Skip to content
Part 40 of 71 in the Series So Da Buri by Bulama

Sai da yaga numfashinta yana shirin d’aukewa tukunna yayi wurgi da ita sannan ya sake jeho mata tambayar
“who are you??” Yana huci.

Cikin tsananin tsoro Jalila take kallonshi kafin ta ankara taga ya sake yiyowa kanta yana shirin damk’ar wuyanta a karo na biyu, yace “Naga take taken baki da shirin fad’amin gaskiya ta cikin sauk’i!”

Da sauri cike da tsoro Jalila ta ce “me kake so ka sani to?” Tana mai ja da baya.

“Wacece ke! Meye alak’ar ki da Arshaad sannan mecece alak’ar shi da waccar Yarinyar??!”

Da sauri ta ce “wajenta yake zuwa a gidanmu! Ni ban tab’a ganinshi sosai bama sai yau, ban sanshi ba bai sanni ba! Ai kai ne ka ce i nce na sanshi, amman ni ba mu tab’a magana bama sai yau!!”

Takaici ne ya hana Auwal yin magana. Can kuma cikin tsananin b’acin rai yace “kin san da duk wannan amma shine baki tab’a gayamin ba sai yau?”
Ya k’arashe maganar cikin tsawa!.

Jalila gaba d’aya duk ta rud’e ta gaza fahimtar inda Auwal ya dosa. Gashi yadda taga ranshi a b’ace tayi mugun tsorata hakan yasa cikin rarrashi tace
“To ai naga nayi abunda ka fad’a ko?
Gashi har sunyi fad’a! Menene kuma laifina a nan?”.

Da k’arfi yake sauk’e ajiyar zuciya!
Tabbas Micheal yayi masa shirme
to amman kuma ta bakin Jalilan ‘ai gashi sun yi fad’a!’ One of abunda yake so ya faru ai farun ai at last! But still ya zama dole ya koyawa Jalilan itama hankali..

Fuskar nan babu walwala ya kalle ta, kafin yace “Mai yasa da na fara zuwa, baki fad’amin cewa baki da alak’a da shi ba? Eh? Kika barni a duhu?” Cikin rashin fahimta tace “Wallahi ni ban gane komai ba! Dan Allah ka fahimci ni”.

Shiruuu, Auwal yayi yana d’an nazartarta yana kallonta. Can! Kuma yayi tsaki kafin yace “kije ki tattaro kayan ki, ki wuce wajen Gwaggo Asabe, i’ll get back to you, idan kuma zaki zauna anan d’in ne to zan iya barin ki but ki tuna abunda na fad’a miki d’azu!”.

Da sauri ta nufi d’akin ta na sama, kafin minti goma ta tattaro komai.

Auwal ji yake kamar ya shak’e ta yayi ta dukanta! Kawai dai ya barta ne ya samu ta rabu dashi for now dan baya so Daddy yazo kiranshi da kansa!
Amman tabbas sai ya koya mata hankali, duk da ya fahimci kamar jahilcinta da dak’ik’ancinta ne ya janyo komai.

A gate d’in estate ta had’u da su duk sun fito har Gramma wadda ta kawo su Shuraim don tun jiya da suka k’i bacci da safe kuma suka dinga yiwa Abba kuka akan suna son Ummi ta dawo, ya kaisu wajenta. Da kyar ta lallab’asu bayan tace musu “Ummin tayi y’ar tafiya ne amman soon za su dawo, suyi hak’uri.”

Hudan tana k’arasowa Gramma ta kamo ta, tace “Ki kwantar da hankalinki Ki bisu kinji, na san kina kewar Maman ki, amman na san Abba da kansa zai kaiki idan komai ya gama daidaituwa, kinji y’ar albarka?”.

A hankali ta d’aga mata kai tana jin k’aunar matar da girman ta suna ratsa zuciyarta. Dad shima abunda ya fad’a mata kenan sannan yace “duk abinda take buk’ata idan sunje ta rubuta ta bawa Arshaad ya kawo mishi already anyi mata d’an siyayyan abubuwan da zata buk’ata for now suna cikin mota.”
Da “to” da kuma godiya shima ta amsa mishi.

Auwal yana fitowa daga mik’a Jalila wajen Gwaggo Asabe suka fara shirin tafiya. Abba ne ya bud’e mata gaban wata mota yace ta shiga, tana shirin shiga dai dai nan Gwaggo Asabe wadda ta fito yanzu ta k’araso taja Hudan tayi hugging d’inta, ji suke kamar kar su rabu dan har sun saba a cikin y’an wuni biyun da suka yi tare.

Auwal yana gefe in banda tab’e baki babu abunda yake yi, ji yake kamar yaje ya shak’e ta! Shi fa ya tsani yaga ana fifita wani, kuma ya lura kamar hakan a jinin y’an gidan yake! K’iri k’iri sun iya nuna banbanci, gashi yanzu ma akan y’ar k’ank’anuwar Yarinya an kwashe Surukan gida kaf! An kai cell, an bar mahaukaciya!
Ya ja tsaki yafi a k’irga k’arshema mota ya shige yana ta mita a ranshi yana cewa “kamar duk ba a tsatso d’aya muka fito ba!” Mu an maida mu kamar wani bole especially ma ni….kowa idan ya tashi k’orafi sai kaji yace ‘Auwal’.” Shi kad’ai haka yayi ta mita yana ta faman kumbure kumbure.

Su kam bama su san yana yi ba. Sallama suka yiwa juna kafin Gramma ta ruk’o hannunta (Hudan) da kanta ta saka ta a mota ta juyo.

Daurewa kawai take yi, amman Abba yana zuwa da yayi hugging d’inta sai ta kasa ci gaba da daurewa ta fara hawaye. Da kyar suka lallasheta sannan suka maidata gida, suka fito, suka kama hanya ba dan ransu yanaso ba, suka fice a estate d’in suna masu jin dumbin kewar gida cike a zuk’atansu.

Suna fita suka had’u da motar Kaka da Madu, horn suka d’anyi musu don haka suka dakata! Dan shi Abba bai ma gane su ba.

A ɗan gaba kad’an suka yi parkin, dan haka suma su Kaka suka juyo da akalar motar tasu suka isa inda suke suka yi parking.

Suna fitowa Abba ya gane su dan haka ya k’arasa ya cewa su Aslam su zauna a motar, shi da Dad kuma suka fita suka samesu.

Suna wucewa itama Hudan ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar amman sai ta jita a rufe! Cikin d’an tsare gida ta ce “zan je wajen Kakannina!”

A k’ufule ya ce “Ba za ki ba!”

Wani takaicine ya rufe ta taji kamar ta rufeshi da duka, taya ga su Kaka tana kallo suna kallonta, amman ace ba zata je wajensu ba? Inaaa, ba zai yiu ba! Dan haka ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar ta k’arfi! Tun k’arfinta.

Ta gefen ido yake kallonta, tana ta dambe da handle d’in motar, tun k’arfin ta. Ta fi minti biyar tana fama ganin ta kasa yasa ta juyo da d’an ladabi ta ce “Ya Aslam dan Allah ka bud’e inje wajen su mana.”

Ta bashi dariya sosai amman ya danne, still amsar d’azu ya sake maimaita mata babu alamun wasa a fuskarshi “ba za ki ba!”

Wani k’ululun takaici ne ya tokare mak’ogwaronta, dama ga haushin Arshaad da take ji tun d’azu! (Don Abba har yana shirin shiga motar da take amman ya janye shi yace “yazo zai tuk’a shi”) Yanzu gashi ya had’ata da wannan boss d’in! Shi bai bari ta tafi da Abba ba kuma shi ma ya kasa shigowa su tafi tare ko da yake ta san
saboda yana jin kunyar had’a ido da ita ne shiyasa! Kuma ya san koda ya shigo d’in ma fita zata yi ta bar mishi motar dan haka d’in ta gama shiryawa a ranta. Amman kuma at least ai da ya gwada Instead yana kallonta amman ya shige motar Abba yaja suka tafi da shi da su Shuraim. Abunda Huda bata sani ba shi kuwa Arshaad fushi ya d’auka da ita bana wasa ba ata dalilin zargin da tayi mishi!.

Bata iya rashin kunya ba amman bata san lokacin data tak’ark’are ta zabgawa Aslam wata uwar harara sannan ta murguda mishi baki ba!
A tunaninta su Abba yake kallo dan direction d’insu taga yana kalla
amma abunda bata sani ba shine duk abunda take yi yana kallonta ta gefen idonshi. Tunda yake a rayuwarshi bai tab’a ganin harara da murgud’a bakin da ya yi matuk’ar burgeshi da bashi dariya irin wannan ba, hakan ya sanya wani sassanyan murmushin da ya dad’e bai yi ba wanzuwa akan kyakkyawar fuskarshi, wanda har sai da Hudan taji sautin murmushin tayi saurin juyowa tana kallonshi amman ga mamakinta sai taga still su Abba yaketa kallo wadanda suka tsaye a setin su.. Gani tayi kamar Madu yana magana da fad’a fad’a! Cikin takaici ta juyo tana kallon Aslam a ranta tana aiyyana “wato dan yaga ana fad’a shine yake murmushi, lallema wannan mutumin!.”

A chan wajen su Madu kuwa abu bai yi dad’i ba! Dan tun farko da Madu ya tambayi Abba “dalilin da yasa ya d’auko Hudan lokaci guda haka?”
Abba ya k’ule! A ganinsa dan mai yasa Madu zai yi mishi tambayar ‘dalilin d’aukar y’ar sa da yayi’ bayan shekaru da dama da yayi ba tare da ita ba!.

Daga k’arshe dai, Abba tafiya yayi ya bar wajen dan baya son yayi musu rashin kunya.

Daddy ne ya tabbatar musu da “sun je har unguwar da Hudan ta taso kuma sun ji irin zaman da Huda tayi a gidan Baba, wajen mutane bakwai suka tambaya amman duk maganarsu d’aya ce! Ba abunda basu sani ba a halin yanzu na irin zaman da Hudan tayi na azaba a hannun mutumin nan, har k’usar da Ja’afar ya buga mata a ciki suna da labari!” Ya ce musu “Tun jiya suke ta faman lallab’a Abba, da kyar suka samu ya hak’ura amma daa cewa yayi sai ya kulle Usman kuma yayi shariah da su!”

Daga k’arshe yace musu “dan haka, ko kotun da Madu yake ik’irarin zai je sai dai ya kulle kanshi da kanshi dan wannan dalili kad’ai ya isa a barma Abba custody d’in Huda!.” Yana gama fadin haka shima yayi musu sallama cikin girmamawa ya wuce ya koma mota Auwal ya ja suka yi gaba suka barsu a wajen, daman su su Abba sun dad’e da wucewa.

Tunda suka shigo gidan Huda take bin had’add’en mansion d’in mai hawa biyu da kallo! Har Aslam ya gama parking bata sani ba, sai da yace
“Na bud’e lock d’in, ki fita sai kin fi jin dad’in kallon!”

Tukunna ta dawo hankalinta, gaba d’aya kuma sai kunya ta lullub’eta.

A hankali tasa hannu ta bud’e ta fito, still mutane wadanda suka kwashe kaya daga chan gidan sunata kai kawo, da alamun basu gama jeran ba, dan gashi har sets d’in kujeru wasu ba a shishshigar ba. K’ofar shiga gidan biyu ne manya manya! Kamar yadda Dad ya fad’a gidan wajen zaman mutum uku ne ma amma k’ofar farko ta gefen dama yafi girma dan wajen d’akuna sha biyar ne da faluka bakwai (shine mutum biyu zasu iya using dan hatta kitchen biyu ne) Sai d’ayar k’ofar gefen hagu ta d’an gefe kad’an na d’auke da 7 bedrooms da 4 parlourns.

Mai girman Abba ya d’auka
Daddy kuma ya nufi d’ayar k’ofar (side d’in mutum d’aya wanda bai kai na Abba ba). Suna shiga Hudan ta kusan daskarewa. Duk da gidan chan estate d’in shima yana da double height ceiling amman ko rabin wannan bai kai ba, ga wata mahaukaciyar chandelier da tunda take bata tab’a tunanin akwai irinta ba, wasu irin kwayayene da suke k’ok’arin makantar da ita tsabar haske a gidan!
Waiting parlour yana a ta gefe a cikin wani d’an glass door kafin ka k’arasa shigowa makeken main parlourn k’asa wanda girman parlourn zai iya cin set d’in manya manyan kujeru 6 ko bakwai! Gefen dining daban, sai
wata had’add’iyar matattakalar bene doguwa da zata kaika sama. K’aramin Kitchen d’in na ata gefen waiting parlour kana iya hango cikin shi dan bangon half ne bai kai har chan sama ba Main kitchen d’in kuma yana ta gefen dining Amman shi rufaffiyar k’ofa babba gareshi. Akwai wasu k’ofofin still a cikin parlourn wanda take da tabbacin d’akuna ne.

Sama suka yi gaba d’ayan su, Parlour ne nan ma biyu d’aya a gefen dama d’aya a hagu masu masifar kyau, duk da basu kai na k’asan girma ba saboda double height ceiling d’in da aka yanka ya cinye kusan 1/3 d’in saman amman suma sun had’u sosai ba a magana!
Pop kam kamar ka kirashi ya amsa ta jikin bango ta ceiling hatta k’afar bene shima ba a barshi ya huta ba.

Wata matattakalar suka sake bi suka hau chaan sama. Suna hawa suka nufi side d’in su Sudais, d’akunan su da parlourn su yayi matuk’ar burgeta.
Sudais yanata murna Shuraim kuwa miskili bai ce komai ba Sudais shi a shirmen shi ya d’auka har da Huda, dan haka ya hau tsarawa ‘Za su d’auki d’aki daya ita kuma ta d’auki d’aya, sannan ya cewa Abba “ai da anyi mata nata gadon pink ba kalar blue ba”…’

Dariya dukkansu suka yiwa shirmen shi, kafin Abba yace “a’a ita nata d’akin daban ne bara in kaita in dawo ko?” Yana shirin fita yaji Shuraim yace
“Abba yaushe Ummin zata dawo?
Gramma ta ce za kaje ka d’auko ta”

A lokaci d’aya duk suka d’auke wuta..
Gabad’aya duk sai Hudan taji ba dad’i, yadda taga Abba ya had’e rai ne yasa ta kasa cewa komai “ba na son yawan tambaya!” Shine abunda yace daga nan ya fice daga d’akin.

Ganin haka yasa itama Hudan tayi musu sai anjima ta fice. Tana ta kallon parlourn nasu har ta fita, ta jaa musu k’ofa ta rufe.

Sai a sannan Abba yace “tazo suje ya kaita d’akinta” yana mai kama hannunta. A gefen parlourn da suke a ciki suka shiga wani dogon corridor, k’ofar tana achan k’arshe suna isa ya sa hannu ya zura key ya murza k’ofar ta bud’u! Sanna ya jaa hannunta suka shige ciki. Set d’in kujeru biyu ne
Peach da black, sai wani d’an k’aramin dining mai mugun kayau mai d’auke da kujeru biyu a gefe, da wata had’add’iyar tv babba mai curve.

Wucewa suka yi suka shiga bedroom a nan ta sake shiga mamaki, gadon nata pink ne mai rumfa da net a jiki (princess tent) ga wasu had’add’un resting da coffee chairs guda bibbbiyu a kusa da tvn bedroom d’in, fad’ar had’uwar d’akin kawai sai wanda ya gani! Kawai.

Still toilet d’inta ya nufa da ita don ya nuna mata. Ta closet suka bi kafin su isa cikin toilet d’in A nan kuwa ta saki baki, wajen wanka har uku shower da wani had’add’en jacuzzi, sai kuma wani makeken bathtub da mutum hud’u ma za su iya shiga su kwanta kamar gado da Showers a jikinshi ta ko ina. Ba abunda yafi bata mamaki irin wutan pop da take gani na sama, da taga yana ratsowa ta k’asan toilet d’in toilet d’in ta ko wanne angle.

Bata gana dawowa dede ba, taji Abba yana cewa “duk abunda bai yi miki ba ki fad’a sai a chanja! Munata sauri ba a samu anyi komai a nutse ba, so if you need anything just say it sai a chanja miki ko a siyo, an d’an zab’a miki kad’an jiya kayan suna mota mostly abaya ne da shoes da sauran y’an abubuwa, zan kawo miki tab zuwa anjima, sai kiyi shopping duk abunda kike buk’ata, in kuma a furnishing akwai abunda kikeso ki fad’a shima sai a kawo.”

Ita dai mamakine ma ya hanata yin magana, wai a nan d’in amman still ana tambayanta ko akwai wani abun da takeso a kawo!

Girgiza kai kawai tayi, kafin tace
“Abba na gode komai yayi Allah ya k’ara Arzik’i. “

A hankali ya dafa kanta yana mai jin tsananin kaunar y’ar tashi tana ratsa ko Ina na jikinshi sannan ga tsananin tausayinta da ya hanashi sukuni! Ji yake kamar yaje ya kama Usman yayita dukanshi har sai yaga baya numfashi tukunna ya kyaleshi!
Jiya yadda yaga rana haka yaga dare tsabar bak’in ciki…Jin yadda zuciyarshi ta fara tafarfasa ne yasa ya kawar da tunanin yace “Ki huta bara a kawo miki tab d’in da kayan, anyi order abinci shima na san kafin ki gama freshining up ya zama ready sai ki sauk’o muci ko?”

D’aga mishi kai kawai tayi ta kasa d’ago kanta, saboda kwallar da ta tarar mata! Dan tana ganin inda aka kawota a matsayin mallakinta Mama ce kawai ta fad’o mata.

A tare suka fito daga toilet d’in suka shigo d’aki.

Ganin Abba yana shirin fita yasa tunanin ta ya katse tayi saurin cewa

“Abba” juyowa yayi yana kallon ta.
A hankali ta k’arasa wajen da yake sanna ta ce “Dan Allah Mama, mun yi waya da Sakina tace min Maman tana asibiti tun shekaran jiya”ta k’are maganan hawaye na zubowa daga idanunta.

A hankali ya kama hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace “Zan kaiki wajenta anjima da daddare. Ki daina kuka”
Da sauri tasa tafin hannunta tana share hawayen duka biyu.

Kallonta yayi tukunna ya ci gaba
“Amman idan kin je, ina so ki yi promising d’ina zaki dawo, 30 minutes kawai za kiyi, zan jiraki a mota!
Ku gaisa ki dubata daga nan ki ce musu kina zuwa, in kin fito sai mu dawo. And karki ce musu ni na kawo ki”.

Da sauri ta d’ago ta kalleshi kafin tace
“to ai kamar na yaudaresu ne idan nayi hakan, kuma Mama ba zata ji dad’i ba.” Mik’ewa ya yi kafin ya ce
“Shine ni kuma zaki yaudare ni ki tafi kik’i dawowa ko?” Kuka ta fashe da shi, saboda daman ta san ko da ace ta yarda zata dawo d’in su Mama ba za su barta ba!.

A hankali ya ce “Hudan nima mahaifinkine kamar Maman ki, na san ba lalle ki fahimci komai ba, amman ina so ki san cewa ‘ban tab’a k’in ki ba’ Yadda Mahaifiyarki take sonki nima haka nake sonki, kina gani a gabanki na hukunta waɗanda suka yi nasarar raba ni dake! Ba zan tab’a yarda in barki ki koma gidan da kika taso ba, dan duk halin da kike ciki a gidan na sani. Idan kin yarda kullum idan kina so to za kije ki dinga duba Mamanki, amman Hudan ba zan sake bari ki yi nesa dani ba. I want to take care of you
Make it up to you, Make you forget all the sufferings that you go through.
Amman hakan ba zai tab’a faruwa ba, sai da had’in kanki! Ba zan b’oye miki ba har ga Allah banji dad’in yadda kike yi mini ba kwata-kwata Huda, it’s like kamar ma ba kya farin ciki da ganina, komai ke kawai Mamanki! Ko maganan 10 minutes ban tab’a yi da ke ba! Yanzu ma kalli yadda kike yi
min kukan in maidake wajen ta kamar irin na satoki d’in nan?” Ya k’arashe maganar a hankali.

Gabad’aya Hudan sai taji jikinta yayi sanyi, ttabbas bata kyauta ba! Ya kamata ta nuna mishi shima Mahaifinta ne tunda gashi ata dalilinta har gidansu ya bari da shi da d’an uwansa don kawai ya zauna a tare da ita. Tunaninta ne ya katse jin yana cewa “I’m sorry Hudan dan unless you promise me ba zan tab’a barinki ki je ki ganta ba.”

Shiru, d’akin ya d’auka kafin ya ji tace
“Tam” Kallonta yake yi, kamar zai ce mata wani abun kuma kawai sai ya juya ya fita.

Kamar yadda ya fad’a haka aka kawo mata kayan da ya ambata. Ita dai Hudan mamaki ta shiga yi dan bata ga kuma abun k’ari ba anan, komai akwai hatta inner wears sai dai kawai kamar ba za suyi mata ba, dan haka ta d’au tab d’in ta hau shopping. Sai da ta hau d’in kuwa tukunna tayita gannin abubuwa dan haka ta zazzab’a, bayan ta gama ta rufe ta ajjiye.

Tana idar da sallar Magrib ta sauk’a k’asan kamar yadda Abban ya ce mata.

Bata samu kowa ba, amman dai ga uban abinci nan shak’e a kan dining d’in wajen kala nawa. Ga kuma wata maid cikin uniform sai kai komo take yi tsakanin kitchen da dining d’in tana jera su plates. Bata yi minti uku a zaune ba, suka shigo daga masallaci.
Su Sudais ne suka fara shigowa, Sudais yana ta tsallen tsallenshi, Shuraim kuwa ya mazee, kallonsu take tana mamakin kamanninsu dan ita kam miskilancin Shuraim ne kawai yake sawa take iya gane su. Tana murmushi tanata kallonsu tana jin tsananin k’aunarsu a ranta su Abba ma suka shigo dukkansu, har a Auwal wanda Daddy ya matsawa akan dole sai yazo sun gaisa da cousin d’inshi! Sai kumbure kumbure yake yi, ba wanda yabi ta kanshi haka nan suka shigo abunsu ana d’an tab’a hira kowa yana fara’a banda shi.

Suna shigowa da Daddy suka fara had’a ido dan haka ya yafitota da hannu. A hankali cikin nutsuwarta ta nufi dogon dining d’in mai kujeru kusan ashirin inda taga sun nufa
kamar an tsamota a ruwa a haka ta k’arasa wajen, Abba ne da kansa ya jaa mata kujera ta zauna, ita har kunya take ji yadda ake wani lallab’a ta ana janta a jiki musamman ma Abba yadda yi mata kamar ya goya ta yayita zagaye garin da ita.

Cikin ladabi ta shiga gaidasu suka amsa, su Aslam kuma tayi musu jimla tace “ina wuninku”. Aslam ne kawai ya amsa mata, a hankali ta d’ago ta kalle setin da Arshaad yake taga ya wani had’e rai ya d’auke kai ko inda take bashi da niyyar kalla ma! Nan kuwa ta k’ule, tana mamakin shi, a ranta tace “tabarmar kunya yake son nad’ewa da bori!”

A take ta d’auke kanta itama bata sake kallonshi ba, tana jin haushi da wani tuk’uk’in kishin dake sake taso mata.

Tana cikin wannan tunanin taji Daddy yace, “Sorry dota mun barki ke kad’ai ko? Za kini shiru kam, gashi Aaima na school, ya kamata a nema miki Abokiyar hira gaskiya!in ba haka ba ba zaki ji dad’in zaman ba kwata kwata
tunda su Sudais suma islamiyyarsu da boko a had’ene sai pass 5 suke dawowa.” Da sauri cikin tarar numfashinsa Auwal yace
“ai daman da ace Ummi tana nan ba a kaita cell ba to da zata ji dad’in zama sosai, gashi Gwoggwo Asaben ma da naga kamar sun d’an saba itama ta saka an baro inda take! Dole ta sha zaman shiru kuwa ai!.”

Dakatawa Abba yayi da zuba mata abincin da yake yi ya rik’e serving spoon d’in kawai still yana kallon plate d’in! Yana mamakin Auwal!! Wato rashin kunyar tashi yau ta hauro kanshi kenan, a gabanshi haka yake zuba mishi magana. Yana shirin yin magana yaga Daddy ya taso ya nufi Auwal d’in a zuciye, da sauri Abba ya mik’e ya rik’e shi haka ma Aslam ya mik’e yana cewa “Daddy dan Allah kayi hak’uri ka kyale shi.” Arshaad kuwa ko motsi bai yi ba dan shi kam tasa kad’ai ma ta isheshi, ba k’aramin k’ok’ari yake ba wajen share Hudan da yake yi, gashi tunda ya zauna yake d’an satar kallonta amman yaga kamar ma ko inda yake bata son kalla!.

Cikin fushi Daddy yace “Dan uban ka iskanci naka yau a kanmu zai k’are?
Auwal wallahi zan yi mugun sab’a maka fa!!”

Cikin katse shi Abba yace “ya isa haka Daddy ka kyale shi kawai! Dan Allah”

Cikin rashin jin dad’i Aslam ya cewa Auwal d’in “you can leave, tunda ka ganta gashi har kun gaisa ma.”

A fusace Auwal ya kalle shi, yana shirin yin magana Daddy ya daka mishi tsawa yace “Get out aka ce!! Stupid boy kawai!!!”

Fuu!! haka ya tashi ya fita kamar zai tashi sama.

Daddy da kyar ya koma wajen zaman shi ya zauna gaba d’aya guiwanshi a sace! Ya so a ce a kusa da Auwal ya zauna yau da sai ya sauya mishi kamanni ya nuna mishi still da ragowar k’arfinsa shima har yanzun, dan yaga alamun Auwal d’in ya kawo k’arfin da yawa shiya sanya yake jin kanshi a sama kamar yafi kowa!.

To dai dinner d’in haka ta wakana babu dad’i, kowa da abunda yake damun ranshi.

Sai wajen 9 Aslam da Arshaad suka yi musu sallama suka tafi, bayan an yanke yin wata sauk’ar gobe amman sai dare za a kammala, kowa zai yi izu biyu bayan sallar farilla sai su tafi da ruwan addu’ar a shafa mata .

Suna fita Abba ma yace mata “ta d’auko hijabinta ya kaita ta duba Mama”. Murna a wajen Hudan ba a magana dan da gudu ta haye benayen, bata yi minti uku a saman ba ta sauk’o sanye da hijab har k’asa wanda ta gani a cikin kayan da aka bata.

Ya lura da yadda jikinta har karkarwa yake yi, shiyasa bai b’ata mata lokaci ba yace “su je”. Da sassarfa ta shige motar. Shi dai Abba kallonta kawai yake yi, tabbas Hudan da shi take kama komai da komai amma idan tana wani abun sai ya dinga ganinta kamar Maryam!! Wani d’an murmushi ne ya sub’uce mishi, a hankali cikin sanyin jiki ya murza key ya tada motar ya nufi gate.

Masu gadin gidanjensu na chan estate su suka d’auko suka taho dasu. Suna Isa gate d’ayan ya ajjiye rediyonshi a kan dogon bencin da suke zaune su wajen biyar harda driver da mai wankinsu da gyaran fulawar, yaje ya bud’e musu makeken gate d’in, suka fice.

Tunda suka fita Huda ta kasa sukuni, tsabar zumud’i, gani take yi kamar Abba baya gudu, har d’an tasowa take yi ta d’an lek’a gaban titin ta gaban glass d’in motar. Dariya ta bashi sosai dan haka yace “Gani kike kamar bana gudu ko?” Ya fad’a yana dariya sannan ya k’arawa motar wuta. Itama murmurshin tayi ta koma ta zauna da kyau a mazaunin ta.

Tafiyar minti ashirin ce ta kaisu AKTH emergency, dan ma sun d’an tarar da go slow a hanya. Tana shirin fita taji yace “You promised Hudan, right?”

A hankali ta d’aga mishi kai, sannan tace “Na gode sosai Abba”, sannan ta fita.

Da kyar security suka barta ta shiga bayan tayi ta nacin ce mishi Mamanta ne a kwance, Allah ya taimaketa, wanda yake gadi ne a wajen ranar da suka kawota ita da Aslam, kuma d’azu tabbas yaga Maman nata an fito da ita tana d’an zagaye, shiyasa ma ya barta ta shiga, don ya tunata tun ranar da suka zo ita tana kuka shi kuma yana ta mamakin had’uwar Yarinyar, haka nan yake ta ganin hoton fuskarta a zuciyarshi amman ya san ko hauka yake ba zai ma yi tunanin tunkarar ta ba.

Dube dube ta hau yi bayan ta shiga, da kyar da sid’in goshi ta hango su. Mama da Ummu a kan gadon a zaune suna magana da alamun mai matuk’ar mahimmanci ce sai Sakina ita kuma a gefe kan kujerar mai jinya da waya a hannunta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 39So Da Buri 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×