Skip to content
Part 21 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Ina masu buƙatar karin haske game da Aunty Gyaɗa? To ku matso kusa. ku jaraba wannan da yardar Allah zai yi muku. Auni gyadarki Hajiyata kwano ɗaya, ki kai ki ajiye, debi kofi daya na gyadarki, sai ki wanke ta ki gyara ta, sai ki zuba a cikin tukunya. Daga nan sai ki zuba ruwa kofi uku, e kofi uku za ki sa, cikin gyadar nan da kika zuba a tukunya, sai ki ɗora a wuta, ki tafasa ta, tafasa daya. Sai ki sauke ya huce idan ya huce, sai ki ta ce, Ruwan gyadar nan za ki kasa uku, ki sha kofi daya da safe, da ga nan ki sha daya da rana, ki sha daya da daddare, ban da fa gyadar ruwan za ki shanye, dan Allah. Hajiyata ki jaraba wannan abu ki yi sati kina yi, koma kwana goma da yake yanayin jiki jiki ne, wata ta na shan abu za ta soma jikewa, wata kuma za ta daɗe kafin ya soma aiki a jikinta, dan haka ƴan’uwana mata a jaraba matsi da ni’ima, wasu ma sun ce yana wanke mahaifa.

Allah ya sa mu dace.

*****

Zama nayi a ɗaya daga cikin kujerun da ke falon, na soma gaishe ta, cikin nuna girmamawa tana amsawa cikin fara’a. Ina tsohon mijinki? Tahir ya tambaye ta “Malam, ya fita ta’aziyya nan bayan mu.”

“Kin yi girki ko in fita in samo muku abin da za ku ci, daga Asibiti muke, bata da lafiya” “Ash sha, sannu kin ji, Allah ya kawo sauki, mutane suna ta fama da zazzaɓi.” saurin cewa ya yi “To ita ba zazzaɓi ba ne, ciki ne da ita.” Wayyo! ji na yi kamar ƙasa ta buɗe in antaya, dan kunyar da na ji, ita kam murna ta hau yi da addu’o’i na Allah ya inganta, yasa wannan karon su ga kwansa. Ruwa ta kawo mana ya sha sai ya yi mata sallama ya ce in mata wuni, zai dawo ya ɗauke ni. Dawowar yan biyu daga makaranta, yasa na gane inda ya kawo ni, ba su manta ni ba suka hau murnar ganina, tsohon mijinta ya dawo.

Zuwa la’asar nayi sabo da dattawan masu matuƙar karamci da dattako.Ni nayi musu abincin dare duk da hana ni da take wai bani da lafiya, na ce yanzu ban jin komai, a cikin firar mu take bani labarin ƴar ta Maman su ƴan biyu, “Mijinta dan dakinta ne, tun da aka kai ta gidan su, indai za ta yo aike shi ne dan aikenta Allah kaɗai ya san shakuwar da ke tsakaninsu, shekaru bakwai kenan Allah ya bata rabo aka yi ta murna, ashe hanyar tafiyar kenan, aiki aka yi mata aka ciro su sai dai ko farfadowa bata yi ba.” Wani hali dattijuwar ta shiga, da alama mutuwar ta dawo mata sabuwa, hakuri nayi ta bata da yi wa mamaciyar addu’ar samun rahma. Sai da ta natsa sai ta cigaba, mijinki shi ke tsaye akan mu ni da malam, komai da ɗa nagari zai yi wa mahaifansa shi yake mana.

Mun yi ta firar mu har magrib ta gabato. Wanka ta umarce ni in je in yi, “Ki gyara jikinki kafin dawowar mijinki, ba abin da ke kara ba mace muhimmanci a zuciyar mijinta irin tsafta da gyara.” Na ce “To Haj” wankan nayi na fito, kayan kwalliyar da ta ajiye min suka bani mamaki kamar ta san tunanina, “Mijinki ke famar kawo wa su ƴan biyu, kamar wasu yammatan kirki.” ƴar dariya nayi na soma shafa, na fesa turare, zan mayar da kayan jikina ta nuna min wata leda “Ga kaya nan, tsarabar Makka aka kawo min, ina ni ina saka kayan yara.” Na ɗauka na buɗe, doguwar riga ce, kalarta pink, ta sha kwalliyar duwatsu, sosai ta bani sha’awa, da na saka ta ajikina ba ƙaramin karbata tayi ba.

Na zauna ta miƙo min fura, “Maza ki sha, mijinki baya gajiya da kawo mana da nono me kyau”.na ce “Cikina ya cika Haj, kar ya fashe”. ta ce “Wa ya ce miki ɗanyar fata na fashewa? na kafa kai kenan, gardin furar ya ratsa ni, na tsinkayi sallamarsa, tare da su ƴan biyu ya shigo, suna riƙe da shi, ledojin da ke hannunsa ya mika wa Haj, ta karɓa tana fadin “Kai dai ba ka gajiya”, gasassun kaji ne, guda biyu, kusa da ni ya zauna ya karɓe furar hannuna, ya kai bakinsa, sai da ya shanye sai ya dire mug din, “Tashi mu tafi”. Haj da ta shigo daga kai wa Malam ta shi kazar ta ce “Wane irin ta tashi ko naman bata ci ba, ga furar ka shanye mata”.”Ci namanki tsohuwa, ita ma na saya mata nata.” “oho, to zubo mishi abinci.”

Na tashi na kawo mishi, lomar farko ya gane ita tayi, Allah ya yi wa yarinyar baiwar girki ta sarrafa shi ya yi daɗi, duk yanda yaso ya ci kaɗan dan abincinsa na gida, bai ci ba ya fito ɗaukar Ummulkhairi, kasa hakuri ya yi sai da ya ji ya yi dam,.har zumudin ace abincinta zai ci yake duk da Halima ma ta kware, ita ganin kyashinta ne matsalarta. na kwashe kwanonin “Tashi mu je gida” ya bani umarni, na miƙe yan biyu ma suka miƙe, dan su da gaske suke bi na za su yi. Na ce “A dauko min kayan su, kakar ta ƙi ta ce Bani da lafiya idan na warke a kawo su.

Mun shiga dakin Malam, tsohon na kishingide kan lallausan carpet din da ke malale a falon, yana sauraren Radio, muka yi mishi sallama sai shi mana albarka yake ya ce min “Zo nan yarinya” na matsa kusa da shi hannunsa ya sa ƙarƙashin tuntun da ya ɗora hannunsa, kuɗi ya ciro “Amshi yarinya, Allah ya baku zuri’a da za ta ji kanku”.Turus! nayi na waiwaya na dubi Tahir, daga min kai ya yi in karɓa, na sa hannu biyu na karba ina mishi godiya, Tahir ya matso bandir ya ciro na yan Naira ɗari “To ga shi malam, kudin sayen goronka” a gefensa ya ajiye masa, yan biyu dai da ƙyar muka rabu. Jingina kaina nayi da kujerar motar, na lumshe ido, kewar dattawan da na wuni da su yau kaɗai, tana ƙara rufe ni, sai kuma na tuna nawa iyayen, sai dai muyi waya, ina ji kamar kar in koma wannan gida, da za ka yi ta zama kai kaɗai kamar maye, babu me hulɗa da wani. Gudu sosai ya yi dan dare da ya soma. Bamu samu kowa a falon ba, na wuce ɗakina, ya wuce dakin Basma da ke da girki.Satin da ya zagayo Tahir ya shirya tafiya Ƙanƙara. Ba magiyar da ban mishi ba, ya tafi da ni amma ya yi funfurus, tare suka tafi da Halima, danbun nama nayi na ba shi na ce ya kai wa Haj. Ban san za shi Dutsinma ba, sai ranar Lahadi da daddare, ina kwance Ummata ta kira ni, ce min tayi “Godiya sosai za ki yi wa mijinki idan ya dawo, ya cika mu da hidima”. na ce “Bayan ya ki zuwa da ni” ta ce “Tun da dai ana zaune lafiya, ai shi kenan, yawon ba shi da wani amfani” na ce “Kai Ummata, amma ai zan zo bikin su A’isha” ta ce “Idan ya bar ki babu laifi.”

“Ina son ganinki Ummata” dan murmushi tayi wanda na ji sautinsa a kunnena, “Ai auren kenan, Ummuna.” sallama muka yi dan wayar Tahir da ke ta shigowa tana yankewa. cikin siririyar murya na mishi sallama “Da wa kike waya tun dazu? abin da ya fara ce min kenan, jin muryarsa kamar ya hasala yasa na dan yi murmushi “Da Ummata ne ranka ya daɗe” sai na soma gaishe shi “Me kike har yanzu ba ki kwanta ba? ya kuma tambayata “Ai barcin zan yi yanzu, ina Haj? “Tana ɗakinta” ya amsa min “Kai kuma kana tare da matarka.”

Maganar me kama da subutar baki, ta fito bakina ta isa kunnensa. Dan murmushi me sauti na ji ya yi “Matar tawa ai bata nan, tana gidan su, amma na san tana hanya”. “Sai da safe” na fadi ina shirin kashe wayar, “Har kin gaji da ni? ya tambaye ni “Uhm uhm, na faɗi cikin jin kunya “Mu kwana lafiya” ya faɗi yana kashe wayar. Na maida kaina na kwantar, ina mai jin dadin kular da nake samu daga mijina.

Washegari Litinin sammako suka yi suka taho. Shi maigidan ma bai dawo gida ba, Office ya wuce sai rana muka gan shi.Wata safiyar Alhamis, tsaye nake gaban mirror sai kallon kaina nake cikin shigar da nayi, ta riga da wando ne Pink, sai gaban rigar aka ratsa fari tana da stones. Takalma flat shoe na ciro shi ma fari, sai gyale me yala yala shi ma fari. Na kasa fita dan ba zan iya tsayuwa gaban Tahir a haka ba, dan sun lafe a fatar jikina, hatta dan cikina ya fito ya zauna das, shigowar sa tasa na fada gado na dukunkune, ya tako zuwa inda nake yasa hannu ya ɗago ni, ya haɗa ni da jikinsa.

“Tashi in ga kwalliyar da kyau, ko bani aka yi wa ba? ƙara sunnewa nayi, “To tun da ba za ki tashi in gani ba, mu je ki raka ni kar in makara.” Na ce. “To bari in ɗauko hijab” “Ki wuce mu je, waye a wajen? mai wanki bai zo ba.” ban so ba, haka nan na bi shi, da na buɗe mishi kofa ya shiga bai rufe ba, tsayawa ya yi yana kallona, Halima wadda ta fito cikin sauri dan tafiya wurin aiki tsayawa tayi turus! hango Tahir tare da munafukar yarinyar nan me fama da hijabi kullum.

Mamaki ya kashe ta ganin dressing din da tayi, wani zafi kirjinta ya dauka, idonta ya canza kala, in ma ba idonta ke mata gizo ba ciki ne jikin yarinyar. “Impossible, ban haihu ba ba shegiyar da za ta haihu! ta fada a fili, kamar me magana da wani. Cikin sassarfa ta ƙarasa inda motarta take, cin taya tayi sai ta dibe ta a guje a tare muka bi motar da kallo, ina mamakin diban karan mahaukaciyar da tayi da wata kujerar canopy da ke kan hanya, murmushi Tahir ya yi, dan shi sam abin da tayin bai ba shi mamaki ba saboda sanin da ya yi yanda take masifar sonsa haka take kishinsa, yasan ganin sa da Ummulkhairi ne yasa ta wannan fushin.

Dan ya hakikance duk a matansa ba me mugun kishi kamar ta, rufe motar ya yi sai ya bar gidan.Tana tafiya tana share zufar da ke keto mata.Bata iya haƙurin ta bari ta isa Office ba kamar yanda zuciyarta ke ruwaita mata, wayarta ta ciro babbar aminiyar ta ta kira “Kina gida kuwa? abin da ta fara cewa ƙawar kenan, “Yanzu na fito gida, akwai inda za ni lafiya? wa ya taɓa min ke? “Ina son ganin ki yanzu, kuma ina kan hanya za ni wurin aiki”.”Kar ki damu, zan same ki wurin aikin.”

Halima ta katse wayar. A motar Halima suka kulle kansu. Ta zayyana wa kawar ta ta matsalar da ta taso mata.Kafadarta ta dafa, “Ki kwantar da hankalinki Aminiyata, kamar yadda waccan ta yi yunkurin haihuwa ya’yan suna bin makwarara, wannan ma hakan ce za ta kasance. Ki kwantar da hankalinki auren ma ai dan rufe shi ya yi ba mu ji da wuri ba, nan da sati daya cikin nan ya zama labari ni nayi miki wannan alƙawarin. Kina tashi wurin aiki ki kira ni mu wuce, ki dai kira mijinki ki san me za ki fada mishi”.Halima tayi ƙwafa “Ai Basma, mahaifar gaba ɗaya aka lalata min, yaushe rabon da ki ji na ce miki tana da ciki.” ƴar munafukar dariya ƙawar tayi “Ai na kan tudu yasan aikinsa.

Da haka suka rufe hirar, kowacce tayi nata wajen amma zuciyar Halima bakikkirin kamar ta janyo lokacin tashi. A ranar dai Tahir ya tara mu ya bamu labarin takardar da ya samu a teburinsa yau, ta canjin wurin aiki da aka yi mishi zuwa Lagos.Ranakun da suka biyo baya, shirin tafiya Tahir yake tayi. Halima ta samu nasarar zuba maganin da ta karbo wurin malaminta ko bokanta za a ce, dan zubar da cikin Ummulkhairi wata safiya tana haɗa abin da za ta karya da shi. Ana gobe zai tafi ni ke da shi dan haka shiri nayi sosai yanda zai ji ni zam zam, yanda ko ya tafi zan tsaya a ransa. Duk wasu dabaru da na sani na yi har Hafsa na kira na nemi taimakon ta, har maganin Haj Shema’u da na kasa yarda in yi amfani da shi yau na yi karambanin amfani da shi, kuma babu karya a yanda ta kambama maganin nata. Ƙarfe goma na safiya ya sallame mu. Suka kama hanya da wani mutumi da ya dauka dan ya tuka shi.Wuni nayi ina barci a ranar. Sai washegari na koma kan al’amurana, marata na ji tana min ciwo kadan kadan, ban damu ba bathroom na shiga dan in dan watsa ruwa, ɗan jini jinin da na gani yasa gabana bugawa, na dai yi wankan na fito, har zuwa dare ban kuma ganin komai ba. Na kwanta ƙarfe sha biyu kamar an tashe ni. dan wani mafarki da nayi wai ina tafiya jini na zuba. Ai kam cikin jinin na ji ni kwance male male, hankalina ya tashi na shiga bathroom na tsarkake jikina na dawo na kwanta. Wasa wasa jini ya ƙi tsayuwa kwana nayi ina zurga zurga a bayi, ana fitowa sallar Asuba na kira wayar Tahir wayar a rufe take, sai kawai na hau shiri. Sanda na fito kowacce tana ɗakinta, da ɗaiɗai na buga kofar su, kuma na fada musu bani da lafiya zan wuce Hospital, lokacin da na fito gari ya soma haske, mai yin wanki ba gidan yake kwana ba, da safe yake zuwa, shi ke buɗe get bai kai ga zuwa ba, dan haka ban ga kowa a harabar gidan ba. Kofar me tafiya a kafa na buɗe sai na fice. Hajiya Hajara ta tafi ta’aziyya ƙanƙara.

Da kafa na taka har titi inda na samu motoci sun soma zirga zirga, me keke napep na tare, sai dai duk yadda na so tuna sunan Hospital din da muka je da Tahir kasa hakan nayi, sunan Barau dikko ya fado min da na ji su Haj da malam sun ambata lokacin da na je tudun wada. Dan haka can din na ce ya kai ni, ɗari biyar ya ce zai kai ni.Da isar mu sauka kawai nayi, na shiga raba ido, har sai da na samu wata baiwar Allah na tambaye ta. Rakani tayi har inda na sayi kati, na ƙara gaba wurin bin layi, har lokacin kuma ina jin zubar jinin, sa’adda layi ya zo kaina ƙafata ta fara rikewa, ina ganin likita nayi mishi bayani takardar scanning ya rubuta min. Da tambaya na gano inda ake yi, bayan na biya aka yi min na kawo wa Dr, yana dubawa rubutu ya yi sai ya miƙo min takardar, “Maza ki sawo wadannan kayayyakin ki zo in raba ki da wannan masifar.” Ya kuma gaya min kuɗaɗen wankin cikin da zai min, na ba shi sai na fito.Da tambaya nan ma na sawo duk abin da ya rubuta, duk abin nan da ake ina tafiya idona na tara ƙwalla na auren nesa, da a garin mu nake da yanzu ƴan’uwana na kewaye da ni. Na sawo na kawo, ya tsallake patient din da ke son ganin sa ya wuce cikin sauri ina biye da shi. Maternity muka nufa, masu haihuwa biyu muka samu suna fama, drip aka fara sa min wanda aka zuzzuba ma allurai kafin aka sa min wani magani kasan harshe, sannan likitan ya soma aikinsa, barci ke fizgata amma masifar wankin cikin ya hana. Bayan wasu mintoci aka kammala, na dan kwanta jim bisa gadon kafin na buɗe idona wanda na kasa hana hawaye zuba a cikinsu, wadda ke kusa da ni da ta riga ta haihu ta ce “Baiwar Allah, ina ƴan’uwanki? na share hawaye da bayan hannuna “Ba anan garin suke ba”. ta ce “Ina mijinki?

Na ce “Yana Lagos” bata gaji ba ta kara cewa “To ba wanda za ki kira, ya zo ku tafi?sai sannan na tuna wayata da na baro gida, miƙewa nayi na shuri takalmina “Zan iya tafiya na gode” ina fitowa dakin wa’anda suka haihu ba lafiya jiri ya ɗebe ni na tafi luu! wasu mata suka tare ni. Nan ma miƙewar na ƙara yi na fita mutanen da ke harabar asibitin suna bi na da kallo dan yadda nake tafiya ina haɗa hanya dan wani uban barci da ke fizgata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 20Wa Gari Ya Waya 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×