Skip to content
Part 51 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ni da na haihu haihuwar fuju’a na fi shi karfin zuciya, ni na bashi shawarar ya kira ambulance a tafi da Kaka maimakon ya yi tukin mota a halin da yake kuma ya kira min likita ta. Dana ga ya kasa kiran wayar ma ni na karba na kira asibitin mu, na yiwa likitar da ke duba ni bayani cewa tazo gida na haihu ba zato, dan kuma bai yi kuka ba har yanzu kuma muna da tsohuwa mara lafiya ta taho da hospital van.

Ko mintuna ashirin baa rufa ba motar asibitin ‘Mayo Clinic’ ta iso gidan mu, likitoci biyu da ma’aikatan jinya biyu suka shiga baiwa Kaka taimakon gaggawa ni kuma tawa likitar ta shige bincike a kaina da abinda ya janyo wannnan haihuwa haka ta gaggawa bayan lafiya kalau awon data yi min kwanaki biyu da suka wuce ya nuna har ta gyara min kwanciyar jaririn, ga dan ta fahimci ya koma, ga jinin da ya balle min ya ki tsayawa. Duk irin kwakwar su na son jin gaskiyar abinda ya faru na ki yarda in saka sunan Kaka.

Daga bisani cewa na yi zamewa na yi na fadi shine dalili. Hamzah yana gefe rungume da gawar dan sa ya kalle ni cikin tausayi jin amsar dana bayar, sai ya kama kuka riris kamar ba namiji ba. Ga yaron sa baki kamar sa, mai kama da shi sak, ga suma a kansa yala yala sannan hatta farcen sa na kafa dana hannu duk irin nasa ne kamar ya yi khaki.

Yaro chocolate colour irin wanda nake burin haifa tare da Hamzah dare da rana. Ni dai in haifi yara masu mixed colour da zan gan su kamar ruwa biyu shine buri na a baya, yau gashi Allah ya bani, amma ko fuskata bai gani ba. Nima na shiga kukan ba kakkautawa.

A lokacin Aunty Nasara ta iso, ita kadai ta iya karbar gawar yaronnan daga hannun sa ta kaiwa Young Abba da suke tare wanda ke ta sintiri a falo bayan an yanke cibin jaririn. Shi ya wuce dashi zuwa inda za’a yi masa suttura, musulmi su binne shi 

Aunty Nasara da Doctor Rita suka taimakamin na tashi daga kasa zuwa toilet suka gyara ni suka yi min wanka, likitar tace zata wuce dani asibiti don su duba lafiyata sosai. Tuni dama sun wuce da Kaka.

An karbi Kaka a emergency, abinki da kasar da aka san muhimmancin lafiyar dan adam, tuni suka shiga bata taimakon gaggawa, ba’a fito da ita ba sai bayan awa daya, ta farfado amma ta ki yin ko motsi, ta ki yin magana. Da ta rufe ido hoton Mawonmase take hangowa suna sallah shi da matar sa abinda ke neman farka mata zuciya da gusar da hankalin ta, bayan ta farfado aka kaita dakin hutu, sannan ne Hamzah ya samu ganin ta. A lokacin na samu karfin jiki na Amma likita ta rike ni nima a sibitin tace ai nan da kwanaki uku zata sallame ni idan na samu karfin jiki na ta kuma tabbatar da koshin lafiya ta. Tuni Young Abba ya sa an binne yaron.

Amma wani ikon Allah ko Anti ban gayawa Kaka ce sanadin haihuwar bakwaini na babu rai dana yi ba, don na san maganar sai ta zama babba, ga Kakar itama tana can rai a hannun Allah. Likita yace ta gamu da cardiac problem (matsalar zuciya) bayan hawan jinin ta.

Muna tsaye gaban gadon ta ni da Hamzah a washegarin ranar, tana hawaye amma ta kasa cewa komai don bata son ko bude ido ta ganni gaban ta, na saka a raina ba Kaka ce ta kashe min Da ba Allah ya yi na amfanin can ne, ta doke ni ba da niyyar inducing mini labour ba sai don ta huce haushin ta na musuluntar mata da jika da na yi. In ta tuno Mawonmasen ta ne yake jan sallah matar sa na bayan sa, which means shima ya musuluta har ya iya limanci ba kamar yadda ta ke zaton matar ce kadai musulma ba, zuciyar ta yi take kamar zata buga.

Ta tuno mafarkin da ta sha yi a kan sa cewa ya canza addinin sa na iyaye da kakanni (christianity) zuwa na Annabi Muhammad PBUH ashe dai gaskiya ta gani a cikin barcin ta?

Ta bude ido da kyar tana duban sa don ni ko son gani na bata yi, muryar ta bata fita sosai tace.

“Mawonmase me yasa ka kawo ni asibiti? Me yasa baka bar ni zuciyata ta buga da bakin cikin ka na mutu na huta ba? Idan na rayu menene amfanin sauran rayuwata tunda ka bar mu? Mace ta janye ka……”.

Ta saka kuka wiwi tana cewa “I regret coming…. Had I know abinda zan gani kenan a kasar nan da ban zo ba!”.

Hamzah yace cikin sarewa, don shi bai saba da irin wannan masifar ba, daga zuwan ta zuwa yanzu kuwa ya tabbata da za’a auna jinin sa shima za’a ga cewa ya hau har fiye da nata. Don dai ya kasance namiji ne kawai Yace.

“Kaka, kina so in fadi nima ko? Duk mu taru mu mace kamar yadda kika yi sanadin mutuwar Da na na farko a duniya? ina jin Siyam ta gaya miki juna biyu gare ta amma baki yi la’akari da hakan ba kika nemi kashe ta wanda sakamakon hakan ni kikayi ma asarar yaron da na kallafawa rai. Dan da shi kadai a matsayin jinina a duniya bayan ke.

Ni karamin yaro ne da zaki zaba min addini Kaka? Ko kuwa kabari daya za’a saka mu in mun mutu? Cewa nake soyayyar da ke tsakani na da ke iyakacin ta gidan duniya? A lahira duk ba zamu amfanawa juna da komai ba, wannan inace ko a bible kin san shi cewa lahira gaskiya ce?

So ki bar ni in yi addinin dana zaba, cikin nutsuwa please Kaka, kema ina miki addu’a Allah yasa kina da rabo, bazan taba son ni ina aljannah ke kina wuta ba, don babu addinin da ya kai musulunci dadi da kwanciyar hankali, ki zauna lafiya damu, bazan taba gajiya da zaman ki ba, na yi alkawarin kulawa da lafiyar ki.

Don Allah Kaka in har kina so na to kada ki kara magana akan addini, kada ki kara kai hannu jikin matata, kin jawo mana asarar da bazamu mayar ba, amma Siyam ta rufa miki asiri yau da ta fadi kece sanadin accident dinnan you will surely go to jail, ki nemi gafarar ta, kuma kada ki kara daga hankalin ki a kan addini na.

Kowa ya yi wanda ya zaba, babu mai ingiza wani zuwa nasa addinin tsakanin ni da ke, ina so ki san cewa Siyam bata saka ni shiga Islam ba ni nasa kai na, don na dade ina sha’awa kin sani tun lokacin muna yara ni da aboki na Hamzah Mustapha, kuma canjin addini na ba zai shafe ki ko ya rage ki da komai ba”.

A wannan gabar, Kaka Veronica ta gama sarewa da al’amarin jikan nata, ta yarda Mawonmase data sani a baya ba shine yanzu ba, wannan ya gama yin nisa, daga kalaman sa zaka yarda ba abinda zata yi da zai dawo da shi addinin Christianity, ta soma wata irin jijjiga kamar mai farfadiya tana fadin “zai shafe ni mana, daga ni har zuri’a ta duka, tunda kuwa ‘ya’yan ka ma shi zaku sa su yi?! Ba zasu bi Jesus ba.”

Kaka ta fada tana share hawaye da bayan hannun ta jikin ta yana rawa da wata irin kyarma. 

“Shikenan na rasa ka, duk wahalar da na sha a kan ka yau ka zabi kyakkyawar mace da addinin ta akai na da addinin da ya haife ka. I will not disown you, Mawonmase, sabida bani da kowa sai kai, amma a yau ba sai gobe ba kayi min booking in koma Jos.

Ni Veronica bazan taba kwana a gidan da ba’a bautawa Jesus ba. Bana son lafiyar da zaka nema min din, bana so mutuwa nake so! Gara mutuwa ta da rayuwa ta ina ganin ka cikin bata da tabewa.”

Hamzah ya dafa hannayen ta dake ta makyarkyata, yace “ni kuma lafiyar ki matters a lot to me Grandma, baki ga ta mutuwa yanzu ba sai kin goya ‘ya’ya na musulmai a gadon bayan ki”.

Kaka tace “over my dead body! Zan goya mata ‘ya’ya, kai ni ko kusa da kai na daina zuwa. Idan baka mayar dani gida a gobe ba sai na yi fiffike na tashi zuwa kasata a kan iska.”

Hamzah yayi dariya ya ce “sati biyun nan da kika yi alkawarin yi sai kin yi su a U.S, lafiya sai kin same ta in sha Allah, ko da tsiya ko da arziki sai kin rayu, sai kin goya mana ‘ya’ya Grandma”.

Ta dube ni da idanu a warwaje tace “na bar ki da Yesu, ya saka min cutar da kika yi min”. Na yi mata murmushi na kama hannun ta nace “Kaka kema zaki shigo cikin addinin gaskiya da iznin Allah nan bada jimawa ba” ta yi maza ta fizge hannun ta tace “idan ke mayya ce, to kurwa ta kur. Ruhi na ba irin na Mawonmase bane sabida ni na rike Jesus, na rike addini na fiye da komai, shi kuwa tuntuni dama gafalalle ne” Hamzah na dariyar tsokana ya kama hannun ta yace “har na hango sunan da zamu saka miki “Nana Khadija”. Kaka ta fashe da kuka tana cewa da karfi.

“Da na sani da ban zo gidan ka ba, Mawonmase ka riga ka halaka!”.

Haka muka kwana a kanta suna tafka rigima ita da jikan ta. Ko nawa gadon jinyar ban koma ba, kwanciya nayi a daya gadon dakin na juya musu baya ina jin su ina hawayen rashin da na gudan jini na. Wannan haihuwa da komawar dan, sun kara sa min nadama a kan Abba, sun sa na kara sanin darajarsa, sun dugunzumar da zuciya ta bakidaya ga son komawa gare shi. Duk fadan nan nata da tashin hankali da munanan kalaman data ke jefa masa, shi Hamzah kokari ya ke shi ya maida shi wasa irin na jika da kaka.

Kamar da wasa, cikin dare ina toilet ina fitsari a falon asibitin, bayan an saka mata karin ruwa sakamakon ta ki yarda ta ci komai ta kuma daina magana ma bakidaya. A lokacin Hamzan yana wajen likitan ta suna tattaunawa a kan lafiyar ta, ya gama da likitan cikin tashin haknkali ya dawo dakin domin likita ya tabbatar masa zuciyar Kaka ta tabu (ciwon zuciya) ya kama ta, wannan ya girgiza Hamzah ya shigo dakin da zummar lallashin ta da kwantar mata da hankali,

Sai ya ga kumfa tana fita daga bakinta idanunta a warwaje harshen ta ya fito waje. Lokacin na bude kofar toilet nima na fito.

Kallo daya muka yi mata ni da shi muka fahimci babu ita, ma’ana zuciyar ta ta buga; ta rasu. Saboda bakin cikin Hamzah ya musulunta.

The Mourning

Iyakar gigicewa da shiga tashin hankali irin wanda da zai shiga a lokacin da ya rasa iyayen sa Hamzah ya shige su a dalilin mutuwar Kakar sa, Grandma Veronica.

“I’m now alone on earth, my child and my grandma are gone, is only you I have SIYAMAH”.

Su ne kalaman da Hamzah ke yawan fada tun bayan rasa Kakar sa da babyn sa.

Hakika na tausaya masa halin dimuwar da ya shiga na rashin Kakar sa wadda ta rage masa tal a duniya, fadin halin da Hamzah yake ciki a washegari bata baki ne, and I feel for him too, tunda kuwa zukatan mu sarke suke da na juna. Ya ce min babbar damuwar sa da Kaka ta mutu ba tare da ta musulunta ba.

An rike gawar Kaka a asibitin zuwa Hamzah ya gama shirin tahowa gida Najeriya domin a binne ta a Jos. Duk da yace baya so ‘yan kabilar su su binne ta, nace masa kuma bazai yiwu a yadda yake tunani ba, wato musulmai su binne ta a makabartar musulmai. Dole akan haka ya hakura ya fara shirin tahowa Najeriya tare da gawar ta.

Ya kuma ki yarda ya tafi da ni burial din Kaka, a cewar sa ‘yan kabilar su mutane ne masu rikicin addini da kabilanci na gaske. Masu tsananin kiyayya ga addinin musulunci da musulmai da ‘yan arewa. Ba zasu karbe ni ba, har dai in suka ji sanadin bugawar zuciyar Kaka, cewa bakin cikin musuluntar sa ne kuma a dalili na.

Ana I gobe zai tashi Najeriya da gawar Kaka Aunty Nasara da Young Abba suka zo masa gaisuwa/ta’aziyya. Gani na a kwance ko tashi da kyar nake yi sabida nima ba wai na gama samun lafiyar jiki na bane, ga mutuwar kakan ta bugeni ga mara ta ta tsananta min da ciwo. Aunty ta roki Hamzah izinin tafiya da ni gidan ta zuwa dawowar sa. Sai yace ta bari sai na raka shi airport a washegari ya tashi sai in taho gidan ta.

“Ai da kyar zata iya raka ka airport din, kalleta a kwance fa.”

Hamzah ya dukar da kai kasa, kafin ya dago yace “kiyi hakuri Aunty, bazan iya kwana a gidan babu Siyama ba. Ita kadai nake da yanzu. Bani da kowa bani da magaji.”

Aunty Nasara ta ce “kana da Allah. Kuma kana da mu Hamzah, mu iyayen ka ne, sannan Allah zai musanya maka da wasu yaran masu albarka.”

Dole suka koma gida suka bar mu tare. A daren na yi kuskuren gayawa Aunty maganar gynotype dina dana Hamzah. Ba don komai ba sai don na ga ya kamata ta sani.  Cewa Hamzah Mawonmase AS ne, nima kuma Siyama AS ce. Wanda ke nufin duka ‘ya’yan da zamu haifa wasu zasu zama ‘sicklers’ wasu ‘normal’ wasu kuma will become ‘carriers’.

Aunty Nasara ta shiga tashin hankali, ta shiga salati tana fadin “laifin Baban Ahyan ne, kamar ba dan zamani ba, ai yanzu an daina irin wannan kuskuren, sabida shi ya fi kowa gaggawa a duniya, bai ko yi tunanin a yi awon jini kafin auren ku ba, kamar a kan sa kike zaune. Shi dai kawai ya yi miki aure da wanda kika zaba. Ko ta bakin mahaifin ki ya ki saurarawa ya ji sai ka ce shi ya haifa masa ke”.

Ta nisa, kafin ta ce “Allah ya kawo mafita ta alkhairi, Ameen, amma dole zan gaya masa don ya dauki darasi a gaba”.

Hamzah bai san mun yi wannan maganar da Aunty ba. Yana dakin sa a lokacin yana hada kayan tafiya Najeriya a washegari Young Abba ya kira shi a waya.

Ban san me suka tattauna ba, na ga Hamzah ya shigo min at a mart pace (afujajan) yana min wani irin kallo kwayar idanun sa na juyawa kamar ba nasa ba.

Bakidaya ya birkice min. Wani ‘hidden side’ din shi da ban taba sani bane ya bayyana a gare ni yau, na rashin tawakkali da karbar kaddara da maida allura garma. Na fahimci wannan dabi’a ce ta masu shan barasa. Yana neman rasa hankalin sa, sakamakon wayar da Young Abba ya yi masa.

Yace min kai tsaye ba tare da sakayawa ba “Siyam, giya nake son sha, in ba haka ba zan zautu.

A matukarr firgice na dago na dube shi. Ba tare da ya nuna damuwa da firgicin nawa ba ya cigaba da maganar sa “Yau na tabbata ni maraya ne tun kafin in binne Uwata-Kaka ta, kuma Grandma ita kadai ce jini na a duniya, ita kadai ce za ta kaunace ni da dukkan nakasu na, iyayen ki naki ne ke kadai. Karya suke da suka ce zasu zame min iyaye, karya suke da suka ce zasu tsaya mi matsayin iyaye!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 50Sakacin Waye? 52 >>

2 thoughts on “Sakacin Waye? 51”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×