Skip to content
Part 1 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

SADAUKARWA

Na sadaukar da littafin nan ga iyaye na abun alfahari na,na gode bisa tarbiyar da kuka bani ina muku fatan alkhairi a ko da yaushe

GARGADI

Ban yarda wani ko wata ya juya min littafi ba ko kuma ya yi amfani da shi ta han yar da bata da ce ba, ko ya d’aura min a wani website ba tare da izini na ba. Kuma zaku iya samun wannan littafi a website dina na.

(Oum Ayshat)

Bis_millahir_rahmanir_rahim

*****

Yammaci ne me cike da sanyin damuna ga wani irin iskar dake tashi ga hadarin da ya had’u sosai a garin kaduna garin ya yi ba’ki’k’kirin sosai, wata mota ce ‘kirar prado na ga ta yanko bakin titin da gudu sosai bana hankali bama.

Gudu motar ke yi sosai kai da gani ka san da alamar tambaya a wannan gudun, wasu matasa biyu ne acikin motar d’aya yana tu’ki d’ayan kuma na zaune abayan yana latse- latsen wayar shi.

Gefan shi kuma wata mata ce wadda ba za ta haura shekara 27 ba take kwance gefe kuma jaririya ce kwance tana bacci ita ma uwar bacci take kwasa.

Wanda ke tu’kin ne ya juyo ya kalli d’ayan

Ya ce”Kai Mazaa ya a ka yi ne na gaji fa gara mu san nayi da matar nan kafin mu kai wajen masu baka’ken kayan nan fa”

maganar da yake kai da ka gan shi ka san irin ri’ka’k’kun ‘yan tashan nan ne a kayo hayar su domin su aikata wata ‘barna.

‘Dayan ne ya d’ago

Ya ce”Bari na kira Hajiyar dai muji”

‘Daya wayar dake gefen shi ya d’auka ya lalubo wata namba ya fara kira se da ya kira wajen sau uku a na hud’un ne wayan na gab da katsewa aka d’auka, ko sallama bai yi ba

Ya ce”Haba Hajiya haka a keyi kin bar mutane ko kira baza kiyi kiji yadda ake ciki ba kawai, kina yawa fa Hajiya kin san tafiya daga jigawa zuwa kaduna fa ba ‘karamar tafiya bace ko?”

Daga can Hajiyar Ta ce”Haba Mazaa mai da wu’kar yanzu za kuji alert wani uzuri ne ya sha gabana amma ya matsiyaciyar kun yar da ta ko?”

“A’a tukuna dai”

Cikin tsawa da wata iriyar murya, Ta ce”Haba Mazaa baka da hankali ne? Ya za ku tsaya baku yar da ita ba har yanzu tun jiya fa nace ku yi nisa da jigawa ku yar da ita, to wallahi ba ruwana duk abin da ya biyo baya kar ku ambaci sunana”

Dariya ya yi irin ta su ta ‘yan duniya, Ya ce”Hajiya ai hakan ma ba zata faru ba yanzu dama kiran da muka miki kenan mun iso kaduna da zamu yar da ita ne”

“Ku dai kuka sani”

Tace tare da kashe wayar.

Kallon me tu’kin ya yi

Ya ce”Kai Alamz tsaya a nan”

Wani waje ya samu ya yi parking tare da fitowa lokacin ma magrib ta gabato ga yayyafin da aka fara, cikin sauri-sauri su ka fara kiciniyar fito da matar nan su ka yar da ita a gefen titin tare da fito da jaririyar ita ma su ka a je ta dai-dai kusa da matar.

Jaririyar ta tashi se mutsu-mutsu ta ke yi cikin sauri da rashin imani suka tafi suka barta awajen, lokacin kuma ruwan ya d’an fara saukowa.

Nan da nan jaririyar ta fara tsala ihu, ihu take sosai daga gani ka san na yunwa ne da tsabar wahala, gashi bakin titin ba kowa sai gonakin mutanen ‘kauyen, titin ma ba kowa ko mashuna da su ke wucewa babu kamar an yi yasa.

Jigawa

Guru qwaters

Wasu tamfatsa- tamfatsan motoci ne guda biyu su ka mi’ko titin unguwar, tafiya su ke a han kali d’aya na bin d’aya.

Dai dai wani tamfa tsetsen gida su ka tsaya su ka yi parking, gida ne had’ad’d’e tsayawa fad’in had’uwar shi ma ‘bata lokaci ne da gani kasan gida ne na babban mutum attajiri mai kud’i sosai.

Motar gaban da ta kasance ta masu tsaron mutumin sune su ka danna horn, da hanzari masu gadin ‘kofan su kayi sauri su ka wangale fad’ed’an kuma ‘katon gate d’in wanda mutun d’aya ma baze iya bud’e shi ba.

Nan su ka kunno kan motocin zuwa cikin gidan, wani ne naga ya fito da gudu ya zo motan na biyu tare da bud’e ‘kofar baya.

Wani mutum ne ya zuro ‘kafafun sa kafin daga bi sani ya fito daga motar, fari ne sosai kai da ganin sa kaga bafulatanin usuli.

Yana da madaidaicin hanci sai dai idanun sa jajaye ne fuskar nan a had’e in bacin farin fuskar da Allah ya bashi da idan ka kalleshi ba zaka so ka ‘kara kalla ba fuskar nan a hade take tam.

Yana fitowa ma’aikatan su ka fara zubewa suna kwasan gaisuwa ba wanda ya tsaya ya tanka mishi, duk ba wanda ya mi’ke daga du’kawan da ya yi se bayan da ya shige ciki.

*ALHAJI BUHARI KENAN ( MUGU BAI DA KAMA)* d’an asalin jahar Adamawa ne amma ya dawo jigawa da zama, a sanin kowa ya na da mata d’aya Hajiya Jamila wadda batu ta’ba haihuwa ko da so d’aya da shi ba.

Hajiya Jamila irin munanan matan nan ne ita, ba bahaushiya ba ce nupe ce Alhajin ya aureta.

Hajiya Jamila bata da mutunci ko ka d’an gata bata da imani duk matar da ta ra’br mata miji ba abun da ze hana bata kashe ta har lahira ba saboda kishin shi da take kuma ba wai son shi take ba kawai kud’in hannun shi take kwadayi.

Cikin sallama ya shigo falon Hajiya Jamila na kwance a kan kujera 3ster ta na jin sallamar da ya keyi amma ta kyale shi sema rufe ido tayi kamar me bacci.

Shima shareta ya yi ya haura sama zuwa part d’in shi, kaya ya rage tare da shiga toilet ya watsa ruwa tare da yin alwala ya fito ya sa kananan kayan sa tare da shimfid’a dadduma yahau domin yin sallah, kome ya tuna zumbur kuma se ya tashi ya fita a dakin da sauri har yana tuntu’be ya fita.

Wani d’aki naga ya nufa da saurin sa, bud’e d’akin ya yi tare da shiga.

Tsayawa ya yi sa’ka’ka yana kallon cikin d’akin daga bi sani ya shiga duba ko ina na cikin d’akin kamar ta’ba’b’be, sai kuma ya fito da gudu ya nufo falon cikin tsawa.

Ya ce”Jamila ina Sadiya ta shiga?”

Mi’kewa ta yi ta ‘kare masa kallo sama da ‘kasa sannan.

Ta ce”Ka ba ni ajiyar ta da zaka tafi gantalin na ka? Za ka zo ka na tambaya ta ko rainin hankalin na ka ne ya tashi?”

Cikin kwantar da kai kuma naji.

Ya ce”Haba Hajiya Jamila don Allah ina take?”

Dariya ta yi, Ta ce”Da ka zo ka sau ke min buhun haukan ne abun ka da mahaukaciya har se ka tambayi inda zata kaje ka tambayi wanda kaba tsaronta kila ta bude mata kofa ne ita kuma tayi gaba abun ta”

Juyawa ya yi don ba yan da ya iya da Hajiyar ta sa don ta riga da ta mallake shi, domin ba baya ba wajen shige-shigen malaman su.

Da sauri ya nufi sashin ‘yan aikin gidan ya na zuwa ya gan su kowa na nata aikin cikin sauri yace musu.

“Ina Talatu?”

Cikin tsoro da ganin Alhaji da kan shi ya zo su kace ta tafi garin su yau kwana 2.

A tsawa Ya ce”Ina ne garin na su?”

Wata ce daga cikin su.

Ta ce”A kano take”

Ya ce”Maza ki shirya muje garin”

Ya fice cikin sauri y koma d’akin sa wayar sa ya d’auka cikin sauri ya lalubo number amininsa Alhaji Sale kira d’aya ana biyu ya d’auka.

Ko sallama bai yi ba.

Ya ce”Saleh akwai matsala fa”

Alhaji Saleh daga can gidan shi suna hira da matar shi jin an ambaci matsala ya tashi ya bar wajen ya nufi d’akin sa.

Ya ce”Meya faru?”

Ya ce”Kasan na dawo ko ba Sadiya a gidan nan”

“What!?”

Alhaji Saleh yace tare da mi’kewa tsaye, kafin ya sake.

Ce wa”To garin yaya?”

Ya ce”Wallahi ban sani ba kasan naje sokoto na yi kwana 4 a can to yau na dawo bata nan, amma akwai wadda na ba wa tsaron ta kuma an ce ta tafi garin su to yanzu za muje garin na su ne ka shirya mu wuce”

“To”

Yace tare da kashe wayar.

Sai za gaye d’akin yake zufa na keto mai sosai ko canza kaya ya kasa yi duk abun nan ya san baze wuce makircin matar shi Jamila ba, haka ya daure ya tashi ya canza kaya tare da d’aukar key ɗin motarsa ya fito.

Ko da ya fito Hajiya Jamila ta bar falon can ya jiyo muryar ta tana waya da aminiyar ta hajiya Zubaida.

Wuce wa ya yi da sauri ya fito nan ya tarar da yar aikin na jiran shi tun d’azu gudun yin wani laifi.

Motar ya nufa nan masu rakiyar shi suka

nufo shi hannu kawai ya d’aga musu alamar baya son rakiyar, motan ya shiga tare da yar aukin sai direba mai tuka shi duk.

Gaba d’aya a firgice take jikin ta se rawa yake kamar mazari Kai tsaye gidan Alhaji Saleh su ka nufa shima kamar jiran su yake suna zuwa suka d’auki hanya se kanon dabo…

*****

Tafiyar awa d’aya da rabi½ ya kai su garin kano, cikin wani ‘kauyen su ka shiga har ‘kofar gidan su Talatu su ka yi parking jummai yar aikin ce ta shiga cikin gidan tare da yin sallama.

Can ta hango Talatu ‘kwance a tabarma da alama ma ita ‘kadai ce a gidan.

‘Kara sawa ta yi Talatu sai bin ta ta ke da kallo tuni tsoro ya ka mata.

Ta ce”Jummai lafiya dai ko?”

Jummai ko zama ba ta samu damar yi ba.

Ta ce”Lafiya ƙalau Alhaji ne yake neman ki tare da shi ma muka zo”

A firgice ta mi’ke tsaye jiki na ràwa tayi d’aki tana, Ce wa”Kije ki ce masa baki same ni ba kin ji dan Allah”

Jummai Ta ce”Ba ruwa na wallahi ki zo mu wuce kin san Alhaji har cikin gidan nan ze iya shigowa kuma ya tafi dake, gara ki zo a san wacce za’a yi”

Horn d’in motar su ka jiyo da sauri Jummai ta fita Talatu ba yadda ta iya ta d’au ko mayafin ta ta nufi wajen motar.

Tsugunawa ta yi tare da gaishe shi murya na rawa.

Fuskar nan a had’e ko amsawa bai yi ba, Ya ce”Shiga mota”

Cikin sauri su ka shige direba ya ja mota su ka yi jigawa ko da su ka i so kai tsaye wani gidan su dake wata unguwa da ban su ka je ko matan su ba su san da wannan gida ba.

Horn su ka yi mai gadi ya fito ya bud’e mu su su ka shiga gate d’in ,bud’e murfin motar ya yi tare da fitowa su Talatu su ka fito kamar kajin da kwai ya fashe wa a ciki.

Falon su ka bud’e su ka shiga su ka zauna su suna tsaye.

Cikin tsawa Alhaji Sale, Ya ce”Ku zauna munafukai kawai Kazaman talakawa”

Zama su ka yi har suna rige-rigen zama.

Cikin tsawa Alhaji Buhari Ya ce”Ina sadiya ta ke?”

Cikin rawar jiki da tuna gargadin da hajiya ta yi mata.

Talatu Ta ce”Ban…sa…ni…ba”

Da ‘kyar ta i ya had’a kalmar ta fad’a.

Cikin zafin nama Alhaji Buhari ya wanke ta da wani azababban mari kafin ta ankara Alhaji Saleh ma ya ‘kara mata wani.

Cikin dawowa daga d’an ‘karamin haukan da ta yi.

Ta ce”Zan fad’a wallahi! zan fad’a!”

Tana tsoron Hajiya Jamila amma ta san duk rashin imanin Hajiya Jamila ko rabin Alhaji bata kai ba.

Cikin rawar murya, Ta ce”Washe garin ranar da ka tafi hajiya ta zomin da barazanar kashe ni har da a halina in dai ban bata key d’in d’akin Sadiya kuma tazo ne da wasu manyan matasa guda biyu shi yasa na bata amma ka yi hakuri”

Wani lafiyayyen mari ya ‘kara mata tare da, Ce wa”Ban ce ko da uwatace zata dawo karki bata key d’in ba”

Ta ce”Kayi ha’kuri don Allah”

Tashi ya yi tare da kiran yaran sa ya ce a d’aure masa ita a d’aki kar a bari ta fito,sannan suka fita suka bar gidan.

Gidan Alhaji Saleh su ka nufa su ka zauna suna alhini da tattauna yan da za su ‘bullowa al’amarin.

Alhaji Buhari ne Ya ce”Wallahi da akwai han yar da zan rabu da wannan mata da tuni na yi domin ta isheni”

Alhaji saleh Ya ce”Na san yadda za’ayi kai dai kabar komai a hannu na kawai, zan san yanda za’ayi kafin mu koma wajen malam za’a ganta”

Cikin jin dad’i da yar da da aminin nasa.

Ya ce”Shikenan nagode”

Nan su kai sallama ya tashi ya wuce gida.

Koda ya isa gida Hajiya Jamila na falon ita da ‘kawarta ko kallon su bai yi ba ma ya wuce d’akin sa don kullum tsanar ta yake ji yanzu aran sa.

Su kuwa su ka cigaba da hirar su ko ajikin ta, se shewar su su ke yi.

A ‘bangaren Alhaji Saleh komawa ya yi gidan da su ka bar Talatu ya sa aka kawoma sa ita, cikin tsawa da jan ido.

Ya ce”Su wane mazan da su ka tafi da Sadiya?”

Cikin tsoron abinda ze biyo baya, Ta ce”Wallahi Hajiya kasheni za tayi don bata san ma na san d’ayan ba”

Cikin tsawa yace mata.

“Ki fad”‘amun ko na kashe ki kafin ita ta kashe ki”

Cikin rawar murya Ta ce”Mazaa ne”

Ya ce”Mazaa na gidana?”

Ta ce”Eh shine”

Cikin sauri ya mi’ke, Ya ce”Ku cigaba da tsareta”

Ya fita ya nufi gidan shi ya kira wani daga yaran shi ya tambaye shi mazaa yace ai baya garin nan kwana2 da su ka wuce yace bani number shi yace ai duk cikin mu ba wanda ke da number shi don baya sati da layi daya.

Alhaji Ya ce”Shikenan yanzu kuma ba ku san in da zamu same shi ba?”

Ya ce”Wallahi ba in da zamu same shi sai idan shi ya dawo da kan sa”

Alhaji Ya ce”Shikenan jeka”

******

Alhaji Buhari kodaya koma gida d’akin shi ya shiga ya yi kwanciyar shi do min ya samu hutu don abubuwa sun yi mai yawa,

be da d’e da kwanciya ba wayar shi ta fara ringing jawo wayar ya yi sunan Abbas ya gani na wayo a kan wayar d’auka yayi tare da karawa a kunne yace

“Assalamualaikum my son”

daga can bangaren akace

“wslm dad ykk.?

” lpy lau my son ya karatu?

” mungode Allah” ya ce tare da cewa, “dad seyaushe kuma zaka dawo sokoto “?

“dariya ya yi” tare da cewa haba my son yau kwana na2 ne fa amma har ka kosa na dawo.! , cikin dariyar shima yace

” ehh dad,”

“to shikenan”

“vary soon “

insha Allah na kusa dawowa, ya mom ku da Fatima na.?

“Suna lpy, dad se anjima.!

“to” yace sukayi sallama ya kashe wayar,tare da komawa yaci gaba da baccin shi.

Kaduna

Ruwa akeyi se dai ba irin me yawan nan bane ya yin da matar nan ke kwance ba alamun tashi kamar gawa jaririyar kuma bata fasa ihu da take yi ba.

Garbati! Garbati!! Garbatiii!!!

Daga can gonan dake gefen hanya naji ana kwala kira can naga ya taho da gudu tare da cewa “yi hakuri baffa”!

” wlh na zagaya ne”

“ba wani nan” ai kai haka kake da shiririta tun safe ace munzo gonan nan baza kayi abun arziki ba se shashanci,! kai kad’ai ma ya kamata kazo ni na huta ko kuma mu tafi kiwo.!

“ayi hakuri baffa “

ya ‘kara cewa cikin sunkuyar da kai.

“Shikenan ai had’o mana kayan mu, gashi an fara ruwa muyi sauri mu karasa cikin gari, “to”

yace tare da zuwa ya tattaro kayan da suka zo dashi cikin sauri suka kamo hanyar titin don komawa gida dayake gidan su se an tsallaka titin can ba nisa kuma da gonan tasu.

Tunda suka fito bakin hanyar suke jin kukan jariri tsoro ne ya kama garbati yace “baffa kaji abun da nake ji kuwa”! kallon shi yayi yace “to ni din kurma ne kome iyeeh!, muyi sauri mu tsallaka mu gani ko kuwa ka tsaya tambaya na ne!

Cikin sauri suka tsallako titi dede gurin da aka yarda matar nan ga jaririyar da take kuka ga kuma mata gefen ta a kwance!

salati sukayi, sannan baffa ya tsugunna ya dauki jaririyar yace “Kai garbati yi sauri ka dauko mana a malanke mu shiga da matan nan gida”, shidai garbati duk atsorace yake yasan rayuwar nan yanzu ba taimako ka taimaki wani ne yasa ka a rana kuma kai yazo ma ba mutum bane tunani da yake a zuciyar shi kenan ko maganar da baffa ke yi beji ba.

Cikin tsawa! baffa yace “Garbati!” d’agowa yayi daga tunanin da yake yi Baffa yace

“kai sakaren ina ne”

“ka karbi yaron ka kai wa innar ka ka taho mani da amalanke nace ko”!. Mika hannu yayi cikin addu’a ya karbi yarinyar cikin gugu- gudu, sauri-sauri ya kai ta gida ya bawa innar shi.

“kai yaro a ina ka samu yarinyar nan”

“ina zuwa inna” yace tare da nufan wajen da su ke ajiye amalanke lokacin ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya, cikin sauri ya koma bakin hanyar gurin baffan shi ya kama matar a tare da sakata aciki garbati ne ya tura cikin sauri ko kafin su isa ma dukan su sun jike har da matar, koda suka isa gidan kai tsaye d’akin inna suka wuce da matar, inna ko se binsu take da kallo ,Baffa ne ya dube ta yace “kije ki canzawa uwar da yar kaya naga sun jike sosai, idan na dawo sallah zan miki bayani” to tace tare da komawa dakin shikuma suka fice zuwa masallaci.

‘Dakin ta nufa tare da jaririyar a hannun ta wan da zuwa yanzu ma tayi shiru don wahala!

Koda ta shiga d’akin matar ta tashi tana zaune tare da dafe kanta se juya kai take, karasawa gurin ta tayi tare da ce mata “sannu dago kai tayi ta zuba mata ido, jarriyar inna ta mika mata cikin sauri ta mika hannu ta karbeta tare da bata mama.!

Se da tasha ta koshi lokacin ma se bacci yazo mata nan ta kwantar da ita , hannu ta d’aga cikin yaran kurame “tace wa inna za ta yi sallah, kamo hannun ta tayi suka fito wa je, ta bata buta tayi alwala tazo ta gabatar ta sallolin da ake binta,

Bayan ta idar ne inna ta zo ta a jiye mata kwanan abin ci kallon inna ta tsaya yi daga mata kai tayi alamar taci ba musu ta sa hannu ta fara ci,! sosai taci abincin don yanda yayi mata dadi kadan ta rage duk yawan shi.

Bayan ta cinye ne inna tabata wasu kayan tasaka tasakawa jiririyar wasu amman sunyi mata yawama, suna gama sawa ta kwashe nasu taje ta shanya a ‘yar rumfar su da suke shanya kaya, tana gamawa ta dawo tayi mata shimfid’a a ‘kasa ita da yarinyar ta, nuni ta yi mata alamun ta kwanta karasawa ta yi ta kwanta, inna ta miko mata yarinyar suka kwanta ita kuma fita tayi tare da jawo mu su kofar ta fito.

lokacin ma su baffa sun dawo sallah abin ci ta gabatar musu su da yaran nasu guda hudu biyu mata ne tagwaye se biyu2 maza

akwai yayar su amma ta rasu ita ce babbar yarinyar inna, se Abubakar wanda suke kiran shi da garbati shi ne Na biyu2 yana da shekara 16, se kuma me bin mi shi Bashir mai shekara 13 ,se Hassana da Hussaina, su hud’u yaran mallam muhammad se matar sa guda daya maryam wanda su ke kiran ta da inna,

suna cikin farin ciki sosai duka domin sunyi sa’ar iya ye ba ruwan su da son abun duniya.!

Suna da rufin a sirin su yana noma kuma yana kiwo yana da shanaye masu dumbin yawa ga kuma tumaki shiyasa kullum abincin gidan shi me kyau ne gashi da nama aciki.

Matsala d’aya ne suke fuskanta awajen garbati, shi yana son yayi karatun boko ne domin soja yake son ya zama, soja shine kawai burin shi inda kuma suka samu matsala da baffa yace baze yi ba amma har yau ranshi na matukar kaunar aikin,

akwai dan mai garin su wanda yake karatun boko sosai dan yanzu ma yana degree2 ne, Usman sunan shi amma suna kiran shi Usama yana karatu a Abuja ne wajen kanin baban shi, garbati yana zuwa wajen shi sosai ya koya mai karatun boko, ba tare da sanin baffan shi ba amma inna ta sani.

kuma yana da haza’ka sosai don shi kan shi Usman yana mamakin shi domin duk abun da ya koya mai to in sha Allah gobe se ya kawo shi ba ‘batan ko daya shiyasa yake son shi so sai kuma yanajin dadin koya mai karatu.

Duk da ba sa’an shi bane ya bashi wajen shekara sha d’aya, yana da shekara 27 haka suke karatu sosai cikin mutum tawa da girmama juna ba girman kai kuma,

kullum shi yasa ba ruwan shi da aikin gona don idan baffa ma ya bashi se dai yayi wahalar bata bakin shi don garbati in banda shirme ba abun da yake yi sabanin bashir da yake matukar son aikin gonan da kiwo.

Suna zazzau ne suna cin abin ci baffa ne yayi gyaran muraya tare da yiwa inna bayanin tsintuwar matar da yayi abakin hanya inna ta tausaya mata sosai don ta san awannan zamanin ba abun da baza ayi ba kila ma wani ne ya sato ta yazo ya yarda ita anan sun dade suna hira daga bisani kowa ya wuce dakin shi ya kwanta.

Jigawa

Alhaji Buhari da Alhaji Saleh hankalin su ba karamin tashi yayi ba na batan da Sadiya tayi ba don kowannan su ya kasa sukuni suna zau ne kamar kullum a dakin Alhaji saleh.

Alhaji Buhari ne ya d’ago ya kalli aminim nashi tare da cewa “yanzu ya kake gani zamuyi kasan fa asatin nan zamu koma wajan mallam gashi ba sadiya duk hankalina atashe yake!

Alhaji Saleh ne ya numfasa yace “insha Allah zamu same ta kafin wannan ranan!

“Domin Talatu ta fad’amun maza ne suka sace ta tare da temakon Haj. Jamila, yanzu mai wuyan inda zamu samu mazan shine kawai, amma nasa anemo min shi domin yasan in da ya yarda ita kuma ze iya zuwa ya d’auko ta,

shiru kawai Alhaji buhari yayi don shi kadai yasan abunda yake ji aran shi.

Da haka sukayi sallama inda ya koma gidan shi cike da fargaban had’uwan su da mallam.( ko in ce bokan nasu.)

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.4 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Wata Rayuwa Ce 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×