Skip to content
Part 19 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Hankalin Gwaggo da Kulu a tashe yake matuƙa, dukansu sun kasa samun stability, sam sun kasa yarda Mairo ta ɓata ɓat, har gwara Kulu ma na iya jurewa, amma Gwaggo kuwa tun da rana ta faɗi ya tabbata babu Mairo babu dalilinta, shikenan ta yanke jiki ta faɗi, shikenan duk wani budget nata akan Mairo ya rushe, nan da nan aka ɗauketa zuwa asibiti, kuma a lokacin ne Kulu ta fito dan ta sulale ta gudu amma halin da Gwaggon ke ciki yasa dole ta janye ƙudurinta domin idan tayi hakan tayi butulci, daga ita sai Inna Zulai aka bari a gida, bata da aikin komai sai share hawaye lokaci zuwa lokaci.

Gwaggo ce kwance kan gadon asibiti, a kallo ɗaya zaka gane fitar hayyacin da tai, amma dai for now ta fara regaining conciousness, likita ya shigo ya auna BP ɗinta sannan ya kalli Malam yace,”to Alhamdulillah jininta ya sauka, zuwa Magrib zamu iya sallamarku sai dai a kula dan Allah wajen kiyaye damuwarta, and then da shan magani in time saboda gaskiya lafiyarta na cikin haɗari.” Malam ya ɗaga masa kai da cewar,”tom za’a kula…sannu da ƙoƙari”.

zuwa Yamma aka sallamesu suka koma gida, tun bayan dawowarsu kuma gida ya ɗinke da jama’a sai shige da fice suke ana jaje kamar gidan mutuwa, da waɗanda su ka zo jaje tun ranar farko da masu dawowa yanzu dan duba jikin Gwaggo sai gidan ya zama babu matsaka tsinke. Yagana duk wanda yay mata jaje bata iya cewa da shi komai sai kallo da ido, bini-bini kuma sai ta sa gefen mayafi ta matse ƙwalla. Matar Liman tazo ana gaggaisawa ta tambaya ko waɗanda su kai garkuwar da ita sun kira waya?, Amarya tace da ita,”ai Hajiya babu lallai Kidnappers ne tun da har yanzu babu wani saƙo ta waya, munfi tunanin ko ƴan yankan kaine suka saceta, yanzu kwanciyar hankalinmu ma bai wuce ace ko gawarta ne a gani ba zamu fi samun nutsuwar ruhi”

Hajiya Saratu ta girgiza kai cikin jimanta al’amarin,”to ubangiji dai shi ya san a halin da yarinyar nan ke ciki. Allah yasa ta faɗa hannu na gari…in Allah ya yarda za’aita adu’a dan yanzu haka ma tun jiya Malam yasa almajirai suka sauke mata alƙur’ani”. Yagana ta face majina cikin muryar kuka tace,”ai duk wanda ya ɗauke yarinyar ba zai gama da duniya lafiya ba, kuma sai Allah ya isar mana tsakaninmu da shi…fatanmu Allah ya tsareta ya kareta a duk hannun da ta faɗa”.

wata cikin ƴan jajen tace,”kwanaki mu ma fa haka akayi a layinmu, daga fitowar yaro da daddare ke tun ana zuba ido ana saka ran zai dawo shiru har yanzu kusan wata biyu kenan, iyayenma sun cire rai da shi tun da babu irin neman da ba’ai ba, cigiya har gidan talabijin”. Marka me koko tace,”ai waɗan nan azzalumai Allah dai yay mana maganinsu shi ne adu’a kawai”.

Sunusi ya shigo rungume da buhun shinkafa, Lukman na biye da shi ɗauke da kwalin taliya biyu da na makaroni ɗaya, sai ga Mu’azzam shi ma ya shigo da galan ɗin manja. kafin Amadu ya mara musu baya bakinsa ɗauke da sallama, sai dai kana ganinsa kaga wanda ke ɗauke da matsananciyar damuwa, a tsaitsaye ya gaida jama’ar da ke tsakar gidan sannan ya wuce ɗakin Gwaggo. kishingiɗe jikin pillow ya taddata, ya ƙarasa gabanta ya zauna, har tsawon wasu daƙiƙu bai ce komai ba sannan ya buɗe baki kamar mai shirin yin kuka yace,”sannu Gwaggo, Allah ya ba ki lafiya”. ta amsa da,”amin

Amadu, ashe kana tafe”. “ehh da yake ma tafiyar  mota ce shi yasa na makara”. Sai Gwaggo ta fashe da kuka,”Mairo dai ta ɓata, ban san a wani hali take ciki ba yanzu”. yay saurin kawar da fuskarsa dan ba ya son ganin hawayenta, ya lumshe idanunsa da su kai jazur ya buɗe kana yace,”su da ba fita suke ba dan ubanta gidan uwarwa taje a ranar?”

Yay tambayar a zafafe. Gwaggo na goge hawaye tace da shi,”to ai ita kasan bata rabo da gidan Yagana, laifinma dai nawa ne kuma duk da haka Allah ya riga ya shirya faruwar hakan, kuma ita Yagana tace lafiya lau su kai sallama da ita ta wuto gida, to ƙarshe sai da safe da ana laluben hanya aka tsinci ledar dubulan ɗin da ta bata a hanya, ananne ma aka tabbatar ɗauketa akayi”. yana huci yace,”ni dama gidan Yagana ba son zuwanta na ke ba tunda ba wani iya kula da ita za tai ba…ita ma shashasha da ta ga daren yayi ai sai ta haƙura ta kwana acan”

Gwaggo tace,”ko ɗaya ba laifin Yagana bane kasan Mairo ma da shegen taurin kai, kaifi ɗaya ce”. “duk da haka akwai laifin Yaganar”. Yagana ta faɗo ɗakin tana matse ƙwalla ta hau sababin,”yo ni dama tunda akace min zaka zo garin nan na sallama babu wanda zaka ɗorawa alhakin ɓatanta sai ni, to ni dai sai dai nace Allah ya saka min tunda yana ji yana kuma gani, ai kowa shaida ne ina ƙaunar Mairo, ta ya za’ai nasa a saceta, me ta tare min, kuma ni wallahi ma bani da wannan matacciyar zuciyar da zansa hannu a cutar da rai”

Tunda ta fara maganar Amadu ke kallonta, har kuma ta gama bai ce mata ƙala ba, sai da ta gama sharar hawaye sannan ta dube shi da cewar,”yanzu kuwa ɗan nan ba zaka nemi yafiyata ba?”. ko kallonta bai ba ya miƙe yana zura hannu a aljihun wando, ya zaro ƴan ɗari biyar guda shida ya miƙawa Gwaggo, ta amsa tana saka masa albarka. “yanzu ina zaka je? da kayi zamanka anan ka huta kai da kasha hanya”. “Gwaggo zanje asa cigiyarta ne a gidajen radio, idan nace zan zauna babu lokaci kwana ɗaya ne aka bani a wurin aiki”. “tom shikenan sai ka dawo…Allah ya bada sa’a yasa a dace”.

Yasa kai zai fita Yagana tace,”ni dai dama bance ka ban silanka ba balle ka dinga hararata har kana neman bigeni, ɓatan Mairo shi ya dameni ba karɓan kuɗinka ba”. He is not in the mood ɗin da zai tsaya bata amsa amma duk da haka dai ta ba shi dariya, sai ya gimtse kawai ya wuce ɗakin mahaifiyarsa.

Ganinsa yasa Inna Zulai ta rasa inda zata tsoma ranta dan daɗi saboda yanda ɗanta ya sauya cikin watannin da basu haura biyar ba. ji take kamar ta maida shi cikinta, sauyin weather yasa yayi wani looking fresh, shaddar da ke jikinsa kanta ba ƙarama bace ga wata makekiyar waya da yake riƙe da ita a hannu, cikar haibarsa ta ƙara fitowa, kana ganinsa kaga wanda kuɗi suka soma zaunar masa. ta kamo hannunsa ta zaunar da shi bakin gado tana yi masa sannu da zuwa, shi ma kuma anasa ɓangaren yana ta farin ciki da ganin mahaifiyarsa.

Ta ɗebo ruwan sanyi a randa ta kawo masa ya sha, suka zauna su na hira duk da cewar shi ɗin dai ƙarfin hali yake amma hankalinsa ba ya kwata-kwata. yana dubanta yace,”Inna ya na ganki ke kina cikin ɗaki ga jama’a kuma a waje”. fuskarta na nuna damuwa tace,”to kasan halin Kakarka ai, naga tana neman ɓatan raine shi ne nayo ɗaka kamin zuciyoyinmu ni da ita su huce”. ya miƙe tsaye yana faɗin,”Allah ya kyauta”. sannan ya zaro dubu biyar ya bata, ya kuma shaida mata zai je kano asa cigiyar Mairo a radio, ta bishi da adu’a da fatan nasara. yana jin Yagana san da zai fita tana faɗin,”miskili kawai”.

*****
Yau kwanan su Mairo biyar a hannun kidnappers, kullum kuma sau ɗaya ne ake kawo musu abinci shi ma biredi ne da zuma za su tsoma suci, daga nan sai washe gari su da ƙara ganin wani abincin, sai uban ruwa da ake ɗirka musu, bayin Allah duk har sun saba da hakan.

Mairo dai gaba ɗaya tafi kowa lalacewa saboda yanda taga anata ɗaɗewa ana barinta, wasu an biya kuɗin fansarsu wasu kuma an gaji da ajiye su ne sai a siyar, ko kuma dan rashin imani sai a kashe su.

Matar da ta saba da ita ƴan’uwanta sun zo sun fansheta, shi yasa bata jin daɗin wurin gaba ɗaya, ita yanzu jira take kawai su kasheta ta huta, domin ta jima da sallamewa da rayuwa tun a sanda taji adadin kuɗin da za a bayar kafin a bayar da ita, da ma ita tasan bata da me biyan wannan kuɗin, dan kaf danginsu babu me shi, yanzu tashin hankalin da aka sasu aciki ma sa iya cinye kuɗin a magani.

La’asar ɗin yau su na zaune aka banko ƙofar ɗakinsu, su ka zabura suka zubawa ƙofar ido, in da sabo yaci ace sun saba da su to amma sanin cewar basa shigowa su fita ba su kashe rai ba yasa basa samun nutsuwa da zuwansu, kuma yau dan mugunta ma ko abinci har yanzu ba’a basu ba.

Su uku ne su ka shiga su na saita kan bindiga, a tsorace kowa ya dinga ja da baya musamman Mairo da ke daga bakin ƙofa. Ogansu ya nuna wani Dattijo ya manyanta sosai yace,”taso”. sannan ya kalli Mairo yace,”ke kuma ki shirya”. sannan su ka fice tare da wancan mutumin. manyan mutanen da duk suka san nufin maganarsa akan Mairo sai su ka fara hawaye. ta kalli wata sabuwar mata da aka kawo jiya da ta fara sabawa da ita tace,”Yaya ina za su kaini?”. ta rungumeta tace,”nima ban sani ba”. hankalinsu ya karkata kan wani mutum da ya kalli gabas ya ɗaga hannu yana adu’a, “ubangiji Allah ka dubi wannan yarinya ka ceceta daga hannun azzaluman nan, Allah kar ka basu ikon keta mata haddi.”

Ya duƙar da kai tare da fashewa da kuka. kamin su ƙara motsi aka kuma banko ƙofa, wanda ya shigo ya kalli Mairo acikin kaushin murya yace,”taso muje”. jikinta ya hau rawa saboda tsoro, ta ƙundundune jiki tana kuka tana ba shi haƙuri, uwar tsawar da ya sakar mata yasa ta gimtse baki, ya ƙaraso ciki ya figo hannunta su kai ƙofa, mutumin nan da ke ta bin Mairo da kallo yana jin inama ace yana da damar da zai ƙwaceta yace,”dan Allah ku tausaya mata yarinya ce ita…ku ƙara haƙuri iyayenta za su zo su fansheta amma karku lalata rayuwarta.”

Wani mugun kallo ya juyo yaywa mutumin yana kai sigari bakinsa ya zuƙa, ya saki ƙwafa ya juya za su ƙarasa fita mutumin ya ƙara cewa,”Ƴata kiyi ta ambaton Allah cikin hukuncinsa da ikonsa za ki kuɓuta insha’Allah”. yana rufe baki mutumin ya saita ƙirjinsa ya ba shi harbin bindiga take ya mutu, shi kuma yaja Mairo da ke turjewa ya fita.

Cikin wata rumfa da suka kafa na leda ya nufa da ita, yana zuwa ya tankaɗata ciki tare da cewar,”Oga gata nan a huta lafiya”. tsohon ya taso ya nufo gareta fuska babu annuri, yay tsaye kanta yace da ita,”tuɓe”. ya faɗa murya a ɗage. take sabbin hawaye suka shiga kwaranyowa Mairo, tsoro ya ƙara ninkuwa a zuciyarta, tana girgoza masa kai tana faɗin,”a’a”. yasa ƙafa ya take mata ƙafa cikin kakkausar murya ya kuma ce mata,”kamin naje na dawo ki tabbatar da kin tuɓe idan ba haka ba kuma zan kasheki.”

Ta rumtse ido ta buɗe kafin ta sami ƙwarin giwar ce masa,”Ya Kabiruna ya faɗa min abun da kake neman yi ba shi da kyau cin zarafin ƴa mace ne ubangiji ya haramta…”.bata ida zancen ba yasa bakin bindiga ya gwaɓe bakin nata nan take ya fashe. “wannan ɗan ƙaramin wa’azin naki babu amfanin da zai yi anan dan haka ki rufe min baki, kiyi abunda kawai nace.”

“Sai dai ka kasheni amma ba zanyi abunda kake so ba”. ya jinjina kai sannan ya daki tsakiyar kanta da gindin bindigar, ta saki wata ƙara,”ba za ki gane abunda nake nufi ba saina dawo na sameki a yanda na barki”. yace da ita tukunna ya miƙe yasa kai ya fita ya barta da ruzgar sabon kuka, tare da neman tallafin ubangiji.

“Bana tunanin akwai wani abun cutarwa da zai riskeki ki kasa guje masa saboda ke ɗin ƴar baiwa ce. ba wannan macijin da kika gani kaɗai ba, har mutum sai kin so zai ya cutar da ke, dan haka duk sanda wani abu mara kyau ya riskoki ki ambaci Allah sannan kuma kiyi kamar yanda na faɗa miki.”

Wannan Kalaman na Kulu suka haska a cikin kaina a wannan lokaci, dan haka ban tsaya wani aune-aune da tunani ba na dunƙule hannayena tare da rumtse ido tsam. tsohon ya dawo daga shi sai sauran gajeran wandon da ya rage masa yana ƙoƙarin cire shi. sa’annan na buɗe idanuna na watsa su cikin nasa, sauyin launin da ya gani a ƙwayar idon nawa yasa shi razana yaja da baya, sai kuma ya dake ya ƙara tamkewa yana dawowa zuwa ciki, a lokacin na buɗe tafin hannuna da ya jima a damƙe aikuwa nan take wani abun mamaki da alajabi ya bayyana wanda ni kaina sai da na tsorata.

Kunamu ne manya kamar su na fitowa ne daga cikin jikina, sai dai ba daga jikin nawa su ke fitowa ba, nan da nan kuma suka cika ɗakin kamar a rumbunsu, gaba ɗaya sai suka yi kan mutumin kamin ya farga daga guduwar da yake so yayi tuni sun haye masa jiki, ya fara ihu tare da kiran sunan ƴan’uwan nasa akan su zo su taimake shi, wanda ke gadinsa a baƙin ƙofa shi ɗaya ya iya jin ihunsa, dan haka ya shigo ciki a guje, sai dai abunda idonsa yay tozali da shi yasa ya dakata yana jefawa Ogan tambayar meke faruwa. cikin tsananin azabar da yake ciki yay masa nuni da Mairo wadda ke rakuɓe daga jikin bango tsoro duk ya gama cikata,

“Ku fita da ita ba mutum bace…wayyo Allah ku nemo maganin kunama karsu ƙarasa kasheni”. Yaron yace,”to Oga”. ya juya da sauri ya fice ya zagaya ta baya, ya zuge rigar rumfar ta ɗaya ɓarin ya janyo Mairo waje da lallaɓawa yana faɗin ta ɓace musu da gani, sannan ya zuge rigar rumfar duka wai ko da hasken rana zai sa Kunamun su koma inda suka fito ko kuma su mutu, amma ga mamakinsa sai ya ƙara ganin su na sake shigewa jikin mutumin shi kuma yana ihun harbin da suke masa. sauran abokan harƙallar suka yo kansa anata ƙoƙarin ganin an janye shi daga cikin kunamun amma babu hali, ni kuwa a wannan lokacin ba zan iya kwatanta tashin hankalin da nake a ciki ba, dudduba ko’ina nake a jikina, domin gani nake na zama matsafiya, na durƙushe na fasa gunjin kuka dan a ganina idan mutumin can ya mutu to alhakin kisansa na kaina, bayan kuma ni ban san ta ya akai kunamun ma suka fito ba, ni dai nayi abin da Kulu kawai tace mun.

Ina duƙen ina faɗin Allah ka yafe min sai naji an janyo hannuna, mutanen da aka yi kidnapping ne duk suka sami daman fitowa saboda babu attention ɗin wani security akansu, hankulansu yayi kan Ogansu da ganin ta yanda za’ai su kuɓutar da shi daga kunamun da suka cika ɗakin.

“zo mu tsira da ranmu”. Matar da ke riƙe da hannuna ta faɗa tana jana ni kuma ina turjewa, kai nake girgizawa ina faɗa mata,”Ki tsaya a cire masa wancan kunamar ni ban san ya akai tazo ba”. Matar bata saurare ni ba ta ƙara figata ganin sauran mutanen na neman tsere mana. duk yanda naso na ƙwace kaina daga hannun matar amma na kasa, ƙarshema mutum biyu suka haɗar min suka jani ta ƙarfin bala’i. haka muka nausa jeji muna ta gudu, babu hanklin kowa da ya kawo kanmu sai daga baya ne muka fara harbin bindigu. mun yi nisa sosai muka ji wasu na bayanmu na faɗar an yi nasarar harbar ƴan can bayanmu.

Munyi gudun kusan awa sannan aka fara rarrabewa kowa na ta kansa. ni kaɗai na fito titi ina tangal tangal ina haki, idanuna ko gani basa yi bare na san inda nake jefa ƙafata. nayi nisan tafiya ina yiwa kaina jagora, ƙafafuna kuwa sai zubda jini suke saboda irin abubuwan da na taka kasancewar babu takalmi a ƙafata, ga raɗadin zafin da ƙafar keyi min, ga ban san a inda zan iya tsayawa ba bare na zauna na huta, haka dai na shiga lalube da hannu har na kai ga wata bishiya na taɓota, na sauke ajiyar zuciya nauyayya na jingina da jikin bishiyar sannan naja jiki na sulale na zauna ƙasa. babu abunda nake buƙata a wannan lokacin irin ruwa, maƙogarona ya bushe yawun bakina ya ƙafe.

Cikin azama na miƙe naci gaba da tafiya a wahalce dan ban manta da maganar mutanen da muka gudo tare ba su na jadadda min akan kar na tsaya ko hutawa sai na tabbatar da na kawo inda mutane su ke, ba su san da cewar ji kawai nake ba amma ganin Mairo ya ɗauke tuni, kuma ganin ana cikin nafsi-nafsi yasa ban faɗa musu a halin da nake ciki ba, illa godiya da nai musu na kamo hanya har Allah ya fito dani, ban san ko ina ne ba nan ɗin, sai dai na kanji kamar sautin gimlawar ɗai-ɗaikun motoci.
a san da naji na ɗora ƙafata bisa kwalta, daga gefe naji an hankaɗani nayi sama na faɗo ƙasa tim. cikin kwakwazo na tsala ƙara, Kafin na samu damar yin wani tunani akan abin da ya sameni ko neman taimako sai naji duk jikina yay collapse, idanuna sun rufe da kansu, sannu a hankali kuma na ɗauke wuta gaba ɗaya kamar zarar rai.

Duk yanda mai motar ya kai maƙura wajen taka burkin motar tasa dan ganin ya kaucewa Mairo abun ya faskara. yasa duka hannu biyu ya doki stearing tare da kifa goshinsa akai. yay shiru kamar ba zai ɗago ba, can ya shiga ɗago da kansa a hankali yaja dogon numfashi ya furta,”help me Jesus”. muryar tasa ta fita acikin wani irin amo, sannan ya ɗago ya dubi Mairo da ya buge sheme ƙasa jini na malala, da hanzari ya buɗe motar ya fita ya ƙarasa gareta da sassarfa ya ɗago kanta, bakinsa motsi kawai yake amma ya kasa cewa komai sai bin jikinta yake da kallo da kuma jinin da ke zuba daga kanta. ya ruɗe, ya rikice, ya dabarbarce ya rasa abun da ya dace yayi, sai yaji kawai ruwan hawaye sun cika masa ido, ya janyota zuwa saman cinyarsa yana tattaɓa fuskarta, “Girl, Girl open your eyes.”

A sama-sama take jin maganarsa, sai dai sam bata fahimtar me yake cewa, ta buɗe lumsassun idanuwanta ta zuba ƙwayar idonta akansa tamkar tana ganinsa, sai kuma ta mayar ta rufe, numfashinta na up and down, da murya can ƙasa tace,”ruwa”. bai ji me tace ba dan haka ya kai kunnensa saitin bakinta yana cewa,”say it clearly i can’t hear you well”. ba dan taji me yace ba sai dai ta ƙara maimaitawa dan a yanzu babu abun da take buƙata sama da ruwan, Daga haka bata sake sanin komai ba jikinta ya saki gaba ɗaya. nan take Emanuel ya kuma ruɗewa, kun san inyamuri da tsoro, gani yake da ya miƙe da ita mutane zasu yi masa caa aka duk da hanyar ba hanya ce ta jamaa ba, babban tashin hankalinsa ma kar yarinyar ta mutu.

Ya ɗaukota jini duk ya wanke mata fuska, ya buɗe bayan mota ya zirata aciki, hannunta ya faɗi akan ƙirjinsa ta damƙo sarƙar cross ɗin da ke wuyansa ta tsinko. ya dubi sarƙar ya dubi hannunta ya rumtse ido, da ma shi tun tasowarsa daga abuja yaji ajikinsa something bad will happen to him, daɗi da ƙarawa da yaga star ɗin jikin sarƙar tayi duhu.

Wawiyar ajiyar zuciya sauke sannan ya buɗe hannunta zai cire sarƙar sai yaji ta riƙeta da kyau dan haka ya barta ya rufe murfin ya zaga ya shiga yaja motar with high speed, tuƙin yake amma hankalinsa gaba ɗaya na kanta, ya miƙa hannunsa ɗaya ta baya ya riƙo nata, yaci gaba da dariving da hannu ɗaya, fatansa karta mutu, ga shi there is no any hospital nearby bare ya miƙata, haka dai har ya shigo garin ikoyi.

<< Sirrin Boye 18Sirrin Boye 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×