Skip to content
Part 30 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Yau din ta kasance Asabar, ni da Aunty duk muna gida bazamu je office ba, muna kitchen ne kowa da abinda take yi a cikin kitchen din, ni wanke wanke nake yi Aunty kuma yanke-yanken ganyen ‘Ugu Leaf’ da zamuyi miya da shi take yi a kan island din kicin din. Muna yi muna hira. A haka Young Abba ya shigo ya tadda mu, cikin shirin fita, yana sanya links din hannun rigar shi. Suka yi magana da matar sa har zai fita sai kuma ya tsaya ya dube ni yace.

“Am Siyam, kina da bako yau, kiyi kokari ki yi masa abinci da hannun ki.

Hamzah zai zo officially domin ku fahimci juna.

Maganar ta wuce kai tsaye ne daga kunnuwa zuwa cikin brain dina. Wallahi tun daga babbar yatsar kafata har cikin kwakwlwata sai da naji wani irin shock, gudun jini ya dakata na dan lokaci a cikin jiki na. 

Na dakata da wanke kofin dana ke yi ba tare da na juyo ba ko na amsawa Young Abba. Ya ce “Siyama bata ji na ne?” A sanyaye nace “ina ji Abba” yace “yawwa, to ayi masa girki mai kyau”. Da haka yasa kai ya fice. Ya bar mu ni da Aunty bayan yayi mata sallama.

“Me ya kamata a girka masa? Don yace anan zai ci abincin dare” Aunty Nasara ta tambaye ni, na yarfar da kai nace “ban sani ba Anty” na bata amsar ne cikin jin mutuwar jiki na dada mamaye ni. Ni me na sani a kan Hamzah banda infatuations? Ban san komai da ya shafi rayuwar sa ba. Balle a zo ga batun sanin kalar abincin da yake so.

Kamar anty ta san abinda nake tunani sai tace “wannan dama ce kuke da ita ta sanin duka abinda kuke son sani a kan junan ku kafin aure. Don haka yin shiru ba naki bane. Kiyi kokari ki san duka (likes and dislikes) din sa kafin ki shiga gidan sa. Don kada ku zo kuna samun sabani a kan kananan abubuwa.

Ki san irin abincin da yafi so, kalar da yafi so, me yake burge shi me yake bata masa rai da sauran su.”

“Umh” kawai nace da aunty because I’m speechless a wannnan lokacin. Sai yanzu da maganar aure ta soma tashi gadan – gadan na fara raina kai na, na kuma fara jin tsoro na mamaya ta, 

“Shin ya iyayen sa da dangin sa zasu karbe ni? Na soma hango kaina tsakiyar kiristoci ‘yan addinin Almasihu a matsayin surukai na.”

Wani matsanancin tsoro mai hade da fargba mai yawa suka kama ni, na kuma shiga taraddadin yadda nawa Abban da tawa Ummatin zasu karbi al’amarin. Suna daya da bazan jure wani ya kira Hamzah da shi ba shine a ce masa ‘tubabbe’. 

Aunty ta gaya min watanni uku masu zuwa zamu tafi gida a daura mana aure ni da mijin da na zabawa rayuwa ta, don bai kamata in ce kaddara ce ta zaba min Hamzah ba. Kaddara kanta suna ta tara. Abinda zuciyata ke so ne Allah ya bani tunda “Al mar’u ma’a man ahabba” ko ko ince addu’ar da nake yi kullum ta Allah ya bani mijin mafarki na ce Allah sami’uddu’a’I ya amsa. Lokacin zai yi daidai da na gama internship dina, da mun dawo zan koma makaranta in karasa ragowar shekara daya na in karbe kwalin digiri na.

Daga ni har Aunty mun yanke shawarar mu yi masa tuwon Acca da miyar ganyen Ugu da Anty tagama gyarawa yanzu, sai muyi amfani da manja da naman rago da kifi busashshe a ciki. A gefe zamu gasa fresh/danyen kifi Tilapia wato (grilled Tilapia) irin local grilling ba gashin inji ba. Sai kuma farfesun bindin Sa. Ta fannin abin sha Aunty ta zabi kunun zaki na gero nikuma na zabi tataccen zobo drink nace a saka mishi fresh abarba a ciki maimakon sugar.

Kafin magriba mun gama komai mun adana, Aunty tace inje in yi wanka zata yimin kwalliya ne da kan ta.

Kamar zan yi kuka nace “Aunty kwalliya kuma? Ni fa hijabi zan saka. Mutumin nan bai gama koyon addini ba tukunna da sauran sa. Abu kadan ya nemi kama hannun mutum” Aunty tace “addinin ya bashin damar ya ganki yau babu Hijabi”. Sai na ja baki na nayi shiru.

Dana fito daga wanka Aunty na taras tana jira na a gefen gado na da dan ‘make up kit’ din ta a gefe da kayan data dinka min. Sai ta bani dariya sai ka rantse wata ‘make up artist’ ce aka dauko take jiran amarya ta fito daga wanka. “Ki yi dariya da kyau, kwanannan zata koma kuka yarinya, ranar da zaki bar Anty Nasara ki koma gidan Hamzahn VOA.”

Ai kuwa sai na soma hango ranar. Tuni na bare baki na soma kuka kamar yau ne ranar, ina cewa “Aunty ni fa ba auren da zaku yi min wallahi ba auren sa nake so ba, dama so nake ya musulunta kuma ya musulunta” kuka sosai wanda ya baiwa aunty matukar dariya tayi har ta ishe ta. Sai ta koma wakar.

“Ka ji min fulako irin na fulben Mambillah. Yarinya Ke kika ce kina so, har da shan fiya-fiya, da baki ce kina so ba da bamu baki shi ba.”

Kuka na ya karu, kuka sosai nake yi don ji nayi kamar Aunty zagi na take yi.

Da kyar ta samu na yi shiru na goge ido na. Na yarda suna da damar fadin komai a kaina idan inada tsinkaye. Wa ya aike ni shan fiya-fiyar in the first instance? Certainly ina nadama. In dai Hamzah ne da na yi hakuri ba abinda zai canza kaddarar mu. Hausawa suka ce matar mutum kabarin sa.

Sannan ta taimakamin na saka sabon lace ruwan makuba mai kwalliyar orange roses a jikin sa, ta tsane hawayen da suka bata min fuska kafin ta soma tsantsara min wani serene light make up.

Bamu kai ga kammalawa ba Ahyan ya shigo da gudun sa, yana gaya mana Daddy da Uncle Tall sun zo, Daddy yace Anty Siyama ta zo Uncle Tall yana kiran ta.”

Bansan meyasa hankali na ya dugunzuma ba, ji na yi kamar yau ne za’a kai ni gidan Hamzan a irin kwalliyar da Aumty ta yi min. Rabo na da saka Hamzah a ido an doshi watanni biyu, ko a office baya zuwa department din mu. Sau daya na hango shi zai shiga mota na yi maza na labe sai da ya bar wurin na fito na wuce gida.

Yau ga Hamzah Mawonmase ya zo gidan mu da sunan zance irin na neman auren saurayi da budurwa, a matsayin cikakken musulmi mai rangwamen zunubai tunda an ce wanda ya shiga musulunci tamkar jariri sabon haihuwa yake komawa kuma daga lokacin ne littafin zunuban sa zai fara. 

Bansan meyasa jiki na ya soma vibrating ba. Na kasa fita na kasa koda motsi bayan wucewar Anty, da cewa da ta yi in same shi falon Young Abba.

Tsahon mintuna ashirin ina zaune na yi tagumi, ni ban fita ba ni ban mike ba, ko ruwa ban kai masa ba. Damuwar duniya ta yimin lullubi idan na tuna Abba da Ummati. Shin zasu karbi Hamzah idan suka ji asalin sa da kuma background din sa?

Ko dai in roki Young abba akan ya boye? A je a zuwan na samu mijin kawai ba sai an gaya musu tubabbe bane? Tunaninnikan da suka hana ni sukuni kenan. Suka hana ni tabuka abinda ya dace na zauna ina ta saka da tufka da warwara. Auren da duk aka gina shi bisa karya to tubulin toka ne. Ina wannan tufkar Sai maganar Young Abba naji daga bakin kofa yana fadin “wane irin rashin hankali ne wannan Siyama? 

Kin bar mutum tsahon awa guda yana ta jiran ki, kina nan kina tunanin banza da wofi? Salon wulakanci ne ko wani ya kawo shi ba ke ba? Ko wani yayi miki dole a kan sa?”

Da sauri na mike jiki na yana rawa jin abinda Young Abba ke fadi na san na matukar kai shi bango.

Zan wuce ta gaban su Aunty tace “baki dauko abincin ba” kafafuna na rawa na juya zuwa kicin na kinkimo tray din data shirya abincin akai na sake wucewa ta gaban su. Aunty ta bi ni da kallo tana fadin “yi a hankali kada ki zubda, sai kace yau kika fara ganin Hamzan, wannan rawar jiki haka duk na menene?”

Yana tsaye harde da hannayen shi a faffadan kirjin shi, a tsakiyar falon bakin Young Abba yana kallon wani katon hoto ‘window size’ namu na iyalan gidan mu hudu, Anty ce kawai baka a cikin mu amma fa kowa yayi kyau. Kamar ya sanya hannu ya ciro Siyama daga cikin su ya jefa a aljihu ya wuce da ita gidan sa. 

Sai ya ji motsin ana taba kofa. Ya juyo gabagadi yana kallo na ina shigowa da tray a hannu.  Karasowa yayi ya karba ya aje a gefe, yana fadin “ni ban zo don inci abinci ba, na zo ganin mata ta ne, amma ta shanya ni sabida rashin iya kula da hakkin miji”. Wata irin kunya ta kama ni na ja gefen gyale na na rufe rabin fuska ta, gabadaya ya zame min sabon mutum. Haiba da kamala na hasken muslunci sun lullube shi sun ratsa shi, sun fiddo zahirin ilhama da cikar zatin sa.

Maimakon in zauna a kan kujerar da yake zaune ko wadda ke fuskantar sa, sai na zame na zauna bisa kilishin tsakiyar dakin, har yanzu ban iya na bude fuska ta daga lullubin dana yi mata ba.

Tasowar sa da isowar sa gabana duka ban sani ba domin kaina a sunkuye yake, sai kamshin atmosphere din dana ke shaqa da naji ta canza zuwa kamshin Guarlain Vetiver, mai nuna cewa hatta turaren da yake amfani da shi a baya wato Sauvage ya canza shi da Guarlain Vetiver yanzu. (Entirely Islamist).

A jiya na ga dogon rubutun da yayi a shafin sa na Twitter dana Instagram wanda ya kira taken sa “A TRANSITION FROM DARKNESS TO LIGHT wato (Canji Daga Duhu zuwa Haske)”. A twitter kuma  yace  “How I escaped from Ignorance”. 

Bai fito fili ya fadawa masoyan sa da duniya bakidaya cewa ya musulunta ba, don a ganin sa wannan din (is a private affair), amma idan kana karanta rubutun da abinda ya kunsa mai dumama zuciya, ka kuma san Hamzah Almustapha in reality a matsayin sa na Christian dole ka fahimci ya musulunta, kuma kalaman da yayi amfani da su, su jefa ka cikin shaukin son jin komai da ya shafe shi, in kai mai raguwar zuciya ne su fiddo hawaye daga idanuwan ka. Musamman inda yake cewa bai san ya dade cikin bata ba a wata sadara da yake cewa;

“I stayed in sheer ignorance until the day I met HER. Ours is extraordinarily unique and special. It’s pure and passionate LOVE from ALLAH SWA that has no comparison with every love-story in the world, which is destined to be my way of escape from darkness to absolute light. 

I chose HER to be mother of my children, mother of my happiness…… The damsel “S.” I truly love HER!”

(Na kasance cikin tsagwaron jahilci har sai ranar da na gamu da ITA. Namu daban yake kuma wanda babu irin sa sannan na musamman. Tsarkakkiyar soyayyah ce daga Allah SWA da bazai kwatantu da kowanne labarin soyayya a duniya ba, wanda ya zame min hanyar tsira (kubuta) daga duhu zuwa haske mai tsanani, na zabe ta ta zama uwar ‘ya’ya na, uwar farin ciki na…. ZINARIYA “S” ina kaunar ta)”.

Yanzun ma da yake durkushe a gaba na kalaman da ya sake maimaitawa kenan kamar a lokacin yake rubuta su. Wadanda suka ciko hawaye taf! Daga idanuwa na, ban takura su ba na basu damar zubowa don na samu sa’idar zallar tausayi da SO da suka yi min katutu. 

Na dago a hankali na dube shi. Yana nan a yadda na san shi, nake imagining din sa cikin mafarki da ido biyu; bakin dan Najeriya, mai tsayin da har ya rankwafa daga tsayayyun kafadun sa, mai cikar zati da kykkyawar suffa, mai yawan gargasa a saman giran idon sa da zagayen fuskar sa (man’s pride). Kallon sa kawai nake ina hawaye because today THE DREAMS ARE ABOUT TO BE BORN ALIVE. Na yi alkawarin duk wani challenge da zai biyo baya daga iyayen mu zan jure. Hamzah is now a fresh Muslim kamar kowa wanda yafi mu rangwamen zunubi. Da shi da wanda aka haifa cikin musulunci basu da maraba. 

Hannu yasa a aljihun sa ya dauko hankicin sa ya miko min “zan so in goge miki su da kai na, in gaya miki ‘how much I love you’ a kan kirjin nan nawa. Amma nafi so in yi hakan a lokaci mafi dacewa, wato lokacin da addini zai bani damar sanyaki cikin jiki na in sumbace ki ta ko’ina son rai na, ba tare dana yi laifi a gun Ubangiji ba.”

Na dukunkune kai na cikin cinyoyi na ina fatan kasar ta tsage in shige. Hamzah bai dubi halin da ya jefa ni ba ya cigaba da fadin “Siyam, yau nazo ne gare ki da kokon barar neman hannayen ki zuwa cikin rayuwar aure. Zan samu hannayen ki cikin nawa Siyam?”

Kukan ne ya kwace min, kuka sosai, ganin idanun sa sun ciko da hawaye muryar sa tana rawa a lokacin da yake wannan furucin. Tsoron sa Allah tsoron sa kada in ce masa a’ah. Idan nace a’ah din, hakika na yi wa Allah butulci kuma ban cika ladan dana fara samu ba, duk da a halin yanzu zuciyata tafi karkata ga son in komawa dan uwa na Omar, don in samu shiryawa da mahaifi na ba don soyayya ba. 

A shekarun hudun nan nayi missing soyayyar Abba na data Aunty Wasila yadda harshe bazai iya bayyanawa ba, biro ba zai iya rubutawa ba, amma hakan zai karya zuciyar Hamzah ya ga cewa kamar na yaudare shi. Allah ya gani na dade da hakura da abinda zuciyata ta afu gare shi, kuma buri na shine Hamzah ya tsira daga azabar wuta koda ban aure shi ba.

Kamar ya san abinda nake sakawa ina kwancewa a zuciyata cikin in’inar sa ya ce “in kika canza min wadannan MAFARKAN baki yi min adalci ba. Bar min su Siyam in maida su REALITY in a unique special way. Su cigaba da gudana a rayuwar mu ta zahiri yadda ubangiji ya tsara mana su. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 29Sakacin Waye? 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×