Skip to content
Part 1 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Juma’ar da ta gabata ne duk wani gini da Safina ta yi tunanin ta gina a bisa tubalin rayuwar aurenta ya rushe. Ta muskuta a kan gadonta da ta kwana a kai wanda rabon da ta yi baccin dare a kansa har ta manta, sai dai na rana. Ko jego take yi ba sa raba makwanci da Hassan. Ko cikin bacci ta mirgina gefe takan ji ya matso yana naniƙe mata. Wani lokacin har bata so, musamman cikin zafi idan nepa sunyi halin nasu, randa tayi mitar yana goga mata zufa zai ce,

“Idan ban ji ɗumin ki ba baccin baya mun daɗi”

Namiji, namiji ƙanin ajali. Idan bai kar ka ba, to babu shakka zai saka jinya. Da idan aka faɗi sai tayi dariya ƙasa-ƙasa tana ganin yanda kalmar tayi nisa da gidan auren ta, idan akace namiji, a ranta sai tace Hassan, kamar fadin sunan shi da tayi zai tsame shi daga jerin kuɗin goron da ake yiwa maza.

Hassan! Wannan karon zuciyar ta ta faɗa tana maka shi cikin jerin kuɗin goron harma tana kai shi matsayin dilan su, a wajen shi suke sari sai su rarrabama sauran maza.

Hassan! Shi ya saka ta a halin da take ci. Halin da zata iya kwatanta shi da na ruɗani. Ya hana ma ƙwaƙwalwarta aiki kamar yanda ya kamata. Bata iya saƙa komai ba balle ta kai ga warwara. Tunani ƙwaƙƙwara ta kasa yin sa.

Hausawa suna cewa duk juma’ar da zata yi kyau, tun daga Laraba ake ganeta. To me ya faru ranar Laraba? A iya tunaninta Larabar da ta gabata ta zo mata dai dai babu wata tangarɗa. Kamar yanda ta saba, ta yi ma yara wanka ta shirya su Hassan ya ajiyesu a makaranta. Mai aikinta Suwaiba ta zo suka gaisa lami lafiya kamar yanda suka saba ta hau aiki yayinda ta koma ta kwanta tare da Ilham wacca ko juyin farko bata yi ba.

Wajajen tara da rabi Ilham din ta tashi daga bacci dan haka ita ma ta gama nata. Baki ta wanke mata sannan ta dama kunun yara ta bata. Zuwa lokacin Suwaiba ta gama aikinta har ta tafi. Dama shara ne sai goge – goge. Ta yi ma Ilham wanka ta shiryata sannan ta soma shirin girkin rana.

Hassan ya ɗauko yara daga makaranta ya ɗauki abincinsa na rana da ta zuba masa a filasai masu ɗan karen kyau wanda ta ware saboda fitarsa da abinci ya ƙara ficewa tare da yi mata alƙawarin ana sallar La’asar zai zo ya ɗaukesu ya kai su bikin sunan ƙanwarsa da ake yi a gidansu kasancewar babban gida ne mai wadataccen fili.

Mai yi ma yara lesson aikin makaranta kawai ta koya musu ta tafi. Safina ta yi musu wanka dan lokacin uku har ya ɗan gota. Yanzu Hassan ya dawo basu shirya ba ya dinga fada kenan. Kaya ta saka musu sabbi gal! Dogayen riguna masu kalar peach wanda aka saya musamman saboda taron sunan. A gurguje ta shirya cikin nata tsadadden leshin wanda launin sararin samaniya ne sai adon launin da ya tafi da na yaran.

Hassan na shigowa ya gansu ya dinga ɗaga mata gira. Bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba.

“You all look beautiful my darlings.”

Ya faɗa yana jefa Ilham sama yayin da Iman da Ihsan suke dariya. A gurguje ya watsa ruwa ya saka shaddar da Safina ta fito masa da shi launin sararin samaniya. Ita kanta ta san duk wanda ya gansu ya san sun dace da junansu. Ta san sai iyalin nasu ya burge kowa.

Ƙanƙanin lokaci ya kai su gidan da ake taron sunan kasancewar babu yawan motoci a hanya sannan gidan babu nisa sosai da nasu. An soma taruwa a gidan wanda babu makawa ‘yan uwan mai jegon ne na kusa. Sai da mai gadi ya bude musu gate suka shiga cikin gidan. Faram faram suka gaisa kamar yanda suka saba ana wasa ana dariya.
Zabura Safina ta yi a dai dai lokacin da wani tunani ya faɗo mata. Bata san ta tashi zaune ba sai da Ilham ta yi motsi.

“Ƴan abu ta kazan uba!”

Ta lailayo ashar ta maka musu. A zuciyarta tace munafukai! Ashe son ƙarya suke mata? Kai dangin miji munafukai ne na ƙarshe! Ita zasu munafurta? Zahra harda ce mata.

“Uwargida kuma amaryar Hassan Mai saƙa! Daga ke babu wata. Kina sha’aninki Safin Umma.”

Ita kuwa ta juya idanu tana rausaya kai.

“Safin Hassan dai. Kina fasa min kai da wannan kirarin.”

Zahra ita ce kawarsu a gidan. Ita da Nabila, matar Hussaini.

Hajiya Mama mahaifiyarsu Hassan ta dinga nan – nan da ita. Ta saki wani tsaki. Tana jin ciwon yanda suka rufeta. Aka ci aka sha aka yi hotuna sai da aka yi sallar Isha’i sannan suka koma gida. Wannan daren sun raya shi ne bayan Hassan ya zuzuta yanda ta yi masa kyau take kuma ƙara yarinta.

Larabarta ta yi kyau matuka gaya. Babu abun bacin rai ko saka damuwa da ya gifta a ranar. Sai kuma Juma’arta ta zo mata a bai bai?

Bayan sallar juma’a ne Hassan ya gama cin abinci suna kallo yayin da yaran suke ta wasansu ya riƙo hannunta yace,

“Safina, kin san ina son ki.”

Ta kara shigewa jikinsa tana cewa,

“na sani. Baka kuma gajiya da gaya min.

Ya sauke numfashi,

“An saka ranar aurena nan da watanni uku.”

Idan ta ji mutane suna cewa sun ji saukar aradu a kansu sai ta ga kamar daɗin faɗi abun yake musu. Amma a wannan lokacin, zata rantse saukar abunda ya fi aradu ta ji. Kunnenta ya toshe, ƙwaƙwalwarta ta tsaya cak! Banda bugun zuciyarta babu abunda take ji, sai kuma jinin jikinta da take jin yana gudu zuwa ƙwaƙwalwarta. Da a tsaye take babu abunda zai hanata faɗuwa. A zaunen ma dan tana jikin Hassan ne. Ga dai bakinshi yana motsi amma bata jin komai.

“Hassan, ban ji mai kace ba.”

ta yi ƙarfin halin faɗa dan tana tunanin ko dai mafarki take ko kuma ta fara jiye – jiye. Idan ba hauka ne zai kamata ba kuma toh. Ta gyara zamanta tare da saka ‘yan yatsunta manuniya a cikin kunnuwanta tana ɗan yawo da su dan abunda ya toshe mata kunnuwa ya fito ko ya faɗa ciki ta samu ta ji me Hassan zai ce.

“Aure zan yu Safina. Wallahi ba dan bana son ki bane. Kawai ƙaddara… Dariyar da ta fashe da ita ne ya katse shi. Eh tabbas hauka zata fara. Banda hauka ma me ya haɗa Hassan da zancen aure? Auren ma ba da ita ba. Wai Aure. Hassan dinta fa. Ta girgiza kai tana murmushi.

“Hassan kenan. Yau kuma ta inda wasanka ya ɓullo kenan.”

Sai kuma ta turɓune fuska ta turo baki.

“Ni bana so ka daina.”

ta faɗa a shagwaɓe tana shura ƙafafunta.

“Wallahi Safina da gaske nake. Ranar Asabar aka je mana tambayar aure ni da Hussain. An tsayar da lokaci nan da wata uku.”

Kallon cikin idanunsa take yi a lokacin da yake magana. Ta gano tsantsar gaskiyarsa yake faɗa. Bata san lokacin da ta miƙe tsaye ta shige ɗaki ta bar shi ba. Shigar da har yau bata ƙara fita ba. Yau. Yau safiyar Asabar. Ji take kamar ta shekara cikin damuwa.

Har ɗaki ya biyota da abinci yana lallashinta kan ta tashi ta ci. Shigewa banɗaki ta yi dan kar ya dameta da yaudararsa. To yaudara mana. Banda mayaudari waye zai ƙara aure ya zo yana nuna ma matarsa so da kulawa? Sai da ta tabattar baya ɗakin ta fito. Fitila kawai ta kashe ta kwanta.

Wajen karfe goma ya dawo yana mata magana kan su je su kwanta ta yi burus da shi. Ilham ya kawo ya kwantar a gefenta sannan ya koma ɗaki. Wanda hakan ya yi mugun ɓata mata rai. Ina laifin ya zo ya kwanta tare da ita tunda sun saba. Da asuba ma tana jin shi ya leko yana tashinta ta ƙi kula shi. Sai da ya tafi ta tashi ta yi sallar sannan ta koma ta kwanta. To shi ne har yanzu bacci bai ɗauketa ba. Dama jiyan ma sai dai saceta baccin ya yi.

Dole ma ta zauna ta yi tunanin menene mafita. Zuwa zata yi ta same shi su yi magana kafin ta shirya makaman yaƙinta. Saboda wallahi babu wacca ta isa ta zo ta lalata mata rayuwa!

“Mimi na shanye” yarinya ‘yar kimanin shekaru uku da ke zaune a kan dandamali a kitchen ta faɗa tana nuna mata kofin hannunta.

Murmushi ta yi mata

“Say Alhamdulillah”

ta fada tana juya fankason da ke kan wuta.

“Na fada. Baki ji bane”

yarinyar ta bata amsa. Kai kawai ta girgiza tana murmushi. Halin Hajja sai ita. Ta kwashe fankason ta saka a kwalanda sannan ta tsoma hannunta cikin ruwa ta maida cikin kwaɓin funkason.

“Ba’a gama bane?”

Ta jiyo muryarsa daga bayanta. Tana jin shi ya matso gefenta yana leka abunda take yi.

“Saura kaɗan”

Hajja ta soma yi mai surutu yana biye mata. Ƙarshe ma dauketa ya yi suka bar kitchen ɗin cike da kamshin turarensa da na man gyaɗa.

Tana gama yin wanda zai ishe shi ta ɗauki filas din abincin ta nufi falo inda yake zaune. Kallon tashar Aljazeera yake yi yayinda Hajja ke mishi hira yana amsata. Ledar cin abinci ta shinfiɗa sannan ta jera mishi duk abunda zai buƙata. Ta koma ta ci gaba da aikinta. Wani filas din ta cika sannan ta zuba ma mai gadinta.

Lokacin Hussaini ya fita shi da Hajja sun shiga cikin gida.Ta so bashi abincin da tayi ma Alhaji dan ta san yana jin daɗi idan ta kai mishi abinci. Musamman na gargajiya. Bata tsaya cin abincin nata ba ta saka dogon hijabi har ƙasa ta ɗauki kwandon abincin ta fita.

Tana shiga gidan ta wuce bangaren Alhaji. Ta san war haka duk suna zaune suna cin abinci a falon nashi. Cikin sanyin muryarta ta yi sallama. Da sauri Habiba ‘yar shekaru goma sha ɗaya wacca ita ce autar gidan ta zo ta karɓi kwandon abincin hannunta.

Har ƙasa ta durkusa tana gaidasu ɗaya bayan ɗaya suna amsawa. Su kuma yaran suka gaisheta ta amsa.

Inna ce ta fi kusa da Alhajin dan haka ita ta buɗe mishi filasan. Murmushi ya yi ya ture kwanon ɗumamen tuwon da ke gabanshi yana mai cewa

“Hajiya Asma’u zuba min funkason nan. Allah ya yi miki albarka Nabila. Na gode.”

Bata iya ce mishi komai ba sai murmushi da take yi tana sunkuyar da kai. Tana ƙara yin murmushi lokacin da Alhajin yake kwatanta santi yana kuma cewa a cika mishi kofi da kunun gyaɗar da ƴar sa ta kawo mishi. Sallama ta yi musu Alhaji na ƙara yi mata godiya.

Hajja da ke kan cinyar Umma tana wasa da wayar Umman tace zata bi ta. Ce mata ta yi ta ɗan kara zama in ya so sai Habiba ta rakota gida idan lokacin Islamiyya ya yi. Duk abunda ake yi, Hussaini bai nuna alamun ya san ta shigo wajen ba dan idanunsa na kan wayarsa.

Hijabin ta cire lokacin da ta isa gida. Ta ƙara kimtsa gidan sannan ta nemi waje ta kwanta dan akwai bacci a idanunta.

Ganin har lokacin Islamiyya ba’a dawo da Hajja ba ta san sun wuce Islamiyyar. Yanda Umma take da Hajja sai mutum ya rantse jikarta ce ba ta Hajiya Mama ba. Tana ajiye da setin kayan Hajja har da uniform ɗin Islamiyyarta. Hakan yana matukar daɗaɗa mata. Tana son duk mai son ‘ƴar ta.

Bayan sallar magariba Hussaini ya dawo tare da Hajja. Duk da cewar ta ajiye mishi abincin rana, bai dawo ya ci ba kuma bai kira ya mata wani bayani ba. Idan da sabo ma ta saba. Amma hakan baya hana zuciyarta sosawa a wasu lokutan.

Ganin Hajja ta fara gyangyaɗi ya saka ta yi mata tayin abinci amma tace Ummanta ta bata abinci harda cake mai daɗi ita da Aunty Laila sun cinye. Murmushi ta yi sannan ta mike ta shiga daki domin tambayar Hussaini yanzu zai ci abinci ko sai bayan Isha.

“Zauna zamu yi wata Magana.”

Abinda ya ce mata kenan madadin ya bata amsar tambayarta. Sosai ta shiga cikin dakin ta nemi waje bakin gadon ta zauna tana jujjuya wayarta a hannu. Ba kasafai bane Hussaini yake zaunar da ita dan su yi magana ba. Amma duk lokacin da suka zauna dan su yi din, to abu ne mai mahimmanci. Kamar fara zuwanta ganin likita kan zancen haihuwa, ko shawarar sunan da za’a saka ma Hajja, sai shawarar makarantar da za’a saka Hajjar. Abubuwa dai masu mahimmanci yakan zaunar da ita su yi shawara. Harda launin motar da zai saya. Hakan ya sanyata yin murmushi a wannan lokacin da ta tuna.

Ta bi shi da idanu a lokacin da ya gyara zamansa a kan gadon, ya harɗe hannayensa biyu sannan ya haɗe lebensa na sama da ƙasa yana kallonta kamar mai zurfin tunani. Gira ya ɗaga kafin ya buɗe baki yace,

”I don’t know how to say this but, zan yi aure nan da watanni uku”

Shiru ne ya biyo baya. Yana jiran jin mai zata ce, ko mai zata yi. A nata ɓangaren kuma, ji tayi kamar numfashinta ya ɗauke. Ta kyafta idanunta sau biyu kafin komai ya zauna mata. Eh aure zai yi babu makawa. Sai kuma me? Ita yake kallo. Kallo na cikakken nazari.

“Kin ji me na ce?”

Ya tambaya yana ɗan jan hancinsa. Kai ta ɗaga mishi a hankali tare da yin murmushi. Mikewa ta yi ta faɗa bandaki wanda bai wuce taku biyu tsakaninta da shi ba. Ta yi nazarin cewar kafin ta isa bakin kofa ta fice daga dakin, abunda bata so ne zai faru.

Rufe kofar banɗakin ta yi tare da murda makulli. A nan jikin kofar ta sulale a dai dai lokacin da hawaye ke rige rigen fitowa daga idanunta suna shafar kuncinta zuwa haɓarta. Rarrafawa ta yi ta tafi can ƙuryar banɗakin ta hade cinyoyinta da kirjinta yayinda ta saka hannuwanta ta toshe bakinta tana kokarin rage sautin kukan da ya suɓuce mata. Kuka take yi irin wanda numfashinta ke neman suɓuce mata ba dan tana ɗauke da wata cuta da take da gami da numfashi ba.

A hankali ta soma ƙoƙarin tsaida numfashinta ba dan ta gama kukan ba sai dan kar nunfashin ya ƙwace mata ta rasa yanda zata yi cikin banɗaki gashi ta kulle. Mikewa ta yi ta nufi kwamin wanke hannu ta kunna ruwan. Kallon fuskarta ta yi na ɗan wani lokaci kafin ta sakar ma kanta murmushi. Hannu ta dinga tarawa ta debo ruwan tana mutsukkawa a fuskarta. Ta kuma murmusa ma kanta kafin ta nufi kofar ta bude ta fito.

Wayam! Babu Hussaini a ɗakin babu alamunsa. Hakan ya saka zuciyarta yin ƙaiƙayi gashi babu halin sosawa dan hannu bai isa ya kai ba. Wayarta ta ɗauka ta wuce ɗakinta.

Wajen adana lambobi ta shiga ta duba lambar mahaifiyarta ta danna kira.

“Assalamu alaikum Nabila.”

muryar mahaifiyarta ya sauka cikin kunnuwanta a hankali. Nan take ta ji wasu hawayen na gudana. Can ƙasan makoshi ta iya amsa mata sallamar.

“Lafiya kuwa Nabila? Me yake faruwa?”

“Mummy… “

“Yi magana mana Nabila. Kowa lafiya ko?”

Ta kara tambayar jin Nabilar ta yi shiru.

“Hussaini ne Mummy.”

Ta fada da kyar saboda yanda zuciyarta ke harbawa

“Aure…. Mummy Hussaini”
Ta karasa muryarta na karyewa. Ta kasa haɗa kalmomin su jeru su bada jimla mai ma’ana. Amma tana da yaƙinin Mummyn ta fahimta. Shiru ne ya ɗan ratsa na wasu daƙiƙu, inda Nabila ke faman share hawaye da bayan hannunta.

“Ki dinga faɗin Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Faɗi mu ji.”

Babu musu Nabila ta fara karantawa tare da mahaifiyarta. Kamar an kunna famfo hawayen ke zuba amma a hankali sai ta ji zuciyarta na sanyi, numfashinta na ƙoƙarin daidaita. Sai da Mummy ta ji Nabila na faɗi tiryan – tiryan cikin nutsuwa sannan ta dakata.

“Na san kila baki yi sallah ba. Je ki yi sallah ki yi shirin kwanciya sai ki kara kirana. Ni bari na yi shafa’i da wuturi.”

Kai Nabila ke ɗagawa tamkar mahaifiyartata ne kallonta. Bata jira ta ce komai ba ta kashe wayar, hakan ya saka Nabila ajiye tata ta nufi banɗaki. Alwala ta yi tai sallah inda ta dinga zubar da hawaye har ta idar. Hannayenta biyu ta daga sama domin addu’a amma leɓenta da zuciyarta sun kasa tariyo abunda zata roka.

Allah kai kadai ka san abunda ke damuna, Allah ya Allah ka min maganinsa.

Falo ta koma ta ɗauko Hajja ta saka tayi fitsari sannan ta canza nata kayan zuwa na bacci ta gyara mata kwanciya. Lokacin ne ta ɗauki waya ta kira Mummy.

“Me yake faruwa Nabila?”

Murmushi Nabilar ta yi.

“Ba komai Mummy. Dama Hussaini ne ya gaya nin ɗazu zai kara aure. Shi ne.”

Ba wani abu. Babu abunda ya fi karfin addua. Ki samu dai ki yi bacci kin ji? Damuwar namiji bata ƙarewa.”

A nan gaɓar suka yi dariya a tare kafin Mummyn ta ci gaba,

“Kar ki saka ma ranki wata damuwa ki zo ciwo ya kama ki. Ki yi ta addu’a kina salloli kina tasbihi.”

“In Allah ya yarda Mummy. Zan samu lokaci na zo kwanan nan In shaa Allah.”

A nan suka yi sallama sannan ta kashe fitilun ƙwai da suka mamaye ɗakin. Kwanciya ta yi tana janyo Hajja jikinta ta yi musu addu’a ta shafa. Abun mamaki cikin kankanin lokaci, bacci yayi awon gaba da ita. Dalilin samun baccin nata da wuri, idanuwanta, ƙwaƙwalwarta, da kuma zuciyarta a gajiye suke.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Soyayya Da Rayuwa 2 >>

2 thoughts on “Soyayya Da Rayuwa 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.