashim ya dubi Shuraim.

“Kira ita Humairar naji.”

Shuraim ya fita tsakar gida ya kwalamata kira ta fito daga dakin ta bi bayansa. 

Durkusawa tayi tana dubansu.

“Ɗiyata, Humaira ko?”

Ta gyada kai da ɗan murmushi jin ya kirata da ɗiyarsa. 

“Wane aji kike a makarantar boko?” 

Nan da nan ta ji kwalla sun cikamata idanu. Ashe rawar kai ma wuri ya samu, gaba daya kwanakin nan tun da wannan abu ya faru ga Mamarta ta zama wata saliha. 

“Kin yi shiru Humaira, yi magana.” Fadin Yaha. 

“Bamu soma zuwa Boko ba, wannan karon Malam ya ce ya barmu muje. Sai muka zo biki Yobe sai..”

Kukan da ta soma ya hanata ƙarasawa. Anti Khalisat ta jawota jikinta tana rarrashi. 

“Ya isa haka.”

Tausayinta ya kamasu gaba daya. 

“Za ki yi karatu in Sha Allah ɗiyata. Ki kwantar da hankalinki.”

Ta gyaɗa kai ba ta ji wani dadi can ba don ba shi ne kan gaba ba yanzu a zuciyarta. Karshe ta mike ta bar su a anan suna hirarrakinsu. Da kadan kadan har suka dan saba da Amira a ranar, har wurin Maryam ta shiga ta gaisheta, Maryam ta gyada kai da yi mata alama da hannu don ta gane gaisheta take duba da yanda ta ɗan russuna da kuma motsawar leɓɓanta.

Yaha ta shigo.

“Humaira, ki ce za’a zo a gaisheta.” Ta amsa da toh. Takardun da aka bata ta jawo ta rubutawa Maryam da Hausar ajami. Ta bata, Maryam ta mike ta sanya hijabinta ta zauna. 

Ba jimawa Hashim da Anti Khalisat suka shigo da sallama. Tsayawa ya yi daga ƙofar yana kallonta, Maryam ta kauda kai ta sunkuyar.

“Muje mana.” Fadin Anti Khalisat da tsaf ta lura da kallon da yake bin Maryam da shi wanda nan da nan ta ji ranta ya sosu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 13Rumfar Kara 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×