Skip to content
Part 24 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

As a devoted Catholic – Christian ya san darajar mata, ya san menene kame kai da mutunta kai, kuma addinin sa ya hore su da zabawa ‘ya’yan su uwa tagari ba mara wadannan qualities din na sama ba. Duk irin kyawun matan kabilar BIROM wadanda tarihin – tarihi ya nuna cewa Biroms daga Ethiopia suka bullo, suka bulla Sudan, sannan Chad, kafin su dire a Niger, inda suka zauna na dan lokaci kafin su yo Hijira ta din-din-din su dawo ‘Jos Plateau’. 

Mafi yawan al’ummar kabilar Berom kiristoci ne da suka karbi addinin Christianity a hannun turawan missionaries, dukkan su mazan su da matan su Manoma ne na tun tali-tali, masu wani irin sassanyan fitinannen kyau na hakikanin bakaken mutanen Africa. Amma cikin su kaf bai taba ganin wadda ta dace da ra’ayin shi ba. 

Kakar sa ta sha nema masa aure yafi sau shurin masaki yana bata kunya. Don yace ‘yammatan Berom basu da maraba da “Tumaki” a idanun sa…..musamman adon su rankacau da baya masa kyau, he prefers everything cool in a woman. Yanzu kuma tana maganar ‘yar sarkin Kabilar Berom bakidaya wato TINA GYANG… wadda take diya ga Moses Gyang sarkin Birom na lokacin. 

Yayi rantsuwa a ransa ba zai auri ‘yar kabilar Berom ba, ba don yana underestimating matan kabilar sa ba, sai don ra’ayin kansa ne hakan to marry a foreigner/stranger. Dole yayi tunanin abin yi kafin Grandma tayi kuskuren aura masa Tina. Moses Gyang kuwa kowa a Birom ya san matsafi ne babba. Wato mahaifin ta, idan ya sake wata alaqa ta hada su sunan sa sorry domin tsaface shi zasu yi ya sani, don haka ya yi biris da umarnin Grandma na tafiya ‘Nzem Birom Festival’.

Tsakiyar Daren Ranar

Dare ya tsala, kasancewar lokacin sanyi ne, hazo ya lullube sararin samaniya, kimanin karfe biyun dare, kowa ya nitse a dakin sa a gidan Adamu Gembu, na tabbata a daidai wannan lokacin Anty da maigidan ta sun dade da yin barci. Na dubi Ahyan da ke nasa barcin a gefe na, sai na ji ina dakacen inama ban girma ba, inama kamar shi nake, babu damuwar komai a ransa sai ta ya ci ya sha yayi barci. 

Yau komai ya tabbata, mafarkai sun kare; imaginations sun zo karshe tunda na ga Hamzah Mawonmase a fili. Hamzah ya ganni shima, koda bai yimin magana ba. At least ya san da fuskar wata halitta mai kama da tawa a raye a duniya. From all indications mafarkai na nawa ne nikadai. Tunani na na cewa our hearts are jointly connected internally ba gaskiya bane, false perception ne.

Ko ba komai zan iya karar da cewa a ko’ina yau na ga mijin mafarki na, koda magana bata hada mu ba kwayar idanu na sun gama gaya masa ba yau na san shi ba, in har shi mutum ne mai saurin fahimta zai fahimci cewa ban yi farin ciki da bayyanar sa a yanzu ba. Ya zo at a wrong time! Lokacin da na na riga na fidda rai da bayyanar sa. Na riga na fuskanci reality na rayuwa ta.

Ina kuma nadamar wahalar da kaina da batawa Abba na dana yi a kan sa. Dukkan tsofaffin emotions sun farfado har sun yi yabanya fiye da baya. Saidai a kowanne dakika kalaman Anti Nasara na “ba musulmi bane” suna min yawo a kwanya suna cin galaba a kan emotions  dina.

Amma saboda Allah ta yaya hakan zata kasance? Ta ya za’a ce wannan (Perfect and handsome GentleMan) ba musulmi bane? 

Ko dai a zahiri Aunty Nasara ta fada ne domin ta samu hanyar da zata raba ni da soyayyar sa cikin sauki? Soyayyar da ke kokawa da cigaba na na neman ilmi a wancan lokacin take hunting duk wani progress dina a rayuwa. 

Idan kuma da gaske Nasara ke yi a ina ya samo sunan Hamzah Almustapha? Na yi wa kaina wadannan tambayoyin yafi sau shurin masaki, tun daga lokacin da aunty Nasara ta fadi zancen nan har zuwa inda yau ke motsi ban samu amsar ko daya ba. I’m extremely intrigued! 

Kawai sai na janyo laptop dina na kunna, na shiga neman ma’anar sunan “Mawonmase” a yanar gizo. Ina son sanin ma’anar sunan da alaqar sa da kabilar da Hamzah ya fito. 

Anan na fahimci Mawonmase sunan ‘yan kabilar Birom ne, wanda ke nufin “I PRAYED AND RECEIVED”. Kenan Hamzah dan kabilar BIROM ne? Kuma ya tabbata ba musulmin ba. Abin “Ba Kama”. Inji Hausawa.

Na soma kalubalantar kaina akan abubuwan da nake yi dinnan duk akan Hamzah suna neman zarta kima su maida hannun agogo baya, Hamzan da alamu sun gama nuna bai sanni ba ko a hanya bai taba gani na ba, yanzu kam na yarda ni kadai nake mafarkin sa shi kam bai sanni ba ko a fuska, duk wahalar nan dana sha a kan sa, nikadai nake koshin wahala ta. 

A halin yanzu na yarda na amince BA KOWANNE MAFARKI NE YAKE IYA ZAMA REALITY BA! Wani mafarkin a mafarki kawai yake karewa. Dreams are conceived, but not all dreams are born alive. Some are aborted. Others are stillborn. (Na tuno kalaman Zaynab Alkali).

Daga wannan ranar na kara ajiye mafarkaina a gefe, zan fuskanci reality. Reality din cewa bani da gami da Hamza ta ko’ina. Bayan kasancewar sa ba musulmi ba shi din bai sanni ba, ni kadai nayi shekaru ina dakon wahala ta ta soyayyar GAIBU. Wadda bakomai bace face Fantasies. Abba na ya fi ni gaskiya…..Umar shine mijin da ya dace da ni ta ko’ina. Zan maida hankali na kacokam yanzu kan fuskantar tantagaryar reality. 

Abu na farko da zan fara yi shine; Zan nemo Ya Omar inyi aure na in huta. Na tabbata kamar yadda ya fada tashi soyayyar will be enough for all of us kamar yadda yace kuma dai ba don soyayya kadai ake aure ba. Dalilai da yawa na assasa kafuwar aure ba soyaya kadai ba.

Zan iya zama da Ya Omar in haifa ma Abba jikokin da yake buri daga jikin O8mar ko don kaunar ‘yan uwantakar dake tsakanin mu. 

Daga wannan ranar na soma yaki da kaina a kan sa, bana zama ni kadai balle tunanin sa ya addabe ni. Na koma zama cikin dalibai ‘yan uwa na idan bamu da darasi. A gida kuwa in dai Anti tana gida bana yarda inyi nisa da ita kullum ina like da ita, tana ayyukan ta ina gefen ta ina taya ta hira.

Na maida tilawar Alqur’ani abokiyar debe kewa ta a dararen da barci ya kaurace min a kan tunanin sa. Goshi na ya zama kullum cikin sujjadar sallahr Tuhajjud don neman dacewa, tare da addu’ar Allah ya raba ni da komai daya shafe shi. Har ila yau, ina addu’ar duk inda Omar yake Allah ya karkato da hankalin sa gida haka. It’s exactly four years (Shekaru hudu kenan cif da tafiyar Omar a dalilin bakin ciki na) wadda ta zo ta kuma wuce (like a blink of an eye) wato kamar kiftawar ido.

Nasara Alkali (My Second  Lifestyle Influencer-2)

Duk wasu experiments data dora Siyama a kan su bayan ganin data yi wa Hamzah ta yarda Siyama bata fadi ko daya ba!

Ta dauka Siyama zata karyata ta, domin ba kowa ke yarda da cewa Hamzah ba musulmi bane, ta dauka Siyama zata bi soyayyar zuciyar ta kamar baya, sai ta ga sabanin hakan. Ta dauka Siyama zata gigice fiye da kima bayan ganin sa a zahiri kamar yadda mata ke gigicewa a kan sa, sai ta ga sabanin hakan. Wannan ya tabbatar mata Siyama ta karbi gaskiyar da ta nuna mata. Amma tabbas da ta samu sabanin hakan ta yanke shawarar mayar da Siyama gaban Ummati, kada wani abu ya faru a zo ayi kuka da ita.

Abinda bata sani ba take kuma son sani a halin yanzu shine infatuation din da ke zuciyar ‘yar tata Siyama a kan Hamzah Mawonmase yana nan har yanzu ko kuwa lafawa yayi? Ko kuwa ya bar ta kwatakwata bakidaya kamar sanda take New York? So far, ko sau daya dai Siyama bata yi mata zancen Hamzah ba, ko da kiwa da tuntuben harshe ne, bayan ganin data yi masa. Wannan yasa ta tunanin cewa SIYAMA TA CINYE JARRABAWAR TA.

A New Voa Intern

An debi watanni biyar da faruwar wannan encounter, wadda ta karkare komai daga zuciya ta na samu lafiya, yanzu kam komai na tafiya min daidai, Al’qur’ani maganin kowacce irin damuwa ne, na ci galaba da zuciya ta a kan sa. Wadda na alaqanta nasara ta da rungumar Alqur’ani kamar a can baya. Lafiya nake zaune da zuciya ta, ina kuma cigaba da fafutukar karatun digiri na a Jami’a.

A karshen wannan zangon karatun da muka kammala year two, wato saura shekara daya mu hada B. Sc din mu a Journalism, hukumar jami’ar George Washington University, ta fiddo da tsarin tafiyar daliban ta masu nazarin aikin jarida internships wato koyon aikin jarida a aikace a manyan gidajen radiyo da talbijin na gwamnatin kasar Amurka. Ya akayi-ya akayi, na tsinci suna na a cikin wadanda zasu yi nasu internship din a VOA.

Kwatakwata na manta da Hamzah Mawonmase balle abinda ya shafe shi. Ina kyautata zaton na gama galaba da zuciya ta a kan sa, na gina sabuwar rayuwa mai ma’ana wadda babu komai a cikin ta sai neman cigaban ilmi na da jajircewa don ganin na fidda class din degree mai nagarta wanda zai bani damar yin aikin da zan dogara da kaina idan na koma kasar haihuwa ta, Najeriya.

A gajiye matuka na dawo gida yau nake gayawa Aunty cewa gobe tare zamu tafi wajen aikin ta zan yi reporting, can wajen su aka tura ni yin internship dina, Aunty ta yi farin ciki sosai, don yanzu bata da damuwa a kaina, ta ja kunne na a kan in tsaya akan abinda ya kaini, in maida hankali in fidda kwali mai nagarta. Kullum tare muke tafiya gidan radio na VOA da Anti, amma ba tare muke dawowa ba. Taxi nake biyowa in dawo gida kasancewar Anti wataran har aikin kwana take yi.

An kai ni karkashin ‘political department’ wato bangaren dake kula da shirye – shirye na watsa labarun siyasa, a matsayin reporter, office din da aka kaini nikadai ce bahaushiya kuma musulma a cikin dalibai ‘yan uwa na da muke koyon aiki tare da su, shiyasa sau da dama in bani da aiki ko wani muhimmin abu a gaba na bana maida hankali a kan hirar abokan karatu na, sai in sa earpiece a kunne na ina sauraron karatun Al’qur’ani daga cikin waya ta wanda shine abokin rayuwata a yanzu. Sosai nake lakantar duk abinda ake koyar dani amma naki sakin jiki na ko kadan yadda ya kamata a gidan rediyon VOA. 

A kullum a darare nake, cikin fargaba da zullumi. Kullum rokon Allah nake kada yasa in kara ganin Hamzah ko daga nesa ne, kada Allah ya kara hada fuskokin mu, domin rashin ganin sa sauki ne kuma waraka mai yawa a gare ni. Sai na gan shi ko naji muryar sa infatuation dina a kan sa ke dawowa baya. 

Kwana biyu Anti bata gari sun tafi wani gari wai shi Atlanta on official assignment, wanda zai dauke su tsayin sati guda, don haka Anti ta dauki Nanny wadda zata taya ni kula da Ahyan kullum ya dawo makaranta kafin in dawo, kasancewar yana riga ni dawowa don ni ina kaiwa karfe hudu kullum. Young Abba yana Florida shima bansan dai abinda ya kai shi ba. Daga ni sai Ahyan sai Nanny Clara a gidan namu. 

Karfe hudu daidai na hada komatsaina wato jakar computer laptop, wayata da sauran tarkacen abubuwan amfani na duk, na hada su cikin jakar na rataya ta a baya na don barin office, ganin hadari yana gangamowa gashi da kaina zan koma gida a taxi, ina sanye da doguwar riga Abayat kirar Damman na yi rolling da mayafin ta akai na, da sauri na yiwa Gloria da Esha da muke office daya sallama na kama hanyar barin ofis din mu.

Sanda na fito waje har yayyafi ya soma sauka yaf -yaf a saman ginin wajen, don haka na kara sauri don shiga lifter da zata sauke ni zuwa kasa, inda daga nan zan taka in samu in isa Bus Stop na Federal Building, inda nake hawa mota zuwa gida kullum. 

Ina shiga lifter din na danna G, wato floor na karshe, lifter ta kulle ta soma gangarowa kasa da ni, sai kuma ta dakata a hawa na goma alamar an tsayar da ita a wani floor din, kafin mu kai ga isa kasa. Kofar ta bude. Mutumin da ya danna tsayawar lifter din ya shigo ciki. Kaina a sunkuye yake, kuma na juya baya na daga fuskantar kofa but i felt his presence again all over me, sannan gaba na ya mulmula ya doka, ya dungura ya wani irin fadi da karfin gaske duk a lokaci guda. 

Mu biyu ne kacal a cikin lifter din ta soma gangarawa damu kasa. Dagowar da nayi, tayi daidai da juyowar shi, muka kuma hada ido, Hamzah ne. 

Mugun kallo mai hade da muguwar harara na sakar masa kafin na yi dogon tsaki na soma kokarin fita daga lifter din, domin lifter ta iso kasa wato inda zan sauka.

To amma? Sai ya ki matsawa ya bani hanya in wuce, sannan shi bai fita ba, kamshin turaren sa Sauvage ya kara birkita nutsuwa ta. Ya ki matsawa ne da gangan. Dalilin tsakin da aka yi masa yake son sani, a matsayin sa na dan jarida mai neman ba’asin komai. Hannu biyu yasa ya rike kugu. Ya babbake hanyar wucewa.

“Hey Ma’am, please are you hissing at me? 

Idan zan iya tunawa this is not the first time, ranar dana fara ganin ki tare da Field Reporter dina Nasara Alkali, kin min irin wannan kallon, kin min irin wannan hiss din (tsakin), a kan wane dalili baki sanni ba ban san ki ba? This is insurbordination saboda ina sama da ke.

Sai dai idan kina da hujjar kin sanni a wani waje, kuma na taba yi miki wani babban laifi! Amma haka siddan?”

Kafin in samu abin fadi lifter ta kara kwasar mu ta kara yin sama damu, ta shilla zuwa can sama, domin ta bamu mintunan data ke bayarwa automatically don mu fita bamu fitan ba, Hamzah ya bi ya babbake kofar har wani daga can sama ya danna kiran liftar. Ta kuwa sake kwasar mu tayi can sama damu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 23Sakacin Waye 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×