Skip to content
Part 7 of 9 in the Series Soyayyar Da Na Yi by Habiba Maina

Bata durkusa domin ɗaukan takardun nata ba, sai tsayawa tayi ta ware idanu tana kallon shi, shima ɗin har cikin idanu yake kallon ta. zuciyarta, ta tsinke Kat! wadda ta ke tunanin ma anya zuciyar tata na jikin ta kuwa? wannan tsoron yasa ta kasa cewa komai, haka kuma shi Abdul ɗin ya kasa cewa komai, ta kuma kasa tsunkuyawa ta ɗauki takardun nata. Abdul kamar ya fahimci wani abu daga gare ta, gyaɗa kai ya yi kawai sannan ya zame, ya ci gaba da tafiyar sa.

ai kuwa magana sai ya ɗauki sashen nasu tsakanin ɗaliban, sai kuskus kake ji, wanda tsegumin nasu ya kasa shiga kunnen mai sauraro. 

mamma tafi minti biyar tana tsaye, ta kasa motsi, sai hasbunallahu wani’imal wakil! ne ya biyo bakinta. Tare da ajiyar zuciya, ta dubi takardun ta durkusa cikin sanyin jiki da hawayenda suka maƙale mata a idanu cikin rawar murya take sake faɗin,

“Don Allah don Annabi na roke ki ƙaddara kada ki haɗa Ni da Abdul.” addu’ar nan tayi Sa’annan, ta nufi ajin su a inda yake ta bayan Library, su kuma ɗalibai mazan na karkashin bishiyar da ke kallon librarin, a yayinda ta hango ɗaliban nasu a zaune sun cika benci. ta ƙarasa tayi musu sallama suka amsa sukayi Musabaha. ɗaya daga cikin su take ce da ita,

“new comer Sai yanzu?” tana mai ƙare mata kallo duk da ta fahimci wata damuwa a fuskar, mamma amma bata tambaye ta me ke damu ta ba, saboda basu saba ba, yau ne ma ranar da magana ta fara haɗa su, don haka sai ta ƙara da cewa,

“gashi su maliya ma basu karaso nan ba, ɗazu dai na gansu a department amma har yanzu shiru…, Basu iso nan ba.”

“okey! Kina nifin suna department kenan? to Bara in jira a can.” Ta faɗi a yayinda ta nufi wurin zama.

“to shikenan.’ inji ɗalibar.

Abdul kuwa zuciyar shi tafasa yake yi, ji yake mamma da gangan ta buge shi, kamar dabara ce irin ta neman soyayya, don haka ya kumbura matuƙa yana tunanin yadda zai yi ya dakatar da ita daga dukkan wani gwaji. shamsu kuwa ya fahimci haka, duk yadda yaso ya kwantar da hankalin Abdul akan yadda, abunda ya haɗa shi da mamma, amma shi sam! ya ƙasa fahimta. cikin haka ne ya zabura zai je ya same ta, amma shamsu ya riƙe rigar sa.

“Abdul karka je ka tinkari yarinyar nan, kaga da kai da ita duk masu laifi ne tunda duk kun bigi juna, kuma bisa rashin sani. to me dalilin da zai saka zuwa yi mata gargaɗi? ina mai baka shawara kada kaje kayi abinda zakayi da na sani.” Kallon shamsu Abdul ya yi da gefen fuska da ido ɗaya ya kauda kai, yana wa Shamsu kallon be fahimci abinda shi ya fahimta ba, sai fisge rigar sa ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya nufi wurin mamma.

mamma kuwa taje ta zauna kan wani benci da ke gefe tare da ajiye jakan ta, baironta ne ya faɗi ta tsunkuya domin ta ɗauko, sai hannuwa Taji sun sauka kan desk ɗin kamar saukan dutse, saukan hannuwan nasa ne suka sake firgitata, ta ɗago kai da sauri don ganin waye domin dama a cikin firgicin take.

Ido hudu sukayi da abdul, shi kuma kallon ta yake bai ce komai ba, kaman wanda yake kirkiro abun faɗa. mamma ta zaga cikin tunanin ta tayi duk wani hasashe amma ta kasa hasashen me Abdul yazo ya faɗa mata, cikin karfin hali da da dabara ta kau da tsoron da ke fuskarta ta tambaye shi,

“Yanzu Kuma me kazo ka sanar da Ni?” ta faɗi zuciyar ta na bugawa, kai da gani kasan jarumta ce kawai domin bugun zuciyar ta na fitowa a fili numfashi take yi da kafaɗar ta yake yin sama yayiyo kasa, sai kakkausar tambaya ya yi mata da gargaɗi. 

“Me yasa kike tunanin Ni zan so ki?

Me yasa kike sawa ranki abunda bazai taɓa yiwuwa ba?

To ina so in yi miki gargaɗi na karshe.

Ina so ki sa a ranki cewa, Abdul bazai taɓa son ki ba.

Bana sonki Ramlat! kuma bazan taɓa son ki ba.

Saboda haka ki kiyaye, idan ba haka ba, zaki sha wahala.” Abdul yana faɗin hakane da karfin murya wadda ya jawo hankalin ɗaliban duk sukayi ca…! Amma babu wanda ya dakatar da Abdul.

Nan take mamma Taji duk wani tsoro da fargaba sun ɓace a ruhinta tare da ɓacin rai ta miƙe tsaye wanda yasa Abdul ɗin ya saki desk ɗin nata da ya dafa suka miƙe tare suna kallon juna har cikin idanu. babu abunda take ji a ranta na tsoro, burin ta kawai a yanzu ta furta wa Abdul ɗin abunda ke cikinta, ko me zai faru ya faru. don abun ya ishe ta, ta yaya za’ace abinda bata taɓa tunanin shi ba, a ce yau shi za ayi mata gargaɗi a kai. suna cikin haka ne sai maliya da na’ima suka zo, ganin taron yasa suka zo da gudu, maliya ce ta kutsa tsakanin su ta isa wurin mamma ta dafa kafaɗarta, tana cewa,

“Ramlat… meke faruwa ne?” ta dubi Abdul ɗin ta ƙara da cewa,

“yau kuma me ya sake haɗa ki da Abdul?” Kallon ta mamma tayi na ɗan minti ɗaya sannan ta ce,  

“maliya… yau ina so in isar da sakon zuciya ta zuwa gare shi, saboda yau Nima gargaɗi na na karshe a gare shi kenan.” ta faɗi sannan ta ci gaba da cewa,

“Abdul ina so ka sani, kamar yadda kake tunkaho baka soyayya to haka Nima bana yi, ban taɓa yi ba kuma ban san yadda ake fara ta ba. 

Kuma kamar yadda kake ji babu wacce kake so, kuma babu wacce zaka so a makarantar nan, 

To Nima haka babu wanda nake so kuma babu wanda zan so a makarantar nan. haka kuma ina so ka sani, idan Ni zan so wani ɗa na miji a makarantar nan, to bazan so ka ba.

Saboda haka, ka cire duk wani tunani na cewa, Ramlat! tana sonka. domin indai Ramlat ce, to ko a mafarki haka bazai taɓa faruwa ba…” ta dakata da faɗin haka na ɗan minti ɗaya sannan ta ci gaba da cewa,

Saboda karatu ya kawo Ni makaranta ba soyayya ba,

“Munyi karo ɗazu Ni da kai, cikin rashin sani mun bigi juna, kayi hakuri.” Ta dakata da faɗin haka tana kallon cikin idanun sa shima haka yana kallon ta ba giftawa, cikin mamaki Abdul ɗin yake kallon ta domin wannan karon babu tsoro a idanun mamma.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayyar Da Na Yi 6Soyayyar Da Na Yi 8 >>

1 thought on “Soyayyar Da Na Yi 7”

  1. Waiyyoh Ni ba na fahimci Abdul ba gargadi ne kawai yake mata akoi halan soyaya ko menene gaskiya labarin yayi dadi muna jiran na gaba Allah ya kara basira

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×