Skip to content
Part 50 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Sai da ya kunna motar yayi reverse zai fita daga parking lot din, sannan na ce “Sannu da zuwa Grandma, sannu da hanya. Welcome to Washington”. Ko kula ni bata yi ba, sai fiffizga take yi kaman ta ci babu, yace cikin damuwa,

“Kaka ba kya ji ana gaida ke ne?” Ai kamar jira take ya tanka ta balle mana. Cikin hargagi ta ce, “idan kuma ni din kurma ce fa Mawonmase? Sai aka ce dole sai na amsa? Idan Jesus ya sa na kurumce daga sanda ka baro ni a Jos, zuwa yanzu abin mamaki ne? Nace abun mamaki ne? Ko kuma idan na ji sai aka ce dole ne sai na amsa?”

Don haka daga ni har shi ba wanda ya kara cewa komai muka kama kan mu, muka kuma kama bakin mu har muka iso gida.

Shi ya dauko kayan ta ni kuma na bude gidan muka shiga dukkan mu, ina gayawa raina zan jurewa wannan tsohuwar da duk abinda ta zo da shi albarkar ‘soyayyah’ da ‘amanar kaunar’ dake tsakani na da jikan ta. Ba don haka ba bazan dauki tsawa da diban albarka ba wanda ko tawa Kakar bata taba yi min ba.

Grandma Veronica na shigowa falon gidan mu da katoton frame baki mai rubutun golden ta yi tozali an rubuta “ALLAHU-MUHAMMAD” a jikin sa da Arabic. Ba wai ta iya karantawa bane amma ta san ‘is a symbol of ISLAM’. Abin takaicin a gidan Mawonmase tunda ya zabarwa kan sa auren musulma, ta kada kai cikin tashin hankali ta juyo gare mu ni da shi duk muna tsaye cirko-cirko mun yi tsuru-tsuru sabida tsabaragen bala’in da muka hango cikin jajayen idanun ta.

Sai ta ce masa “na ga ‘symbol’ na nata addinin daga shigowa ta an kafa a gidan ka, kai ina hoton Jesus Christ? Kamata yayi tunda ta zame maka dole a ce duka biyun akwai, don kowa ya samu albarkar nasa, tunda gidan ba nata bane ita kadai”.

Hamzah ya nisa, sabida shi bai saba tashin hankali ba, duk ya muzanta. Ya ce cikin lallashi.

“Kaka, ziyara kika zo mana ko neman Magana?  Kamata yayi ki zauna ki huta ki ci abinci ki yi wanka, son samu ma ki kwanta ki yi barci, kin yi kwanan zaune a jirgi you need to rest first, sabida blood pressure din ki, ba neman rigima ba”. Yayi maganar ne cikin yaren Birom, Kaka ta ce. “Uban ka Ezekeil da ke ‘heaven’ shi yake rigima amma ba ni ba!

Mawonmase ka yi disappointing Jesus, da kyar in albarkar ‘Christ’ bata bar jikin ka gabadaya ba.

Bana raba dayan biyun ta dage ta aure ka ne don ta ja ka nata addinin kaima, idan kuwa ta yi wannan nasarar ka gama yin asara da haihuwarka gwara barin ka”. Ta fashe da kuka ta tsugunne a wurin, ta hada hannayen ta biyu ta na kuka tana fadin “Oh Dear Jesus, forgive my Grandson, have marcy on him, ba laifin sa bane, she charmed him!”. Hamzah ya kama ta ya mikar da ita tsaye, ya rike ta cikin hannayen sa yana fadi cikin lallashi da rawar da jikin sa ya soma, “stop crying Grandma, everything will be alright, now, go to bedroom and rest. Siyam zata kawo miki abinci.”

Da jin haka kuwa Kaka ta fasa sabon ihu tana cewa “abincin Moslem girl zan ci? Ai gara yunwa ta kashe ni na san direct paradise zan wuce.”

Hamzah ya ce “okay-okay Grandma, take it easy, let me wear my Apron and cook for you”. Sannan ne ta yarda suka wuce tare zuwa dakin da muka tanadar mata wato daki na. Suka bar ni tsaye a falo kamar an dasani a wurin.

Amma tana shiga ta sake yin tozali da window-size frame na Ayatul Kursiyya sai ta ja baya da sauri tana fadin “Jesus Christ, have Mercy! Ba zan kwana a dakin nan ba, tukunnama dakin waye a cikin ku?”

Hamzah yace cikin fara kosawa da rikicin ta, “Grandma I think I told you that my house is small, very small, kika ce you can manage with us a hakan, Siyam ta hakura da dakin ta ta bar miki, I think this fis respect to you, yanzu kuma kin ce bazaki shiga ba” tace “sai an cire wannan abun fadar min da gaba yake yi”.

Hamzah ya dube ni cikin idanun bidar neman yarda ta, dai-dai lokacin dana biyo su dakin jin hayaniyar ta taki karewa, na kuma ji me ta ce, na kuwa yi kicin kicin da fuska ba rahma ko kadan a kan fuska ta, zan ga wanda zai cire min Ayatul Kursiyyu a daki na sabida wata katuwar kedara, mushrika, ta fara kure hakuri na wallahi.

Hamzah ya ga babu fuskar ma da zai nemi wannan yardar daga gare ni, ta a sauke ‘frame’ na Ayatul kursiyyu, sai ya ce mata “to ina zan kai ki Grandma? I have no guest room na gaya miki tun kafin ki zo”. Na ce ba matsala Habeeby, pls bear with her, kai ta naka dakin amma shima akwai ‘frame’ din Bisimillah, ya za’ayi kenan?”

Hamzah ya shiga tsaka mai wuya, ga fuskata ba rahma ga Kaka ta kasa ta tsare tana jira ta raka a cire mata Ayatul kursiyyu a daki. Sai ya ce a wahale.

“Grandma, kina so jikan ki guda daya tal zuciyar sa ta buga ko?” Tace “no, no, no” ya ce “in bakya so zuciya ta ta buga ‘stop creating commution’, ki shiga daki ki huta a kawo miki abinci.”

Kaka sai ta rintse ido sannan ta shiga dakin nawa da kafar hagu, tana fadin “Jesus save me!” Na juya na wuce kitchen ba tare da na dube shi ba sabida yadda dariya ke son kama ni, na wuce don na kawo mata abinci, sai ya biyo baya na da sauri.

Ina cikin harhada abincin akan tray ya riko kuguna ta baya, “Siyam please, i know she’s worrisome, ki yi hakuri ki taimaka min mu zauna lafiya da ita, ina so in kaita asibiti ne akan hawan jinin ta so probably tayi sati biyu”. Na ce “in dai ni ce kada ka damu, amma ya maganar tafiyar mu Najeriya?” “Magana tana nan, ki bani lokaci in kammala da hidimar asibitin Kaka, in taji sauki….”. Na katse shi da cewa “na rantse da Allah b azan haihu a kasar nan ba, haihuwar fari, ga dan an ce mara lafiya ne, tukunnama tsakani da Allah ka fada mata ka musulunta?”

Hamzah yayi shiru, kafin ya ce “I lacked the courage! Sabida hawan jinin ta kada ta samu ‘stroke’ kuma” Wato ya rasa karfin zuciyar fada mata. Nace “then imanin ka na da rauni har yanzu Hamzah!”.

Ya kankame ni sosai jikin sa yana rawa ya ce “ina tsoro ne ta tsine mini” na ce “ta dade bata tsine ba, ba abinda tsinuwar ta zata yi maka, babu biyayya ga kowa wajen sabawa Ubangiji, har iyaye kuwa.

Ka daina boye musuluncin ka ka fito da shi fili ga kowa in dai ka amince don Allah ka musulunta ba don ni ba”.

“Siyam duk abokai na sun san na musulunta, haka abokan aiki, duk wani na jiki na ya sani ita kadai nake shakka wallahi” na ce “ni kuma bana jin zata iya rabuwa da kai wai don ka tuba ka musulunta, inace addini ra’ayi ne ga baligi? Besides, na ga kaunar ka mai yawa cikin idanun ta. Baka ji bama gafara take nemar maka wajen Jesus dinta duk da ka bata mata rai”.

Dariya yayi ya sumbace ni a goshi, ya ce muje ki kai mata abincin da kanki, haka zamu yi ta hakuri har su sakko”.

Tare muka shiga dakin nawa muka tarar ta bude Bible tana ta addu’a. Kasa zama nayi don bana son sauraron wannan kwarmaton mai neman kashe min dodon kunne saboda rashin dadin sa, na fita, sai shima Hamzah ya biyo ni, muka jera kamar wani mai take min baya.

Dakin sa da muka hade tare ya zama namu mu biyun yanzu sakamakon na bar ma Kaka nawa can muka nufa, muna shiga na zauna a gefen gado cikin kokarin boye damuwata, amma Hamzah sarkin fahimtar abu sai da ya fahimci damuwar da nake boyewa din, dama kuma cikin damuwar muke tun kafin zuwan ta ba wai damuwar ta sake mu bane, zama ya yi a gefe na, yace “I know this will surely happen, shiyasa na baki hakuri nace ki jure tun kafin ta zo,

I’m very sorry Siyam, na san baki saba da tashin hankali ba, ba yadda zan yi da rigimar Grandma.

Amma ki sani ta yi min komai a rayuwa har fiye da wanda uwa da uba zasu su yi wa dan su, itace tsanin duk wani mataki dana ke kai a rayuwata yau.”

Na ce “ni ba wannan ne damuwa ta ba Habeeby, karewa ma in don ta ni ta zo kenan bazata koma Jos ba, ko Allah ya sa watarana mu saka ta a hanyar gaskiya, na saba da rigimar tsoffi don Ummati ta fi ta rigima kuma a hannun ta na taso.

Damuwata shine ka da ta kore min mala’ikun rahma dake daki na da wannan karatun nata da take yi don anan nake ibadodi na”, Hamzah ya yi dariya ya ce.

“Lakum Deenu kum wa liya Deen” ayar Ubangiji ce wadda tun ban dandani zakin  musulunci ba na san ta a bakin musulmai, bana jin zamanta da practicing addinin ta cikin gidan mu zai yi affecting din addinin mu da komai, Allah yana ko’ina kuma buri na shine watarana itama ta musulunta, ta dawo cikin hasken shiriya” nace “na yarda da kai, amma duk da haka bari inje in kwashe Alqur’anai na da kayan sallah ta daga dakin”.

Na shiga dakin sadaf-sadaf kamar barauniya, har yanzu tana ta addu’a tana wani gyada kai kamar na kadangaruwa, na lallaba na kwaso Al’qur’anai na da carbi na da littafan addu’o’I na su Hisnul Muslim da su Alma’asurat, na kuma sauke frame na Ayatul kursiyyun don hankali na ya ki kwanciya in bar su a dakin.

Na juya kenana zan fita sai naji muryar ta daga baya na tana magana cikin nutsuwa, kamar ba ita ce mai hargagin nan ba, yanzun Magana take a nitse, yanayin yadda take maganar kamar wadda ake yi wa wahayi.

“Me kike so da jika na?”

Nayi shiru ban ce mata komai ba. Ban fita ba ban kuma dawo dakin ba. Kaka ta tako a hankali ta cimma ni, muka fuskanci juna gaba da gaba kamar masu shirin dambacewa ga mamaki na sai ta sassauta murya ta ce cikin muryar lallashi.

“Ki fadi a nawa zaki fansar min da auren ki da shi. Ina da manyan gonakin dankali, duk zan sayar in mallaka miki kudin, ina da gidan kai na tankarere a Jos, shima  zan baki, ke har shanu da akuyoyin da nake kiwo a gidan gona ta zasu zama mallakin ki a rubuce da shaidu, in dai har kin yarda kin amince zaki rabu da jika na (Mawonmase) ki bar masa gidan sa ki koma gaban iyayen ki.”.

A wannan lokacin ne na dago ido a hankali na dube ta, idanuna fal hawaye na ce, “Kaka, ni din kuma sai aka yi rashin sa’a ba ‘yar mutsiyata bace, soyayyar gaskiya ce tasa na aure shi, har na rabu da nawa iyayen saboda shi. Ina son sa Kaka, son da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Har ga rabo Allah ya bamu, ina zan je kuma da aure na da tsohon ciki?

Ba zan iya fansar da aure na da shi da komai ba, da kin san tarihin soyayyata dashi da baki ce haka ba, ina fatan in mutu ne da igiyar auren sa a kai na.

Ki bar ni in rayu da jikan ki cikin salama da kwanciyar hankali, ki bar mu mu ji da kaddarorin da ke jiran mu a gaba na’ya’yan da zamu Haifa, kada ki zama mai tayar mana da hankali don already cikin tashin hankali muke, har abada na miki alkawarin ba zan taba cutar da jikan ki ba, Tsakani na da shi soyayya ce da amana”.

A hankali Hamzah da ya sawo kai zai shigo dakin, jin shiru-shiru Siyama bata dawo ba, hakan ya sa ya biyo bayan ta, sai ya ja da baya a hankali, ya koma dakin sa. Bayan ya gama jin amsar Siyam ga Kaka.

Bai taba jin kalaman da suka yi masa dadi daga Siyam suka faranta masa suka wanke zuciyar sa irin wadannan ba. Ya kara mata matsayi mai girma a zuciyar sa, domin ya ji dadin amsar data baiwa kaka.

Kaka tace “amma kin san ba addinin ku daya da shi ba, don me zaki aure shi? Me yasa baki nemi dan naki addinin kin aura ba? Ko rasa miji kika yi cikin addinin naku?

Salon ki sa watarana ya fita daga addinin sa mai albarka na iyaye da kakanni, ya shiga naki ko, sabida kin ga yana da rauni a halayya da dabi’a, kuma kin same shi yadda kike so ya riga ya mutu a son ki?”

Na yi murmushi, cikin harshen hausan dana san bata ji na ce “Kaka ai sai dai kada a kuma, sai dai wani Hamzan ba wannan ba”.

Na fice na bar mata dakin tana kururuwar cewa “Jesus zai yi hisabi tsakani na da ke, muguwa -azzaluma!”.

Maganar ta ta karshe tayi min ciwo, amma haka na shanye na koma daki, na same shi ya yi tagumi a gefen gadon sa, ina shiga yana mikewa ya riko ni. Sai kawai ya hau ni da mahaukacin kiss. Na soma kokarin zamewa ina fadin “Mawonmase sallah zanyi fa” yace “taimake ni Siyam, ki ara min bakin ki in tsotsa, jikin ki da lokacin ki ki bani su ko na minti biyar ne, in nuna miki godiya ta bisa amsar da kika baiwa Kaka, kada zuciyata ta fashe da soyayyar da ke gudana a cikin ta”.

Sai na kyale shi domin ya samu nutsuwa ko yaya ne, don na lura yana cikin damuwa ba ‘yar kadan ba a kan rigimar Kaka. Sai da ya sabbaba min wanka sannan. Yana zaune bakin gadon sa ina kan stool ina shafa mai na na din-din-din wato lotion din Dr. Teal’s. Hamzah yace “Siyam, amsar da kika baiwa Kaka, da ta ce ki fansar mata da aure na. I must confess, I’m highly impressed, na gode”.

Kamar in ce masa nima na gode da soyayyar dana samu yanzunnan, zan iya cewa tafi ta kowacce rana cika min zuciya, tana cikin jerin ranakun mu da ba zan manta ba, wasu abubuwan da yawa baka san ka yi su ba, wasu kalaman daka fada min baka san ka fade su ba amma yau na ji su. Mawonmase, wannan ce addu’a ta. “Allah sa mu raka rayuwar bakidaya tare”.

Amma a fili murmushi kawai na yi.

Ya tada sallah, nima na tayar, don tare muka yi alwallah yau, yana kuskure ina gyara masa a haka muka yi. Bayan mun kammala alwala na ce shi zai mana Limanci. Ya yi gardama “amma dai kin san ban iya limanci ba ko?” Nace “koya zaka yidaga yau Imamuddeeni, komai da koyo akan iya”. Dole ya yarda ya tada sallahn na bi shi a baya.

Muna cikin sallah muka ji tamkar an bude kofar dakin kasancewar muna cikin sujjadah sai bamu waiwaya ba, sai can an jima kadan cikin sujjada ta naji saukar abu a gadon baya na kamar tabarya kamar kujera sai da na kai kasa akan ciki na.

Stool din mudubi Grandma ta dauka ta kantara min a gadon baya na. Na baje na yi flat a kasa sabida azabar dukan wanda ya sa na saki ‘yar kara, babu bata lokaci kuma jini ya balle min na soma sakin nishi cikin azaba. Ba shiri Hamzah ya sallame sallahr sa ya juya ya yi ido biyu da Kakar sa dake tsaye tana huci kamar macijiya, Hamzah ya ce.

“Kaka!” Cikin karaji. Yayo kaina ya dago ni jikin sa bakidaya, yana fadin “na shiga uku, ta kashe min Siyamah!?”

Duk da azabar da nake ji a mara ta da gadon baya na da jini da ya soma naso a kasa sakamakon katakon da Grandma ta rafkka min ban kasa hango rigimar da Kaka da shi kan sa Hamzah zasu iya shiga idan ya kai ni asibiti ba, don haka na daure ina cije baki don naga ya rude sosai ya gigice ya rasa takamaimai abinda ya kamata ya aikata.

A wannan hali kuma idan ya kai ni asibiti a kasar nan ‘yan sanda ne zasu shiga maganar su bi diddigin komai wanda hakan zai iya daure Kaka. Nace “a’ah, ban mutu ba Shaheed. Kyale ni ka ji da ita, look, zata fadi kasa… she’s in severe anger, komai na iya faruwa da ita, kuma ka ga tana da hawan jini kada ta fadi ya zama paralyses”.

Ai kuwa kamar na fada da bakin mala’iku sai gani muka yi rikija! Grandma ta fadi kasa tana shure-shure tana sambatu. Hamzah ya rasa inda zai sa kan sa, ya rasa wa zai ceta tsakanin nida ita, a karshe ya ya sake ni don na ce ya ji da ita zan iya kula da kai na, ya ciccibeta duk nauyin ta yayi motar sa da ita.

Kafin ya kai Kaka mota ya dawo don nima ya dauke ni kan yaro kyakkyawa ya danno, babu wani ciwo mai yawa na haife yaro bakwaini cikin mintunan da basu gaza goma ba. (So Grandma induced labour).

Dan da na haifa ko kuka bai yi ba har yanzu da Hamzah ya dawo dakin, ni kuma na yada jiki a gefe ina maida numfashi sai ga Hamzah ya shigo da nufin nima ya dauke ni ya sa a mota ya yi asibiti da mu. Gani na da Da,  da mahaifa da mabiya duka a gefe ya kusa haukata shi. Ihu ya saka yace “haihuwa kika yi Siyam? Na shiga uku ni Hamzah, Kaka zata kai ni prison a kasar nan, yanzu yaya zan yi da ku?” Daga kwancen da nake na ce masa “cibin zaka yanke” Hamzah jiki na rawa ya ce “Siyam ta yaya? Babyn ma ba ya motsi fa” janyo wayar sa da ke yashe kusa da hannuna nayi na mika masa nace “kira min Aunty kawai, jaririn nan ina jin ya koma”.

Maimakon ya kira Antin sai ya ga ba zai iya barin dan sa haka a kasa cikin cibiya ba. Hannun sa da jikin sa duka suna rawa ya sa zani na ya rufe jaririn sannan ya dauke shi da cabin da komai idanun sa na fidda ruwan hawaye yana tambaya ta “Ban gane hausar ki ta jaririn ya koma ba? Ina ya koma?”. At the same time, hannun sa daya na danna waya yana kiran Anti.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 49Sakacin Waye? 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×