Skip to content
Part 13 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Washegari da hantsi ne na nufi gidan Hafsa, ina shiga gidan da malam na fara cin karo da alama fita zai yi, bai amsa gaisuwata ba ya ce “Wai Malama Ummu lafiya kwana biyu ba ki zuwa koyarwa dalibanki na ta complain.” Kafin in yi magana Hafsa ta fito “Kila har ta ajiye aikin” ta faɗi tana murmushin shegantaka.” Dan tsaki na ja “Ka bari kawai malam, abubuwa ne sun min yawa, ni ko zan shiga ajin ai ba gane abin da zan koya musu zan yi ba. Saukina daya da muka kammala namukaratun, da yanzu nake yi ai da tawa ta same ni.” Dariya suka min shi da Hafsa.

Ɗakinta na shiga na baje kan kujera, ta shigo bayan na ji fitar malam.Amarya yar shagali, meye labari? Rausayar da kai nayi “Ba labari Hafsa”Na shiga bata labarin matsalolin da suka taru suka damalmale min tunani. Wata roba ta ciro ta miƙo min, na buɗe. “Meye wannan ɗin? Na tambaye ta, ta ce “Labari aka bani hadin yana gyara skin, mankade ne, sai man zaitun, da man alayyadi da man kwakwa, aka haɗa wuri ɗaya.Ki gwada kafin mu fara gyaran amaren.” Na fadi “Na gode.” Miƙewa tayi ta buɗe fridge, robar Swan ta ciro “Tsimin sassaken baure nayi miki, wanda aka dafa ya dahu sosai da karanfani da yar citta. sai a zuba zuma, da mazarkwaila bayan an sauke.” Ta kuma ciro wata gorar “Nan kuma sassaken kuka na dafa miki da karumfani, shi ma yana saukar da ni’ima, ai sosai nake so mu rikita me mata biyun nan.

Dan wallahi Ummu kin yi mijin nuna ma sa’a, muna me mata biyu, ashe haɗadde ne dan gaye abin sa.” Tsaki nayi na karbi gorukan ina yamutsa fuska, “Ni wallahi sai in ga kamar zolaya ta sa mutumin nan cewa yana so na, ke kin ga haɗaɗɗiyar matarsa, ban da malam ya kawo shi Allah cewa zan yi wata manufa yake da ita a kaina, ba dai so ba.” Hannu Hafsa ta kada”Kar ma ki soma wannan tunanin, kyau daban kauna daban, da kyau ke sa a so mace da wasu matan har su mutu ba su samun mazan aure. Kauna Allah ke dasa ta a rai, ballantana ke ɗin ma ba mummuna ba ce ko baki da shahararren kyawun fuska, Allah ya azurta ki da kirar jiki me kyau, kyan fuskar ma kina da daidai gwargwado. Kyan kirar jiki kuma ai shi ne mace. Na ce “Uhmm ke dan ba ki ga matar ba, daga jikin har fuskar ta haɗa “Ta taɓe baki “To sai me? ba yana ganin ta ya kuma zo gare ki ba? me zai dame ki ke kam?na ce “Kin san wani abu Hafsa?ta ce “Sai kin faɗa”Na ce”Magungunan mata basa min, idan na sha maimakon ni’ima ni ɗauke min tawa suke, na rasa dalili shi yasa ban ko damu da su ba sanda ina gidan Abakar”Ta ce “Ikon Allah lamarin naki akwai ban mamaki, amma gobe in sha Allah zan zo mu je gidan Malama Jamila, ki yi mata bayanin matsalarki za ta ba ki magani” Na hura iska “Allah ya kaimu”Kamar yanda Hafsa ta ce ta biyo min mun je gidan Malama Jamila nayi mata bayanin matsalata, Ta ce “Yanzu ba maganin mata ya kamata mu fara ba.” Wani sassake ta ɗauko ta hado da wata roba cikin ta ya’yan hulba ne, ta ce “Ki dafa ki riƙa sha na infection ne. “Duban juna muka yi ni da Hafsa na ce infection kuma? ai ni bana ganin alamun da aka ce masu ɗauke da shi suna gani”Hafsa ta ce “Daga ta ji matsalarki kuma ga abin da ta ba ki, ki karba kawai.”

Na gyaɗa kai. Sai garin habbatus sauda ta ce “Ki riƙa kwaba shi da zuma kina sha ko ki sha da nono me kyau, sai ganyen magarya ki rika tafasawa idan ya sha iska, sai ki rika shiga ciki. Ki yawaita shan zuma musamman da daddare, kayan fruit ya zamana kamar abincinki a yanzu, ki yawaita shan su, musamman kankana, da aya da gyaɗa.Cike da mamaki Hafsa ta ce “Gyaɗa kuma Malama?Ta gyaɗa kai “Kwarai gyaɗa tana daga cikin abin da ke gyara mace kwarai da gaske sai dai rashin sanin amfanin ta”.Hafsa ta ce “Faɗa mana yanda ake amfani da ita dan Allah Malama”Ta yi mana bayaniHafsa ta ce “Da mun fita kafin mu kai gida, zan saya mana kwano biyu ni da ummulkhairi” Malamar tayi murmushi. Hafsa ta ƙara matsawa kusa da ita “Aure za ta yi Malama, mijin matansa biyu, shi ne take cike da fargabar shiga cikin kishiyoyi.Ina so ki gyara min ita ciki da bai.” Kallona tayi cikin wani yanayi sai ta matso ta dafa ni, “Kar ki ji komai kin ji ƙanwata.Ki riƙe Allah ki nemi taimakon sa, indai kin shiga da zuciya ɗaya Allah zai taimake ki. Mu ga hannunki na miƙa mata.Ta ce “Ya kamata mu fara gyara tun saura sati biyu, duk wani abu da zai taimake ki zan miki shi in Sha Allah”. Ta ce kuɗaɗen maganin da ta bani dubu biyar. Sai na gyaran da za a yi mini hada lallen biki wannan Hafsa ce me biya ita ta faɗa ma adadin kuɗaɗen. Ta biya nima na biya nawa, mun daɗe tana ta koya min dabarun zama da miji, da yanda za ki kama shi a hannu ba boka ba malam. Ke dai ki gyara kanki kar ki zama koma baya wurin miji.Har za mu tafi na ce”Akwai abu ɗaya Malama sai dai ina jin nauyin ki”Ɗan murmushi tayi “Ki yi maganar ki ni ma mace ce yar’uwarki. “Rage murya nayi “Ni sam bana jin sha’awa, har aurena ya mutu ban taba jin daɗin da ake cewa ana ji ba. Murmushinta me kyau ta kuma jifa na da shi, Ba matsala, abin da na ba ki za su yi miki maganin duka in sha Allah.” Godiya muka yi mata muka tashi muka fito.Da zamu rabu Hafsa ta ciro kuɗaɗe a hand bag ɗinta, ta miƙo min. “Gudummuwarki ne in ji malam.” Sosai nayi godiya na ce ki taya ni mishi godiya kafin in zo Dubu talatin ne cif. Ina zuwa gida na nuna ma su Ummata da Gwoggo kuɗaɗen suka yi ta godiya da sa albarka. Hafsa fa ta buɗe min wuta kullum da abin da za ta aiko min, garin zogale in sha da madara peak, sai garin tafarnuwa ina shan sa da ruwan kal, sai garin ganyen idon zakara ina shan sa da madara shi ma, Ni kuma a bangarena kullum ina aikawa a sawo min kayan fruit in sarrafa abi na in Sha.Saura sati biyu bikin tafiya ta kama Tahir zuwa warri, daga wurin aikin sa ne, kuma ko zai dawo sai ranar daurin auren ko washegari, tuni Malama Jamila ta shiga gyara ni, kuɗaɗe masu dama Tahir ya turo min ya ce “In yi ƴan gyare gyare na. Saura sati guda biki yayana Sani ya aiko da kayan furniture’s masu matuƙar kyau, bayan saitin sai kuma ya hado da wani gado ya ce a sanya min idan daki biyu ne, ba ƙaramin alfahari bane samun wadannan kaya domin sun hadu dan’uwana ya fitar da ni kunya.Ni kuma na haɗa da kudin sadakin da gudunmuwar da na samu , hatta Ummata gudunmuwar da ƴan’uwanta suka haɗa mata bani su tayi ta ce in yi sayayya ta. Labulaye na saya masu kyau da tsada sai carpet, zannuwan gado, yan kayan ƙyale ƙyale sai kayan kitchen wa’anda ban wani cika ba.Ina son fridge da tv amma ba kudi sai na haƙura, Babana ya yi min Gara, kuɗaɗen da Tahir ya turo min sai na sayi kayan da zan yi kwalliyar biki, Atamfofi biyu na saya sai shadda sai less ɗai ɗai ɗinkuna na musamman aka yi min, dan na ji mutane sun fara magana kayan lefe fa in yi mishi magana. Ni kuma bai yi min maganar su ba ba zan mishi ba, dan ko gwoggo ana saura kwana uku bikin Hafsa ta zo muna zaune sai ta leƙo Hafsa ta duba. “Wai ku angon naku yaushe zai kawo zannuwan auren? Dan shiru tayi kafin ta ce. “Zai kawo Gwoggo, ya ce tafiyar nan da ta kama shi ta hana shi karasa sayayyar. Ƙila sai ta je zai bata, daga ya aiko da na cin biki.” Gyada kai Gwoggo tayi cike da gamsuwa” To Allah ya rufa asiri ya sanya albarka a auren” Hafsa ta ce “Amin” Gwoggon ta juya sai ta fita. Miƙewa nayi ina rufe jikina dan gidan Malama Jamila za mu za ta min wankan lalle, idan fa ka gan ni nayi shar da ni na fito a amaryata illa dai fargaba da ta cika min zuciya. hararar Hafsa nayi.” Matar malam guda ta zauna ta gunduma ƙarya”Ƴar dariya tayi” Ai ta kare kai ce, kar ki wani damu. Ranar daurin aure jama’a masu dimbin yawa ne suka shaida daurin aurenmu da Tahir. Duk da ba ango ƴan’uwansa masu dinbin yawa ne suka suka zo, matan sai tirirrishin zuwa gani na suke.Ni kam Marka marokiya na rafka guda fargaba ta ta karu, kawayena sosai suka yi min kara, haka malamai mata na makarantarmu, da dalibai. Ƴan’uwana da su Hafsa sun tsaya kan walimar da malaman makarantarmu suka shirya min. Zuwa magrib jama’a duk sun koma gidajensu sai yan gidanmu kawai, ina yin isha’i na hau gado, a maimakon barci tunanin da ya zame min jiki ne ya taso ya dabaibaye ni, Ya zan yi ranar da na zama mallakin Tahir Sodangi? Ta ya zan iya hada jikina da shi?To yau dai ta faru ta ƙare,na daɗe cikin tunani kafin gwanin iya sata ya sulalo ya sace ni. Da asuba da kyar na tashi na gabatar da sallah dan tsananin gajiyar da nake ciki, na koma na kwanta. Dukan da ake daɗa min yasa ni bude ido na tashi zaune ba shiri.Hafsa ce cikin mamaki ina murza ido na ce “Ke kuma daga ina da safiyar nan? Agogo ta kalla “Tara da rabin ne safiya? Kai na jinjina.” Kwanan nan malam ya sake miki da yawa matar nan.” Murmushi tayi “To ya zai yi bikin ƴar’uwa rabin jiki.”

Tana maganar tana tube hijab din jikinta, jakar da ta zo da ita ta buɗe turaruka na jiki da na daki ta ciro “Ki riƙe su a hannunki wa’annan ummulkhairi, kafarki kafar su”.Na amsa na ce “Na gode”Harara ta bani “Kin san abin da ya fiddo ni yanzu? Na girgiza kai “Sai kin faɗa.” Ta ce “Angon na ji suna waya da Malam ya ce lallai yau zai shigo Dutsinma, yana so a wuce da kayan ki gobe. Sai complain yake wa Malam ya kasa samun ki a waya, in ya kira sai ya ji a rufe, shi kuma ya kasa kiran ta Umma, shi ne na roƙi malam in zo in miki kitso. Baki na bude “Lallai babbar magana, yau Hafsa ce da kitso? dan ita ɗin gwana ce ta kware a kitso sai dai makyuyaciya ce ta gaske wurin yinsa, daidai da yarta kwaya daya Ramla bata iya yi mawa.Ta gyara zama “Matso dan Allah mu fara, so nake mu gama cikin lokaci ki shirya kafin zuwan Angon.” Hular da ke kaina na cire, na zare ribbon din da na kama gashin ya watsu kan kafadata, yana daga abin da ke ƙara fidda fuskata yalwataccen gashi da Allah ya bani.Na miƙa mata kan wanda ke ta sheƙi saboda gyaran da ya sha, ta soma yarfa min kitso Umma da Gwoggo suka shigo suna ta yi ma Hafsa godiya kan dawainiyarta a gare ni.Sai sha ɗaya da rabi muka gama, banɗaki Hafsa ta wuce ta haɗa min ruwan wanka wanda ta zuba ma turaruka, wanka me kyau na shiga nayi da na fito na shafa mai humra ta bani na shafe jikina, atamfofin da na dinka na ɗauki daya na sa ta kuwa karɓe ni sosai, sai walkiya nake.Gidan ya dauki hayaniya dan ƴan’uwana sun dawo za su wuce Kaduna shirya min daki, Hafsa ta fesa min turare tana motsa kunun da Umma ta miƙo min, gaba ɗaya turaren na ji ya haye min kai, dan cikina ba komai, tun jiya ban ci abincin kirki ba, yau kuma ko karyawa ban yi ba. Na tashi in ɗauko ribbon din da zai dace da atamfata sai kawai wani jiri ya kwashe ni, kafin in san abin yi na yanke jiki, sai salatin jama’a nake ji,kafin komai ya tsaya min na ji dif. Ban farka ba sai a gadon asibiti na gan ni ana min ƙarin ruwa.A hankali na buɗe idanuna Gwoggo na gani zaune a gefena, ta ce “Alhamdulillahi kin farka ummulkhairi? Sai ta fita da sauri kafin ta dawo da mutumin da na hakkake likita ne, allura ya min ya kuma ba nurse din da ta biyo shi umarnin cire ruwan da ake ƙara min ta canza wani. Wani barcin na koma, sa’adda na farka kaina ya min nauyi kwarai, na shiga juya idona cikin dakin an cire min ƙarin ruwan, Tahir Sodangi ne kaɗai a dakin yana ta Safa da marwa a filin dakin.Sanye yake cikin wata farar shadda, glass ɗinsa na rai da rai na manne a idonsa, juyowar da ya yi sai muka haɗa ido,da sauri ya karaso gaban gadon kin farka ina ke miki ciwo? Kai na girgiza. Ba ko ina, jikina ne kawai ba karfi”.Ok to bari in kira Dr “Da wayarsa ya yi amfani wurin kiran Dr Da shigowar likitan tambayoyi ya rika min ina ba shi amsa karshe shawara ya bani in daina zama da yunwa saboda gudun motsawar ulser ta.Ya juya wurin Tahir “Ko yanzu zan iya sallamar ta yallabai ku je gida, amma kasantuwar dare ya soma yi za ku bari sai da safe, idan na kara ganin jikin sai ku je gida a yi kokari yanzu ta ci wani abu. Suka yi musabaha, ya ce Allah ya ƙara sauki, zan wuce gida, dama saboda kai yallabai na kai har yanzu a Hospital”.Godiya ya mishi likitan ya fita.Ya juyo wurina “Taso mu je ki yi brush sai ki ci abinci”ganin ban motsa ba ya ce ko sai na kama ki?ganin ya yo kaina na ce “Zan iya” Na lallaɓa nayo brush din na dawo, tea ya haɗa min me kauri na sha kafin ya zuba min abinci, kan ba yadda zai yi ya ƙyale ni, na koma na kwanta.Zufa ce ta shiga keto min, tsayawa ya yi kaina hannayensa saye cikin aljihunsa ya kafe ni da idanuwansa “Me yasa kike wasa da lafiyarki? har kika sa ulser ki ta motsa?Shiru nayi ganin ba wasa sam a tattare da shi.Sai da ya ƙara maimaitawa na ce “Ka yi hakuri zan kiyaye nan gaba” zufar da nake ta yawaita ga tea me zafi da na sha,ga tsare ni da Tahir ya yi da mayun idanunsa, a hankali na yaye hijab din jikina ina maida numfashi, bi na ya shiga yi da kallo wanda har ya sanya ni kallon jikina, ɗinkin matsatstse ne ya fitar da surata.Jikina na ji ya dauki rawawaiwaye na shiga yi inda na ajiye hijab din, gefen Sodangi na gan shi, wanda ban san sanda ya fakaice ni ya ɗauke shi ba, na kai hannu na shafa kaina, ba dankwali, juyawa kawai nayi na ba shi baya,

“Dan matsa min ni ma in kwanta”.Muryarsa ta ratsa dodon kunnena. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 12Wa Gari Ya Waya 14 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×