Skip to content
Part 16 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Hajiya Mama ce zaune a kan filo da aka ajiye mata a ƙasa a kan kafet da ke jingine jikin bango. Ƙafarta da ke daure da bandeji ma na kan wani filo. Kula kula ɗin abinci ne a gabanta wanda ƴaƴanta mata da matan ƴaƴanta maza suka kawo mata suke aiko mata kullum. Amma babu na gidan Hussaini a ciki. Lawisa ba daɗin jikinta take ji ba amma ta san da babu makawa sai ta aiko mata. Bata san dalilin da ya sa Nabila bata kawo mata ba. Gwanda da halinta ya fara fitowa kowa ya gani.

Tunda ta ɗora idanunta a kan hoton Nabila ta ji bata yi mata ba. Bata yi kama da matar Hussaini ba. Duk tsare tsarenta na rayuwarsa, ita Nabila bata da mazauni a cikinsa. A hotunan saukar Zahra ta fara ganinta. Bata taɓa damuwa da ta ga hotunan ba sai da ta ji ƙawar Zahra ce kuma ta zo saukar sannan ta buƙaci Zahra ta nuna mata.

Ta so ace ƴar farar ce. Amma sai ta ga wata yarinya fayau babu ko hoda a fuskarta sai maiƙo take yi. Wani abu ya tsaya mata a wuya. Anya ma Hussaini yana da idanu? Ya tsallake waccar kyakkyawar yarinyar ƴar gayu ya tsaya kan wannan?

“Wannan ƙawar taku fa? Farar nan, an mata miji ne?”

Ita ce tambayar da ta yi ma Zahra. Bata ga yanda Zahra ta yamutsa fuska ba saboda idanunta na kan farar

“Oho ni ba wata ƙawata bace. Ƙila an mata din.”

Ta zaunar da Hussaini ta tambayeshi ko da gaske son Nabila yake ya jaddada mata son ta yake. Bata ce komai ba amma ta kuduri niyyar ko ba daɗe ko ba jima sai ta aura ma Hussaini matar da take ganin ta dace da shi da kuma rayuwar da take tsara mishi a ƙwaƙwalwarta.

Sai kuma ta ji sakamakon binciken da ta sa aka yo mata a kan ita Nabila. Take ta ji ba zata iya barin ɗan ta ya auri wacca zata cuce shi ba.

“Sai dai fa dangin mahaifiyarta basa zama da kishiya”

Ita bata iya bin malamai ba. Kuma a kan ƴaƴanta ba zata fara ba. Kuma ba zata iya zama tana kallo a mallake mata ɗa ba. Ta samu Alhaji ta gaya masa damuwarta amma ya kori maganar da cewa shirme ne nasu na mata. Ta nemi wata hujjar. Ba da son ranta aka yi auren nan ba.

Hankalinta bai taɓa kwanciya da Nabila ba. Ta saka idanu sosai a kan lamuran Hussaini ko zata ga wani sauyi a tattare da shi ta yi hanzarin tarar abun. Amma sai ta ga babu wani sauyi. Ta ɗauka ma da ya ɗauko auren Lawisa zasu san yanda zasu yi su hana. Ta san dai ta hana idanunta bacci a kan kar Allah ya basu ikon tarwatsa auren Hussaini da Lawisa. Allah ya amshi addu’ar ta gashi har an samu rabo.

Sallamar Hussaini ta ji sai ta ɓata rai ta amsa mishi a ciki.

“Hajiya ƙafar ce? A kira mai gyara?”

Taɓe fuska ta yi kafin ta ce

“Ni ƙafata kalau. Amma zuciyata ce babu daɗi”

“Subhanallah Hajiya Mama me ya same ki?”

Ganin yanda ya kwalalo idanu har wani zakuɗowa ya yi daga inda ya samu waje ya zauna sai ta ji ranta ya yi mata daɗi

“Kalli kwanukan nan, akwai na gidanka a ciki?”

Ba sai ya kalla ba dan ya san babu, amma hakan ya juya ya kalli kwanukan tare da girgiza kai

“Ita Lawisa na san tana kwance bata da lafiya amma ita ɗayar fa?”

Jin ta yi shiru alamar tana buƙatar jin ta bakinsa sai yace

“Eh gaskiya Hajiya ni nace kar ta kawo ganin yawan abincin da ake kawo miki. Ba cinyewa kike iya yi ba”

“To ina ruwanka? Idan ni ban ci ba babu wanda zan ba? Ai ko daɗi na ji a zuciyata zan saka maka albarka. Wannan a gefe, raini ne ko meye zai saka matarka ba zata iya zuwa ta min ya jiki ba? Katangarmu ɗaya fa! Ko a waya ba zata kira ta gaida ni ba? Nan Lawisa da ke fama da jiki kullum sai ta kirani babu dade babu rana..”

“Zata zo In shaa Allah. Bata ji daɗi bane”

“Ban san lokacin da ka fara ƙarya ba. Sai wani kakkare mata kake yi”

Tsaki ta yi ta rufe idanunta ta yi biris da shi yana ta bata hakuri. Tashi ya yi ya fita. Ya ciro wayarsa daga aljihu ya lalubi lambar Nabila. Bugun farko ta ɗaga, alamun wayar na hannunta a lokacin. Bayan ya amsa sallamarta ya ce

“Dan Allah alfarma zaki yi min. Farfesu nake so ki yi min na kifi. Zan samu?”

Ya san ba zata ki ɗin ba amma ya tambaya duk da haka. Mota ya hau ya tafi domin siyan kifi. Daga kan Alhaji har zuwa matansa gudu uku, duk wanda ya kwanta rashin lafiya to kuwa Nabila ta dinga jigilar girki kenan sau uku a rana. Ya taɓa ji tana tambayar Umma, bayan ta kawo mata abinci

” Ba kya son wannan ɗin? Me kike son ci?”

Da cikin Hajja ma bata fasa yi ma Hajiya Mama hidima ba. Shi ya rasa wannan rashin so na meye. Bai ga aibun Nabila ba. Bata da makusa. Bata gaza ta ko’ina ba. Lawisa ma abunda ya saka shi aurenta, soyayya ce. Yana sonta matuƙa.

Ko da ya isa gida, ya tarar har ta soya kayan miyanta ta tsai da ruwa. Kifin kawai take jira ta wanke ta jefa a ciki. Jikin kanta ya tsaya yana kallon abunda take yi. Bai taɓa yin girki ba, amma da gani zai yi wuya. Ya yi tunanin wanke kifin abu ne mai sauƙi amma sai ya ga lokaci na ta wucewa amma bata gama ba. Tsayuwa na neman gagararsa amma ita ko alamun gajiya babu a tattare da ita dan haka ya daure ya tsaya ɗin.

Da ta gama ta ƙara ruwa a cikin wanda ta riga ta haɗa ta ƙara maggi da wasu abubuwa. Sai da ta zuba kifin a ciki ta rufe tukunyar sannan ta juya ta koma ɗaki ba tare da ta kalli ko inda yake ba. Sai ya ji abin ya taɓa mishi zuciya. Sau nawa yana ƙin ce mata komai? Haka take ji?

Yana nan a tsaye ta dawo kitchen ɗin. Ta buɗe tukunyar ta ga ta dahu sai ta kashe. Food flask mai kyau ta ɗauko ta juye dukka ta saka mishi a cikin kwando.

“Ba zaki ci ba? Ɗibar mana idan na dawo mu ci”

Babu musu ta ɗiba musu. Yana son ta je ta duba Hajiya Mama amma yana duba yanayinta. Kamar ita ma bata da lafiya. Idan ya dawo zai zaunar da ita ya ji.

Kaɗan Hajiya Mama ta ci ta matsar da kwanon da ta ɗan ɗiba

“Irin wannan yaji haka? Allah ya kyauta”

Sam sai ya ji hakan bai yi mishi daɗi ba. Dan haka ya tashi ya yi mata sallama ya tafi gida. A ɗaki ya sameta tana kwance ta yi shiru.

“Tashi zamu yi magana. Me yake damunki? Baki da lafiya ne?”

Lumshe idanunta ta yi kafin ta tashi zaune

“Tambayarka nake son yi”

Ya yi mata kallon rashin fahimta amma ya bata damar yin tambayar

“Me yasa ka aure ni bayan ba ni kake so ba? Lawisa kake so na sani. Me yasa ni ka ce kana so na zaka aure ni?”

Yawu ya haɗiya kafin ya sauke numfashi

“Ni nace bana son ki?”

“Ba sai ka fada ba. Alamu sun dade suna nunawa ni ce dai ban gane da wuri ba”

“Ban ce bana son ki ba”

Ganin bai shirya gaya mata gaskiya ba sai wani zagaye zagaye yake mata ta tashi ta bashi waje. Ta san jin dalilin auren nata bayan Lawisa yake so ba zai ƙara mata komai ba amma tana son sani. Tana son sanin dalilin da yasa aka aureta bayan ba sonta ake yi ba. Ko shi yasa Hajiya ta kasa son ta? Saboda ɗanta ba ita yake so ba. Duk soyayyar da ya gwada mata karya ce? Duk wani ‘ I love you ‘ da ya taɓa gaya mata na yaudara ne?

Yana yawan aiko mata da saƙonni duk ƙarya ne ashe? Duk wannan kulawar ta mece ce? Duk zuwan nan da yake yi a gajiye ya saka ta a idanunsa na mene? Ko na saka ran zai ga Lawisa ne? Zuciyarta ce kawai take suya. Saboda a ganinta an maida ita shashasha mara wayau. Rabon Hajja ne ya saka Hussaini aurenta

**

“To ka gaya mata mana. Kar ka je ka saka ma ƴar mutane damuwa ba gaira babu dalili”

A gajiye Safina ta ƙaraso ta zauna a kujerar kusa da shi. Haka boko yake da azaba? Wanda bai isa ba ma sai ya dinga raina maka wayo. Tun biyu ya kamata a ce sun dawo. Amma wani ɗan yaro wai shi lakcara ya ce su tsaya fixed class. Kamar ta kifa mishi mari. Da ƙyar ya barsu suka fito bayan la’asar. Ko sallar bai samu a jam’i ba.

Mayafinta ta cire tana linkewa shi kuma ya dawo da hankalinsa kan ta dan ya gama wayar.

” Ƴar wa za’a saka ma damuwa?”

“Ƙawarki aminiyarki”

Ba sai ya yi mata karin bayani ba ta san zancen wa ake yi. Ta taɓe baki

“Na nawa kuma? Allah dai ya raba mu da hawan jini”

Girgiza kai ya yi yana murmushi kafin ya ce

“Ameen. Ya makarantar?”

Ta gaya mishi duk wani abu da aka yi a makarantar sannan ta ƙara da ce mishi ranar alhamis zasu fara test. Addu’a ya yi mata na samun nasara. Wata leda ta hango a gefenshi take tambayarsa ta mece

“Afrah ce ta bada aka saya mata rogo”

Kallon juna suka tsaya yi. Ba sai ya ƙara cewa komai ba, ciki ne da Afrah.

“Madallah”

Shi ne abunda ta iya samu bakinta ya furta kafin ta miƙe ta nufi sashenta. Ba abun mamaki bane. Dama ai ta san komai daren daɗewa hakan zata faru. Ta shafa cikinta bayan ta kalli kanta a madubi. Ita ma tana son ta haihu. Amma an hana a asibiti. Sun ce a shawarce ta bari sai bayan ɗan lokaci. Idan ba haka ba kuma a yi mata aiki a ciro abunda ke cikinta gudun lalacewar wannan aiki da aka yi mata. Ita kuma duk wata harka da za’a feɗeta gudunta take yi. Ta ɗebar ma kan ta shekaru biyu.

Sai ta tuna ai rabonta ma da ta saka Afrah a idanunta an fi sati uku. Nan ƙwaƙwalwarta ta fara lissafin yaushe aka yi auren na su. Bai ci ace ta haihu ba. Auren dai zai yi watanni kusan bakwai. Duk yanda zata yi ta ganta kuwa yau sai ta gan ta. Ko zuwa zata yi bangarenta ta yi mata Allah ya sanya alheri? Bari dai idan ta ga bata ganta ba hakan zata yi.

Ta yi sauri ta shiga ta yi wanka ta fito da alwalarta ta yi sallah sannan ta saka dogowuwar riga mara nauyi na wani yadi. Falon Hassan ta je. Ta san da wuya Afrah ta je tunda ba ranar girkinta bane. Haka dai ranar ta ƙare bata ga gilmawar Afrah ba.

Sai wata dabarar ta faɗo mata. Dafadukar shinkafa ta sa aka yi mai manja wanda ya sha daddawa da barkono ta tafi makaranta da shi. Bata yarda ta tafi makaranta babu abinci tunda bata san iya dadewar da zata yi ba. Ta saka aka ajiye mata ragowar a fridge. Da ta dawo ta ɗumama ta saka a cikin flask na abinci ta tafi falon Hassan

“Ko zaka tambayeta idan tana sha’awar shinkafa mai man ja. Na san masu ciki basa rasa son shi”

Sai ya ɗan yi jim kafin ya kaɗa mata kai. Ya san Safina farin sani, duk kirkinta bai kai ta yi ma kishiya tayin abinci ba. Ko dai ta fara saukowa ne? Waya ya ɗauka ya kirata yake tambayarta ko tana so ta ce eh. Ya ce ta zo ta karɓa.

“Da har zan bada abincin kuma sai na tuna muna da mai ƙaramin ciki”

Bai dai ce mata komai ba sai ya janyo kwanon abincin ya ci loma biyu. Ya yarda Safina ba zata cuci wani ba amma kuma ɗan Adam bashi da tabbas. Ya ji shiru cikinsa bai juya ba sai hankalinsa ya ɗan kwanta.

Yana kallon yanda Safina ta bi Afrah da idanu bayan ta gaisheta ta nemi waje ta zauna. So yake ya karanci abunda ke kan fuskarta amma bai samu dama ba.

“Ashe an samu ƙaruwa. Allah ya raba lafiya”

“Ameen”

Shi ne abunda Afrah ta ce tana ɗan murmushi. Kwanon ya mika mata. Ko ta kan cokali bata bi ba, ta saka hannu ta fara ci. Nan da nan ta cinye. Ta so tafiya amma ya ɗan tsayar da ita ya ce ta zauna abincin ya tsirga mata.

Ita kuma Safina bata samu ganin abunda take son gani ba saboda katon hijabin da Afrah ta saka na fama. Kasa haƙuri ta yi ta tambaya ko ta fara zuwa awo. Ta bata amsa da eh. Hakan ya sa ta yi hasashen cikin ya tafi kusan watanni huɗu ko fi ma. Ta kaɗa kai

“An kusa sauka ma ai tunda an ci rabin tafiyar. Kin san EDD ɗinnan bai fiya zama dai dai ba fa. Haihuwar Iman August suka ce min ƙarshe amma tsakiyar July na haihu”

“Na ɗauka ai ƙara sati ake yi ko a rage”

“Haka dai ake cewa amma ni tun kan Iman na dawo rakiyarsu. Yaushe suka rubuta miki?”

Sai a lokacin Hassan ya harbo jirginta. Kamar ya fashe da dariya amma ya kanne sa ya yi saurin cewa da Safina

“Ɗan ɗauko min wayoyina a kan gado zan leƙa na duba Hajiya Mama”

Kamar ta saka kuka haka ta ji. Ta danne zuciyarta ta miƙe ta shiga ɗakin nashi. Ta duba kan gado da durowowin gefen gadon bata gansu ba. Ta duba teburin jikin madubi nan ma bata gani ba. Ko da ta fito gaya mishi sai ta ga babu Afrah babu dalilinta. Ran ta ya kai maƙura gurin ɓaci.

“Ban gan su ba”

Ya saka hannu ya shafa alhijun wandonsa

“Ah kin gan su a nan. Zaki raka mu ne? Da yaran zan tafi”

“Na gaji. Sai dai gobe”

Ita kaɗai take ta kumbure kumburenta tana kwafa bayan sun fita. Haka kawai ta samu dama amma Hassan ɗinnan ya rushe mata shi. Ɗazu daurewa kawai tayi tana jan Afrah da magana. Yarinyar da bata ƙi ta buɗe idanunta ta ga bata gidanta ba.

Wayar Hassan ce ta shigo. Ta amsa tana tura baki

“February zata haihu”

Ya ce mata yana dariya

*****

A yi min afuwa. Na san shirun ya yi yawa. Amma ku daure da comments ku ga update kwana kusa In shaa Allah.

Nifa ban gane ma Hussaini ba

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 15Soyayya Da Rayuwa 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.