Skip to content
Part 2 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Kaduna

Kiran sallar Asuba ya tashi mallam Muhammad in da bisa al’adar gidan shi yake fara tashi kafin ya bi d’akunan yaran nashi ya tashe su kowa yayi sallah ya tashi matar shi tare da ce mata ta shiga ta shi bakuwan, nan kafin ya rufe baki suka jiyo ihu..! daga d’akin matan da gudu sukayo wajen d’akin tare da budewa matar nan suka gani dafe da kanta se jujjuya kai take tana ihu daga bisani kuma ta saki kan ta fara fisge-fisge so sai tana yaga kayan jikin ta cikin sauri Baffa ya karasa wajen ta ya fara tofa mata addu’o’i ta dena fisge-fisgen amma se guranani take yi sosai Inna ta cika da mamaki sosai baffa ne ya kalle ta tare da ce mata “ta samo mai igiya” cikin minti da befi d’aya1 ba inna ta dawo dauke da igiya a hannun ta ta mi’ka mai, kar’ba yayi ya d’aure matan nan don ya riga ya fahimci hauka ke damunta!

Bayan ya d’aure ta Inna ta dauki jariryar da har yanzu bata tashi ba tana ta bacci abun ta suka fita suka bar dakin cike da mamakin wannan abu d’ayan dakin inna ta shiga tare da kwantar da yarinyar ita kuma ta fito don yin sallah yayin da Baffa da yaran shi suka wuce masallaci don yin nasu sallan.

Bayan sun dawo sallah ne suka shiga dakin baffa duka yaran gidan domin yin karatun asuba wanda al’adar gidan ne duk idan anyi sallar asuba ze zauna da yaran domin su yi karatu ze karbi wanda ya mu su jiya tare da ‘kara musu wani yayin da inna take waje domin hada musu abun kari.

Jigawa

Yau Alhaji Buhari hankalin shi atashe yake domin yau zasu je wajen mallam gaba d’aya ya kasa sukuni.

Wanka ya shiga yayi tare da shirin fita tsab ya sauko falon gidan anan ya tarar da Hajiya Jamila zaune ta d’aura ‘kafa d’aya kan d’aya tana kad’a kafafi har ze wuce ba tare da ya kalleta ba tace “sannu Alhaji. juyo wa yayi yace “ya akayi kallon shi tayi cikin yamutsa fuska tace “magana nake son yi da kai ba musu ya samu waje ya zauna tare da tsura maya idanu dariya tayi tace ‘naga kana kare min kallo ne.! , “to lefi ne idan na kalle ki d’in! , tace “a’a, “naga kwana biyu ka sharenine ko d’aki na ma baka shigowa bana sanin dawowar ka da fitan ka ko don yar gold ta gudu ko, to ka sani muddum baka janye batun kara aure ba to wlh ba matar ba har kai ma zaka nemi kan ka ka rasa don wlh kai nawa ne ni kad’ai ba me shiga tsakanin mu nan gani nan bari ,wani kalan kallo ya wurga mata yace “abun da kika tsareni ki fad’a mun kenan , “a’a, ni dama kud’i nake bukata ba wani abu ba, yace “me zakiyi da kud’i?

Kallon sa tai tace “yar dasu zanyi tafad’a tana kad’a kafa, “sauri nake fa kika tsaidani ko? Cikin yatsina fuska wanda batasan kara mata muni yake ba tace rike ka nayi ka wuce ga hanya mana , tsaki yaja tare da wurga mata Atm din shi ya wuce dariya tayi tana fad’in “se Alhaji nawa.

Banza yayi da ita tare da ficewa daga d’akin.

Kai tsaye inda yayi perking d’in motar shi wadda yake fita da ita shi kad’ai da ita nan ya nufa tare da shiga masu mai rakiya basu bata lokacin bin shi ba don sun san in dai ya shiga wannan motar to tafiyar shi shi kad’ai ce kai tsaye gidan aminin shi ya nufa shima ya gama shirin shi tsab kai tsaye suka wuce…

Kaduna

Bayan sun gama karatun kowa ya fito suka nufo inda inna ta had’a musu abun kari kowa ya zauna tare da yin Bismillah suka fara cin abin ci inna ce ta d’ago ta kalli Baffa tace “mallam yanzu ya zamuyi da wanna matar ne.? d’agowa yayi bayan ya kur’bi ruwan shayi yace nima tunanin da nake yi kenan idan na gama cin abin cin zanje gidan mallam na kira shi domin ya duba mana wannan lamarin, ‘shikenan tace tare da cigaba da cin abin cin ta.

Zamfara

Cikin wani kasurgumin ‘kauye na hangi Alhaji Buhari da aminin nashi suna yankan wani daji wanda shi kanshi ‘kauyen baza ka taba zaton da halitta acikin ta ba duk ga gidajen mutane amma ba ko mutum daya awaje kai ko kaji baza ka hanga a wannan ‘kauyen ba, bare dajin da ke bayan ‘kauyen se wanda ya cika mara tsoro sannan ze iya shiga wannan daji.

tafiya suke kai da ka gan su kasan ‘karfin hali ne da kuma fad’in Hausawa da suke cewa “wanda yayi nisa baya jin kira” domin sunyi nisa wajen son sabon Allah tafiya su kayi mai d’an nisa daga bakin titin ‘kauyen inda sukayi perking d’in motar su zuwa wani waje mai kamar kango don ba rufi ta saman wajen amma an zagaye shi, yaji fenti irin mai kyallin nan ja jur da ku ma bakin fantin, ba kyaun gani!

suna zuwa wajen kuma se naga sun juya baya suna tafiya da baya da baya zuwa wannan wajen har suka shige ciki wasu irin abubuwa na hango a cikin wajen wanda se da suka matukar firgita ni na juyo da gudu na bar su awajen.

Kaduna

Bayan sun gama cin abin ci baffa ya mike domin zuwa gidan mallam da yake gidan ba nisa da gidan shi.

“Mallam magaji ya kasance babban malami ne a ‘kauyen ko ba ‘kauyen bama garuruwa da yawa na zuwa wajen shi domin wata matsala tasu in da kuma ya kasance malamin baffa ne sosai kuma abokin baban shi.

Koda ya isa gidan sallama yayi, Yadikko matar mallam ce ta amsa tana fadrin “wanene”? baffa ne yace “matar mallam nine” da yake matar mallam suke ce mata fitowa tayi da fara’ar ta tace” haba kai kullum kamar ba dan gida ba ka shigo amma se ka tsaya kwala sallama, yace “a’a! wajen mallam kawai nazo,” “to bara na kira maka shi” tace tare da shigewa gidan d’akin mallam ta nufa ta fad’a mai ana sallama sannan kuma ta wuce ta ci gaba da aikin ta.

shi ko mallam be 6ata lokaci ba ya fito Baffa ya mishi bayanin abun da yake faruwa kai tsaye suka wuce gidan tare da mallam din sallama sukayi baffa yayi mai iso suka shigo kai tsaye d’akin matan suka nufa koda suka shiga matar ta samu bacci, mallam ne ya du’ka yana mata wasu addu’o’i nan ta farka ta fara fisge-fisge tana wasu kalan abubuwa, addu’ar ya ci gaba da yi mata se kuma ta koma bacci, tashi yayi yace ma baffa suje waje, fita sukayi daga d’akin.

Tabarma Baffa ya shimfid’a musu suka zauna sannan Mallam ya fara bashi labari cewa “Wannan matar lafiyar ta lau asiri akayi mata na zama kurma da kuma na Hauka bayan nan da wasu ma amma in sha Allah zata samu lpy zanyi mata magani na wata daya1 insha Allah zata dawo dai- dai da yardar Allah “godiya Baffa yayi sosai sannan mallam ya koma gida shima.

‘Dakin inna ya dawo yaga tana ta fama da jaririyar se kuka take yi, inna ce tace “mallam ko za’a siyo madara ne a gwada bawa yarinyar nan tun da kaga mahaifiyar ta halin da take ciki, ‘to yace tare da fita kud’i ya bawa bashir yaje shago ya siyo madaran don Garbati ma baya gidan yana gidan mai gari d’aukan darasi.

Bashir be jima ba ya dawo da madarar da aka aike shi nan inna ta had’a ta ba ta, ba lefi tasha sosai se tayi shiru , ta dai na kukan kallo inna take, itama inna ‘kare wa yarinyar kallo take ‘yar kyakykyawa da ita kuma daga ganin ta sabuwar haihuwace don bata tunanin tayi arba’in 40ma kwantar da yarinyar tayi bacci ta koma inda inna ta fito domin d’aura abincin rana.

Zamafara

Alhaji Buhari ne shi da aminin sa zaune gaban wani ‘katon mutum gashi baki ne sosai be da ko kyau gani gaban shi kuma wasu tarkacen kayan tsafi ne irin nasu wanda abun se ya baka tsoro suna zaune sun gurfana kamar masu neman gafara.!

Cikin d’aga murya mutumin yace

“Ina sadiyaaa?”

Bana ce zuwa na gaba lalle ku zo nan da ita ba Alhaji saleh ne yace “Allah ya taimaki boka sadiya ta gudu ne bamu ganta ba kuma dama mun zo ne domin a duba mana ko zaka iya sanin inda take “

wani irin mahaukaciyar dariya yayi mai ‘kara mai kuma razanar wa wanda duka dajin se da ya amsa yayi wasu yan tsafe-tsafen shi sannan yace” ya rage naku kuje kusan inda take domin aikin mu ya gagara akanta domin akwai addu’o’i sosai zagaye da ita duk Aljanin mu da muka tura daya je jikin ta yake kone wa domin akwai masu mata addu’a da yawa don haka kuyi irin taku na gani ,kuma kunsan cewa jibi ne ranar da nasa na auren Buhari da sadiya ko?”

Alhaji Buhari ne yace “muna sane boka!”

yace “to kar ku sake ranar ta wuce baku samota ba idan ba haka ba akwai ga garumar matsala kunji ko “

cikin had’a baki suka amsa da ehh munji yace “to ku wuce ku bani waje kuma duk halin da ake ciki jibin kuzo”

“to” suka ce hade da mike wa jiki ba kwari suka fice tafiya suka ‘kara yi sosai sannan suka iso inda sukayi perking suka hau motar su se jigawa state.

Kaduna

Tun da yarinyar tayi bacci inna ta fito ta kama aikin gida, Baffa kuma yau kiwo suka tafi shi da Bashir don Garbati bai dawo ba, baffa har ya gaji da jiran shi shiyasa ma ya tafi don yasan lamarin garbati se addu’a.

Bari mu le’ka gidan mai gari

gida ne me kyau don duk ‘kauyen gidan yafi kyau daga shi kuwa se na su garbati duk da garin nasu ba wani ‘kauye bane sosai, tun da komi na more rayuwa akwai a garin bugu da ‘kari gashi akwai ilimi sosai agarin.

koda na shiga gidan d’akuna ne da yawa aciki yana da mata uku d’akin Usama ne a farko da ka shiga, d’aki ne mai girma sosai, d’akin nashi ya had’u sosai dai-dai na me ‘karamin karfi tun da har yana da kayan kallo a d’akin, da yake akwai wuta agidan,

can na hangi garbati kwance saman ‘katuwar katifa yana kwance gaban shi kuma littafi ne ya dage se rubutu yake yi aciki daga gani ma shi kadai ne ad’akin, se rubutun shi yake yi ganin haka nima na janyo mai kofar d’akin tare da fito wa waje.

A bangaren su Alhaji tun da suka koma hankalin su ya matukar tashi da abun da mallam yace,

Alhaji Buhari ya tsinewa matar shi yafi a kirga don ita ta saka shi cikin wannan halin da yake ciki bayan isar su kowa gidan shi ya wuce domin ya huta inda kuma sukayi gobe za su had’u da safe domin cigaba da shawarar yanda za’ayi.

Alhaji saleh bayan ya koma gida wani yaron shi ya sa ke kira ya tambaye shi maza ya dawo ya fad’a mishi “jiya ya kira shi ya kuma shaida mishi gobe ze shigo Nigeria domin baya kasar” cikin hanzari Yace “bani number shi daya kira ka jiya” number ya bashi ya kwashe yace je ka se na kara kiran ka tafiya yayi shi kuma number ya fara gwada kira yayi sa’a ta shiga amma kuma tana ta ringing ba’a d’auka ba ya kira yafi sau biyar amma ba’a d’auki kiran ba haka yasa ya hakuri da niyar anjima ze kara gwadawa.

Garbati bashi ya dawo gidan ba se wajen 12:00pm lokacin ma Baffa basu dawo ba koda ya shigo gida inna ce kadai ke ta aiki, su hassana ma basu dawo makaranta ba d’akin baffa ya shiga sad’af-sad’af ya d’auko fatanya yayi sauri ya nufi gona don yana gudun fad’an Baffa, shiyasa ze kare kan shi domin idan yaga yayi aiki sosai agona ze rage fushin da yakeyi akanshi domin Garbati Allah yayi shi yaro ne me hankali da nutsuwa ga girmama iyayen shi baya tsallake maganar su kuma baya so yaga 6acin ran su abu d’aya ne kawai ake fama dashi karatun boko.

Domin son abun aran shi yake da ace akwai yanda zeyi ya ha’kura da yayi amma bayajin hakan sannan addu’ar shi kullum Allah yasa Baffan shi ya yarje mishi akan karatun shi ya tafi birni.

Sosai ya dage yayi aiki a gonan ba’a son ran shi ba kuma haka ya d’aure inna dan tasan halin d’an nata, su Hassana na dawowa ta zuba musu abincin hade da ruwa suka kai mishi don tasan baya juran yunwa.

Jigawa

Kamar yadda sukayi zasu had’u da safe haka akayi a safiyar Alhaji Buhari yazo gidan aminin nashi in da suka ‘kara gwada number maza, yana ta ringing amma ba’a d’aga ba, sake kira yayi wayan na gab da yankewa sukaji an d’auka,

“Hello”

sukaji ance abun da ya basu mamaki kuma muryar mace ne Alhaji saleh ne yace “ina me wayar cikin kashe murya tace “baya kusa “to don Allah idan ya shigo ki bashi kice mai Alhaji saleh ne to tace tare da katse wayan.

ta dubi mazaa tace

“aji me akace “

mazaa dake kwance kan gado yace” ya za’ayi naji”

tace “wani ne ya kira wai Alhaji saleh ne mi’kewa yayi yace “ta samu kenan!”

“Oga nane fa kira shi muji ya ake ciki kinsan ina cikin matsalar kud’i fa,

d’aga wayan tayi ta kira bugu d’aya aka d’auka mi’ka mai tayi yace

“Hello”

daga can maza yace “Allah ya taimaki oga!”

Yace “mazaa kana ina ne?

yace

“oga ina dubai fa naje sha’katawa ne “

yace “mazaa ta samu kazo yau d’in nan “

dariya yayi irin nasu na ‘yan duniya yace” oga baze samu bafa sede gobe “

yace “haba mazaa kar muyi haka dakai ina neman ka ne”

yace

“oga kayi ha’kuri fa yace tare da yanke wayan”

wani irin dariya ya saki har yana tun tsurawa kasa! yace “Alhaji ka kawo kan ka se na tatse ka sosai”

kira ne ya kara shigowa wayan seda ya yanke wani ya kara shigowa sannan ya d’auka dama al’adar sa idan yana so yayi aiki ya samu kud’i sosai se ya ja ma mutum rai ya gama mai wulakan ci inda ze samu kud’i sosai,

yana d’agawa Alhaji yace “mazaa wannan fa babba aiki ne ka fad’i ko nawa kake so ni kuma zan baka tun kafin kaji aikin dan nasan sunan ka na nan MAI NASARA duk aikin da ka fara sunan shi ‘kararre “

Dariya yayi yace “Alhaji million 40 nake so” yace “ka samu zan tura maka ma yanzu idan kana bu’kata, sannan kuma akwai na kashemin jin dad’i da kayi shi kuma million goma, “ba matsala mazaa zan tura maka 50m yanzu amma anjima zaka dawo yace” Ehh ina nan durowa anjimam” “to” yace sannan suka yanke wayan, Suna addu’a Allah yasa da gaske ze dawo Ameen suka ce tare da yin sallama

Kaduna

Koda Baffa ya dawo kiwo lokacin ‘karfe 3:40pm don amfara kiran Sallar la’asar ma a masallacin garin.

Garken shanun su ya wuce ya d’aure dabbobin sannan ya dawo gida inna ce tayi mai sannu da zuwa yace” yawwa ina yaron nan ?”

ai ya tafi gona tun d’azu “hmm bayan ya dawo yawon ne ya wuce gonar ko ?”

shiru tayi bata ce komai ba, yace “ya ba’kuwar?”

Tace” tana nan har yanzu bata tashi ba, le’kawa d’akin yayi sannan ya fito ya wuce masallaci don bashir kai tsaye yayi masallacin tun kafin su shigo gida.

Jigawa

Bayan sun gama waya da mazaa Alhaji saleh tashi ya yi ya tafi gidan shi da niyar da yamma zasu had’u idan Mazaa ya dawo.

Haka ko aka yi Mazaa ya shigo garin jigawa da yammacin ranan in da Alhaji Saleh ya kira aminin sa ya fad’a masa zuwan Mazaa shima ya d’auko hanya yazo domin su san yanda za’a yi kafin gobe suje ga babban boka.

Kaduna

Baffa be shigo gidan ba se wajen karfe 5:30pm kuma tare da malam Magaji suka shigo.

‘Dakin da matar nan da ke kwance suka shiga har lokacin bacci take yi addu’ar ya ‘kara tofa mata a ruwa ya yayyafa mata motsawa ta yi ka d’an sannan ta koma taci gaba da baccin ta.

Wajen Inna suka koma Baffa ne ya tambaye ta yarinyar, d’aki ta shiga ta d’akko mai ita kar’ba ya yi ya bawa malam ita ma addu’ar ya yi mata tare da sa mata albarka suka fi ta da nufin idan an yi magrib za su dawo.

Bayan fitan su ne Inna ta cigaba da aikin ta in da su Hassana kuma suna rike da jaririyar da bata da aiki se bacci kamar ta san halin da mahaifiyar ta ke ciki.

Cikin sauri-sauri Inna ke aiki saboda dare ya yi mata yau bata fara da wuri ba har gashi a na kiran magrib amma ta kusa gamawa ma, d’akin da matar nan ke ciki ta shiga don d’auko kwanonin da zata raba abincin,

mamaki ne ya kama ta ganin matar nan zaune se ‘ko’karin kwance d’aurin da aka mata take yi kamar ba ita ba,tsoro ne sosai ya kama inna kawai se ta juya ta fita don matar ma bata gan ta ba, tunani ta tsaya yi ta kwance matar ne ko kuma ta bari malam ya zo?.

Bata da wata mafita a ran ta da ya wuce ta bari su zo d’in, hakan yasa ta koma wa cikin fargaban wannan abu.

Dai-dai lokacin ne kuma Garbati ya shigo don an idar da sallar magrib Inna, Ta ce”Yaron nan ina Baffan ku yake?”

Garbati da ke shirin zama, Ya ce”Yana ‘kofar gidan malam don nagan su tare”

“To yi sauri ka kira min shi”

Mikewa ya yi ya fita da saurin shi, ko minti biyar ba’a yi ba se gashi da Baffa da malam.

Inna ce ta kalle shi, Ta ce”Malam matar nan fa ta farka”

‘Karasawa d’akin su ka yi har da inna ta d’auki abun da zata d’auka ta fita ta ba su waje.

‘Karasawa su ka yi wajen ta Baffa ne ya dubi malam, Ya ce”Malam kamar ta dawo dai-dai”

Mallam daga kai ya yi ba tare da yace komai suka fara ‘ko’karin kwance ta, har suka kwance ta duka.

Kallon matar malam ya yi yace mata.

“Sannu ko!”

‘Daga mai ka yi tare da yi mishi alama da hannu zata yi sallah.

Inna suka kira ta taimaka mata suka fita don ta yi alwala su kuma suka koma masallaci cikin al’ajabin wannan abu haka.

Alwala ta yi Inna ta shimfid’a mata abun sallah ta yi sallah sannan ta zauna cikin maganar kurame ta ke tambayar ‘yar ta.

Fita Inna ta yi ta je ta zo mata ta ‘yar ta ta cikin sauri ta kar’beta tare da d’agawa Inna hannu alamar na gode.

Murmushi Inna ta yi mata ga mamakin Inna se ta ga matar ta yi mata murmushi ita ma.

‘Dadi sosai Inna ta ji, matar kuma ta kwanta mata a rai jin ta take kamar ‘kanwar ta, kuma matar na burge ta daga jiya zuwa yau ta lura tana da son ibada don da ta tashi ba abun da take fara yi se sallar se kuma ta tambayi ‘yar ta.

tashi Inna ta yi ta fita don ta samo mata abin da zata sa ka a baki, bata jima da fita ba ta shigo d’auke da kwanon abin cin.

Tarar da matan ta yi tana kuka sosai da hawaye tana kallon yarinyar ta da sauri Inna ta ‘karasa ta dafa ta tare da ce mata.

“Ki yi ha’kuri ki de na kuka”

Share mata hawaye Inna ta yi sannan ta matso mata da kwanon abin cin kar’ba ta yi ta fara ci.

fita Inna ta yi nan ta samu su Baffa har sun dawo tabarma Inna ta shimfid’a mu su su ka zauna ta gabatar musu da abinci.

malam ne ya yi gyaran murya ya kalli Inna, Ya ce”Ya jikin na ta?”

Inna Ta ce”Alhmdllh! yanzu ma na bar ta tana cin abinci ne”

“masha Allah”

Malam ya ce sannan ya ci ga ba da magana.

“Wato kamar yan da na fad’a muku a baya wannan matar an yi mata asiri ne na hauka da kuma na rashin magana,amma kuma ta na ji, amma sakamakon addu’o’in da kuma yawan ibadan ta asirin se be kama ta sosai ba shine za ku ga da an yi magrib se ta dawo dai-dai amma kuma ana yin asuba haukan na ta ze dawo”

Jin jina kai Baffa ya yi cike da al’ajabin wannan lamari, sannan, Ya ce”Malam yanzu ya za’a yi?”

Se da ya numfasa sannan, Ya ce”Insha Allah akwai maganin da zan mata na sati uku zuwa wata d’aya1 da yar da Allah zata dawo dai-dai”

“To Allah ya yar da”

Inna tace tare da mi’ke wa ta nufi d’akin da matar take zaune.

wannan shine littafi na na farko ko da zaku ga gyara ko kuskure a gyara min dan Adam ajizi ne, Nagodei

Kaduna

Bayan Kwana 3

Mallam sosai yake yi wa matar nan magani, don yanzu jikin se sau’ki ya ke yi, da dare har da ita suke zaman hira se de bata magana.

Amma de har yanzu haukan ta yana nan se dai yanzu yayi sau’ki idan mallam ya yi mata addu’a se de ta wuni bacci da anyi magrib se ta ta shi, se de ta dinga bin su da ido kawai.

Ta na tuna rayuwar ta na baya kafin wanda ta fi tsana a duniya ya wargaza mu su rayuwa, sosai familyn Baffa ke burge ta, ta ji dad’i da Allah yasa ta fad’o wannan gida, domin gara mata zaman nan gidan akan Gidan Buhari.

Yau ma kamar kullum a gidan Baffa suna zaune bayan sallar isha’i, su na fira, Matar nan na gefe kusa da inna yayin da Bashir ke musu tatsuniya Shi kuma garbati ya na zaune gefen innan shi kusa da matar nan yana rubutu, don malamin nashi ya koma Abuja jiya se yayi sati ze dawo, Shine yace yaje yayi ta karatu kafin ya dawo, matar ne ta zuba ma abun da Garbati ke yi ido sosai yana ta rubutu kuma yana da hand writing sosai.

Baffa ne ya kira garbati tare da cewa “yazo ya aike shi shago ya sayo musu lemo, tashi yayi tare da barin littafin a wajen ya ta fi,

hannu matar nan ta sa tare da d’aukan littafin, kawai taji tana sha’awar ta gabatar musu da kanta ko da sunan ta ne domin basu sani ba,kuma ta ji hankalin ta ya kwanta tare da su, rubutu tayi kamar haka,

“Sunana Halimatu-sadiya, sannan ‘ya ta khadijatu (Ilham), ni ‘yar asalin jihar adamawa ne, zan baku labari na da yarda Allah, nagode da Karamcin da kuka nuna min, Nagode sosai”,sannan ta rufe,

Dai-dai lokacin garbati ya dawo daga aiken da Baffa yayi mishi ya zauna tare da d’aukan littafin shi, rubutu ya gani se da ya karanta duka sannan ya d’ago ya kalli matar, ita ma shi take kallo murmushi yayi mata ta yi mai alama da ya karan ta musu,

Ba musu ya fara karanta musu abun da ke rubuce a littafin,

Baffa ne yace “ashe ma yarinyar mamata ce Allah ya raya khadija” suka amsa da “Ameen” basu juma ba kowa ya tafi d’akin shi domin yin bacci.

Jigawa

Alhaji saleh ya ‘kara neman mazaa inda ya shaida mishi lallai a d’auko Sadiya tare da ƴar ta,

mazaa ya shaida mishi har yanzu be samu labarin inda alamz yake ba amma yana nan yana neman shi, Sannan ya wuce.

Alhaji saleh ya kira abokin nashi ya fad’a mi shi yadda sukayi da mazaa,

yace to “Allah yasa ada ce” sannan ya shaida mai tafiyar da ze yi sokoto, gobe asabar, yace mai zeyi kwana 4 huɗu ze dawo ranar laraba, tun da ranar alhamis za su wuce wajen boka.

Bayan sun gama tattauna wa ne sukayi sallam.

Alhaji Buhari ya nufo gida, koda ya shigo gidan be samu Hajiya jamila agida ba kuma gashi yana son ya yi mata sallama domin yasan halin ta, kai tsaye d’akin shi ya wuce ya watsa ruwa sannan ya had’a abubuwan shi da zai bu’kata, domin idan ya tashi tafiya sokoto baya zuwa da kaya ko ze saka kaya be fi ya saka biyu zuwa uku ba, sannan ya aje shi saman drawer d’akin ya samu waje ya kwanta don ya huta kafin magrib, kasancewar magrib ta gabato, be dad’e da kwanciya ba ya ji ‘karar mota tayi perking a compound d’in gidan, ta hundon d’akin shi ya leka,in da ya ga Hajiya Jamila ce tsaki yayi sannan ya fito falo ya zauna yana jiran kara so war ta, bud’e d’akin ta yi ta shigo, kallon ta ya yi sannan yace “Jamila da izinin wa ki ka fita”?

kallon shi ta yi sannan ta ce “sabon salo yau ni kake tambaya da izinin wa na fita.? ” “to da izinin kaina na fita se akayi yaya kuma”?, murmushi ya yi sannan ya ce” to yi haƙuri mai da wuƙar zauna mana kar ki gaji” “to ina ruwan ka da gajiya na”

shiru ya yi don ya ga alama yau hajiyar ta sa a fusace ta ke, kallon ta yayi yace “dama nazo na miki sallama ne gobe zani sokoto”, ko kallon shi batayi ba tace

“adawo lpy”

sannan ta wuce d’akin ta, murmushi ya ‘kara yi tare da mamakin wannan mata tashi, mi’ke wa yayi ya fita waje don lokacin an fara kiran sallar magrib din.

Sokoto

Yaya! Yaya!! Yaya!!!

Wata yarinya ce na hango wacce ba za ta wuce shekara 4 ba take kwala kira yayin da ta ke nufo wani d’aki, tana gudu har ta zo bakin kofar d’akin ta murd’a za ta bud’e,

bud’e kofar wani had’ad’d’en yaro na gani wanda shekarun shi baza su gaza sha 12 ba, da ka gan shi kasan bafulatani ne na usuli yanda yake fari sosai ga dogon hanci, ran’kwashi na ga yayi wa yarinyar na wasa yace “ke har yanzu baki san kin girma bane za ki din ga kwala ma mutum kira tun daga d’akin momi fa nake jin kina kira na ban hana ki ba ko”?

rau-rau tayi da ido zatayi kuka, jawo ta yayi ya na shafa kan ta ya ce “yi haƙuri autar momi kiyi hakuri kinji amma ki de na kwala min kira haka kin ji”

Make kafaɗa tayi sannan ta ce “a’a kuma se na faɗawa dad ma”

sannan tace “momi tace ka zo” ta juya ta na ƙunƙuni ta wuce , kallo ya bita da shi yana mamakin wannan yarinyar me shegen surutu da saurin fushi, d’aki ya shiga ya rufe littafin da yake karatu aciki sannan ya juya yana fad’in momi ko me zan mata asanyin safiyar nan,

sannan ya nu fi d’akin momin nashi

“Assalamualaikum”

wata mata na hango zaune akan kujera wacce baza ta wuce shekara 30 ba fara ce sosai kai da ka ganta kasan Bafulatana ce kuma wanda hutu ya zauna a jikin ta sosai, amsa sallamar ta yi,

shigowa ya yi ya nemi waje ya zauna kasan kujeran da take tare da shafa kafan ta yace “momi na kin tashi lpy”?, murmushi ta yi najin daɗi da ƙaunar ɗan nata ta ce “lpy lau my son ya karatu dan nasan shi kake yi” sosa kai yayi sannan yace “Alhmamdulillah momi”

sannan ya ɓata fuska cikin salon shagwaba da ita kan ta momi ke mamakin shi wani lokaci kamar wani yaro yace “momina se ki rin ‘ka turo min wannan yarinyar ta ki mai kama da redio fm tazo ta cikamin kunne tayi ta kwala ma mutum kira, banajin dad’in haka Allah kuwa” murmushi momi ta yi sosai sannan ta ce autar tawa ce Redio fm ko?

Dai-dai nan ta shigo d’akin dama ta na bakin kofa tun ɗazu tana fushin rankwashin da yayi mata, shigowa ta yi ta rankwashe shi a kan shi sannan ta juya da gudu ta fad’a kan momin ta na dariya ta ce

“na rama!, na rama!”,

dariya yayi ya ce

“zan ka ma ki!”,

ta ce “kayi hakuri yaya don Allah!, kasan ba na son a rankwashe ni ne fa”, momi da tun d’azu ta zu ba musu ido tana murmushi se yanzu tayi magana ta ce “fati na kije ki ba wa yayan ki hakuri kinji”

mikewa ta yi ta zo ta tsugana ta ce “kayi haƙuri yaya kaji!”

dariya yayi ya ce “an’ki ayi hakurin!”

“don Allah fa!”,

yace “an’ki d’in!”,

Juyowa tayi tace “momi kin ga ya ‘ki ya haƙura ko!?”

momi ce tace “haba my son ayi ma auta hakuri ka ji”

murmushi yayi yace “momi ki ‘kyale ni da wannan autar taki kawai, ko home work d’in ma na fasa nuna miki tun da haka ne”

da gudu ta fad’a kan momi ta na kukan shagwaba tace “momi kin gan shi ko”

“Ki kyaleshi kawai idan ya’ki yi ni ki kawo nayi miki kinji, dariya tayi tare da rumgume momi ta ce “ina son ki momi na” sannan ta juyo ta yi mai gwalo,

kallon momi ya yi yace “momi kin ga abun da take yimin ko”?

“Kai Abbas me tayi maka kuma”, momi gwalo ta yi min fa,

“Kai momi sharri ne ban yi ba fa.”

girgiza kai yayi kawai yana murmushi, momi ce Ta ce “fati na ina antyn ki”?

Ta’be baki tayi tace “momi wlh naje na tashe ta, kuma ta koma bacci ta ‘ki ta shi, don ta ga ba school, ai an kusa komawa next week ne”, Abbas ne yace “Allah momi autar ki ta iya tashin mutane baza ta barsu suyi bacci ba indai safiya tayi shikenan ko wa kawai ya tashi” dariya ta yi ta ce “to ai malamin isalamiyar mu ma yace “ba kyau baccin safe ma.”

Share ta ya yi don idan ya bi ta wannan yarinyar se su wuni suna abu daya.

<< Wata Rayuwa Ce 1Wata Rayuwa Ce 3 >>

1 thought on “Wata Rayuwa Ce 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.