Skip to content
Part 50 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Yau aka sallamesu daga asibiti da tarin sharuddan kar Aisha ta dinga ayyuka masu nauyi. Hakan yasa dole aka kawo mata mai aiki, daga gidansu aka samo mata, sanin halayenta na tsantsaini da sonyin komai da kanta. Amman itama yanzun tasan anzo gabar da dole ne zata ajiye mai aikin, tunda dalilin yin hakan ya shafe kowanne uzuri nata. Sai take ta ganin kamar batayi sati har hudu a asibiti ba, kamar kwanakin sunyi saurin wucewa. Ko dan gabaki daya hankalinta yana kan Jabir ne? Yanda yake ta ramewa na damunta sosai, duk da ya warware, yana hira, yana dariya, yana cin abinci. Kawai wani yanayi take gani cikin idanuwanshi kamar wanda yayi rashi. Sautin dariyar tashi ma tanajin ya canza mata, akwai wani abu tattare da sautin, wani abu da ta kasa dora dan yatsa akai balle harta gano ma’anarshi. Wani abu ya faru da mijinta, wani abu da batajin tunda ya dauki lokaci haka zai fada mata.

Kuma sai yau dinne data nutsu tukunna Sa’adatu ta fado mata a rai, taja numfashi, ta sauke. Ashe gaggawa sukayi, da sun kara jira, na wasu yan watanni da basu jawota rayuwarsu ba. Ta kai hannu ta shafi cikinta tanajin wani abu yanayi lullubeta, a gefe daya kuma tunanin matsayin Sa’adatun a rayuwarsu yanzun ya bijiro mata. Ta manta rabon da maganar Sa’adatu ta hadata da Jabir, tunda ta kasa danne zuciyarta akanta ta tayashi suyi abinda ya kawo Sa’adatun rayuwarsu. Kuma ai har zuciyarta bata hango cewa zata kasa ba, saboda a lokacin bata tunanin komai daya wuce samun da. Sai bayan auren ne tukunna wasu abubuwan suka dinga zuwar mata, ciki harda yanda yaron jinin Jabir da Sa’adatu ne kawai zaiyi yawo a jikinshi.

Sannan yanda ma akayi auren gabaki daya, ko da ta haihu ya saketa, tana da yakinin ba nan take za’a dauki yaron ko yarinyar a mika mata ba, dole ‘yan uwan Sa’adatu dama na Jabir da basa son ganin an dannewa kowa hakkinshi zasuce sai anbar mata ta yaye tukunna a karba, kuma a yanda tasan Hajiya Hasina, to fa har abada wannan abin da za’a haifa za’a dinga dauka ana kaiwa Sa’adatu lokaci zuwa lokaci

“Akan wanne dalili za’a raba uwa da danta?”

Ko zatayi rantsuwa ba zata taba kaffara ba abinda Hajiya Hasinan zatace kenan. To me akayi? Har abada Sa’adatu ba zata fita daga rayuwarsu ba kenan. Kuma duk wata kauna, duk wata sadaukarwa da zatayi akan yaron nan, ba zata taba amsa sunan mahaifiyarshi ba, sai dai uwar riko. Wannan abubuwa ne da son mallakar dan ya rufe idanuwanta ruf, da kuma son Jabir dinma da a lokacin inta kalle shi da yaran ‘yan uwanshi, yanda yake rikesu a jikinshi, ta tuna cewa aure kawai zai kara ya samu nashi, amman ya zauna da ita. Sai ta dinga jin kamar alfarma yakeyi mata, duk kalaman kwantar da hankalinshi sai ta nemesu ta rasa. Ita din bakomai bace face wata mace mai nakasa da ba zata taba bashi dukkan abinda yake so ba. Shisa ma bata zurfafa tunaninta ba har sai bayan da taga igiyoyi sun zarge mata Jabir da wata macen.

Fallen takardar yarjejeniya baya nufin komai. Yanda aka taru, wakilanta dana Jabir aka karbi sadaki aka shaida aurensu, hakama shi da Sa’adatu. Bambancin kawai na abinda yake tsakaninsu ne, amman aure dai duka aure ne, kuma ta kowacce siffa kishiya bata da dadi. Yanda duk zaka dauka ka fahimci lamari na kishi, sai ya fado kanka zaka gane duk hasashenka aikin banza ne. Shisa tayi addu’a sosai, tun daga washegarin ranar da aka daura auren, har kuwa zuwa yanzun bata daina ba. Allaah take roko daya sassauta mata zuciyarta akan kishi, dan ba zata sakankance har abada ita kadai zata kasance a rayuwar Jabir ba, to idan a kaddarar tasu akwai zama da kishiya gara ta nemi Allaah Ya sanyaya mata ranta karya sa ta zama cikin mata da kishinsu yake zame musu halaka, karta kuma zamewa mijinta da abokiyar zamanta matsala.

Dan haka yanzun idan tace tunaninta ya wuce na meye makomar Sa’adatu a rayuwarsu zatayi karya. Kuma tun daga zuciyarta takejin bata da matsala da Sa’adatu da zamanta a rayuwarsu. Ita da Allaah Ya duba da Rahma yayi mata kyauta irin wannan? Bata da lokacin wasu abubuwa banda mika godiyarta da cigaba da kankan da kai ko zai sake dubanta bayan wannan din ya kara mata wani. Kuma ai daman abinda takejin Sa’adatu zata nuna mata kenan, lafiyar daukar ciki da kuma yiwuwar haifewa, abu daya da yayi mata tsaye tun daga makoshi har kasan zuciya. Saboda Sa’adatun zata sami wani abu tare da Jabir da ita take ganin ba zata taba samu ba, to gashi ta samu yanzun. Banda wannan din kuma sai me? Kamar yanda kowa ya dinga fada matane kafin auren Sa’adatu da Jabir din, bata da wani abu da zata nuna mata, a lokacin sai dai ta jinjina kai kawai, amman a yanzun da kalaman suke dawo mata saita tsinci kanta da murmusawa.

Matsalarta dayace yanzun, Jabir da abinda yake damunshi, kuma kamar yasan tunanin da takeyi, ya zabi wannan lokacin ya shigo gidan, ya karasa har kan doguwar kujerar da take kai bayan ta amsa sallamarshi tana kuma dorawa dayi masa sannu, sai dai bai amsa ba, daya zauna a kusa da ita ma, yayi zaman ne yanda ya iya dora tafin hannunshi akan cikinta

“Ya kuke? Ya yarinyata?”

Dariya tayi

“Idan kuma yaro ne fa?”

Sai yayi murmushi

“Duka inaso, amman ai banyi laifi idan na fara da son mace ba ko?”

Kai ta daga masa, kafin ta amsa ya dora da

“Inaso inje inga Hajja”

Yanayin yanda ya fadi maganar kamar ba ganin ya gaisheta bane kawai yanda ya saba, akwai abinda yake so su tattauna, shisa saita danne son binshi da takeyi, tana amsawa da

“Ka gaishemun dasu…”

Kuma saida ya sumbaceta tukunna ya mike, da tayi kokarin mikewa saiya girgiza mata kai

“Ki zauna ki huta”

Dan yasan rakashi zatayi, bata ga alamar musu dashi zai kaita ko ina ba, sai kawai tabi umarninshi tana yi masa addu’ar dawowa lafiya. Haka ya fice daga dakin zuwa wajen mota, ba iska akeyi a garin ba, shine dai a kwanakin yakejin kamar ba akan kafafuwanshi yake tafiya ba, kamar wata iska ta daban tana son daukar shi. Wata irin ma rayuwa yakeyi a satikan da baisan kanta ba. Zai tashi da safe, yayi wanka da abinda ya kamata, zai karya, zaije kasuwa, kuma zai amsa duk wanda yayi masa magana harma su taba hira, sai dai ko dariya yayi sai yaji dariyar ta koma cikin kunnuwanshi da wani sauti kamar ba nashi ba. Ranar da Kawun Sa’adatu ya kirashi, yaga kiran, duka kiran daya jera masa, bai dauka bane saboda yanata kallon number din da yanda akayi bashida ita, tunda ya kira layinshi ne da bakowa yake dashi ba. Haka sauran kiran daya dinga jera masa, inda Sa’adatu ce ba zata kirashi ba, zata tura masa sako.

Kuma ai yama bada wayarta an kai mata, har cefanen kayan da yake tunanin zata bukata. Kuma yini yayi ko ya wayarshi tayi kara saiya duba ko ta tura masa wani sako, ba godiyar kayan yake jira ba, tace masa ma ta karbi wayar, duk da yasan ta karba din. Ya dai ga sakonta a wayarshi, shiru, shikuma daya dauki wayar saiya rasa abinda ya kamata yace mata. A satikan ma sau nawa yaje gidan? Ai ba zai kirgu ba, tunda wasu lokuttan ma baya sanin ya karya kan motarshi har saiya ganshi a kofar gidan tukunna. To da Kawun ya tura masa sakoma baisa ya daga kiran ba, idan ya daga me zaice masa? Yasan akan sakin da yayiwa Sa’adatu ne, yaje yace musu me? Auren yarjejeniya ne daman sukayi, akan inta haihu saiya biyata kudi ya saketa ya karbi abinda ta haifa din, kuma yanzun matarshi ma ta samu ciki, shikenan? Ko a cikin kanshi maganar batayi hankali ba.

Kuma ya rasa yanda akayi daga shi har Aisha babu wanda ya hango abinda zai faru bayan ya rabu da Sa’adatu, bata bangaren danginta kawai ba, harda nashi. Tunda zuwa nawa yayi dan ya gayawa Hajiya Hasina bakinshi yanayi masa nauyi? Amman shirun da yaji daga bangaren su Sa’adatun ma yana tabashi, kafin tunanin zuwa gidansu su sami Hajiya Hasina yazo ma wani a cikinsu, gara ya fara zuwa ya fada mata da kanshi, duk da har yanzun da ya shiga da motarshi cikin harabar gidan, ya kashe ya budeta ya fita yana takawa zuwa hanyar da zata sadashi da kofar babban falon gidan nasu baisan ta inda zai fara ba. Haka har yayi sallama, ya kuma yi sa’ar hada idanuwa da Hajiya Hasina da take zaune akan doguwar kujera, jikinta sanye da wata doguwar riga, haka dankwalin kanta ma na rigar ne.

A lokuta irin yaune idan ya ganta haka, hannuwanta da baya rabo da awarwaro, haka labbanta da kamar jan janbakinta mai saukin kala ya rigada ya samu waje ne ya zauna, ko ta saka ko bata saka ba zakaga alamunshi, sai yaita mamakin irin sa’ar da mahaifinshi yayi na samun kyakkyawar mace irinta, dan yana da yakinin ko a lokacin ‘yan matanci Hajiya Hasina na daya daga cikin ‘yan matan da suke yiwa maza tsananin kwarjini, balle yanzun kuma da shekaru suka saukar mata da wata irin kamala, gayunta da yake danne asalin shekarunta na kara taimakawa wajen haska kwarjininta a idanuwan mutane. Ko da gaskiyarka a gaban Hajiya Hasina sai ka iya daburcewa, balle kuma Jabir da yakejin bashi da gaskiya ko kadan, tunda yana jin nauyin laifin da yayi mata a kafadunshi tun kafin ma tasan yayi laifin.

Kuma yau data kalle shi bayan ta amsa sallamar da yayi, saita gyara zamanta akan kujerar, bai kuma tsaya gaisheta ba, ya zauna a kasa yana dora hannuwanshi akan kafafuwanta, kafin kuma ta furta wani abu yace

“Yau danki mai laifi ne Hajja…kina dadewa bakiyi mun fada ba, nasan yau dai son da kikeyi mun ba zai rage girman laifin nan ba”

Numfashi Hajiya Hasina ta sauke, a cikin yan uwan Jabir kaf, manyan da kanana babu wanda bata tambaya ko yasan abinda yake damunshi da yasaka shi yaketa ramewa ba, tunda tambayar duniya tayi masa yace mata babu komai, kuma tana ganin irin damuwarta a fuskokin ‘yan uwan nashi kamar ta kalli mudubi. Zuwa yanzun kam koma menene fatanta fadin da zaiyi su samu maslaha. Ya rage wannan damuwar da yake ta fama da ita suna tayashi duk da basu san tushenta ba. Sai da Jabir ya kara gyara zamanshi tukunna ya samu yaja wani irin numfashi

“Na saki Sa’adatu…”

Maganar ta fito masa, kuma kaffara ba zata hau kanshi ba idan yace maganar ta dakeshi kamar a lokacin ne sakin ya faru, duka fiye da wanda yake ganin tayiwa Hajiya Hasina

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Ta furta tana dafe kirjinta da yayi wata irin mummunar bugawa. Anya a wajen mata, a kowanne yanayi, in dai na zamantakewar aure ne akwai wata kalma mai firgici irin saki? Ko da kuwa kai da kanka ne ka nemi sakin. Ita Hajiya Hasina ma takance ko wani kaji an saka sai taka zuciyar ta buga, to idan kuma akace kaddarar akanka ta zagayo ya zakayi? Ita a kurkusa ma, zata iya cewa wannan ne karo na farko da saki ya faru da wani a kurkusa da ita haka. Ko Ibrahim a shekararsu ta biyu da matarshi, babu karshen hakurinshi da bata lalubo ba, ita ta hanashi ya saketa. Wani dogon hutu na watanni shida daya batane, kuma a cikin watannin ya nemi wani auren saita shiga natsuwarta. Sai kawai shi yanzun yazo yace mata ya saki Sa’adatu? Aiko Babangida ma batajin yayi girman da zai yanke hukunci irin wannan tunda dai tana numfashi, balle kuma Jabir

“Ina taso in fada miki bansan ta inda zan fara bane Hajja, yau sati hudu, sunata kirana ban daga ba, bansan me zance ba idan na daga”

Mamaki, shine abinda yake nema ya danne firgicin Hajiya Hasina

“Sati hudu da me?”

Ta tambaya tana so yayi mata karin bayani ko zata fahimce shi sosai

“Da na saketa, an shiga sati na hudu”

Hannuwanshi da suke kan kafafuwanta ta fara kamawa ta raba da jikinta, saboda a karo na farko taji tana gab da wanke Jabir da mari, wani abu da bai taba faruwa. Kallon da takeyi masa da kuma yanda ta rabashi da jikinta yasa shi kara daburcewa, saboda yau dai ya hango bacin rai kwance a cikin idanuwanta, ba kuma akan ‘yan uwanshi bane shi yana gefe yanda ta saba, tunda ai Hajiya Hasina ce, shima din shine, duk laifinshi a idanuwanta ba laifi bane kuruciya ce, wauta ce da shekaru zai tafi da ita kamar abubuwa da yawa.

“Daman saboda Aisha ba zata samu ciki bane, kuma yanzun ta samu”

Kamar wani dadden littafi da shafi daya ya bace a cikinshi, shafi kuma mai muhimmanci, haka maganar Jabir ta zauna mata, a wannan bataccen shafin. Lokacin da yazo da maganar karin aure, zatace tafi kowa murna, tunda ai koshi Jabir din batajin yafita son ganin zuri’arshi, kuma karin auren abune da ta daina masa magana akai saboda yanda ya nuna mata bashi da ra’ayi ta koma saka shi a cikin addu’a, batayi mamaki ba, ta dauki hakan a matsayin karbuwar addu’arta. Amman da ya bude bakinshi yace mata Sa’adatu zai aura sai ga mamakin ya bayyana kamar daman baiyi nisa ba. Akwai kaddara, babu ta sigar da bata faruwa, amman kaddarar da zata hada Jabir da mace irin Sa’adatu, to fa ko a cikin kaddarorin sai an natsu anyi dogon nazari za’a samar mata suna. Tazara ce bayananniya da ko makaho zai shafo balle kuma mai ido.

Me ‘yan uwanshi suka dinga ce mata? So, a cikinsu mutum nawa ne ya kira mata so har saida ta amince da maganar Sa’adatun, kuma tun daga lokacin ta karbi yarinyar da dukkan zuciyarta, musamman hankali da natsuwarta. Bata taba suruka irin Sa’adatu ba. Ashe ba so bane ba, aurota yayi ta haifa masa yaran da matarshi ta kasa, yanzun kuma da zata iya amfaninta ya kare. Sosai take kallon Jabir tana son ganin inda ta kuskure a raino da tarbiyarshi harya zama mai son kai haka

“Kice wani abu Hajja, dan Allaah kice wani abu”

Jabir ya karashe muryarshi na karyewa, shirunta yana dafa shi. Sai dai kallon nashi takeyi, me zatace masa? Bayan ya rigada yayi sakin? Wanne kallo ahalin Sa’adatu sukeyi musu zuwa yanzun? Ta tabbata sun hada sunyi musu kudin goron da talakawa da yawa sukeyiwa masu kudi na cewar basu san darajar talakawa ba, bama su san darajar dan adam ba gabaki daya, saboda suna ganin kudinsu ya sai musu wani matsayi da talaka irinta in zai mutu sau saba’in ya dawo da wahala ya taka ko da rabin shine. Ya kora musu yarinya, babu wani kwakkwaran dalili, kuma sun nemeshi yaje dan ta tabbata suna son manya su shiga maganar ne aji meya faru, me tayi masa? A samu maslaha, saiya kara nuna musu da gaske fa su din bakomai bane a wajen shi.

Sai yaranta matan suka fara gilmawa ta cikin idanuwanta, ta fara kokarin saka musu takalman Sa’adatu, ta kuma saka na ahalinta a tata kafar. Wani radadi ya daki zuciyarta. Ai in ba tsananin rabo ba, namiji dai ya wulakanta mata yarinya haka, ta gama zama dashi har abada, in kuwa ta koma to batajin zata taba samun natsuwar zuciya, kullum zata dinga kallon zaman hakuri yarta takeyi a wajen da ba’a san darajarta ba, mijin yana can yanajin tunda aka dawo masa da ita ai shikenan, hakurin zama dashi ya zame mata dole.

“Hajja…”

Jabir ya sake kira yana riko hannunta data fisge

“Ka tashi kabarmun gida Jabir…”

Bude baki yayi tayi saurin katse shi kafin ma ya samu cewa wani abu

“Idan har bakaso inyi maka abinda ban taba ba, ka tashi ka tafi kawai, idan zuciyata ta sauko saika dawo”

Mikewar yayi, jikinshi nayi masa wani iri, a karo na farko da Hajiya Hasina tace batason ganinshi, kafin ta sake furta wani abin da zai karasa shi, gara ta tafi, inta huce kamar yanda tace saiya dawo. Kuma ma ai shine, Jabir, Jabir dinta, amanarta kamar yanda take fada. Yana da yakinin ba zata iya dogon fushi dashi ba, tana kallon shi ya fice daga falon

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Ta sake furtawa, ta dauki wayarta tana tunanin tsakanin Babangida da Farhana waya kamata ta kira, idan ta kira din me zatace musu? Aje a bawa su Sa’adatu hakuri? Tasa Jabir ya dawo da ita? To ai a idanuwan Jabir din dalilin aurenta ya kare masa, anya akwai adalci idan ta dawo da ‘yar mutane hannun mijin da tun farko lalura ce ta sakashi aurenta?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 49Tsakaninmu 51 >>

4 thoughts on “Tsakaninmu 50”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×