Skip to content
Part 17 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Sanye yake cikin sabuwar shaddarsa wanda ya ɗinka na musamman. Ƙamshin turare kawai ke tashi daga jikinsa. Ya ɗauko brush na taje kai ya shafe kan shi da ya sha mai yana sheƙi. Ya juyo ya kalli Hussaini da ke kishingiɗe a ƙasa da jikin gado yana latsa waya ya ce

“Wai kai ba zaka tashi ka shirya ba? Ka san dai babu hirar dare ko?”

“Kai ni ka ƙyale ni. Ka je kai kaɗai mana. Dole sai da ni?”

Hula ya ɗauko ya saka a kan shi

“Wai kai ba an ce ka haƙura da wannan  yarinyar ba? Lausa take ko wa?”

Hassan ne ya fara samun Alhaji da batun ya samu yarinya yana so a nema mishi izinin zuwa wajenta. Alhaji ya kira Hussaini ya tambayeshi ko shima da wacca yake so yace mishi eh akwai. Ya karɓi sunayensu da sunan unguwa ya ce su je zai neme su bayan ya yi bincike.

Ya ji Labari mai daɗi a kan Safina. Amma Lawisa dai hankalinsa bai kwanta ba sam. Saboda irin rayuwar da ya ji ana yi a gidan mijin mahaifiyarta. Sannan da yawa kam an ce akwaita da kule kulen samari duk da wannan ba shi ya dame shi ba. Tarbiyya yake dubawa kuma daga abunda ya ji, akwai ƙarancinta a gidan da take zaune ciki. Dan haka ya ba Hussaini shawarar ya canza wata tun abun bai yi nisa ba dan shi gaskiya hankalinsa bai kwanta ba.

Nan Hassan ya yi saurin cewa ai akwai wata ma Nabila ƙawar Safinarsa ce, aminan juna ne ma kuma ya san ba za’a samu matsala ba. Nan ya yaba halayen Nabila da ya sani amma yace a yi binciken a ji. Haushi ne ya hana Hussaini magana a lokacin. Saboda shi ya san mahassada ne suka shiga suka kitsa zancen. Ƙila ma wani wanda yake son ita Lawisar ne ya bada wannan rahoton.

“Na ce maka ban haƙura ba ko me?”

Haushi ne yake ƙara lulluɓe shi idan ya tuna. Dan kar ya dame shi ya saka shi tashi ya saka kaya fuskarnan babu annuri ya bi shi.

A can ɓangaren kuma Safina ta kafa ma Nabila ƙahon zuƙa a kan sai ta yi kwaliyya. Nan ta zaunar da ita ta sakata shafa hoda da ɗan janbaki harda zagaye bakinta da baƙin kwalli. Basa fita zance da mayafi sai dai hijabi kuma babu turare, sai dai ba zaka ji wari a jikinsu ba. Sun tashi cikin ƙoƙarin kiyaye dokokin addinin musulunci.

Nabila ce ta fara fita ta yi ma samarin nasu iso. Duk kunyar duniya ta isheta wai ita ce take ma saurayi kwaliyya. Hassan ne ya ke leƙa hanyar shiga gidan yana tambayar gimbiyarsa. Hakan sai ya bata dariya har ta yi murmushi.

Hussaini ya kafa mata idanu. Sai yau ya taɓa lura da murmushinta. Murmushi ne wanda ke bayyana kaɗan daga cikin haƙoranta. Kuma ya yi matuƙar amsarta. A nan Safina ta zo ta same su. Suka gaisa kowa ya samu waje da ƴar budurwarsa suka zauna suka yi hira. Ranar ne ma Hussaini ya san ya saki jiki ya yi mata tambayoyi a kan abunda ya shafeta. Shi bai ma san hirar me suke yi ba a da idan sun haɗu. Ya dai san basa wuce mintuna talatin sun musu sallama sun tafi dan an hana su dogon zance.

“Ka bata chance (dama) ka gani. Tana da hankali. Ga nutsuwa da kunya. Me kuma kake buƙata?”

Abunda Hassan ya ce mai kenan bayan sun shiga mota suna hanyar komawa gida. Amma ta yaya zai yi mishi bayani ya gane? Bayanin irin macen da yake so. Allah ya sani yana son farar mace. Shi duk ƴan matan da ya yi babu baƙa. Baya ma kallon inda suke balle su burge shi. Yana kuma son ƴar gayu. Mace mai wayewa ta sakawa a gaban mota. Matar da ba zai yi shakkar fita ko’ina da ita ba.

Ita kuma Nabila baƙa ce. Ga ƙumbiya ƙumbiya wanda mutane ke cewa kunya ce. Idan ya fita da ita ba zata saki jiki ba. Gashi yana da burin zaga ƙasashe da matarsa su buɗe idanu. Shi kawai bata yi mishi ba. Amma murmushinta, ya tsaya mishi a rai.

A hankali ya fara sabawa da Nabila. Ya san tunda Alhaji ya ce ba zai aura mishi Lawisa ba dole ya haƙura da ita. Bai san lokacin da ya saba da Nabila ba. Tana da shiga rai sosai. Sai ya yi ƙoƙarin ganin ya ɗorata kan tsarin rayuwarsa. Shi yasa ya shiga ya fita ya sama mata admission. Abun ya zo mishi da sauƙi da take son karatu. Ko bata yi aiki ba, ya san shiga jami’a zai buɗe mata idanu ya kuma wayar da ita Ya so ta samu BUK amma hakan bai yiwu ba sai Sa’adatu Rimi ya sama mata.

Ya kan zo ya gan ta kawai dan ya ga murmushinta mai sanyaya zuciya.

A ɓangaren Lawisa kuwa, sai ta zare jikinta daga nasu tun lokacin da ta dawo daga duba mahaifinta. Safina bata da aikin yi sai zancen samarinsu. Komai Hassan da Hussaini. Ita kuma Nabila ta dinga murmushin munafurci. Ji take zuciyarta kamar zata fashe idan Hussaini ya kira Nabila a waya. Ƙirjinta har suya yake yi. Dan haka ta ga gwanda ta fita harkarsu kar su hallakata.

Ranar kuwa da ta ji an saka musu rana kwana ta yi tana kuka. Zazzaɓi ya lulluɓe mata jiki. Haushin Nabila ya ƙara kamata. Ita duk wani abun arziƙi sai dai ta gani a wajen Nabila? Mahaifin Nabila ba kuɗi ya fi nata ba amma ya fi nata nuna damuwa da soyayya. Mahaifiya ma haka. Ita mahaifiyarta banda ashariya da faɗa babu abunda ke shiga tsakaninsu. Gabaɗaya ma bata gabanta. Sannan ace miji na kere ma sa’a ma ita zata samu? Ta san ba zata taɓa samun irinshi ba. Shi yasa abun ke baƙanta mata rai

Haka ta daure ta raka su fitar da anko da kuma kayan fitar biki. Shi ma dan mahaifiyarta ta fatattakota ne. Har ta fito bata daina mata faɗa ba. Hankalinta bai ƙara tashi ba sai da ta ga an kawo lefe. Ta san iyayen Zahra suna da kuɗi amma bata yi tunanin zasu samu irin wannan lefe haka ba.

Waje ta samu ta zauna a can baya ranar da ake dinner ɗin bikin. Kallon Hussaini kawai take yi. Kwata kwata basu dace ba shi da Nabila. Sai ta dinga hango kan ta a kujerar suna hirarsu ta masoya. Da aka tashi kai amare ma washegari nemanta aka yi aka rasa.

Da ƙyar ta je gidajensu shi ma sai da Nabila ta isheta da ƙorafi. Sai da suka kusa watanni biyu sannan ta je. Gidan Safina ta fara zuwa daga nan ta je na Nabila. Tana ta jefa idanu taga ko masoyin nata zai ɓullo amma shiru. Haka ta dinga jan lokaci ko zata saka shi a idanunta.

Tana shirin tafiya kuwa sai gashi ya dawo. Sai da ta ji zuciyarta ta yi tsalle. Muryarsa ta sakata ji kamar ta yi tsuntsuwa ta je gaban shi.

Nabila ta yi mishi sannu da zuwa ta karɓi kayan hannnunshi. Shi kuma ya tambayeta ya zaman kaɗaici. Sai da ya zo wucewa ta inda kujerun suke sannan ya lura da mutum. Sai da gaban shi ya faɗi da ya gan ta. Nan da nan ya ji son ta ya taso mishi. Da ƙyar ya amsa gaisuwarta ya shige ciki. Ita ma ta yi mata sallama ta tafi.

A ɗaki Nabila ta same shi ya kwanta duk jikinshi babu ƙwari. Da wanka zai yi amma sai ya ji ba zai iya ba. Zama ta yi kusa da shi tana tambayarsa ko da wani abun. Hannunta ya riƙe yana tambayarta ƙawarta ta ce mishi ta tafi. Rungumeta ya yi yana sauke ajiyar zuciya. Abunda ke gabansa zai riƙe. Ya san cewa shi da Lawisa har abada.

**

Tun kafin ya shigo yake tunanin yaushe rabon da yaga murmushinta? Ba murmushin ƙarfin hali ba ko na takaici ko wanda aka yi shi dan dole ba, wanda ya fito daga cikin zuciya. Gaskiya ya manta. Ba zai ce ga lokacin da ya daina gani ba. Shin me ya shige mishi gaba? Yaushe suka zama baƙin juna? Wata banɗashen gurasa da ake haɗawa da balangu ya biya ya saya mata dan ya san tana so sai kuma kunun aya.

Da ƙyar ya gano wajen dan a ƙalla an fi shekaru uku bai je wajen ba. A hakan sai da ya haɗa da tambaya. Ta yi mishi sannu da zuwa ta ci gaba da kallonta yayin da Hajja ke yin kala a kan wani littafi. Kitchen ya shiga ya ɗauko katon faranti ya juye banɗashen sannan ya ɗauko kofuna uku ya zo ya ajiye a tsakar falo.

Rigarsa ya cire ya baza a kan kujera ya zauna kafin ya kalleta ce

“Doll bismillah”

Yi ya yi kamar bai ga kallon mamakin da take yi mishi ba. A da yakan kirata da hakan saboda a cewarsa tana kama da ƴar tsana saboda ita ƴar ƙanƙanuwa ce. Duk sunan da ya faɗo mishi yana kiranta da shi. Beela ma da ya fi kiranta, rabon da ta ji shi ta manta. Balle wani Doll.

“Sauko mu ci”

“Meema da daɗi”

Jiki a sanyaye ta sauko ta zauna. Da ƙyar ta samu hannunta ya daina kyarma ta ɗauki guda ɗaya ta jefa a bakinta. Daɗin ya saka ta lumshe idanunta.

“Should I feed you?” (Na baki a baki?)

Ji tayi ta ƙware. Ya yi saurin tsiyaya mata kunun ayan a kofi ya miƙa mata. Idanunta har ya yi jaa saboda tari. Idan baya so ta ci ne ai sai ya gaya mata. Idan ba haka ba me ya kawo zancen bata a baki? Kallon ‘ya isa’ ta yi mishi. Ya yi murmushi bai ƙara cewa komai ba har suka gama cin abincin.

Shi da Hajja suka ɗauke farantin da kofuna ya wanke mata hannu ya dawo. Ya ce mata zai kwanta ya ɗan yi bacci. Bata ce mishi komai ba ta ci gaba da kallonta. Kafin la’asar ya tashi ya yi alwala ya ce mata kar ta yi girkin dare ya wuce masallaci.

Bayan magrib ya ce su shirya su fita. Doguwar riga ta saka ta yi kwaliyya harda ɗan janbakinta dan a rayuwarta tana ƙaunar ta ga ta fita tare mijinta. Sai kuma wani tunani ya faɗo mata. Tana shiga mota tace

“Ina zamu je?”

“Kin yi kyau”

“Ina zamu je?”

Ta ƙara tambayarsa

“Zaki gani”

Ta ƙudurta a ranta in dai wajen Lawisa zai kai ta to ko da kuwa kinkimarta zai yi bai isa ya shigar da ita gidan ba. Ta ji ranta yana ɓaci matuƙa. Dama ta san duk abunda yake yi salon yaudara ne. Zai ɗauketa ya kaita wajen masoyiyarsa wacca suka haɗu suka ci amanarta. Bata san hanyar gidan Lawisa ba dan haka sai da suka tsaya gaban gidan abinci sannan ta saki ran ta.

Suka zazzaɓi abunda zasu ci aka tafi kawo musu. Ya rasa hirar me zai yi mata. Da baya rasa abunda zai ce mata. Lokacin sai ya yi masa tamkar wasu shekaru aru aru ne da suka shuɗe. Wayarsa ya ɗauka ya ƙyasta mata hoto. Jin ƙarar ɗaukar hoto ya saka ta juyowa daga gyara ma Hajja maɓallin hannun rigarta. Bai daina ɗaukarsu hoto ba dan haka ta saka hannu ta kare fuskarta

“Shikenan tunda rowar kallon kyau ake min”

Lokacin da suka gama cin abincin an yi kiran Isha dan haka ya yi sallah ya ƙara jan su a mota suka nufi wata hanyar. Sai ya tsinci kan shi da bata labarin wasu abubuwan da ke faruwa a kasuwa. Abun gabaɗaya jin shi take wani bambaraƙwai namiji da suna Hajara. Kawai sai take bin shi da uhm ko Allah ya kyauta.

Katafaren shago suka shiga na sayar da kayan masarufi da kwaliyya da kayan wasan yara. Suka tsinci ƴan abubuwan da basu da shi a gida sai kuma na ƙwalam da maƙulashe. Ya saya mata kayan kwaliyya sai ƴar tsana da kayan girki na yara da ya saya ma Hajja.

Basu zarce gida ba sai da ya tsaya ya saya musu shawarma ko zasu ji yunwa har yake tsokanarta wai ya san ta da ci. A gida ta yi ma Hajja wanka ta saka mata kayan bacci sannan ta yi sallah ta ɗan ci abunda zata ci ta nemi waje ta kwanta bacci.

A nashi ɓangaren ya yi wanka ya yi shafa’i da wuturi ya kira Lawisa a waya. Yana ankare da lokaci, baya so lokaci ya shige har Nabila ta yi bacci. A gurguje ya yi mata sallama ya ce bacci yake ji. Ba dan ta so ba suka yi sallama ya kashe fitilar ɗakinshi ya nufi na Nabila.

Bayanta ya samu ya kwanta. Ji ya yi jikinta ya ƙame. Sai bai ji daɗin hakan ba. Kamar bata son abunda ya faru. Ba wai basa mu’amalar aurr bane. Kawai dai ɗan sumba ne da runguma da ke shiga tsakanin ma’aurata masoya jefi jefi ne ba tare da wata manufa ba aka ɗau lokaci babu shi.

Akwai gyara a al’amuransa. Dole ta ce baya son ta mana. Babu wani kulawa. Nan dukka wasu abubuwan da suka faru suka dinga faɗo masa. Tabbas Nabila mai haƙuri ce. Da shi ne da ya san baƙin ciki ya daɗe da kashe shi. Ga halin miji ga na mahaifiyarsa.

“I’m sorry”

Ya ambata a hankali cikin kunnenta. Nan jikinta ya yi sanyi. Kalaman da bata taɓa ji sun fito daga bakinsa ba kenan. Bai taɓa bata haƙuri a kan wani laifi da ya aikata ba. Ita ce mai bada haƙuri. Ko ta yi abun bada haƙuri ko bata yi ba. Wani lokacin ma tana bashi haƙuri a bisa rashin fahimtarsa.

“Ki yi haƙuri a kan duk wani abu da na miki da sani na da rashin sani na. Ki yi haƙuri a kan duk wani abu da ya faru. Ki yi haƙuri a kan Lawisa. Na san ban kyauta ba.”

Idanunta suka ciko da ƙwalla, tana jin sabon ciwo a ran ta jin ya ambaci sunan Lawisa.

“Ina son ki. Ki daina tunanin bana son ki. Ko ki dinga tantama a kai. Na san ni na janyo hakan amma ki yi haƙuri.”

Bata ce mishi komai ba sai jan numfashi da ta yi. To me zata ce mishi? Cewa zata yi ta haƙura? Ko kuma tace komai ya wuce? Tana jin shi yana ci gaba da tausarta da kalamai masu sanyaya zuciya har dai ya gaji ya yi shiru. Maimakon ta ji sanyi a ranta, sai ma wasu tunane tunane suka dinga mata yawo a rai. A haka bacci ɓarawo ya sace su dukka.

*****

Soyayya lubiya.
Anya akwai abunda Hussaini zai yi ya wanke kan sa a wajenku kuwa?

<< Soyayya Da Rayuwa 16Soyayya Da Rayuwa 18 >>

1 thought on “Soyayya Da Rayuwa 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.