Skip to content
Part 45 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Kwance take akan kafet, tayi matashi da filon kujera, ledojin takeaway din data saka direba ya tsaya da ita, ta kwaso, ko budewa batayi ba saboda gajiya. Lokacin da Jamb ta fito, tasan tayi kokari tunda tambayoyin basu wani bata wahala ba, amman sai da tayi mamakin ganin tana da maki 224. Yanda kuma Jabir ya dinga juya takardar, shi kanshi tasan mamakin yayi, ko kuma baiyi zaton tana da kokari hakan bane ba, yadai ce mata.

“Zanyi magana, saboda da an fara siyar da form a BUK sai a siya miki.”

Ya kuma cika mata wannan alkawarin, ko da tace masa zataje makarantarsu dan ta karbo ainahin sakamakonta na jarabawar gama sakandiri wato WAEC, haka ya dauki kudi masu dan nauyi ya bata, to abinda ake biya dinma ba wani mai yawa bane ba, ta dai hadu da wani Malaminsu na darasin lissafi, Malam Manu, haka ya dinga fara’a, sosai kuma ya nuna mata jin dadinshi data sanar dashi sakamakon data samu a Jamb, da makarantar da take so ta cigaba harma da bangaren data zaba.

“Nayi farin ciki sosai Sa’adatu, saboda kin zabi fannin da zaki taimaki al’umma, musamman mata ‘yan uwanki. Kina cikin daliban dana dinga fatan su samu damar zurfafa karatunsu saboda irin kokarin da kike dashi.”

Da zata tafi kuwa, ta bashi dubu uku tace ya saka kati, da kyar ya karba yanata mata godiya da fatan alkhairi. Haka tazo ta adana, su Indigene kuwa da ake bukata, babu wata wahala data sha saboda magana ce ta in kana da kudinka, babu wanda zai bata maka lokaci, sai gashi ta hada duk wata takarda da za’a iya nema. Ko bayan da aka siyi form din, Jabir kuma ya sanar da ita zatayi jarabawar sharar fage, wato UTME, saita rokeshi daya tambayi Sa’ad ko suna da ajin horarwa, aka kumayi sa’a suna dashi din, ya biya mata. Sai dai karatun yasha bamban da wanda sukayi lokacin Jamb, wannan yafi tsauri, sosai ta dage, yanda taci Jamb dinta haka take fatan karta samu matsala a wannan dinma. Sai dai jikinta yayi sanyi matuka ranar da zatayi jarabawar, ganin yawan mutane, ko a wajen Jamb din da tayi bata ga mutane masu yawa irin haka ba.

To wannan wama zasu ba gurbin karatun wa za’a hana kuma? Ta tabbata wadanda suka ninkata kokari a wajen ba zasu kirgu ba, bata wani diririce ba, kasancewar akwai Haidar da aka hadata dashi, ma’aikacine anan cikin makarantar, tunda suka shiga da direba kuma ta kirashi tana fada masa dai-dai inda suke, shi yazo ya tafi dasu, bayan ya karbi slip dinta yaga inda zatayi jarabawar, a shekaru dai tana masa kallon zai iya girmar Jabir, amman sai sukunyar da kai yakeyi yana kiranta da Hajiya. Duk yasa ta dinga jinta wani iri, nan ya fada mata duk abinda yake tunanin ya kamata ta sani, kafin sukayi sallama, ta rasa inda zata zauna kafin a shiga jarabawar, gashi babu wanda tagani shi kadai a tsaye, kamar kowa akwai wanda ya sani a wajen, ita kadaice bata magana da kowa, hakan kuma ba karamin takurata yayi ba.

“Sannunki.”

Matashin daya karaso kusa da ita ya fadi bayan yayi mata sallamar data amsa tana dorawa da.

“Yawwa, sannunka kaima”

Links din hannun rigar shaddar da take jikinshi ya gyara, tukunna ya tsaya daga gefenta, duk da ba wata magana suka sakeyi ba taji dadi, haka akazo aka gama tantancewar da za’ayi, suka shiga inda zasu zana jarabawar, bawai tayi mata wahala bane ba, bama zatace ga abinda ya gajiyar da ita ba, data fito kuwa, makoshinta ya bushe, ga wata rana da zafin data manta yaushe rabonta dashi ya daketa yana kara mata kishin da takeji, cikin sa’a tana juyawa taga matashin nan da yayi mata magana dazun

“Dan Allaah ina zan samu ruwa anan?”

Ta tambayeshi, da dan mamaki akan fuskarshi ya kalleta

“Sai dai kizo muje, kamar naga wani canteen akan kwanar can”

Numfashi ta dan sauke

“Yawwa nagode kuwa”

Haka suka karasa har inda yace din, amman akwai mutane, shiya turmutsa ya siyo musu ruwan harda coke, ya bata duka robobin biyu

“Nawa kudin ya kama?”

Kai ya girgiza mata

“Haba dai, kibarshi”

Idanma ta tsaya gardama baiyi mata kama da matashin da zai karbi kudin ruwa da coke a wajenta ba, gashi duk da karancin shekarunshi akwai nutsuwa sosai a tare dashi

“Nasir Kabir Getso”

Ya fadi

“Sa’adatu Habibu”

Ya jinjina mata kai, kafin yayi mata sallama ya wuce, bayan ta sakeyi masa godiya.  Haka ta bude ruwan tasha, yana kuwa kulle mata ciki, ko karin safe batayi ba, ta kasa saboda tsoron yanda jarabawar zata kasance mata, haka ta taka dan direban yace zai jirata ne. To taso ma tacewa direban ya ajiyeta gidansu, sai kuma ta fasa, gwara ta ware rana daya, tayiwa su Nabila magana, duk sai su hadu acan din, a zauna asha hirar yaushe gamo. Sai dai suka tsaya tayi siyayyar da gata nan a ajiye ta kasa budewa saboda yanda take jinta a gajiye. Kusan mintina sha biyar ta kara a kwancen kafin ta tashi ta shiga bedroom, ta rage kayan jikinta, ta shiga bayi, wanka tayi da ruwa mai zafi, tayo alwalar azahar ta fito, sai taji dadin jikinta. Har da ta idar da sallar ta kunna tv, tana kallo tana ciye-ciyenta. Wayarta da take gefe tayi kara alamar shigowar sako, ta dauka ta duba

“Ya exam din?”

Ta ajiye cokalin ta, tana rike wayar da hannu biyu, ta rubuta masa amsa

“Alhamdulillah. Akwai rana sosai dai yau, sai yanzun ma na samu nake cin abinci”

Ya kusan mintina biyar, dan batayi tsammanin zai sake cewa komai ba

“Me kika dafa?”

Ya tambaya

“Babu abinda na dafa, siya nayi”

Bai amsa ba, itama bata sake ce masa komai ba.

Kuma bata sakama ranta ganinshi a ranar ba, shisa ta cigaba da sha’aninta har lokacin kwanciya, danma sun tsaya chatting da Nabila, saboda mijinta baya gari, Nabilan tace ana daurin auren abokin wasan shi, to kuma shine babban abokin ango, suna daura, inda can ne za’a daura auren, su tsaya su taho da amarya. Har wajen sha biyu saura sannan ta kwanta. Shisa washegari bata tashi ba sai wajen tara, ta kuma ci karo da text din Jabir yana cewa ta soya masa doya da kwai, batama da doyar, dan haka data shiga bayi ta dauraye fuskarta ta sake wanke baki, saita dauki kudi ta saka hijabinta, taje ta bawa Maigadi, ya taba siyo mata doya, taji dadin doyar sosai, ya iya zabe. Sannan ta koma cikin gidan ta danyi abinda zatayi.

Bai kuwa dade ba sosai ya dawo, bata bata lokaci ba ta dora doyar dan ta dafa, tana da sauran farfesun kayan ciki a fridge, ta fito dashi ta ajiye, kafin ta gama doyar ya saki. Ta dauko wayarta ta kunna wani audio book da tayi downloading daga YouTube, a channel din Abokiyar Hira, dan in ba nan ba to sai kuma channel din Tsakar Gida, su biyun tafi son karatunsu akan na kowa. Komin yawan littafi batajin asarar downloading, ko baiyi dadi can ba, yanayin karatun Abokiyar Hira saiya dan sa littafin yayi armashi, balle kuma wannan din yanayi mata dadi. Ta gama soya doyar kenan, ta juye farfesun a tukunya, Jabir ya shigo kitchen din

“Yunwa nakeji”

Ya fadi a maimakon amsar gaisuwar da tayi masa, hannuwanshi ya karasa ya wanka a jikin famfo, yazo ya dauki plate, da kanshi ya zuba doyar da tayi kyau sosai a ido, sai kamshi takeyi saboda koren tattasai da kuma albasa data yanka a cikin kwan, haka ta dan saka kayan kamshi kadan. Daya gutsiri daya ya tauna kuwa sai daya sauke numfashi, tukunna ya karasa yana sumbatar gefen kuncin Sa’adatu da take kara wutar gas dan farfesun yayi saurin dumamuwa

“Nagode…”

Ya fadi, yana dorawa da

“Ki hadomun shayi, karki sakamun madara amman…”

Ya kuma fice daga kitchen din, tana da shi a flask, data dafa da citta da kuma kanamfari, ta zuba, ta saka masa sikari, da kuma cokali a cikin mug din, taje ta kai masa falo, ta koma kicin din, ta karasa, ta dibarwa maigadi, ta saka hijabi ta fita takai masa, tukunna tazo ta zubo itama ta zauna, sai Jabir ya sauko kasa shima, suka karasa karyawar tare. Ya mike yana zuwa ya wanko hannunshi

“Yau aiki yayi mun yawa a kasuwa, zan koma, amman anjima zan dawo…”

Addu’a tayi masa tana tambayar shi ko ta saka abincin rana dashi, ko kuma akwai abinda yake marmarin ci, ya girgiza mata kai. Kamar yanda yace mata zai dawo, ya koma din, wajen hudu da rabi, ya sameta zaune akan doguwar kujera, tana kallon wani fim, a gefe kuma wani bowl ne cike da kayan marmari data yayyanka dai-dai sakawa a baki, ta kuma saka cokali mai yan yatsu a ciki. Kafin ya zauna saida ya dauko bowl din ya dawo dashi tsakiyarsu

“Banfa yanka da kai ba”

Yayi murmushi yana zama

“Haba yarinya, ke kinma isa”

Shima hankalinshi ya mayar kan fim din yana kuma damunta da tambayoyin da take amsa masa a gajarce

“Ba zaki bani labari yanda zan gane ba ko?”

Turo baki tayi

“Kabari a gama to, sai in baka labarin abinda ya faru daga farko…”

Saboda babu abinda yake saurin cakar da ita irin tana kallo ana damunta da tambaya, saboda ana raba mata hankaline, sai Jabir ya dauki remote din yana kashe tv din gabaki daya, taja numfashi cike da mamaki, data kalle shi saiya daga mata gira

“Yanzun saiki bani labarin kinga”

Hannu ta mika da nufin karbe remote din ya matsa gefe, data sake mika hannu saiya rike, ya ajiye remote din can gefe, ya mike yana mikar da ita

“An fasa kallon nan gabaki daya Sa’adatu”

Sanin da gaske yake, yasa ta fara yi masa magiya

“Dan Allaah ka tsaya kaji, zan baka labari ai”

Kai yake girgiza mata

“Na fasa ji kuma”

Daya fara janta tana tirjewa saiya dagata cak, duk kuwa ihun da takeyi bai sauketa ba, dan yanda yasa karfi ya riketa ma batayi yunkurin kwacewa ba, ya shiga daki dasu wayarshi da take cikin aljihu ta soma ruri, daya sauke Sa’adatu da take maida numfashi kan gadon, saiya zaro wayar, Aisha ce, dan har kiran ya yanke, data sake kiranshi saiya kashe karar wayar gabaki daya. Bawai yau ya fara yi mata haka ba, ranaku mabanbanta, ko idan yana wani aikin, sai idan ya gama ya kirata, amman yau wani abune yakeji na rashin jin dadi na kawo masa mamaya, kamar kuma gargadin shi yakeyi. Sai dai sau nawa yake kin amsa wayarta idan yana tare da Sa’adatu?

Lokacin da yabi Sa’adatu kan gadon, ya kuma saka karfi ya ture wannan abin da yake tason isar masa da wani sako

Ko a mafarki bai hango zai jima yana dana sanin kin daukar wayar Aisha ba

Kamar yanda kuma bai hango yau din zata kare masa bane da wani babban sauyi da ba rayuwarshi kadai zai taba ba

Bayaso yayi wani kwakkwaran motsi da zai raba Sa’adatu da jikinshi, tayi wani luf da ita, duk da daga yanayin yanda take sauke numfashi yasan ba bacci takeyi ba, ya dago hannunta da yake cikin nashi ya sumbata yanajin wani irin yanayi da ya rasa daga inda yake taso masa, ga kuma duhun da yake kara lullube dakin na tabbatar masa da ana gab da kiran sallar Magriba kowanne lokaci, yau dai, yanayin da yakeji na sakashi son kara riketa na wasu mintuna, kara jin duminta da kamshin turarukanta kafin ya zameta daga jikinshi. Dakyar ya iya mallakar kanshi ya zameta ya mike zuwa bayi. Lokacin daya fito bata dakin, saiya saka kayanshi, ya dauki wayarshi ya saka a aljihu, haka ma mukullin motarshi. Ya saba ya wuce ko da baiyi mata sallama ba, gashi an fara kiran sallar Magriba, daya fita daga dakin, saiya taka zuwa na kusa dashi, lokacin ta fito daga wanka, daure da towel a jikinta.

Ita kadaice yaga zata shiga wanka, ta fito daure da towel, amman jikinta da ruwa, har kanta zakaga yana tsiyayar da ruwa, lokutta da yawa sai ya saka wani towel din saman kanta ya murza yana tsane mata shi, haka zai jawoshi ya goge mata sauran fuskarta ma zuwa wuya, yau daya taka saiya tallabi fuskarta, yanajin lemar ruwan da yake jikinta na ratsa hannuwan shi

“Me yasa bakya son goge jikinki?”

Ya tambaya a karo na farko yau

“Mantawa nakeyi”

Ta amsa da dukkan zuciyarta, ita tunda ta tashi a gidansu towel daya ta taba gani, shima wani tsohon towel ne da suke goge tsakar daki dashi idan angama shara, kowa in zai shiga wanka da zani yake shiga ya fito, to ita data gama wanka ta dauro zanin zata fito, kafinma ta dauko kayan da zata saka tazo ta shafa mai jikinta ya gama bushewa. Yanzun kuma ga towel din nan wadatattu a kowanne bayi, amman rashin sabo da kuma mantuwar kamar yanda tace masa, goshinta ya sumbata, ya kuma rankwafa yana sumbatar labbanta a hankali, sanda ya janye, sanyin da takeji jikinta yayi bashi da alaka da sumbar daya manna mata, wani irin sanyin jikine da zuciyarta take ce mata tasan irinshi, ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, amman inda tasan irinshi dinne taketa lalube ta rasa. Lokacin da Jabir ya juya yana takawa da nufin barin dakin, saita bi bayanshi, haka kawai tabi bayanshi har kofa yau.

Ko daya murza mukulli ya bude kofar ma, ya juyo ya kalleta sai zuciyarta ta karye, sanyin jikin da takeji yana karuwa, harya nuna akan fuskarta, murmushi yayi mata, ya mika hannu ya dafa kanta yana yawo da tafinshi akan gashinta yanda yakanyi, da babu kitso ma, zai zira yatsun shi a cikine ya yawata yana hargitsa mata duk wani gyaran gashin da tayi, bai kuma ce komai ba ya fita yana jan kofar

Bata san me yasa take son fassara shirun shi ba

Me yasa take jin a daya daga cikin fassarar akwai bankwanan da bai furta mata ba

Wani irin tsoro ya tsirga mata har yana sa tsikar jikinta tashi, babu shiri ta wuce ta koma daki, ta daura alwala, gara tazo ta tayar da sallah ko zata samu natsuwa, kuma addu’o’in da zata gabatar su zame mata katanga tsakaninta da mugun tunanin da yake neman mamayeta. Jabir ma daya fita, saiya shiga motarshi yana barin gidan, a hanya ya tsaya yayi sallar magriba, bayan ya sake shiga motar, ya karyata zuwa titin da zai sadashi da unguwarsu, sai zuciyarshi ta buga, sai kuma bugun nata yayi masa rakiya har ya karasa ya shiga da motar, yayi parking. Lokacin daya fito daga motar sai yakejin karfin bugun da zuciyarshi takeyi na karasawa har cikin tafukan kafafuwanshi da yake jansu zuwa cikin gidan dakyar.

Sallamar da yayi nufin yima, iya zuciyarshi ta tsaya, bata fito fili ba, haka ya murda kofa ya shiga, baisan dalili ba, saiya tsinci kanshi da kwalawa Aisha kira tun daga falon

“Tasha…”

Muryarshi data koma cikin kunnuwanshi, da kuma shirun daya biyo bayan muryar na sakashi jin wani irin tsoro da bai taba sanin shi ba a tsayin rayuwarshi, daya karasa dakinsu kuwa, ya murda kofar ya shiga, duhun dakin saiya kara masa firgicin da yake ciki, akwai kamshin turarukan Aishar, da kuma ma na daki da take amfani dasu, amman sai hancinshi yake jiyo masa wani abu a tsakanin wannan kamshin, wani abu da bayaso ma yaba kwakwalwarshi damar tantance masa ko menene, saboda hatta bugun zuciyarshi ya ragu, babu sautin, yayi wani kasa, tamkar zuciyar nayi masa barazanar tsayawa a kowanne lokaci, nufinshi ya karasa ya kunna kwan fitilar dakin, yama manta akwai wani makunnin a bangon da yake, saiya taka da nufin ya kunna na kusa da gadon, yaji yaci karo da wani abu a kasa, wani abu kamar mutum, kafafuwanshi suka rasa karfinsu, baiyi wani yunkuri ba yayi kasa gabaki daya.

A kowanne irin duhu, a tsakanin dubban mutanen da zasu kasance cikin duhun, zai tsame Aisha, hannunshi na sauka a jikinta, ko bai laluba ba, zuciyarshi zata sanar dashi itace, kamar yanda ya faru yanzun, sai dai dagota yake kokarin yi, harshenshi yayi masa nauyin daya kasa kiran sunanta, 

Babu ma’aunin da zai dauki girman abinda ya lullubeshi.

<< Tsakaninmu 44Tsakaninmu 46 >>

1 thought on “Tsakaninmu 45”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×