Skip to content
Part 46 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ta kai ta kawo yau Hamzah ya sha da kyau ta kai masa karo irin yadda ya kamata, ya yi min gori Aunty, gori irin wanda ban taba zato ba, ya fadi duk abinda ke zuciyar sa a kaina wanda ban taba sanin yana kallo na da su ba”.

Don haka ki zo yanzu ki dauke ni ba sai gari ya waye ba, in ba haka ba na rantse a daren nan zan kama hanyar Mambillah, ko a kan iska ne zan yi fiffike in koma gaban Abba na.”

“Innalilahi wa’inna ilaihi rajioun” in ji Anty, damuwa da tashin hankali karara a cikin  muryar ta tace, “Siyama kada kiyi saurin yanke hukunci a kan zargi, don kin ga kwalaben giya a motar sa baya nufin sha yake yi, don ya fita ya dawo yayi barci baya nufin ‘Bar’ ya je ya sha giya, zai iya yiyuwa wani nasa ne ya ajiye kwalaben a motar sa din, sannan ki dinga bashi hakkin sa na aure don ya debe kunya ya zo har gida gaya min in miki magana ko ni za ki gaya mun, bai san laifin da yayi miki ba yanzu gudun sa kike yi, alhalin kuna kwana a gado daya kuma bashi da wata matar sannan ya yi alkawarin ba zai yi zina ba, ya gaya min he’s about to get depression akan abinda kike masa, tunda har bai ce ya koma christianity ba, baki da hujjar cewa musuluncin sa bai yi ba, ko ya bar musuluncin.

Sallah abu ce mai nauyi ga wadanda ba musulmi ba, haka wankan janaba da azumi yana basu wuya, musamman wadanda basu girma cikin ta ba, ko a musulmi in kin duba akwai masu wasa da sallah, don haka bear with him fushi irin wannan na farat daya ba shi da amfani don yana iya kaiwa ga mutuwar auren da za’a zo ana nadama, kiyi ta maimaita innalillahi wa’inna ilaihi raji’oun zaki samu nutsuwa.

Zaki iya nuna masa kuskuren sa da bacin ran ki ba tare da kin bar dakin auren ki ba, wallahi maza irin Hamzah masu rauni a kan soyayyah sun fi ruwan sha saukin sha.

Da lallashi da nuna kauna hadi da addu’a, da tuna masa irin azabar da Allah yayi tanadi ga masu wasa da farillah zamu shawo kan sa ba ta hanyar da kika bullo masa ba.

Ko hakkin sa bakya ba shi yanzu, wai kina fushi baya sallah, kabarin ku daya? Ta yaya kike tunanin zai biyu miki ta sauki yayi abinda ya dace alhalin bashi da nutsuwa a tare da ke? A wane dalilin zaki yanke wannan hukuncin bayan ya biya sadakin ki?”

Aunty ta koma fada, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, ko don ba duka kalaman Hamzah na iya gaya mata bane???

Cikin kuka nace “Aunty ban sani bane ko yayi RIDDAH kuma, don ni dai bana ganin yana sallah yanzu sam, sannan kada ki manta har gobe Abba bai amince da auren nan ba fa har yanzu, ta ina zan ga kwanciyar hankali? 

A gorin sa fa har cewa yayi na zabe shi a kan Abba na, ban san martabar iyaye na ba, sauran maganganun suna da nauyi bazan iya gaya miki su ba”, na cigaba da share hawaye na na ce “don haka Aunty ki barni in dawo gida, zan nuna masa na fi son Abba a kan sa yadda yake tunani ba haka bane, a wancan lokacin har da tarin kuruciya darashin wadatar ilmin addini a tattare da ni, na rantse gida zan koma in gyara baya na”.

Na cigaba da kuka.

Aunty ta yi murmushin manya kafin ta ce “kin makara Siyama, it’s too late. Ki manta da bayan, ki yi kokarin gyara gaban ki kawai, kuma ni na ji dadi ba dan kadan ba da yau Hamzah ya koya miki hankali.

A hakan kuma zaki daure ki lallaba abinki ku cigaba da hakuri da juna, wannan itace manufar kalmar hakuri da na bata lokaci ina jaddada miki ranar tahowar ki, cewa ko ba dade ko bajima sai kin ga abinda ba kya so a auren Hamzah ba kuma fata na yi miki ba, a’ah sunnah ce ta rayuwar dan adam wato zo mu zauna zo mu saba” nace.

“Aunty na rantse na gama (making mind) dina, gun Abba zan koma, ko sau daya Abba bai taba kira na a waya ba tun zuwa na U.S, ni in na kira baya dagawa, idan na tura masa sako baya bani amsa, aunty hankali na ya koma ga mahaifi na ina nadamar auren nan tun ba’a je ko’ina ba,  na yi nadama!

Watakila hakkin Abba ne ya hana ni samun kwanciyar hankalin dana ke tunanin zan samu a auren Hamzah”.

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel. Siyama bar fadar haka, ba’a nadama da aikin jihadi, ba’a nadama da bautar Allah, aure bautar Ubangiji ne, haka ba’a nadama da aikin alheri. Kuma duka kin aikata su.

Don haka daure ki jure ki jajirce ki cigaba da jihadin ki, ki nuna masa a hankali cikin soyayya da lallashi, ba da tursasawa ko nuna bacin rai ba. Ko ki yi amfani da hakan wajen hana shi abinda yake halalin sa ba.

Allah ya shaida Hamzah ya aure ki, don haka auren da ke tsakanin ku shine abin tambaya a gare ki wajen Ubangiji, ba yadda Hamzah ya tafiyar da addinin sa ba, wannan tsakanin bawa da Ubangijin sa ne, ke naki kawai tunasarwa ne ba punishment ba.

Abba kuma da yardar Allah zai sakko, wuyar ta ya gan ki a gaban sa, ki tabbatar ya saka muku lokacin zuwa wajen sa hakannan anan kusa”.

Ta aje wayar ta ba tare da mun yi sallama ba saboda naki daina kukan dana ke yi mata

Idan na so in yi amfani da shawarar Anti, na kuma tuna irin bakaken maganganun da Hamza ya gaggasa min, duk da cewa a cikin maye ne amma he sounds serious, kamar wata kalmar so bata taba hada mu ba, kamar bai taba tausaya min ba, sai in ji bazan iya cigaba da zaman ba gara in sato passport dina daga dakin sa, in yi kudin jirgi in tafi kawai, tunda inada kudin da zasu iya sai min tikiti. Ire-iren kudaden da yake bani don in yi shopping idan muka je Miami a lokutan da yanzu nake tunanin ni da sake samun irin su saidai ko in sake ganin su cikin mafarki na.

Saboda ban ga alamar Aunty zata yi komai a kai ba, cewa ma take in rarrashe shi, bana jin zata gayawa Young Abba ma ko don ya dau wani mataki. Bata yi la’akari da cewa Hamzah ya ci mutunci na fiye da kima ta cikin ruwan sanyi ta hanyar da ban taba zata ba.

Amma kuma hakan da ya yi min, ta wani bangaren ya taimake ni, domin ya sa na farka daga magagin dana ke ciki na ciwon nakasar kwakwalwa da mutuwar zuciya a kan tabbatuwar burika da mafarkai cikin rayuwar mutum, da tunani na  cewa zan dauwama cikin dadin mafarkai na da rayuwar soyayyar da nake mafarki wadda hakika na same ta daga baya, na yarda duk abunda Hamzah ya fada din gaskiya ne; ni “wawuya” ce. Wato wadda bata san ciwon kan ta ba.

A yau na tabbata mutum mai kama GAIBU ta saki kyakkyawan REALITY din da ke hannun ta. Sabida wau hujjoji na marassa madafa ta kwadayin auren bakin hadadden namiji wanda yayi daidai da zabi na. YA OMAR is an example of my beautiful REALITY wanda na saki na kama GAIBU; ma’ana na san shi, ya sanni na kuma san komai nasa; asalin sa, tarbiyyar sa, addinin sa da nasabar sa irin tawa, amma na rufe ido na badawa ido na toka na gujewa auren sa helter-skelter, sabida son zuciya da rashin sanin ciwon kai da sanin martabar iyaye.

Yayin da duk wasu hasashe na akan HAMZAH  na cewa ni Siyama zan iya canza shi zuwa yadda nake so ya kasance ya zama cewa na yi amfani da GAIBU. Kuma gaibun ta nuna min har abada gaibu-gaibu ce, na yarda na aikata babban kuskure ga mahaifi na wanda ba zan iya gyarawa ba

Ya yi min zabin da bazan taba kokawa da komai a rayuwar aure da ma rayuwar duniya bakidayanta ba, na yi fito na fito da shi nace a’ah Abba bai iya ba, yace min ya fi ni sanin ciwo na fiye da kowa nace a’ah na fi kowa sanin ciwon kai na, da abinda zai amfani rayuwa ta, nace masa ni na fi kowa iya mafarkin soyayyah kuma mafarki na shi zai jagoranci ragamar rayuwata.

Na manta cewa Zaynab Alkali kan ce “DREAMS ARE CONCEIVED, BUT NOT ALL DREAMS ARE BORN ALIVE. SOME ARE ABORTED, OTHERS ARE STILLBORN”.

(Wato MAFARKAI kamar ‘ya’ya suke, ana yin cikin su amma ba duka ake nasarar haife su da rai ba. Wasu tun suna ciki suke zubewa, wasu mafarkan kuwa a mace ake haifar su).

Na tuna gwabjewar da Hamzah yayi min, ya kuma ambace ni da dukkan kurakuraina, duk da yana cikin halin maye ya fi ni sanin abinda ya kamata, ni da nake cikin hankali na ban sha abinda zai gusar da hankali na ban taba zama na yi tunanin hakan ba wato ban kyautawa rayuwata da iyaye na ba, Abba shine a kan daidai ba ni ba, don haka yau na samu amsar tambayar da ke cikin labari na SAKACIN BA NA KOWA BANE NAWA NE NI AISHA-SIYAMA, da na bari mafarkai da burika suka yi ta sarrafa zuciya ta, aspirations da derives dina.

Kuka nake yi sosai, wani irin kuka na nadama da da na sani, duk da rashin daukar wani mataki da Aunty Nasara tayi akan abinda Hamzah ya yi min, na san gara ita sau dubu a kan Young Abban in dai a kan Hamzah Mawonmase ne. Besides, dana auna wasu abubuwan data fada sai na ga a kan hanya suke, men can do anything out of sex denial daga matar da suke so, don haka na shiga hakurkurtar da zuciya ta ina share hawaye na, na ce bari in rage fushin nawa da Hamzah, in gwada shawarwarin Anty, afterall ko me yayi min bazan daina son sa ba, tunda shi bai ma san a kan me nake fushin da shi ba, ya san dai fushi na ke da shi, (and he admit it). Sai ya kama kan sa daga shiga sha’ani na, don baya son raini, ban taba buda baki na gaya masa akan me nake fushi da shi ba, don kada ya ce na sakawa rayuwar sa da ibadar sa ido.

Na tuna gwabjewar da Hamzah yayi min, ya kuma ambace ni da dukkan kurakuraina, duk da yana cikin halin maye ya fi ni sanin abinda ya kamata, ni da nake cikin hankali na ban sha abinda zai gusar da hankali na ban taba zama na yi tunanin hakan ba wato ban kyautawa rayuwata da iyaye na ba, Abba shine a kan daidai ba ni ba, don haka yau na samu amsar tambayar da ke cikin labari na SAKACIN BA NA KOWA BANE NAWA NE NI AISHA-SIYAMA, da na bari mafarkai da burika suka yi ta sarrafa zuciya ta, aspirations da derives dina.

Kuka nake yi sosai, wani irin kuka na nadama da da na sani, duk da rashin daukar wani mataki da Aunty Nasara tayi akan abinda Hamzah ya yi min, na san gara ita sau dubu a kan Young Abban in dai a kan Hamzah Mawonmase ne. Besides, dana auna wasu abubuwan data fada sai na ga a kan hanya suke, men can do anything out of sex denial daga matar da suke so, don haka na shiga hakurkurtar da zuciya ta ina share hawaye na, na ce bari in rage fushin nawa da Hamzah, in gwada shawarwarin Anty, afterall ko me yayi min bazan daina son sa ba, tunda shi bai ma san a kan me nake fushin da shi ba, ya san dai fushi na ke da shi, (and he admit it). Sai ya kama kan sa daga shiga sha’ani na, don baya son raini, ban taba buda baki na gaya masa akan me nake fushi da shi ba, don kada ya ce na sakawa rayuwar sa da ibadar sa ido.

Ko dazun da a ce ban shiga sabgarsa ba bazai shiga tawa ba, ya bani dama ne in yi ta fushi na har zuwa ranar da jaki zai yi kaho, shikuma ya yi amfani da damar ya yi ta shan giyar saw adda shirin da muke yi yasa yake boyewa, tunda na fita sabgar sa sai ya koma shan abarsa da lasisi, tunda yayi iya lallashin da zai iya ya gaji ban ce ga laifin da yayi min ba.

Sai ya kama kan sa daga shiga sha’ani na don kada ya sayowa kan sa raini. Ya kuma yi wa kansa alkawarin bazai taba forcing Siyama ta kwanta da shi ba, ba Siyama kadai ba, ya fi karfin ya kwanta da mace (out of force), a irin farin jinin su da Allah ya yi masa.

Na sha jin yana fadin baya son mutum mai saka ido ga rayuwar wani, sa-ido sana’ar banza ne mai muni, gashi yanzu so nake kawai mu tafi gida Najeriya in gurfana gaban Abba na, in karbi hukunci komai tsaurin sa, in har zai yafe mini, don haka dole in kwantar da kai ga Hamzah don passport dina yana hannun sa, Young Abba ya damka masa tun ranar daurin auren mu, watakila inna kwantar da kai na dainatsanaar sa a akan rashin addini in samu ya katse komai nasa mu tafi gida Najeriya in gyaro ta da Abba ko na samu kwanciyar hankali, tunda alhamdulillah nan da sati hudu zan kammala karatun digiri na.

Hankali na bakidaya ya koma ga Abba da Ummati, da kuma tsaunin Mambillah tushe na. Kai har ma da Anti Wasila da kannena da aka haifa bana nan. Ban sani ba ko idan aka yi bari ana kwashewa dai-dai?

Yanzun dai gani cikin hayyaci na ina neman Abba da soyayyar sa ruwa a jallo, bayan saukowa daga kololuwar dadin duniyar soyayyahr da Hamzah ya luluka da ni, na gane muhimmancin rashin soyayyar Abba cikin rayuwa ta, mace ba soyayyar namiji kawai take bukata ba, don cikar farin cikin ta, ita soyayyar namiji sau tari ta dan lokaci ce, da zarar an biya bukatar gangar jiki komai canzawa yake yi, soyayyar iyaye kuwa itace eternal abar da bata taba canzawa bata taba yankewa koda rai ya baci.

A yau gani bayan tabbatuwar dukkan mafarkan da kuma burika na, Hamzan dana kusa salwantar da rayuwata domin in tsira da shi ya tabbatar min ni wawuya ce a kan sa, kuma marar sanin darajar iyaye, wadda ta zabi jin dadin ta daga jikin Da namiji akan farin cikin wanda ya kawo ta duniya, ina so na gyara wannan dingimemen kuskuren nawa idan mai gyaruwa ne tsakanina da mahaifi na, koda Abba ba zai bani damar shiryawa da shi kamar da ba, in dai zan samu albarkar sa cikin aure na watakila ta taimaka min…wajen ganin Hamzah ya tsaya ya amsa sunan cikakken musulmi, mai tsaida sallah mai kuma kiyaye dokokin Ubangiji.

Amma shin an taba bari a kwashe daidai???

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 45Sakacin Waye? 47 >>

2 thoughts on “Sakacin Waye? 46”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×