Skip to content
Part 17 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

To ummulkhairi na kira ki ne don ki gyara kanki, kin ga duk wannan rawar ƙafan da Sodangi yake yi da ke, daga zarar kin ƙare amarci in ba dagewa kika yi da gyaran kanki ba juya miki baya zai yi.Ga kishiyoyi kina da su, kowace kokari take ta ga ta zama ta gaban goshi”. ta shiga lissafa min sunayen magungunan matan da ke gabanta, “To dame dame za a ba ki? Kunyarta ta sa na ɗauki wata gorar tsimi, ta ce min dubu biyu, na ce zan bayar a kawo mata, tayi tayi in ƙara wasu abubuwan na ce a’a.

Da fitowata sasan su maman ummi na fada, Amaryarta tana tsifa a ƙofar ɗakinta ganina sai ta gintse fuska na miƙa mata gaisuwa ta amsa a dage, kamar yanda ta saba min tun fara shirina da kishiyarta.Na daga labulan maman ummi zaune take ta tasa katon cikinta haihuwa ko yau ko gobe.Na shiga na zauna murmushi take jifana da shi “Me kika samo mana? ta tambaya tana miƙo hannu sai na miƙa mata robar tsimin, yamutsa fuska nayi sai na bata labarin yanda muka yi da Amma, baki ta rike “To tun wuri ki kiyayi kanki, kin san tib da taya? to haka suke da Halima”.Wani kallo nayi mata “Wace ce Halima kuma? ta gyaɗa kai “Lallai ma uwargidan taki ce ba ki sani ba.” Ajiyar zuciya na fidda”Ina jinki, dan sam ban kawo ta ba””Duk wani shige shige ita ce ke yi wa Halima, shi ne dan rashin tsoron Allah ke ma za ta ja ki jikinta, masallaci ɗaya limami biyu kenan, ko kuma ke tayi miki shigo shigo ba zurfi.

Yanzu nawa ta sayar miki da wannan?Na ce 2000″Kama baki tayi lallai za ta mayar da ke saniyar tatsa, 500 take saida shi, ki yi kokari ki iya da kanki gudun kada ta kaiki ta baro. Kuma Allah na tuba Magungunan Amma ai sai dai rashin sani, gamje gamje ne ba ma ko yi yake ba, tsoro kawai ke sa matan gidan nan saye, dan in bata yi da kai ruwa sai ya nemi gagararka a gidan nan.” Mun ɗauki wani lokaci muna maida maganar kafin na koma wurina. Kwanaki uku kawai aka yi Amma ta kuma kirana ce min tayi yakamata a dafa min kaza, in ci yan shila, kai har ma cicciɓi a dafa min, duk in ci kafin zuwan Tahir. Dogon bill tayi min Na ce yanzu bani da kuɗi ta bari tukun, ta ce ai zan bada wani abu ne saura kuma a hankali ina badawa, na ce ta dai bari in samu. Mata fa ta matsa min Ranar da Tahir ya zo muna daki sai ga yarta ta turo kirana, gaba ɗaya jikina ya dauki rawa ina ganin kamar Tahir zai gane abin da kenan, ban motsa ba har sai da ya ce “Ki tashi ki je mana kin zauna kina rawar jiki”.sim sim na miƙe na fice.

Da isata wani zobe ta miƙo min, “Ungo ki saka a hannunki, kin san tsafi to wannan zoben aikinsa kamar tsafi yake.” A zuciyata nayi Auzubillahi na neman tsari da tsafi “Ki saka shi da duk niyyar da kike so za ki sha mamaki, dubu biyar ne kudinsa kacal, amma aikinsa, tayi ƙwafa, miƙa mata nayi “Bani da kuɗi Amma” ta ki karba ki je da shi ki gwada amfani da shi ki ga yanda zai rika juye miki bakin aljihu, mijinki fa ba ƙananan kuɗaɗe gare shi ba.” Ƙara miƙa mata nayiduk kuma yanda taso tilasta ni in karɓa zullewa nayi. Aikowar da akayi Tahir na kirana ta cece ni, na ajiye mata a hannun kujera na fito na bar ta cikin takaici.Jikina ya soma rawa hango Tahir daga nesa yana kallon ƙofar Amma, da alama fitowata yake tsayuwar jira, ransa a haɗe, hannuwansa rungume a kirjinsa, na wuce shi kaina a kasa, ina shiga yana shigowa “Meye tsakaninki da Amma? ya jeho min tambayar a ba zata, “Ba komai”.nayi ƙarfin halin ba shi amsa “To ko ma dai meye bana son kowace hulɗa ta haɗa ku, bayan ta gaisuwa, jaje da taya murna.” Kai na daga mishi “In kuma wani abu ya biyo baya, wallahi sai nayi mummunan saɓa miki.”

A ranar dai ban gane kansa ba daure min fuska ya yi, sai washegari na same shi na ba shi haƙuri. Kwanan shi hudu da komawa Maman ummi ta haihu, ya mace ta samu. A wurin zaman jegon ne na ji matan gidan suna firar zoben Amma, anan har na ji kuɗin da take saida shi Naira dubu daya, ni kuma ta ce min dubu biyar. Sai na ƙara nesanta kaina da duk wata mu’amala da za ta haɗa mu ni da ita. Kayan maman ummi na wanke mata a laundry. Ina shanya kayan a igiya, na ga Amma ta yo rakiyar baƙuwa, zuwana inda suke tsaye bai sa ta canza firar da suke ba. “Matansa na Kaduna, ta biyun a Abuja take, ta farkon kuma ai Halima ce ta nan gidan su mai waina.” Matar ta gyaɗa kai “Ƙwarai na santa.” “Sai wadda ya auro kwanan nan, ya ajiye a gidan nan. Amma matan da suka amsa mata suna birni, ita kuma tana nan,ai me aiki ya samo wa uwarsa.” daidai nan muka haɗa ido da ita, wani kallon banza ta min, na wuce su zuwa ɗakina, rasa abin da ke min daɗi nayi, har ji na riƙa yi kamar zazzaɓi zai rufe ni.

Dare nayi zazzaɓin ya bakunce ni, sai asuba ya sauka.Tun daga ranar kuma Amma da kishiyar maman Ummi usaina, suka ta sa ni da neman fitina, ina kauce musu. Ko da Tahir ya zo ya yi complain din zafin jikina da daddare, na ce lafiyata ƙalau. Wata ranar Laraba na wanke kayan Haj ina shanya mata, sai ga usaina kamar an jeho ta. “To yan neman gindin zama, ya za ayi ki haɗe min shanya ki sanya naki? duban inda kayan nata suke nayi, sam shanyata bata je wurin su ba. Cigaba nayi da shanyata ban mata magana ba, gabana ta zo tana girgiza jiki, “Ni za ki mayar ƴar iska? Ina miki magana kin min banza. Nan ma ban gwada na ji ma me take cewa ba, kayan da na shanya ta zo ta kwashe ta zubar. Rabi matar Yayan Tahir da ke wanke wanke ta ce,

“Haba meye haka za ki zubar mata da kaya? sam hakan bai dace ba” Raina ya gama ɓaci na ce “Wannan wane irin wulaƙanci ne za ki zubar min da kaya?”An zubar ki dau mataki. Aikin banza kawai, waɗanda aka ɗauka mata suna birni, Kaduna jansin lahirar makwadaita, muna mata kuma, ta rangada guɗa “An bar su a ƙauye, suna bauta.”

Idona na ji ya kawo ruwa na ce “Wai me nayi muku kuke min wannan cin kashin? Sai ga Amma kamar an jeho ta “Yo ƙarya aka faɗi?Suka taru ita da usaina suna min tijara. Matan gidan suka taru duk kuma haƙurin da suke ba su basu samu nasarar tsaida su ba.

Na cigaba da kwashe kayan da suka zubar min idona na cigaba da zubar hawaye, har ana riƙe usaina za ta zo ta duke ni. Shirun da na ji wurin ya dauka ne yasa ni daga idona ina share hawaye. Tahir ne tsaye, hannuwansa harɗe a kirjinsa yana kallon kowa ɗaiɗai ta cikin farin glass ɗinsa, Amma ta fara ankara ta soma sulalewa kafin usainar ta bi bayanta. Na ɗauki bokiti da kayan na wuce ɗaki, a falo na zauna ƙasa ina kuka, Tahir ya shigo kaina ya tsaya yana tambayata me ya haɗa mu. Sai dai juyin duniya na ki magana, juyawa ya yi ya fita, zuwa sasan Hajiya, hankali tashe ya same ta tana sa wa a kira mata ƴaƴanta, duk da gaya mata da ake sun kusa dawowa daga lokacin dawowar ta su ya kusa, bata yarda da hakan ba.Wuri ya samu ya zauna, kallo ɗaya za ka yi masa ka gane ransa a matuƙar ba ce yake, da ɗaiɗai suka riƙa shigowa hada kanenta Kawu Attahiru, wanda sunansa Tahir ya ci, kuma shi ne marikinsa, dan Allah bai ba shi haihuwa ba, tare suka zo da Tahir shi Tahir ya yo ma rakiya. Sai da kowa ya zaunasannan Haj ta kora musu abin da ya faru kamar yadda aka zo aka bata labari, an ce a kira ni ni da usaina da Amma. Ni ce na iso karshe, dogon hijab har kasa na sanyo, na rabe daga bakin kofa, Amma aka nemi ta faɗi abin da ya faru kame kame ta shiga yi ƙarshe magana ta gagara, sai usaina, ita ma ɗin kame kamen ne, da aka zo kaina na fadi duk yadda abin ya faru, har ma da abubuwan da suka yi mini kafin yau. Mamaki ne ya barke a dakin ana tambayar su dalilin su na yin hakan. Yaya Magaji me bi ma yaya Babba, duk ya fi su zafi ya tambayi gaban wa abin ya faru, Haj ta ce an ce gaban matarsa Rabi ne, a waya ya kirata sai ga ta, ya tambaye ta tare da mata gargadin ta gaya mishi gaskiya, yanda na faɗi ta maimaita. Ran kowa a wurin ya ƙara ɓaci, Tahir dai ko tari bai ba Haj ta ce “To kun ji abin da ya faru, wlh ku ja wa matanku kunne, idan hakan ta kuma faruwa ba zan lamunta ba. Babu wacce za ta farraka min kan iyali, wannan yarinya ta wanke kayana, kai lawal matarka ta zubar, kayana lawal, kuma dan tana min aiki shi ne ya zame mata abin gori wurin matanku.” Sai ta kama kuka Yaya lawal na miƙewa ya ce ya saki usaina ta je gida.Dakin aka ɗauki sallallami ana mishi faɗan saurin furta kalmar saki, Yaya Babba ma ya mike Kawu Attahiru ya tsaida shi, amma duk da haka ya rantse sai Amma ta tafi gidan su, daga mahaifiyarsa ce abar rainawarta.

Usaina da Amma suka fita kowacce tana kuka, na yunkura suka shiga bani haƙuri, na fita dakin na koma wurin mu na kara ɗauraye kayan Hajiya na wuce na shanya, na ɗauko bokitin na ga Tahir tsaye yana kallona, wuce shi nayi kitchen na shiga na soma girki, sai da na kawo ma Tahir inda yake zaune shiru a falo, kafin na wuce na kaima Haj ita da kanenta, na samu suna magana shi da Hajiyar, nasiha sosai Kawun ya yi min game da rayuwar aure da duka rayuwar ita kanta. Kafin ya rufe da shi min albarka, da kara faɗa min in cigaba da abin da nake abu ne me kyau, kar abin da wadancan suka yi min yasa in daina Na yi mishi godiya na koma wurina, wanka na wuce nayi, ko da na gama shirina kwanciyata nayi, Tahir ya leƙo, ganina kwance sai ya koma.

Haka muka ƙarasa kai dare da shi, bai ce min ba ban ce mishi ba, har sai da muka kwanta kamar yanda barci ya kasa ɗaukata, shi ma juyi yake ta yi yana tsaki, mirginowa ya yi inda nake, ya sa ni jikinsa.”Ki yi hakuri Ummulkhairi, na rasa abin ce miki bisa abin da aka yi miki, matan ƴan’uwana ne, kuma albarkacin ƴan’uwan nawa suka ci, amma yau da wasu ne can daban suka ci zarafinki haka, da kin gane ko ke wace ce a wurina.

Amma ina rokonki ki yi hakuri”.Hawayen da suka fara gudu suna min zuba suka sauka kan kirjinsa, yasa hannu ya share min, ki yi min magana, ko ba ki haƙura ba?Na ce “Ya wuce” Ya ce “Allah ya shi miki albarka” daga haka wasanninsa ya shiga yi, kafin mu shiga wata duniyar. Sai da komai ya lafa ya ce Jikinki da zafi, gobe zan kaiki ki ga likita, wancan zuwan na ce kin musa min.” Na ce “Ni lafiyata ƙalau.” Sai na ƙara maƙale shi dan sanyi nake ji. Da safe na tashi garas na kama harkokina.

Ɗagowar hantsi Amma ta bar gidan, wanda ban ji dadi ba, dan ba daɗi abu mara dadi ya faru irin haka ace sanadinka ne. Ita kuwa Usaina tun daren ta wuce, da safen ma ni na shirya ma Kawu abin karyawa na kai mishi ɗakin Haj, haka na rana, dan haka ban samu yin wanka da wuri ba, sai da nayi sallar azahar, nayi kwalliya cikin wasu riga da siket English wear, zuwan Tahir wancan karon ya zo min da su. Rigar ta kama ni yankakken hannu gare ta, gashina ana gobe sunan Maman Ummi muka ziyarci Sallon ni da Maman Ummin aka gyara mana, ribbon na sa na kama gashin ta tsakiya, sai duban kaina nake ta madubi, nayi bulbul gaba ɗaya nayi wani narai narai, komai nawa ya ƙara cika.Bedroom din na bari na isa kitchen, cornflakes na haɗo da Madara na taho ina sha.

Tahir da ke kwance rub da ciki a tsakiyar gado yana aikinsa a laptop ya kura min ido tun tahowata “Zo nan yarinya, ki faɗa min shekarunki.” Murmushi nayi na zauna gefen gadon ina nuna mishi da ƴan yatsuna. “Ashirin da biyu? Ya tambaye ni na girgiza kai na ƙara nuna mishi “Ashirin da ɗaya? Na ɗaga mishi kai, cigaba ya yi da kallona har na shanye yana ganin na ajiye mug din sai ya janyo ni jikinsa, “Duk da kishin mutumin nan da ke taso min, idan na tuna ya riga ni sanin ki, wani lokacin kuma na kan ji kamar in gan shi dan in ƙara hakikance girman sakarcinsa na samun mace kamarki kuma ya yi sullancin da kika subuce mishi.Murmushi na yi jin maganarsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 16Wa Gari Ya Waya 18 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×