Skip to content
Part 4 of 5 in the Series Wani Rabon by Deejasmaah

Kukana na yi ma’ishi na share hawayena tuno alk’awarin da naiwa kaina cewa na dena kuka insha allah tunda dai Allah ya gani ba laifina bane na d’auki hakan a matsayin k’addaran da bazan iya kufcewa ba, kwanciyata nai a d’akin dan ban so in koma ciki a yanayin da nake ciki don nasan bestie zata iya zargin halin da nake ciki which I don’t like.

Tun daga ranar nake d’an rage shigewa hidimar sosai musamman a sabgan da nasan zan iya had’uwa da Mama gudun abunda zai je ya dawo nake yi ita kuwa creating scene ba wata damuwa bace a wurinta sannan ma banson abinda zaisa ana aibata Mamie this woman has done alot for us in baza mu yi abinda zaisa a yabeta ba to bai kamata mu aikata abinda zaisa a aibata ta ko a fad’i bak’ar magana akanta

Sannan duk wanda zai hana d’anshi ya aureka saboda wani dalili marar tushe to ba k’aramin mak’iyinka bane though bata gabana ko kad’an don na riga na cireshi a rayuwata sai dai shi d’in ya gagara cireni daga tashi rayuwar hakan yasa Mama tsanata fiye da baya, haka zalika matarshi ma duk inda ta ganni kallon banza ne da habaici but i never care because I’m far better than this abubuwan da suke gabana sunfi k’arfina

Janye jikin da nai da hidimar yasa bestie jin babu dad’i har tai tunanin maganar da muka yi ne ta janyo hakan saida taji ainihin musabbabin hakan wanda bansan daga ina taji zancen ba hak’uri ta bani sosai nikuma na nuna mata babu komai don na manta waccan maganar ma kuma banso ta sani ba don banson ta shiga damuwa akaina

Hakan yasa na sake ba sosai ba aka cigaba da hidima dani duk dama rabin taron a gidanmu akayishi hakan yasa ban cika had’uwa da ‘yan gidansu ba duk wani abinda zai had’ani da zuwa gidan ina kiyayeshi a wannan lokacin don zaman lafiyar zuciya da ruhina

Events mukayi Kala-Kala tundaga bridal shower henna party sai hausa day sannan Kamu tsarin bikin ya k’ayatar sosai domin abin anyishi akan tsari natsuwa da kuma wayewa sai sam barka

Ranar Asabar da misalin 2:30 aka d’aura auren Noosrah Abdullah Maikwanoni da mijinta Sahal Mukhtar Maikwanoni a mafi kyawun sadaki bikin ya samu halartar mutane da yawa inda da dare muka wuce ASAA Pyramid hotels inda acan ne akai gagarumar dinner ta masu hannu da shuni a gaskiya an zubda kud’i iya kud’i don su d’in dukansu ‘yan dangi ne kuma masu abun hannunsu danma wai a hakan babban gwaskan bai zoba wai da ba k’aramar b’arna zaai ba sai fatan zaman lafiya da soyayya a tsakanin ma’auratan

Ko da aka kaita mun zauna muna jiran ango da abokanshi ne saiga Mama ta shigo d’akin tunda ta shigo nasan babu alkhairi a abinda zatai don har sun fita kafin ta dawo daidai kanmu ta tsaya ” da fatan kinji kashedin da akai miki akan barin wainda suka kasa samun miji suyita jelar zuwa gidanki har sai sunyi miki k’ullin da zaisa nakin ya tsinke?”

Kallonta duka ‘yanmatan d’akin sukayi yayinda nikam na sadda kaina k’asa ina maijin wani zafi a zuciyata da sauri bestie tace ” haba Mama miye haka kuma…..? ” da sauri ta katse ta da “miye kike tambayana ? Zaki amsan tambayata ko kuwa ?” da sauri tace “eh mama naji ”

Kai ta gyad’a tareda cewa “very good sauran miki aiki dashi karki yarda ko da wasa inji ko inga hakan..

Ke kuma!!!” tana mai juya akalar magananta kaina “tashi mu tafi tunda ba gidan ubanki bane, wuce mu gani sauran kuma inji kin dawo gidan nan”.

Kafin ma ta kai k’arshen maganar ni na kai k’ofa Ina jiyo bestie tana cewa ” Mama ya zaki min haka dan Allah ” ita kuma tana cewa “ki cigaba da tambaya ta dan ubanki ki bar ganin ke amarya ce hakan ba zai hanani in zaneki ba in yaso shi Sahal d’in yayi jinyarki tunda ke sakarai ce,” sauri na na k’ara jin tana tahowa a baya na tana b’ab’atu

Mutanen waje ne suka fara tambayata ko lafiya na fito sai dai jiyo muryan Mama yasa kowa yai shiru daga tambayata wasu suka fara tausarta suna nuna mata illar hakan wasu kuma goyon bayanta suka farayi da sauri na nufi gate d’in gidan ina mai hawaye d’an tafiya na fara sai naji horn a bayana hakan yasa na tsaya Anty Nafeesah ce ta fito tareda umartana da in shigo motarta.

Ban da zab’i sai na shiga har k’ofar gidanmu ta kaini tana mai lallashina ni ko ban daina kukan da nake ba haba cin mutuncin yai yawa abin har ya wuce daga mu sai ita ya koma har cikin mutane, ina ganin kiran bestie nak’i d’auka har aka sauke ni godiya nai mata sannan na kira Fadeel ya bud’e min gida na shige bayan na d’an saita kaina kad’an d’akinmu na nufa nai kwanciyata ina mai jin zafi a raina

Wani kiran ya k’ara shigowa na sake ignoring gajiya tai da kiran ta hak’ura ba dan taso ba message d’in ban hak’uri da lallashi dubawa kawai nayi ban mata reply ba ina mai jin tausayin mu mu biyun dan nasan abin nan sai ya sakata a damuwa fiye dani kaina don soyayyar ta gareni mai matuk’ar girma ne da kuma kima rashin abin fad’i gareta ne yasa nak’i d’aukar kiran

2 days later.

Tunda abun nan ya faru nak’i zuwa gidan, nak’i kuma kiranta a waya har Mamie ta kira aka ci sa a tana office ta kira Areepha itama tana school fav ma hakan rasa yadda zatai. Da yamma ina parlor a zaune saiga kiran waya bak’uwar number ce hakan yasa na d’an jinkirta kafin na d’auka muryan namiji na jiyo yana cewa ” haba bestien mu mai yai zafi har haka…”

Kafin ince wani abu na jiyo muryarta tana cewa “tunda an ci sa’a ta d’auka ma ai an gode Babe ba ni wayar ” cewa ya yi ” ba wani angode fushi nake yi da ita tunda tak’i barinki ki huta sai wahala take saki da kuka…” Fisge wayar tayi tare da cewa “Baby mana…” Murmushi nayi jin muryanta cikin shagwab’a a hankali na furta “I’ve missed this soul.”

“Kin kyauta!” Ta fad’a a hankali i can imagine her rolling her eyes “da nayi mene kuma” nima na fad’a ina k’umshe dariyar da tazo min ” ai ba laifi kika yi ba kyautawa kika yi” ta bani amsa kunya ce ta rufe ni jin yadds tai maganar nima nasan ban kyauta ba ko kad’an dan haka nace”I’m sorry babe…. Kunyar reaction d’ina na ranar ne ya hanani picking kiranki ”

“Hmmmmmm! Sai kuma kika kasa min message ko kuma kizo tunda kinsan ina buk’atar ki kusa dani ko” ta fad’a itama shiru nayi kafin na sake cewa “I’m really sorry habibtie ” ajiyar zuciya ta sauke kana tace ” ba zanyi ba har sai kinzo inda nake” daga nan muka shiga hirar yaushe gamo har Sahal saida yace “yau dai an manta dani tunda an samu bestie ko is okayyyy ” da sauri nace “bestie sai anjima kinji we’ll chat “.

Sallama muka yi na ajiye wayar ina mai cewa “Ya Rabb ka sanya yalwataccen zaman lafiya da walwala a rayuwar auren wannan baiwa taka…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wani Rabon 3Wani Rabon 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×