Skip to content
Part 17 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Maganar da Inna zata yi min ta katse a lokacin da Baba ya fito daga ɗakinsa yana min magana.

“Ke gobe sai ki shirya zaku je asibitin makka a duba miki idon naki, lokacin karatunku nata tafiya ga su Adawiyya har za su shiga cikin wata guda.”

Kaina na ƙasa cikin ladabi da girmamawa nace, “Allah ya kaimu goben Baba.” Ya amsa da, “Amin”

Inna Amarya tace da shi, “kuɗi sun samu kenan?” ta faɗa tana murmushi. ya amsa mata, “ehh to kusan hakan…yanzu Alhaji Nasiru ya kirani za’a kai icen dubu biyar gidansa…kuma jiya Amadu yace ya tura dubu biyar, to kinga idan aka haɗa insha’Allahu za su isa a biya buƙata.” Innata ta gyaɗa kai tace,”to Allah ya daɗa rufa asiri, gwara ai maganin ciwon tun kamin yay tsamari tun da jiya ma fa da daddare ce tayi bata gani gaba ɗaya, yau kuma kaga duk sai naga idon ya ƙanƙance sose gashi harda ɗigon jini.”

Ta ƙarasa faɗa tana ɗagowa da Baba fuskata a san da ya iso wajenmu. Baba yasa hannu ya dafi goshina ya kalli idon nawa ya furta,”sannu Mairo”. “yauwa Baba”. na amsa masa idona na kawo ruwa saboda tausayinsa da naji ya kamani a yanda yake ta magana tattare da damuwa a muryarsa. “yana miki ƙaiƙayi ne?”

Na kaɗa masa kai,”a’a sai dai zafi da nake ji da yaji-yaji haka”. yay ɗan jim kan yace,”bari idan na fita zan taho da zam-zam, Liman yace a karanta fatiha ƙafa bakwai aciki sai kike ɗigawa.”

Gwaggo ta fito a ɗaki ita ma ta nemi wuri kan tabarmar ta zauna tace da Baba, “naji kana asibitin Makka, yanzu har ma iya yin sammakon zuwa Malam? asibitin da kwana ake can wajen kama layi. ko dai muje na garin nan kawai?”

Yace da ita, “ai mun yi magana da Salmanu na gidan Malam Liman, yau zai shiga kano kuma acan zai kwana, to na roƙe shi nace dan Allah yayi ƙoƙarin kama mana layi tun da ba shi da nisa da inda yake zaune.” Gwaggo ta gyaɗa kai,”ah to da dama ai, hakan kam anyi dabara…mu duka zamu je?”

Baba yace,”ai kuna dai jin da yanda aka sami kuɗin kina kiran ku duka, ayi kuɗin mota da ya ya kenan?…ke ki zauna ba sai kinje ba Uwatta ta kaita.”

Ya faɗa yana duban Innata yana ce mata,”ni dai kuyi ƙoƙarin shiryawa da wuri, asibitin nan ance mai kyau ne.” Inna ta amsa shi da,”to.”

Ashe Inna bata manta da maganar da zata min ba, Baba na fita ta karkato da hankalinta kan Gwaggo tana cewa,”wai kina lura da yarinyar nan kuwa yanda take ramewa kamar wadda ake zuƙa…jifa yanda jikinta ke neman lalacewa, kalla ƙasusuwa kalla yanda fatarta tayi haske kamar jini zai tsarto.”

Gwaggo tace, “hmmm ba ta ƙwallafa tafiyar Kabiru da Adawiyya a ranta ba taya kuwa ba zata rame ba…dan shashanci sai kace waɗanda akace sun tafi ba zasu dawo ba.”

Na ɗan turo baki nace, “to Gwaggo shaƙuwa ce fa.” na faɗa a raunane. ta taɓe baki tace, “kune ma kashin awaki ƙarshe kenan, to ko su idan suka ji zafin rana rabewa suke.”

Bance komai ba, na yunƙura zan miƙe Inna Amarya ta kuma dakatar dani, ta kafa ta tsare akan saina faɗa mata abunda nasa a raina nake wannan muguwar ramar mara kyan gani, ni kuma nace mata ba komai, da ƙyar dai ta sarara min da tarin tambayoyinta tukunna na miƙe naje ƙarasa shanyata, har dai cewa ko dai aure nake so, to wannan tambayar ce ma sai ta sani kuka saboda naji kunya, kuma a ganina idan har zata min wannan fassarar to kenan tana min kallon ƴar iska ne.

Har da Ya Amadu ya kira yaji muryata ya tambayeni me nakewa kuka na faɗa masa Inna ke cewa ina son aure, yace Innarsa ko tawa? nace masa tawa, yay dariya yace nayi haƙuri zolayata take.

Nayi sallar azahar ina zaune kan darduma na zabga tagumi, ɗakin daga ni sai Kulu a zaune, ta baro inda take zaune ta dawo kusa dani ta kama hannuna. ƙasa da murya tace, “meke damunki?”

Na dubeta da idanuna da suka soma shanyewa nace,”wai me yasa ba kya son kowa ya san kina magana?”Na tambayeta ina lura ƙofar ɗaki saboda shigowar wani. ta lakuce min hanci tana murmushin da yake kauda damuwar raina tace.

“Sannu sarkin wayo, ai ni na fara tambayarki dan haka ki fara bani amsa menene ke damunki?, yanzu ba ki da aiki sai tagumi da kuka, kuma duk kin rame kina neman lalacewa”. ta faɗa da nuna kulawa. ni fa har ga Allah idan tana magana idan ba nutsuwa nayi ba to ba gane me take cewa nake ba, saboda yanayin hausarta bata fita sosai, kamar me gwaranci kamar me yin wani yaren na daban, nai ƙoƙarin maida hawayena nace mata,”Ya Kabiru na ke tunani, ban san a wane hali yake ciki ba yanzu, tun da ya tafi ba muyi waya da shi ba, ba muji ya isa lafiya ba.”

Ta janyoni zuwa jikinta ta kwantar tana shafa kaina cikin tattausar murya tace, “kina kewar Ya Kabiru da yawa?”. na ɗaga mata kai alamar ehh. tace dani,”kar ki damu Ya Kabiru yana cikin ƙoshin lafiya insha’Allah, ki hani zuciyarki da munana zato akan tafiyarsa kinji, kiyi yaƙinin yaje lafiya sai ki bi shi da adu’a kuma…sannan kiyi masa uzuri kinga ƙasar can da nan ba ɗaya bane, ana jan kuɗi sosai a kiran waya, shi kuma kin san a irin yanayin da yake ciki na rashi, ki zama me uzuri…amma nasan koma menene yanzu yana can yana fafutukar abunda zai yi ya sami kuɗin da zai kira gida kuma ba dan kowa ba sai dan ke.”


“To amma me yasa ba zai iya aron wata wayar ba ya neme ni, ai tare da Suhail ya tafi why can’t him ya ari wayarsa ya kira da ita…yayi tafiyarsa yana can hankali kwance ni kuma ya barni a damuwa da rashin jin halin da yake ciki.”

Sai kuma na ɗago a ƙirjinta ina goge hawayena nace,”Kulu dama Yaya yana mantawa da Ƙanwarsa?” tayi murmushin da ya bayyanar da haƙoranta tana tayani goge hawaye tace,”ko da Yaya yana mantawa da ƙanwarsa to ina mai tabbatar miki da ke naki Yayan ba zai manta da ke ba…wataran za ki ce na faɗa miki hakan…ki ƙara ba shi lokaci shi ma kina ransa, yau fa gaba ɗaya sati biyu ne ma da tafiyarsa…”

Nai saurin tarar nunfashinta da faɗin,”ba ki iya lissafi bane, wane yace miki sati biyu?, yau fa kwanansa ashirin da biyar da tafiya, amma ko rana ɗaya bai kira wani yace a duba masa halin da muke ciki ba.” maganar nayita ina kuka mai taɓa zuciya, yayinda Kulu ke aikin shafa kaina tana lallashina da bani haƙuri akan nayi masa uzuri nima ina ransa zai kira, ni kam ƙaro ɗan sautin kukana nake ina cewa ko da ya kira nikam ba zanyi magana da shi ba, ba zan ƙara kula shi ba har ya dawo. jiyo motsin shigowa yasa Kulu tai azamar miƙewa ta koma wurin zamanta, ni kuma nasa hannu na goge fuskata gudun kar Gwaggo ta tuhumeni.

Gwaggo ta shigo tana cewa dani, “kije Zulai na kiranki, daga nan ki ɗau abincin Yagana ki kai mata, naga yaran nan har yanzu ba wanda ya shigo”. na amsa da to na miƙe jiki a mace na fita. a tsakar gida na sami Inna Zulai da Innata su na ta shafta, sai Allah wadaran gwamnati suke akan rashin tsaro na ƙasa, Inna Zulai na bada labarin rashin imani da wasu ƴan garkuwa suka yiwa wata mata, abun ban tausayi idan kana jin irin wannan ma duk sai kaji duniyar ta isheka.

“Inna sannu da zuwa”. tace da ni, “yauwa Mairo, ya sauƙin idon?”. na amsa da,”da sauƙi”. “Allah ya sauƙe…kinga dama can inda naje ne naji su na batun maganin ciwon ido na islamic shine na bisu na karɓo a gwada ko za’a dace kamin aje asibitin”. ta faɗa tana ɗauko kwalin maganin daga jakarta.

Ta miƙawa Innata ta amsa tana faɗin,”an gode kuwa. dama yanzu Malam yake cewa gobe za aje asibitin cikin birni ance na can yafi kyau…to amma wannan ɗinma sai a fara gwada shi ɗin kamin goben ai ba’a san ta inda za’a dace ba.”

“Aiko dai an gode wallahi.” Cewar Gwaggona, ita ma ta karɓi maganin daga hannun Innata tana duba shi. Inna Zulai tace, “haba Suwaiba mene na godiyar…ta fara gwada shi yanzu, yace kwalli ne zata ke yi da garin.”

Nima na amsa da, “to Inna an gode”. daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta, ni kuma Gwaggona ta umarceni dana kwashe shanya na kuma wuce na kaiwa Yagana abincinta, na bata haƙuri yaran da za su kawo mata ne basa nan.

A ɗaki Innata ta ƙwace maganin da Inna Zulai ta bayar, ashe bani ɗaya ce ke tantama da sauyin halin Inna Zulai ba na lokaci ɗaya, a hankali Innata take cewa da Gwaggona, “haka kawai wa yasan ina taje ta karɓo, yarinya tayi amfani da shi ya ƙara kashe mata ido ayi me ɗungurin gun…dan ni wallahi wannan tuban na Zulai ban yarda da shi ba, ba haka kawai ba dole da wani nufin, masu iya magana suka ce kaji tsoron muguɓ da ya shiryu a lokaci ɗaya.”

Gwaggona tayi murmushi tace,

“To yanzu ya za’ai da shi?” “ajewa za’ai ace mata ana amfani da shi…ai baka saurin yarda da tuban mutumin da ka san can ba ƙaunarka yake ba.” Ni dai na fita na ɗauka abincin Yagana nayi gidanta, tafiya na ke tsigai tsigai kamar zan faɗi, na shigo lungun gidan naji takun tafiya ta bayana, da ina tafiya a hankali sai na daɗa saurin tafiyata akan wadda nake, duk da cewar ba a hankali nake tafiyar ba dama, amma dai dole na ƙara sauri kasancewar layin shiru ba kowa, tsab sai a yanka mutum ba’a sani ba.

Ta gefen ido nake bin gefena da kallo da son ganin wake biyoni haka saboda duk a tsorace nake, gani na ke kamar wani ne me shirin cutar dani, dan inda mai tafiyar kansa ne to da yanzu yaci ace ya kai ga inda zai je.
ina kawowa ƙofar gidan Yagana sai ganin mutum nayi ya sha gabana. “Mairo dan Allah tsaya ki saurareni.”

Kirjina ya buga saboda faruwar baƙon al’amari a gareni. na ɗaga kai na dube shi, Salmanu ne ɗan gidan Malam Liman, ɗan gayu kuma ɗan bokon garin bichi, saurayin da akayi shaidarsa akan kyawun ɗabi’unsa da nagartarsa a duk samarin bichi, saurayin kuma da ƴan matan birni da na ƙauye ke tururuwa akansa.

Na haɗiye wani yawu a maƙoshina sannan nace da shi, “Ina yini.” Bai amsa ba sai cewa da yay, “Ai ni ya kamata na miƙa gaisuwa ba ke ba.”

Nace da shi,”a’a ai ni ce ƙarama dan haka ka amsa kawai”. “to shikenan na amsa ina kuma godiya”. ya faɗa yana harɗe hannayensa a ƙirji. daga haka ba wanda ya sake cewa komai, shiru ya gimla a tsakaninmu na tsawon ƴan sakanni, sai ni ce na katse shirun da ce mishi,”da wani abu ne?”. ya kaɗa kai sannan yace,”a’a ba komai, nima na tsinci ƙafata ne da biyoki a san da idanuwana suka yi tozali da ke, shi ne zuciyata ta umarceni da na zama bafadanki”. ban ce komai ba dan ni wannan zancen nasa ban san ina ya dosa ba, saboda haka nasa kai na shige gidan Yagana, ina kuma jinsa yana cewa na gaisheta, ban dai tsaya sauraronsa.

Kafafuna na rawa na ƙarasa cikin gidan har bakina na harɗewa wajen yin sallama.
na nemi ƙaramin botikin fenti na ƙarfe na zauna. Yagana na daga can ƙasan rumfar da akayi mata kwanaki ta shan iska, da babban faranti a gabanta tana juye dubulan aciki tana ƴan waƙoƙinta irin na wacca gida yayi mata daɗi babu wani abu da ke damunta.

Sarai ta san da shigowata amma ta baiwa iska ajiyata, nima kuma na shareta kamar ban lura da ita ba, na nemi botiki na zauna akai, har san da ta kammala abunda take ta taso ta wuce ta gabana tayi ɗakinta, tana shiga kuma na miƙe nabi bayanta, da shigata na malale akan katifarta saboda yanda nake jin jikina kamar ba ruwa saboda rashin ƙwarinsa.

Can bacci ya fara ɗaukata salatin da Yagana ta zabga ya farkar dani a zabure, tafa hannu take tana faɗin,

“Kai jama’a ni Rakiya yau na gamu da gamona. yanzu ke wannan abar yaushe kika shigo min gida?, ni dai Rakiya inda raina nata ganin abunda ke neman fin ƙarfina akan jikokin da buwayi gagara misali ya bani…yanzu banda abunki Mairo ai sai kiyi sallama da za ki shigo na san da wani ran bayan ni, to inma ciwon baki kike ai kya min alama, amma haka kwatsam sai na tsinceki shememe akan shimfiɗata kamar gawa.

Ba kiji yanda na tsorata na firgice ba ca nake ma gamo nayi, Allah kayi min magani amma dai magana ta gaskiya kam an shiga da hakkina”. takaici bai barni nace mata komai ba naja guntun tsaki na koma nai kwanciyata. “tsaka ma da tayi tsaki ga yanda aka maida ita nan balle ke, idan halin ƙwarai ne kici gaba da yi.

Ni dai wallahi har nayi tashen ƴan matancina ban raina na gaba dani ba…kuma Adamun zai zo ya sameni naji idan shi ya ɗaure muku gindin yi min irin haka.

Ke ni banma san san da kika sauya daga mutuniyar kirki ba, da babu ruwanki gwanin sha’awa amma yanzu nema kike ki fanɗare.” Na katse mitar tata da cewa,”wai sallamar da nayi a wani sashin jikin naki ta sauka da kunnenki ya gagara jina?”

Ta juyo daga fitar da zatai cikin girmama zancena ta ce, “sallama?, aina?, to ni kam ban san kinyi ba. tun da nake zaune a tsakar gidan nan banga shigowar wani bil’adama ba da yay sallama ba, kinga fa da ilimina na san darajar sallama. kawai ke dai ki bar borin kunya kice biki yi ba, to na yafe miki a wuce wurin, amma kya ƙyala min sharrin naji naƙi amsawa, salon kija a rubuta min zunubi”. saboda a zauna lafiya na huta da jarabatarta nace,”to kiyi haƙuri”

Tace,”to shi ne zance amma yarinya kya tsaya yi min musu bayan kin san kece da rashin gaskiya”. “kai Yagana nace kiyi haƙuri”. sai kuma ta kuma ɗaga murya daga sassautata ɗin da tayi, “to wai da ban haƙura ba kya ga na barki kici gaba da zamar min a gida alhalin kin shigo babu sallama kamar wadda ta shiga gidan kafirai.

Kiyi adu’a kawai Allah ya yafe miki”. ban sake ce mata komai ba na maida murfin idona na rufe, naji da abunda ke damuna ma kaɗai ya isheni balle wannan mitartata me hawa kai.
Yagana na fitowa tsakar gida taci karo da awaki akan kwanon abincinta, daga inda take taja tayi turus, tayi salati da sallallami ta riƙe haɓa da cewar,”kai yau naga abunda ya isheni bai ishi ubangijina ba. yanzu dama Mairo abinci kika kawo min shi ne kika barwa awaki anan saboda mugunta, anya kuwa yarinyar nan ba ki gamu da aljanun tunbotsai ba, dan wallah al’amarin naki kuma ya fara bani tsoro.

Da ma ni tunda kika ce min kin fara gane-gane na fara sarewa da sabbin halayenki da nake gani. to lallai dole na koma wurin Malam Kabiru dan ban yarda ke bace da kanki, Adamu yazo ai ƙoƙarin magance lamarin tunda aka fara da haka wataran za’a iya faɗowa a rufeni da duka a rasa me ƙwatata gida daga ni sai halina…Allah dai ya saka min”. ta ƙarasa tana kore awakin daga kan abinci, ta ɗauki kwanon tana sake sabuwar masifa akan yanzu harda nama acikin abincin amma Mairo ta salwantar mata da shi, to kanta ta yiwa ba ita ba, tunda Uwarta ce ta girka abinci kuma taja mata asarar albarkarta.


Har ta gama gyaran tsakar gidan bata daina mita ba, shaf ta manta ma da batun Mairo a gidan sai da ta koma ɗaki, tana ganinta kuma mita sabuwa ta ɓarke, sababi iri-iri, faɗi take,”ni ai da kika san aiken dole Suwaibar tayi miki da kika zo ƙofar gidan sai ki aiko yaro yay sallama dani na karɓi abuna, amma fisabilillahi sai ki shigo ki zauna min akan sabon botikin da Mujibu ya siyo min, abu ko sati biyu bai yi ba kin fasa min shi, haka kwanaki kika min sanadin robata sabuwa fil”. nace,”yanzu Yagana ni ina naga mazaunin da zan fasa wannan botikin me ƙwari, kawai salon kija min faɗa wurin Baba Mujibu”. ta nuno min botikin tana faɗin,”yo ina zancen jan faɗa, ki gani da idonki mana ki san ba ƙarya nayi miki ba…ni da za ku gane ma ku bar zuwar min gida gaskiya, yarana ba arziƙi garesu ba su na ƙoƙarinsu wajen ganin sun wadatani da abubuwan buƙataduk dan kar naje yawon aro, amma ku dai Ƴaƴan Adamu sai dai idan baku zo min gida ba…to zan faɗawa uwar kowa kar wacce ta ƙara aiko min ɗanta gwara ake aiko almajiri ina bashi sadaƙa, ko in taka inje da ƙafata, haka ɗazu yarinyar nan Zubaida daga zuwa wanke-wanke omon ɗari da ashirin taga bayanshi a kwanuka uku.”

Ni dai duk abunda take ina jinta ban tankata ba amma har ga Allah ta isheni, a zuciyata ina jin kamar na miƙe na ɗaure mata baki irin yanda Sadiya da Sunusi suka yi mata kwanaki, ta ishesu da masifar sun shigar mata ɗaki babu izini, su ko suka ɗaure mata baki da hannu har sanda Allah ya kawoni na kunceta.

“Mairo ki dage kiyi karatun boko don kankin kanki ba kamar yanda wasu suke yi ba dan ace sun yi”. maganar ta haska acikin kwanyar kaina, furucin da mutane uku suka yi min shi a ranaku daban daban, Baba yay min, Gwaggona tayi min, haka Ya Kabiru a randa zai tafi furucin da ya fara yi min kenan, kaina a ɗaure yake tun a ranar dalilin kasancewar furucin iri ɗaya da yanda Baba da Gwaggo suka faɗa babu sauyi. taya akai furucin na su yazo iri ɗaya?, me yasa su ke cewa nayi karatu saboda kaina ɗaya?, na rasa gano amsar taƙamaimai. na buɗe lumsassun idanuna na dubi Yagana, ita dai sam bakinta ba ya shiru, idan ba ta waƙa to tana mita, ko da yake tace ita ko ya ta rufe baki bata magantu ba to idan ta buɗe sai taji bakin ya buga, dan haka bata ga dalilin da zai sa ta dinƙa rufe baki ba haka kawai bayan Allah ya tsaga mata shi dan tayi magana.

“Yagana dan Allah ni kam ku barni na tafi makaranta tunda naji sauƙi haka”. ta kalleni tace,”kin san mun san ciwonki saɓanin ke da baki sani ba, saboda haka ki cire ran tafiya makaranta nan kusa muddin ba warwarewa kika yi gaba ɗaya ba.”

Na miƙe zaune kamar zansa kuka na shiga roƙonta Allah da Annabi amma ƙarshe matar nan sai tasa auduga ta toshe kunne wai lokacin saka maganin ciwon kunnenta yayi alhalin kawai dan ta gaji da roƙona ne, haushi ya ƙumeni, banda ina sonta ina tausayinta da sai nace Allah yasa ciwon kunnen ya kamata tunda shi take fata.

Na ƙaraci kumburina da kukana na miƙe na fita na iyo alwala. gefin magariba muna hira da Yagana, rabin hankalina na kanta rabi na kan dubulan ɗin dana gaji da haɗiyar yawu akansa, wanda a dalilinsa ne akaƙi kulani ɗazu aka kuma fake da cewar ba’a san na shigo ba har ana ɗora min laifin rashin sallama saboda kar a bani. ga labarin da take bani akan wani tsohon bazawarinta na neman ƙullar min da ciki saboda dariya, wai ita tsabar ta iya yiwa maza shagwaɓa har kukan jarirai take yi.

Ina ta dariya na miƙe na shiga uwar ɗakinta, ina ƙara tunzurata da labarin, laluben inda ta ɓoye dubulan ɗin nake amma na rasa, ban san da cewar kwanukan dana taɓa basu zauna da kyau ba a ma’ajiyarsu , sai jin ƙarar murfi nayi ya faɗo ƙasa, ai ban kai ga runtse ido ba Yagana ta rafko sallallami,” Allah yasa ba ɓari kika min ba.” Nace, “ɓari sai kace bana gani, kwanukan da kika jera ne ba’a dai-dai ba suka rikito.”

“Umm to ya zanyi yarinyar nan ce Zubaida da bata iya aikin kirki ba, gyara minsu dan Allah…amma kiyi a hankali akwai ajiyar mutane a wurin kar ki ɓata”. nayi gajeriyar dariya, Yagana ikon Allah, wai ajiyar mutane tama maidani wata ƙaramar yarinya.

A can ƙarƙashin kayan wankinta na ɗauko kwanon dubulan ɗin ta ɓoye shi. “me kike yi aciki ne na jiki shiru?, karfa kiga kayan mutane ki taɓa, ajiya aka bani kayan ƙawata ne Hajiya Fatsima.”

“Babu abunda na ke taɓa miki Yagana ke dai ci gaba da bani labari ina jinki”. nace da ita yayin da nake cika bakina da shi. taci gaba da ce min,”yanzu kinga shi Amadu duk wadda ta aure shi sai ta kamu da hawan jini saboda rashin maganarsa da sakin fuska. shi kuma Kabiru duk wadda ta aure shi ciwon zuciya farat ɗaya zai kamata saboda kishin mata da za su ke rububi akan mijinta…Allah na tuba ance babu kyau amma wannan yaro yanda kika san shi yayi kansa, a gidansa dai aljanun ƴaƴa na kyau za’a ke haifa”. tana ta labarinta ina ta kai dubulan baki, taji shiru ta kira sunana na amsa. “au na ji kinyi shiru.”

“Ba komai ina jinki ci gaba, ina linke miki kaya ne.” Bata dai yarda dani ba sai da ta shigo, tana shigowa kuwa ina naɗar wani ina ƙullewa a leda, mu ka haɗa ido na basar.

“Amma ke kuwa da jan magana kike, ke idan baki taɓa abunda ba naki ba sam ba kya jin daɗi. dubulan ɗin nan fa ba wani yawa gare shi ba aka kawo min kina gani bai fi nayi masa ci ɗaya ba, amma ba za ki barni da shi ba kin tasa a gaba kina neman ganin bayansa.”

“Au ashe naki ne?” “Nawa ne mana ɗazu Saratu tayo min aikensa, ni ban fiya so akesa min ido akan abuna ba wallahi”. ina ƙunshe dariyata nace,”kuma da kika ce ba naki bane”. bata bani amsa ba ganin ba cin hankali nake masa ba, tayo kaina na miƙe na fice da gudu, ta hau sababin ita shi yasa bata so idan nazo na shigo mata ɗaki saboda ni da ɓera halinmu ɗaya.

Muna zaune can tace da ni,”ke ɗazu da kika shigo fa ina kallonki kamar a firgice kike, me ya faru?, naƙi bi ta kanki ne gudun kar ki ce sammin”. nace mata,”Salmanu ne ɗan gidan Liman ya biyoni.”

Ta saki baki tana dubana, “to shi ne kuma sai akayi ƙaƙa?”. nace mata,”ni ban san me zan masa, ya dai ce na gaisheki” Tace,”to Allah yasa biki rashin hankali ba dan nasan halinki.”

Ina ɓata rai nace, “Rashin hankalin me kuma Yagana?”. “akwai wani rashin hankali da ya wuce kiƙi sauraronsa, ke kin san yanda manyan mutane keji da yaron nan a garin nan kuwa, kika same shi ai ba ƙaramin auna arziƙi kika yi ba, wallahi abun sam barka ne wannan yaron ya shiga cikin zuri’arka.”

Da mamaki na ke dubanta nace,”to wai ke Yagana ce miki akai yace yana sona?, kawai fa ce yayi ya rakoni saboda yaga layin ba kowa.” Naga ta ɗaga hannu sama taiwa Allah godiya, na tambayeta mene tace ba komai, kamin ta ce min,

“Jiya jiya Kakarsa ta gama yi min ƙorafin Salmanu yaƙi sauraron wata mace, abun duk damunsu yake su na ganin kamar ko bai da lafiya ne, ga shekaru su na ta ja. tace har gidan ƴan’uwansu akai kai shi gidan kyawawan ƴan mata ko zaiga wacce tayi masa amma yaron nan sai ce yayi shi baiga ma mace ko ɗaya a gidan ba. Allah sarki ashe rabon akan Mairona yake.”

Tai zancen tana janyoni jikinta sannan taci gaba da cewa, “idan ku ka ƙara haɗuwa ya tsaida ke ki tsaya ki saurare shi dan Allah, muddin kika samu yace zai aureki to wallahi Allah ya taimakeki, dan kin samu mijin kerewa sa’a”. ni kam na gaji da jin zancen nata, dan haka na taƙaita shi,”to Yagana naji, insha’Allahu zan saurare shi ɗin naji batunsa”. “yauwa to Allah yayi miki albarka, wallahi tallahi Mairo ina sonki, kaf cikin jikokina albarka, Allah ma shaidata ne”. nace,”nima Yagana ina sonki”.
ban bar gidan Yagana ba sai da akayi sallar isha lokacin ƙarfe takwas da mintuna, babu yanda Yagana bata yi dani ba akan na kwana naƙi nace ni gida zan tafi, tace to nafi ɗin tunda cinyeni zata yi cikin dare. nace mata,”ni bance ba, inda dai zata bani dubulan to zan kwana”. baiwar Allah haka kuwa ta tashi ta ɗauko min kwanon gaba ɗaya tace gashi na cinye dama tunda aka kawo ni ta ajewa saboda ta san ina sonsa, na karɓa nayi godiya nace amma fa duk da haka ni tafiya zanyi ba zan kwana ba na sauya shawara. “Mu kwan lafiya Yagana, gobe ba zaki ganni ba sai mun dawo daga asibiti”. tai min shiru kamar bada ita nake ba. sai da zan fito sannan tace,”ai gwara ki tafi ni dama ba jin daɗin zamanki nake ba, tunda ke hannun ta’adi gareki…shi yasa ɗazu ko da kika shigo ina sane na baiwa banza ajiyarki saboda shegen kwaɗayinki, ki gani ba za ki iya kauda kai ba sai roƙa”.
tafiya nake sauri-sauri gudu dudu duk a tsorace saboda yanda garin yayi shiru, baka jin komai sai kukan tsintsaye a sararin samaniyar subhana, ko hasken farin wata ma babu kasancewar ana hazo, faran-faran nake jefa ƙafafuna burina bai wuce naji na isa gida ba.
na waiga hagu da damana naga babu kowa sai ni kaɗai sai kuma kukan karnuka daga can nesa, hakan yasa na ɗage zanina na arta ana kare, gudun da kona minti biyu banyi na nayi tuntuɓe jina kake a ƙasa tim na kifa, kafin na yunƙura na ɗago naji an toshe min hanci da baki an ɗagoni an sureni sai cikin mota.


Matuƙin motar ya bawa motar wuta da gudun gaske suka bar unguwar, ni dai ƙwala ihu nake ina neman ɗauki sai dai babu mai iya jina, dan duk motar a zuge take da glashi. “Babana, Innata, Gwaggona, Yagana”. sunayen da nake ta kwaɗawa kira kenan cikin ihun murya dana tabbatar dai saceni aka yi. wanda ke gaban mota ya waigo ya saita goshina da bindiga yana cewa,”ko ki mana shiru ko kuma na ɓula kanki”. cikin dakiya da tsiwa nace masa,”ba za’a yi shirun ba, idan ka fasa kuma kai ba ɗan halak bane…wallah ni dai ku barni ko na tara muku jama’a”.

Na kusa dani ya shaƙi wuyana iyakar shaƙa yace, “oh bakinki ba ya mutuwa kenan, oga harbeta”. da naga da gaske mutumin harbeni zai yi jiki na ɓari na runtse ido na shiga bashi haƙuri, daga haka naja baki na gimtse sai shashsheƙar kukana da ke tashi ƙasa-ƙasa. babu yanda ba suyi dani ba akan nayi musu shiru naƙi, mai tuƙin yace, “ku sumarta kawai”. ina kallo na gaban ya kuma waigowa ya baɗo min hoda, take ganina ya ɗauke gaba ɗaya, shi ma jin nawa nema nake na rasa shi gaba ɗaya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrin Boye 16Sirrin Boye 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×