Skip to content
Part 11 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Wani wahaltaccen bacci ne ya ɗauke shi, ƙarar wayarshi ta tashe shi, buɗe idanuwa ya yi bai ko motsa ba balle ya cirota daga aljihu, kanshi ciwo yake kamar zai rabe biyu, agogon ɗakin ya kalla, ko waye ya kira wayar ba ƙaramin kyauta mishi yayi ba don lokacin Sallah ya yi, yana jin ana kira a ƙaton masallacin da ke nan cikin gidansu. Alwala ya je yayi ya fito yana jin wayar taci gaba da ringing ya cirota daga aljihunshi ya duba, ganin Samira ce yasa shi jefa wayar kan gado yana fita zuwa masallaci abin shi. 

Ciwon kai zata ƙara mishi ya sani, ko da aka idar da Sallah, zamanshi yayi a masallaci sai da ya yi Azkar ɗin yamma tukunna ya nufi gida. Sai dai me yana shiga falo ya gansu zaune ita da Fawzan suna hira a falo suna dariya. Numfashi ya sauke yana shiga da sallama, su duka biyun suka amsa. 

“Sannun ku da gida.”

Ya ce ba tare da ya kalle su ba ya wuce yana nufar ɓangaren shi. 

“Raafik…”

Samira ta kira, juyowa ya yi fuskarshi babu walwala, yana kuma ganin yadda Fawzan ke murmushi, yasan yadda ta ja sunanshi ne yake ba Fawzan ɗin nishaɗi, su duka suna ƙara mishi ciwon kan da yake ji. 

“Bansan sau nawa zan gyara miki ba. Rafik, ki daina jan Raa ɗin, kuma Q ne ba K ba… Rafik.”

Ya faɗi ta tsakanin haƙoranshi. Saboda gab yake da ɗaga musu murya su bar falon ko su ƙyale shi ya ji da abinda yake damun shi. Yana kallon Samira ta taso daga inda take tana takowa zuwa inda yake. Jikinta sanye da doguwar riga ta farin less mai jar filawa, sai wata irin hula ja akan ta. Ya kuma tabbata a haka ta fito ba tare da wani mayafi ba. 

“Me ya sami wayarka?”

Ta tambaya tana sauke idanuwanta cikin nashi. 

“Siyarwa na yi.”

Ya amsa yana tsare ta da idanuwa. Shagwaɓe fuska tayi

“Tun yaushe nake kiranka baka ɗauka… Na maka message ya fi talatin baka min reply ba… Ya kake so in yi? Kwana tara yau… Ban saka a idanuwana ba… Don na damu da jin lafiyarka ya zama laifi Raafik?”

Idanuwanshi ya janye daga kanta yana kallon Fawzan da ke zaune a falon ya zubo musu idanuwa. Tsare shi ya yi da nashi idanuwan, babu shiri ya miƙe yana haɗe fuska.

“Ki kira ni in kun gama…”

Ya ce wa Samira da ta ɗaga mishi kai ba tare da ta juya ba tukunna ya fice daga falon. Hankalin shi Rafiq ya mayar kan Samira da ke kallon shi idanuwanta cike taf da hawaye. Ƙarshen abinda zai so shi ne ta fara kukan ta da baya ƙarewa. 

“Hidimomi ne sukai min yawa Samee, kina kira lokutan da banda halin ɗagawa…”

Hannu tasa tana share ƙwallar da ta taru a gefen idanuwanta tukunna ta sake kallon shi. 

“Ka kalleni… Ka kalli idanuwa, me kake so in zama akanka? Danne daraja da jifa da kunyata ta ‘ya mace nace ina sonka kawai bai isa ba? Bai kai ka dinga min sassauci ba?”

Runtsa idanuwanshi yayi yana buɗe su akan ta. 

“Ina son ki.”

Ya faɗi. Lumshe idanuwa ta yi ta buɗe su a hankali. 

“Ba kalar son da nake maka ba…”

“Samee kaina na min ciwo. Ki yi haƙuri ya kamata ko sau ɗaya in bi duk kiranki. Happy?”

Ɗan guntun murmushi ne ya ƙwace mata duk da zuciyarta da ke ciwo, son shi na mata yawo, ko ba komai yau nasara ce tunda ya amsa ya kamata ya kirata, ban haƙuri ba wani abu bane a wajen Rafiq in har ya yi kuskure. Akanta ne dai yake da wuyar sha’ani, kuma alaƙarsu ta sake jagulewa ne daga lokacin da ta faɗa mishi zuciyarta na doka mishi ta wani fannin daban. 

Ya bata haƙuri nan take ya kuma ce bai taɓa mata kallon da ya wuce ƙawarshi ba. Sam baya jinta kamar yadda take jinshi. Sai dai ba zata daina binshi ba, wataƙila ko tausaya mata ne yayi, ta yi nisan da zata iya samun matsala in bata same shi ba. 

“Tam ka raka ni in tafi gida sai ka sha magani ka huta…kar in dameka…”

Bai ce komai ba ya fara tafiya yana nufar ƙofa, murmushi take, ta bi bayanshi. Baya son wani surutu daban, in ma cewa ta yi ya rakata har gida za su tafi sai Fawzan ya bi bayansu ya dawo da shi. Bazai iya dogon surutu da Samira ba. Suna fita harabar gidan motar Daddy na yin parking. Sai da zuciyar Rafiq ta yi wani tsalle kamar zata fito daga ƙirjinshi. 

Da kanshi ya ƙarasa yana buɗe wa Daddy murfin motar tare da faɗin, 

“Sannu da zuwa…”

Tun kafin ya fito, da kai ya amsa Rafiq ɗin, tukunna ya fito, jakar da ke hannun shi Rafiq ya karɓa, zuciyarshi babu komai a ciki banda ganin ya yi wani abu da zai burge Daddy koya yake, ya manta yadda ya fara tunanin zai yi musu da shi akan wani abu. Haka Daddy yake, yanayin shi kawai yana cika idanuwan mutane tun kafin su san kowanene shi. 

“Sannu da zuwa…”

Cewar Samira da Rafiq ya manta tana tsaye a wajen. Murmushi Daddy yayi suna gaisawa cikin fara’a. 

“Zan wuce Daddy. Allah ya huta gajiya…”

Hannu Daddy ya miƙa yana kama jakarshi da ke hannun Rafiq. 

“Bani ku tafi abinku…”

Sakar mishi Rafiq yayi yana murza hannunshi da yake jin alamar zufa a jiki ya bi bayan Daddy da kallo. 

‘Allah kaban ƙarfin zuciya…’

Ya faɗi a zuciyarshi. Ɗan zabura ya yi saboda Samira da ta tafa hannuwanta a saitin fuskarshi. 

“Kana wacce duniya?”

Daƙuna mata fuska kawai ya yi, ta yi dariya kafin ta ce, 

“Na tafi, don Allah ka daga in na kira ka.”

Da kai ya amsata, ta juya tana tafiya, tsaye ya yi a wajen gaba ɗaya gwiwoyinshi babu ƙwarin kirki. Cikin gida yake son shiga, amma ganin Daddy ya tuna mishi yadda musa magana da shi kawai ke ɗaukarshi satittika yana tattaro duk wani ƙarfi da yake da shi, balle kan abu babba har haka. Wani yawu ya haɗiya, yasa hannu yana dafa zuciyarshi da ke tsalle ya lumshe idanuwanshi yana maida numfashi cikin son samun nutsuwa ko yaya take. Ya kai mintina biyu a haka kafin ya buɗe idanuwan shi yana takawa zuwa cikin gida.

Ya kai mintina biyu a tsaye a bakin ƙofa yana maida numfashi. Kafin da ƙyar ƙafafuwanshi sun mishi nauyi ya ja su yana shiga babban falon gidan. Bai ga kowa ba sai TV da ke kunne, yasan Daddy na ɓangaren shi, Nuri ma tana can. Ɗakinshi yake son zuwa ko kwanciya ya yi kafin Daddy ya gama hutawa ya je su yi magana. 

Amma sam bayason ko motsawa daga inda yake saboda baya jin ƙwari a jikinshi, samu ya yi ya ƙarasa kan doguwar kujera ya zauna, kwanciyar na gagararshi. Kanshi da yake ciwo ya ci gaba da sarawa kamar zai faɗo, hakan yasa shi dafe shi da duka hannuwanshi. Bai ji shigowar Aroob falon ba, sai maganarta da ya ji. 

“Yaya? Lafiyar ka kuwa?”

Sauke hannuwanshi yayi yana kallonta tare da girgiza mata kai. Zai iya ɓoyewa kowa halin da yake ciki, banda su, wasu lokutan in ba su tambaya ba, yakan ƙyale su don baya son raba damuwarshi da su, shi ya kamata ya rage musu nauyin tasu duk sa’adda buƙatar hakan ta taso. Amma indai suka tambaya, zai faɗa musu. Ƙarya ita ce ƙarshen abinda zai taɓa haɗa shi da ƙannen shi. 

“Meya sameka? Menene? Nuri ta ce Daddy zai dawo. Shine ko? Me yai maka?”

Aroob ta ƙarasa maganar muryarta na karyewa. Hannu Rafiq ya miƙa mata don baya son yin magana, nata tasa cikin nashi yana janta ta ƙarasa ta zauna kan kujera a gefenshi tukunna ya saki hannun nata. 

“Me yasa Daddy yake haka? Duk inya dawo sai ya maka wani abin…”

Ware mata idanuwanshi Rafiq ya yi cike da kashedi, hakan yasa tai shiru tana turo bakinta. 

“In kawo maka ruwa?”

Ta buƙata, tambayar ta sa shi jin yadda maƙoshin shi ya bushe. Kai ya sake ɗaga mata, ta miƙe tana dawowa da glass cup da ruwa a ciki ta miƙa mishi, sai da ya karɓa tukunna ta zauna. Shanyewa ya yi duka yana maida numfashi kafin ya ce, 

“Nagode…”

Jinjina mishi kai ta yi. Tana kallon damuwa shimfiɗe a fuskarshi da bata san yadda zata taya shi ɗaukarta ba. Ta kuma tabbatar Daddy na da hannu cikin damuwar tashi. Tunda Nuri ta ce musu zai zo ranta yake a jagule. Lokuta da dama ta fi son yai zamanshi, don duk idan ya zo sai ya ɓullo da wani abin da tsantsar takura ce a wajen su. 

Ba don zuciyarta bata cike da ƙaunar Daddy ba, sai don bata son yadda ya fi takura Rafiq ɗin da ɗawainiyar da ke saka shi cikin damuwa, ta san kuma yana ɗauka ne har da tasu, don takurar da yake shiga har da son karta ƙaraso kansu. 

“Yaya ina son zuwa gidansu Juwairiyya…”

Ta faɗi don janye tunaninshi daga koma menene, ita ce kaɗai hanyar da take da ita. Daƙuna mata fuska Rafiq ya yi. 

“Me ya hana?”

Ya buƙata, don tasan dagashi har Nuri basu taɓa hanasu ziyarar ‘yan uwa ba. Zumunci na cikin manyan abubuwan da suke da muhimmanci a wajen Nuri. 

“Ina so in kwana ne…”

Kai ya girgiza mata. 

“Ki je ki wuni ki dawo…”

Turo baki Aroob tayi

“Ba makaranta fa Yaya…”

Kai ya sake girgiza mata, hakan nasa shi runtse idanuwanshi saboda yadda hakan yasa kan ci gaba da sara mishi. 

“Baya aiki Aroob, surutun na ƙaramin ciwon kai ne.”

Rafiq yace yana ɗan dafe kan nashi. Ya gane bawai gidansu Juwairiyya take son zuwa ba, hankalin shi take son ɗaukewa daga damuwar da yake ciki. 

Agogon ɗakin ta duba, biyar har ta yi, da sauri ta ɗauki remote tana ƙaro maganar TV ɗin, kafin ta ɗauki ɗayan ta canza tashar zuwa Star Plus. Aikam sun saka shirin da take son kallo ɗin na Saloni. 

Yadda ta tattara duka hankalinta kan shirin ne yasa Rafiq faɗin, 

“Yanzun meye daɗin shiriritar nan?”

Ware mishi idanuwa Aroob ta yi cike da mamaki. 

“Hmm Yaya baka san daɗin ba wallahi, ya haɗu sosai. Ka ga ita saloni ɗin ko? Saboda kalar fatarta yasa bata samu miji da wuri ba, gashi iyayen suna musguna mata, to wani maikuɗi aka shirya ya zo neman auren ƙanwar, amma basu faɗa mishi cewar yayarta bata da aure ba…”

Daƙuna mata fuska ya yi.

“Saboda me?”

“Ai su abune marar kyau sosai ƙanwa ta yi aure yayarta batai ba, to an shirya ta je wajen addu’a ita saloni ɗin, kafin su zo…”

Sauke numfashi yayi, ko kaɗan Aroob ba gajiya take da surutu ba ya sani. 

“Aroob yi kallon ki…”

Dariya ta yi tana ƙyaleshi tare da maida hankalinta kan shirin da take kallo, shima idanuwanshi kafe suke kan TV ɗin amma baya fahimtar komai, saboda nutsuwarshi bata tare da kallon sam. Bai san iya lokacin da ya ɗauka zaune a wajen ko kuma ga asalin abinda yake tunani ba, sai dai ji ya yi Aroob ta taɓa shi. 

“Sallah ake kira…”

Ta faɗi, sai da ya ɗan ɗaga mata kai tukunna ta wuce, da ƙyar ya ja jikinshi zuwa ɗakinshi ya ɗauro alwala ya fito ya wuce masallaci, ko da ya idar da Magrib yai nafilarshi sa da ya saba ta bayan Magrib, Qur’an ya ɗauka ya zauna ya buɗe yana karantawa da sautin da kunnuwanshi ne kawai suke ji. A nan ya zauna yana jin yadda nutsuwa ke shigar shi a hankali. 

Bai bar masallacin ba sai da akai sallar Isha’i tukunna. Sai dai me kamar damuwarshi jira take ya fito ta sake samun wajen zama tare da shi. Ga zuciyarshi da gaba ɗaya ta karye lokacin da ya shiga cikin gida. Bai ƙara jin faɗuwar gaba ba sai da ya ga Nuri zaune a falon. Sallama ya yimata muryarshi da sanyi. 

“Nuri…”

Ya kira a karo na farko da ganin ta ya kasa samar mishi ƙwarin gwiwar da yake buƙata. 

“Yana ciki…”

Nuri ta faɗi muryarta na fin tashi sanyi. Numfashi ya ja mai nauyi yana saukewa kafin ya nufi ɓangaren Daddy zuciyarshi na wata irin dokawa. Zufa ya ji a tafin hannunshi lokacin da ya ɗago da shi yana ƙwanƙwasa ƙofar.

“Yes…”

Daddy ya faɗa daga cikin ɗakin, muryar shi ɗauke da yanayin nan da yakan sa mutanen da ke kusa ɗagowa su kalli wanda yake ɗauke da muryar duk sa’adda zai yi magana. A hankali Rafiq ya tura ƙofar ya shiga tare da yin sallama. Daddy yana zaune cikin shigar shadda ta alfarma, za ka rantse wata fita zai yi babba, ba wai zaune a babban falon gidanshi ba. 

Kallon shi Rafiq yake yi daga nan bakin ƙofar ya kasa ƙarasawa ciki, sam baya son jin ko wanne bayani ne Daddy yake son mishi, baya son jin yadda ya gama yanke hukunci akan Zafira, yadda babu wanda ya isa ya canza hakan. Runtsa idanuwa ya yi yana ganin fuskar Zafira. 

Farin cikin da ke cikin idanuwanta lokacin da take gaya mishi abinda ke tsakaninta da Muneeb, fuskarta kawai ta nuna mishi yadda Muneeb yake da muhimmanci a wajenta. Girgiza kai ya yi a hankali, sai dai a madadin fuskarta, ta Muneeb ce ta cika mishi zuciya. Tashin hankali da tsoron da ke bayyane akai na sa wani gashi miƙewa a bayan wuyanshi. 

Babu shiri ya buɗe idanuwanshi akan Daddy da ke kallonshi a nutse, yana bashi lokacin da yake buƙata kafin ya ƙarasa cikin falon. Da sauri ya taka zuwa gaban Daddy ya durƙusa. Muryarshi can ƙasan maƙoshi yake soma faɗin, 

“Don Allah kar kai mana haka….Daddy karkai amfani da rayuwar Zafira a matsayin tsanin ɗagawarka….a karo na farko farin cikin mu ya zo sama da naka….ina roƙonka ne Daddy… Don Allah karkai haka…”

Rafiq ya ƙarasa muryarshi na karyewa, ba zai tuna lokacin ƙarshe da hawayenshi suka zuba ba. Saboda ragontaka na ɗaya daga cikin abinda Daddy baya so. Amma yau a shirye yake da ya zubda su akan Zafira, akan farin cikin ƙanwarshi. 

“Ba ƙaramin gida bane ba, yaro ne da ya fito daga gidan mutunci…”

Daddy ya amsa cikin yanayin da babu ƙofar gardama. Murmushin takaici Rafiq ya yi. 

“Gidan mutunci Daddy? Babban gida? Waye shi?”

“Ɗan gidan Alhaji Modibbo…”

Jinjina kai Rafiq yayi yana zama dirshan, fuskarshi cikin hannuwanshi, numfashi yake mayarwa a hankali, babu kalaman da za su bayyana abinda yake ji. Bai kuma da ƙarfin gardama da Daddy. 

“Bama abinda na kiraka don shi kenan ba. Akwai abinda nake son siya a China, ina son ka je ka dudduba min kafin in tura kuɗin…”

Sai lokacin Rafiq ya ɗago da kanshi ya kalli Daddy cikin rashin fahimta.

“Maganar auren Zafira ɗin fa?”

“Sati biyu za ka yi , in ka dawo sai mu yi maganar da kyau.”

Wani abune can ƙasan zuciyar Rafiq yake mishi wani iri, haka kawai bai amince da tafiyar ba, ba don zai iya ce ma Daddy a’a ba, abune da bai taɓa faruwa ba, ba kuma ya jin daga yau za’a fara. Amma kawai baya son tafiyar.

“Daddy…”

Ya soma, katse shi ya yi da faɗin, 

“Kar kaja maganar nan. Sai ka dawo tukunna…”

Numfashi Rafiq ya sauke. 

“Yaushe zan tafi?”

“Gobe in sha Allah. Da yamma… Nasa an gama komai tun last week.”

Kai kawai Rafiq ya ɗaga yana miƙewa. Ba don bashi da abinda zai fada ba. Sai don yasan maganar su ta yau da Daddy ta ƙare, bakuma zai saurari komai ba. Hakan yasa shi ficewa daga ɗakin yana jan ƙofar. 

*****

Wayarta take ta kallo, tun ƙarfe takwas ya kamata Muneeb ya kirata, lokacin wayarsu ne yanzun. Ko da wani uzurin ya riƙe shi yakan mata text ya faɗa mata. Yana gama abinda yake yi kuma zai kira. Tun ɗazun take mamakin ko saƙon shi bata gani ba. 

Ba faɗa suka yi ko wani abun ba, ko da ma sun yi shariya ba halin Muneeb bane. Yakan mata saƙon cewar har lokacin fa bai haƙura da laifin da tai mishi ba. Ta ɗauki wayarta tana ajiyewa da nufin kiranshi yafi sau biyar. Bata yanke hukuncin kira ba sai da taga har takwas da rabi ta yi bata ji shi ba.

Sai dai harta yanke bai ɗaga ba. Zuciyarta da take a jagule ta sake jagule mata. Sai da ta kira sau huɗu bai ɗaga ba tukunna ta tura mishi saƙo. 

‘Don Allah ka ɗaga…ina buƙatar jin ko lafiyarka.’

Sai da ya shiga, ta ga alamar ya buɗe tukunna ta tattara duka nutsuwarta kan wayar ko zata ga amsar shi amma shiru, zuwa lokacin wasu hawaye masu zafin gaske sun cika mata idanuwa. Hannuwanta biyu tasa tana share su. Kafin ta sake ɗaukar wayar ta kira har sau biyar wannan karon ba tare da ya ɗaga ba. Tana ajiyewa ƙarar saƙo na shigowa. 

Da saurin gaske ta ɗauki wayar ta bude saƙon. 

‘Don Allah ki ƙyale ni, zan kira ki da kaina in inason magana.’

Tun kafin ta ƙarasa karatun hawaye suka soma zubar mata. A karo na farko a rayuwarta da ta ji wani abu kamar yana buɗewa a ƙirjinta da ciwo marar misaltuwa. Da sauri ta kai hannu cikin rigarta tana taɓawa ko da gaske tsagar har a waje ne. Bata ji komai ba, da ƙyar take jan numfashi saboda ciwon da take ji a wajen. 

Ga hawayen sun sa dishi-dishi take ganin screen ɗin wayar balle har ta samu ta rubuta wani abu. Da ƙyar ta samu hawayen suka ɗan tsagaita mata. So take ta tuna ko ta mishi wani laifin ne amma ta kasa, mamakin da take shi ne ko da take mishi laifi bai taɓa faɗa mata maganar da ta yi mata zafi har haka ba. 

‘Idan na maka laifi ne ka faɗa min sai in baka haƙuri, in kuma akan ɓoye soyayyarmu ne, na faɗa ma Yaya Rafiq ɗazun.’

Ta rubuta tana turawa. 

‘Banda ƙarfin maimaita magana ɗaya. Ki duba saƙona na farkon.’

Ya sake dawo mata da shi. Wasu sabbin hawayen na sake zubo mata. Bata taɓa sanin haka tashin hankali yake ba sai yau. Ji take kamar babu wadatacciyar iska a ɗakin. Wani kuka mai sauti ya ƙwace mata. Wayar ta ajiye tana saukowa daga kan gadon, bata damu da cewar kanta babu ko ɗankwali ba. Asalima riga da wando ne na bacci da akafi ma laƙabi da Pyjamas a jikinta. 

Fitowa tai daga ɗakin, tafiya take tana sa hannu tana share hawayen da ke bin fuskarta, zuwa lokacin dalili ɗaya ta samu da zaisa Muneeb ya datsa mata magana haka. Inba dai Rafiq ya same shi ya ce ya rabu da ita ba. Bata kuma ga dalilin da zai sa yai mata hakan ba. Ko gani bata yi sosai, bata ga Fawzan ba sai da ta ci karo da shi. 

“Haƙora kike son cire min ne da da…”

Fawzan ya soma, kallon da ya yi wa fuskar Zafira da kuma hawayen da ya gani na bin kuncinta ya katse mishi maganar daya soma. 

“Innalillahi… Zafira… Menene? Me akai miki? Me ya faru?”

Fawzan yake tambaya hankalin shi a tashe. Da duk tambayar da zai mata da yadda kukan ta yake tsananta. Gaba ɗaya ta ɗaga mishi hankali. Hannuwan shi yasa yana tallabar fuskarta tare da goge mata hawayenta. Amma wasu ne suke sake zubowa. 

Zai ce tun girmansu yau ne karo na farko da ya ganta tana kuka haka. Duka gidan babu mai haƙuri da kawaicinta. Bai taɓa ganin yarinya mai hankalinta ba, bawai don ta zo a ƙanwarshi ba. 

“Don Allah ki daina kukan nan Zaf, ki faɗa mulin ko menene…”

Kai take ɗaga mishi, tana saka hannuwanta kan nashi da ke fuskarta, numfashi take mayarwa. Cikin kuka take ƙoƙarin magana. 

“Ya… Ya… Yayaa Rafiq….”

Ta ja kalmar tana sake fashewa da wani kukan. Fawzan bai jira wata kalmar ta sake fitowa daga bakinshi ba ya saki fuskarta ya kama hannun ta. Ɓangaren Rafiq ya ja ta suka nufa, ƙwanƙwasa ƙofar yake kamar zai karyata. Ya ɗaga hannu da shirin sake ƙwanƙwasawa aka buɗe ƙofar. 

Baki Rafiq ya buɗe rai a ɓace, ganin Zafira yasa shi mayarwa ya rufe. Kallonta yai na ‘yan daƙiƙu kafin ya maida hankalin shi kan Fawzan fuskarshi ɗauke da alamun tambaya. 

“Ban sani ba wallahi. Ganinta na yi tana ta kuka. Na tambaye ta kome akai mata, ta kira sunan ka tana ci gaba da kuka…”

Fawzan ya faɗi cike da damuwa. Ɗaga mishi gira duka biyun Rafiq yayi cikin yanayin da ke fassara ‘Me hakan yake nufi?’

“Na ɗauka ko kai take son magana da kai shi yasa…”

Sauke numfashi Rafiq yayi yana ɗan runtsa idanuwanshi ya buɗe su a hankali. 

‘Daddy bakai min haka ba. Baka faɗa mata ba… Ka ce saina dawo zamuyi magana…’

Yake faɗi a cikin ranshi, sai dai kaɗan ne daga cikin aikin Daddy, zai faɗa musu abinda yasan suna son ji ne wasu lokutan, ya yi shi abinda yai niyyar yi, saboda babu wanda ya isa ya canza mishi ra’ayinshi. Hannu yakai ya riƙo na Zafira da ke cikin na Fawzan yana janta zuwa cikin falon yakaita kan kujera ya zaunar da ita. 

Har lokacin kuka take da yake ji har bayan zuciyarshi. Kofi ya ɗauko ya zubo mata ruwa ya bata, sai da ta karɓa tukunna ya samu waje ya zauna. Sosai ta sha ruwan sannan ta ajiye kofin akan table ɗin da ke kusa da ita. Kallon Rafiq ta yi da idanuwanta da suka rine saboda kukan da bata daina ba har lokacin. 

“Me yasa Yaya? Ka faɗa min dalili… Wallahi zan haƙura da shi in har bai maka ba…amma ka faɗa min dalili…”

Ta ƙarasa muryarta na karyewa, wasu hawayen na sake bin fuskarta. Saboda yanayin shi ya nuna cewar ya yi magana da Muneeb ɗin, sai dai tana son sanin dalilin da baya sonta da shi. Bai taɓa nuna mata wani hali marar kyau ba, ta yarda da Rafiq da dukkan rayuwarta, zata iya rabuwa da Muneeb ko da shi ne ƙarshen bugawar da zuciyarta zata yi indai ya faɗa mata dalilin da zai gamsar da ita. 

Miƙewa tsaye Rafiq ya yi. Ba Daddy bane ya yi ma Zafira magana. Muneeb ne ya sata wannan kukan, in ranshi ya yi dubu ya ɓaci, ya ɗauka ba sai ya roƙi Muneeb ba, zai bar yi mata magana sai shi ya fara tukunna, ya ɗauka hankalin Muneeb yakai nan. 

“Me ya ce miki? Muneeb, meya ce miki Zafira?”

Rafiq ya faɗi ta tsakanin haƙoranshi saboda yadda ranshi yake a ɓace. 

“Wanne Muneeb ɗin? Me yake faruwa ne wai?”

Fawzan da ke tsaye yana kallon su ya faɗi. Wani irin kallo Rafiq ya watsa mishi da ya sa shi faɗin, 

“Allah ya baka haƙuri…”

Yana ficewa daga ɗakin gaba ɗaya m. Hankalin shi Rafiq ya mayar kan Zafira. 

“Me ya ce miki?”

Ya sake maimaitawa. Ɗan ɗaga kafaɗarta ta yi, tana jan hanci, kafin ta goge fuskarta da faɗin, 

“Baya son maganar komai da ni…bai ce min komai ba…”

Tsugunnawa gabanta Rafiq ya yi yana riƙo hannunta. 

“Na yi magana da Muneeb ɗazun… Kina jina… Akwai abinda yake faruwa, Daddy ya aikeni China, gobe in Allah ya kaimu zan tafi. Ki ba Muneeb sararin da yake buƙata har saina dawo….zan yi magana da Daddy. Ki daina kuka… Komai zai tafi dai-dai….”

Shi kanshi magana kawai yake ba don yasan abinda yake faɗa ba. Gaskiya yake son faɗa mata ba tare da ya faɗa mata asalin gaskiya ba a lokaci ɗaya bai kuma san yadda zai yi hakan ba. 

“Ina sonki da Muneeb…. Kar wani abu ya faɗa miki akasin hakan… Ina sonki da Muneeb…”

Kai take ɗaga mishi, hawayen da baya son ganin na sake zubar mata. Ta wani fannin ta ɗan samu nutsuwar jin Rafiq ɗin na sonta da Muneeb. Ta fannin da yafi ɗayan girma na cike da tsoron meye yake faruwa ɗin. Amma ta yarda da Rafiq, ta yarda cewar zai gyara komai kamar yadda ya faɗa. 

“Za kai magana da Daddy? Za ka faɗa mishi?”

Kai ya ɗaga mata, yana son ta ga yadda zai iya komai don farin cikinta. ƙila hakan ta gani yasa ta goge fuskarta da ɗayan hannunta tana miƙewa. Shi ma tashi ya yi yana riƙe da hannunta har lokacin. Tare suka fita ya rakata har bakin ƙofar ɗakinta ya ga ta shiga ta turo ƙofar tukunna ya juyo yana nufar ɗakin Fawzan. 

Ƙwanƙwasawa ya yi shiru, hakan yasa shi turawa da sallama. Fawzan ɗin na zaune kan kujera da remote a hannunshi, ganin shigowar Rafiq ɗin yasa shi danna remote ɗin yana ƙure maganar TV ɗin da ta cika gaba ɗaya ɗakin, tana karama Rafiq ciwon kan da yake fama da shi. 

Bai ce komai ba, ya zagaya yana kashe switch ɗin kayan kallon gaba ɗaya. 

“Kallo nake…”

Fawzan ya faɗi yana ƙin kallon Rafiq ɗin. 

“Aure Daddy yake son yi ma Zafira. Ba shi bane babban tashin hankalina Fawzan. Tana soyayya da Muneeb…”

Girgiza mishi kai Fawzan yake yi tunda ya buɗe baki yana magana har ya kai ƙarshe, kallon shi yake kamar wani baƙon abu ya fito a fuskarshi da bai san da shi ba. 

“Bai bani dariya ba ko kaɗan Yaya…”

Fawzan ya faɗi yana sake girgiza kai. 

“Saboda ba wasa bane ba…”

Shiru Fawzan ya yi yana jin yadda hanjin shi suke ƙullewa waje ɗaya saboda tashin hankali, numfashi yake ja a hankali yana jin yadda wucewar shi ta soma mishi wahala saboda ranshi a ɓace yake. Ba kuma na wannan lokacin bane ba, yana haɗowa da wasu na baya ne suna ƙara yi mishi taron dangi. 

Sai yaushe ne rayuwarsu zata zama fiye da tsanin takawa wajen nasarar Daddy? Sai yaushe ne zai daina musu haka, yaushe zai fahimci suma suna da buƙatu nasu na kansu kamar shi. Kanshi ne ya soma ɗaukar zafi kafin ya ji kamar ana gobara cikin maƙoshin shi da take ƙarasawa zuwa ƙirjinshi tana tsayawa. 

Wani irin jan numfashi yake kamar zai shiɗe. Da gudu Rafiq ya ƙarasa inda yake, shi yasa bayason faɗa mishi wani abu da zai ɓata mishi rai, yanzun Asmar shi zata tashi. Inhaler ɗinshi ya lalubo yana saka mishi a hannu, ya kai baki yana dannata. 

“Fawzan don Allah ka kwantar da hankalin ka. In ba so kake zuciyata ta buga ba yau…Shi yasa ban so faɗa maka ba… Ya kuke so in yi?”

Ya ƙarasa yana riƙo Fawzan ɗin tare da ɗaga shi ya ja shi zuwa inda gadonshi yake ya kwantar da shi. Har lokacin bai gama dawowa dai-dai ba. Nan gefen gadon ya zauna yana dafe kanshi da yake sarawa. Ko tunani ya kasa yi, wani amai ma yake ji saboda rashin nutsuwa. Bai fita daga ɗakin ba sai da Fawzan ya samu bacci. 

Shi ma wayoyinshi yaje ya ɗauko daga ɗakinshi ya dawo ɗakin Fawzan ɗin ya kwanta. Don ko zai samu bacci sai da sanin ko da wani abin zai faru da Fawzan cikin daren zai iya sani. Yana kusa dashi, shi da Aroob ne kaɗai suke Asthmatic, saboda Nuri na da shi, amma ya manta lokacin ƙarshe da ya tasar mata. Su kam ko ya ransu ya ɓaci za su iya samun matsala, musamman Fawzan. 

Lambar Muneeb ya lalubo yana tura mishi saƙo kamar haka, 

‘Idan ta sake kuka a kanka zan manta abokantakar dake tsakanin mu.’

Amsa ya dawo mishi da ita cewa, 

‘Idan baka yi wani abu ba, hawayenta za su zuba ne sanadin hakan Rafiq. Zuciyarta na da muhimmanci a wajena, tarwatsewar ta na hannun ka.’

Jefar da wayar ya yi, ba don kujerar data faɗa kai ba da ta fashe. Banda ciwon kai babu abinda saƙon Muneeb ya ƙara mishi. Kwanciya yai ya rufe idanuwanshi yana neman gafarar Ubangiji, saboda akwai samun sauƙi a cikin hakan, akwai ƙananan zunuban da kake tarawa ba tare da sanninka ba, in Allah ya yafe maka su hakan zai iya zama sanadin samun sauƙinka, hakan ya ci gaba dayi har bacci ya ɗauke shi. 

*****

Washe gari sam bai samu ya zauna ba. Tunda ya duba Zafira ya ga lafiyarta ƙalau ya fita. Saboda akwai kayan abinci da za su rarraba gidajen matan da suka rasa mazajen su na ƙananan hukumomi da ke nan garin Abuja ƙarƙashin foundation ɗin Nuri. Daddy ya ce yana buƙatar ‘yan jarida su ganshi a wajen tunda shi ba zai samu zuwa ba. 

Gaba ɗaya zuciyarshi bata mishi daɗi, da masu ɗaukar hotuna za su zuƙo fuskarshi ƙila da mutane da yawa sun fahimci akwai rashin jin daɗi cike a ƙasan murmushin shi. Yana rabawa mabuƙata abinci, yana kuma shiga asibitoci ya kai taimako da kuɗin aljihunshi, ba tare da sanin kowa ba. Wannan ɗin ma ba wai baya son yi bane ba, yasan dai babu lada a cikinshi. 

Saboda ba wai ana yi bane don Allah, ana yi ne don idan duniya, ana yi ne don neman zaɓe, yana ɗaya daga cikin yaƙin neman zaɓe, ya kuma tsani duk wani abu da yake da alaƙa da siyasa duk da kasancewarshi a tsakiyarta.

Komai nata bai mishi ba. Suna yi yana fakar idanuwan mutane yana duba agogon shi. Yana buƙatar zuwa Airport kafin ƙarfe huɗu na yamma. Don haka biyu da rabi dai-dai ya bar komai a hannuwan wakilan Daddy ya ja motarshi ya koma cikin garin Abuja. Ranshi na ƙara ɓaci da Sallah da ya rasa saboda aikin da babu ladar komai a cikin shi. Bai shiga gida ba sai uku da kusan kwata. A gaggauce ya sake watsa ruwa, don ma ya haɗa jakarshi kafin ya fita. 

Sallah ya samu ya yi yana ɗaukar jakar ya fito. Fawzan ya samu a falo yana jiranshi. 

“Nuri fa?”

Ya tambaya. 

“Ta hau sama yanzun…”

Fawzan ɗin ya bashi amsa yana dubar agogo

“Yaya zamu makara…”

“Na sani…”

Ya faɗi yana miƙawa Fawzan ɗin jakarshi, da gudu ya nufi kafar benen yana haɗa bibbiyu lokaci ɗaya.

“Nuri…”

Yake ƙwala mata kira tun kafin ya ƙarasa. Fitowa ta yi cikin hanzari. Numfashi Rafiq yake mayarwa. Ya ƙarasa yana sumbatar kuncinta. 

“Na tafi… Za mu yi waya…”

Ya ƙarasa yana juyawa. 

“Allah ya tsare Rafiq. Ka kula sosai…”

“In sha Allah.”

Ya amsa yana sauka da gudu ya fita zuwa inda Fawzan yake tsaye jikin mota yana jiranshi. Shiga sukai su duka biyun, Fawzan ya ja su zuwa Airport. Babu mai magana a cikinsu. Har sai da suka ƙarasa Rafiq ya ɗauki jakarshi zai fita tukunna ya kalli Fawzan da faɗin, 

“Ka kula da ita don Allah… Ka kula da kanka kuma…”

Kai Fawzan ya jinjina mishi. 

“In sha Allah. Kaima ka kula da kanka.”

Ba tare da ya amsa ba ya fice daga motar. Yana jin kamar akwai kuskure a tafiyar tashi. Kamar wani abin zai faru kafin ya dawo. Sai dai ya danne muryar da ke mishi wannan raɗar da tunanin ba wannan karon bane yake jin kamar in ya barsu Daddy zai musu wani abin kafin ya dawo. 

A masallacin cikin airport ɗin yai Asr. Tukunna ya dawo ya zauna. Yana danna wayarshi don yagae ko ƙarfe nawa. Text ɗin Naadir ya shigo mishi. 

‘Yaya na ji ciwo a kafada, jiya akai min surgery.’

Wani yamutsi Rafiq ya ji da baisan yadda zai misalta ba. Yana da tabbacin an faɗa wa Daddy. Saboda babu yadda za’ai abu babba haka ya samu Naadir makarantarsu bata kira Daddy ba. Cikin kanshi yake ƙirga kwanakin da ya ɗauka ba su yi magana da Naadir ɗin ba. Don kar ya taso cikin takurar da suka taso yai tsaye saida Daddy ya fitar da shi England yana gama primary. Bama ya zuwa gida sai ƙarshen shekara sam. 

Yana kuma yin wasan ƙwallon Hockey ne, makarantar na ji da shi, don sun ce akwai alamar nasara a tare da shi kan wasan. Hannunshi rawa yake yi lokacin daya kira lambar Naadir. Bugu biyu ya ɗaga, muryarshi can ƙasa. 

“Naadir…”

“Yaya zan ci gaba da wasa na nan da sati uku.”

Naadir ya faɗi cikin harshen turanci. 

“Hausa Naadir…”

Dariya ya yi daga ɗayan ɓangaren hakan nasa Rafiq ɗin samun ‘yar nutsuwa. 

“Ya jikin ka?”

“Ya ji sauki. Zaka zo kaganni? Daddy yace yana busy ba zai zo ba. Ina missing ɗinku sosai.”

Naadir ya faɗi. Kai Rafiq ya ɗaga kamar yana ganinshi kafin ya ce, 

“Zan je China ne now. Amma zan yi ƙoƙarin gama abinda zan yi acan da wuri in sha Allah. Then zan biyo in ganka…”

“Okay. Zan jira. Doc ya shigo mu yi magana anjima. Love you.”

“Love you more. Ka kula sosai.”

Rafiq ya faɗi yana sauke wayar daga kunnenshi. Ji yake kamar yai tsuntsuwa ya je ya ga Naadir ɗin. Amma koma menene zai yi sauri ya ga ya gama ya wuce England kafin ya ga Naadir ɗin. Yasan yana samun duk kulawar da yake buƙata. Amma basa sonshi kamar yadda yake sonshi. In yana wajen hankalin shi zai fi kwanciya. 

*****

Wayarta ta ɗauka da niyyar fita daga ɗakin, jikinta sanye da riga da zani na atamfa. Saƙonni ne har huɗu suka shigo, ganin Muneeb ne yasa zuciyarta matsewa a ƙirjinta. Kan mudubi ta ajiye wayar. Ba zata ma buɗe ba ballantana ya sake dagula mata lissafi da safen nan. Rafiq ɗazun ya roƙeta karta saka damuwa a ranta, ta bar komai a hannunshi sai ya dawo. 

Ta kuma yi mishi alƙawari zata yi iya ƙoƙarinta. Ba zata karya alƙawarinta ba. Ficewa ta yi zuwa babban falon gidan. Aroob ta samu ita kaɗai tana zaune kan kujera da plate ɗin soyayyen dankali da wainar ƙwai a hannunta da cokali mai yatsu a ciki. Ammanm gaba daya hankalinta na kan fim ɗin India ɗin da take kallo. 

Girgiza kai Zafira ta yi tana wucewa kitchen ɗin itama. Ba wai don tana jin yunwa ba sai don jikinta na buƙatar wani abu. Anan kitchen ɗin ta haɗa ruwan shayi, ta kukkurɓa, tana ɗan cin dankalin cikin sauri kafin Nuri ta zo taganta tana cin abinci a tsaye. Bata iya shanye shayin ba, don haka ta cika cup din da ruwa ta zubar tana ajiyewa ta fito daga kitchen ɗin. 

Bata zauna falon ba ta wuce ɓangaren Daddy don ta gaishe da shi. Ƙwanƙwasawa ta yi saida ya bata izinin shiga tukunna ta tura ɗakin da sallamarta daya amsa da fara’a. 

“Ina kwana Daddy…”

“Zafira… Kamar kinsan ina neman ki.”

Daddy ya faɗi a maimakon amsa gaisuwarta. Ƙarasawa ta yi cikin falon tana zama a ƙasa gefen ƙafafuwan shi. 

“Na ce ne bari inzo in gaishe ka dama…”

Ta faɗi cikin muryarta mai sanyi. 

“Jarabawa an kusa ko?”

“Nan da Sati biyu in sha Allah Daddy.”

Ta amsa da jin daɗi a muryarta. Don ji take kamar wani nauyi ne zata sauke. Jinjina kai ya yi yana gyara zamanshi, a nutse ya ce, 

“Kinsan komai da nake yi akan ku don shi ne ya fi dacewa ko?”

Cike da rashin fahimta ta ce, 

“Na sani…”

“Da yawan lokuta kuna ganin kamar ina takura ku ne. Kuna ganin bana jin ra’ayinku nake yanke muku hukunci. Yayanku na ganin farin cikin ku ba shi da muhimmanci a wajena…”

Wani abune ya tsaya wa Zafira a maƙoshi. Haka kawai bata son yadda yanayin muryar Daddy take. 

“Ba haka bane Daddy…. Ba haka muke gani ba.”

Ta amsa da sauri. Kai Daddy ya girgiza mata, yana ci gaba da magana. 

“Ba takura miki nake ba akan wannan. Ina son ki sani yana da matukar muhimmanci a wajena, zan rasa abu da yawa in baki amince ba, a karo na farko ina roƙonki da ki amince Zafira…”

Idanuwanta cike suke taf da hawaye. Bata san menene Daddy yake so ta amince akai ba, bata son yadda yake roƙonta kamar bai isa da ita ba, yadda yake tausasa murya kamar ba ita bace ‘yar shi. Abin ya mata wani iri, muryarta na rawa ta ce, 

“Ka daina don Allah… Ko menene na amince Daddy, kana da ikon zartar da hukuncin da bai saɓa wa addini ba akaina…”

Numfashi mai nauyi Daddy ya sauke. 

“Ina son ki auri ɗan gidan Alhaji Yusuf Modibbo ne…”

Ta kai mintina biyu maganar shi na mata yawo kafin ta samu wajen zama a ƙwaƙwalwar ta, ma’anar kalaman shi na zauna mata daram a zuciya. Cikin tashin hankali ta ɗago idanuwanta tana ware su akan Daddy. 

“Auren ki da shi na da muhimmanci a wajena. Karki ce a’a Zafira. Na riga na amsa musu…”

Kai kawai ta iya ɗaga mishi. Saboda jikinta ya yi sanyi. Bata jin ƙarfi ko da na yin magana ne. Kanta kamar an kwashe duk wani abu mai muhimmanci a ciki haka take jinshi. Zuciyarta ta yi wani irin fili kamar an share. 

“Allah ya miki albarka. Na gode.”

Daddy ya ƙarasa da alamar jin daɗi a muryarshi. Sai da ta dafa ƙafafuwan Daddy tukunna ta iya miƙewa. Runtsa idanuwanta take yi tana buɗe su cikin sauri don dishi-dishi take gani, kafin ta samu ta gane hanyar fita daga ɗakin shi. Ɗakin Aroob ne farko a ɓangaren su kafin nata, don haka nan ta faɗa kawai. 

Numfashi take ja tana mayarwa, tana jin kamar zuciyarta zata fito waje saboda tashin hankalin da take ji, ta ɗauka jiya ne ƙarshen tashin hankalin da zata sani a rayuwar ta, sai yanzun ta san jiya bata ji komai ba, saboda hawayenta sun zuba. Yanzun nemansu take amma shiru. Kuka take so ta rusa mai sauti ta kasa. 

Asalima ta rasa yadda akai ta amsa ma Daddy, bata san me yasa ta amsa mishi ba, don a yanzun ji take kamar ana zare mata rai saboda tashin hankali, bata jin zata kai ranar da zata auri koma wanene Daddy yake son haɗa ta da shi a yanayin da take ji yanzun. Inama zata kai soyayyar Muneeb.

“Muneeb…”

Ta furta can kasan maƙoshi. Me zata faɗa mishi. Ta ina zata faɗa mishi ko kaɗan bata yi wani ƙoƙari wajen cikar burinsu ba, na minti ɗaya bakinta bai yi rawa wajen amincewa da auren wani bayanshi ba. Ji ta yi an turo ƙofar ɗakin, bata ko juya ba. 

“Zaf? Lafiya?”

Aroob ta buƙata tana zama ƙasa kusa da Zafira ɗin. Cikin idanuwa ta kalli Aroob tare da girgiza mata kai. Bata tunanin wani abu zai sake lafiya a tare da ita, komai ciwo yake mata. 

“Daddy zai aura min wani Aroob… Da bakina na amsa zan auri wani…”

Idanuwan Aroob da take jin sun ciko taf da hawaye ta ware kan Zafira cikin tashin hankali. 

“A’a don Allah kar haka ya faru… Kar Daddy ya yi haka….”

Aroob ta ƙarasa tana kwantawa a jikin Zafira tare da fashewa da wani irin kuka. Riƙeta kawai Zafira ta yi tana jin yadda take mata kukan da ita ta kasa. Abu ɗaya ne take ji a yanzun. Muneeb take son gani, tana son ganin Muneeb a yau ɗin nan, a yanzun ba sai anjima ba. 

“Ina son ganin shi yanzun Aroob…”

Ta faɗi muryarta a bushe. Ɗagowa Aroob ta yi tana goge fuskarta data soma kumbura, tashi ta yi ta ɗauko wayarta tana miƙa wa Zafira, wani kukan na ƙwace mata, yama za’ai Daddy ya yi haka, wa ya cemishi ana tarwatsa soyayya irin wannan, wa ya faɗa mishi ana ma so haka. Tasan yasan menene So akan Nuri, me yasa bazai bar Zafira da Muneeb ba. 

Text Zafira ta tura ma Muneeb. 

‘Ka zo gidan mu yanzun. Don Allah ka zo, komai zai iya faruwa in baka zo ba. (zafira)’

Ta aika mishi tana ajiye wayar a gefe. Jikinta Aroob ta sake kwanciya tana ci gaba da kukan da take. 

“Zaf ki faɗa ma Nuri… Ki faɗa mata ta yi mishi magana…”

Ɗan murmushi Zafira ta yi da bashi da alaƙa da nishaɗi. 

“Kin taɓa ganin ya yi abinda bata sani ba?”

Girgiza mata kai Aroob ɗin ta yi. 

“Wannan karon kaɗai ya kamata Nuri ta zaɓe mu akan Daddy…”

Zafira bata ce komai ba, in ta ga Muneeb ciwon sa take ji zai rage, haka take ta faɗa wa kanta, yadda take jin duniyar na ruguje mata daga ciki zai dai-daita in yazo, in ta ganshi komai zai yi sauƙi.

“Shi yasa ya tura Yaya China…abinda Daddy yake so ya yi kenan…. Bari in kira Yaya ya dawo….”

Aroob ta faɗi tana kai hannu zata ɗauki wayarta da ke gefen Zafira. Da sauri Zafira ta rigata ɗauka. 

“Karki ɗaga mishi hankali. Komai zai jagule in yazo. Kuma ba zai hana Daddy yin abinda ya yi niyya ba. Karki kira shi Aroob, na roƙeki karki kirashi…”

Miƙewa Aroob ta yi tana komawa kan gado ta kwanta. Kukan ta taci gaba da yi, don ta san abinda ya faru da Zafira shi ne zai faru da ita nan gaba. Daddy ba zai taɓa bari su yi abinda suke so ba. Son kanshi ba zai barsu zaman lafiya ba. 

‘Ina ƙofar gidan ku…’

Text ɗin Muneeb ya shigo. Wani irin matsewa zuciyar Zafira ta yi. 

“Aroob yana ƙofar gida.”

Sakkowa ta yi daga kan gadon tana goge fuskarta. Muryarta a dakushe ta ce, 

“Ki zagaya ɓangaren baƙi. Bari in shigo da shi ta baya…”

Kai Zafira ta jinjina mata tana miƙewa. Aroob kam ficewa ta yi daga ɗakin, hijab ɗin Aroob na sallah ta ɗauka ta zunduma tana ficewa ta nufi ɓangaren baƙin. Falon ta shiga ta zauna, zuciyarta kamar zata fito daga ƙirjinta saboda dukan da take. 

Tana jin takun shigowarshi falon ta ɗago kanta. Fuskarshi ta fara kallo, ta san shi, ta san shi kamar yadda ta san kanta, idanuwanshi kawai ta kalla ta san akwai damuwa a tattare da shi, da rashin bacci, kallonta yake shima, yanayin shi yana ƙara buɗe sababbin ciwuka a zuciyarta daya sata jan numfashin da bata shirya ba. 

Ta ɗauka ganinshi zai sata jin daidaito, sai dai ganin shi na fito da hargitsin da take ji a fili ne. Hannu takai tana dafe zuciyarta da take jin tana gab da fitowa waje. 

“Aure za’aimun Love…. Daddy ya amsa su… Na amince… Ka yafe min…don Allah ka yafe min…”

Ta faɗi wani irin kuka na ƙwace mata, ciwon da take ji a ko’ina na jikinta na sata sakkowa daga kan kujerar da take zaune. Kallon ta Muneeb yake yi, tun a daren jiya yake jin ya rasa ta, runtse bai iya runtsawa ba, alwala ya ɗaura yana sallah, amma baisan abinda ya dinga karantawa ba. 

Yanzun kam da take a gabanshi baisan me yafi tarwatsa mishi zuciya ba, sanin an bayar da ita, ko kuma kukan da take yi. Ba shi da lafiya tun jiya. Zazzaɓi yake mai zafi, da ƙyar ya iya fitowa yazo yanzun ma ko aiki baije ba. 

‘Aure za’aimun Love.’

Muryarta ta dawo mishi da wani irin yanayi. Ƙirjinshi ya dafe da hannunshi yana wani irin jan numfashi, sai dai ciwon da yake ji yana rarrabuwa ne zuwa ko’ina na jikinshi. Kallonta yake yi, ta cikin idanuwanshi yake so ta fahimci yadda zuciyarshi ke tarwatsewa. Ya kasa yarda ita da shi ne a wannan matsayin, ya kasa yarda ƙaddara ta buɗe musu shafin rabuwa da junansu. Muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Bazan iya ba, na kasa tuna yadda rayuwata take batare da soyayyarki ba, wallahi bansan ya duniyata zata kasance babu ke a ciki ba…”

Girgiza mishi kai da take yasa shi yin shiru, wasu irin hawaye ne masu ɗumi suke zubo mata, ganin shi kawai ƙara mata wani irin nauyi yake a zuciyarta, sanin lokutan daya rage a tsakaninsu kawai na sata jin kamar ranar mutuwarta ce ta sani saboda firgici. Na tsawon shekaru da soyayyarshi zuciyarta take numfasawa. Ko bacci take duniyarta cike take da mafarkinshi. Rayuwa zata yi mata fili da girma mai cike da mawuyacin yanayi ba tare da shi ba. 

Bata san yadda zata buɗe ido a matsayin mallakin wani ba. 

“Ki fadi sunana ko sau ɗaya ne…”

Ya buƙata don yasan da wahala ya sake ganinta bayan yau. Dariya ce ta kubce mishi da baisan daga inda ta fito ba. Wai shi ne yake tunanin ganin ƙarshe yake wa Zafira a yau. Inda yasan ALKALAMIN KADDARA ya yi musu wannan rubutun da ya sota daga nesa, da bai bari ya ɗanɗani yadda soyayyarta a kurkusa take ba tunda yasan zai rasa ta. 

Kai Zafira ta sake girgiza mishi tana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Furta sunan shi zai zamar mata kamar bankwana ne take mishi. Ba zata iya bankwana da shi ba, bata taɓa sanin yadda ɗacin rashi na mutuwa yake ba, amma yau tana ɗanɗana yadda ɗacin rashi yake ba tare da giftawar mutuwa ba. 

“Bazan iya ba…”

Ta faɗi muryarta can ƙasa. So yake ya ƙarasa inda take. Amma ba zai iya ba, daga nan ɗin ma gaf yake da faɗuwa. 

“Za ki iya. Allah ba zai ɗora mana ƙaddarar nan ba in da ba za mu iya ɗauka ba. Allah ya sa miki alkhairi a cikin aurenki. Allah ya baki farin ciki a gidan kowanene fiye da yadda zan baki Zafira…”

Muneeb yake faɗi yana jin kalaman kamar suna ƙona mishi harshe. Amma son da yake mata ya kai ya taimaka mata ta yi wa mahaifinta biyayya. Ba laifinsu bane su dukkansu, ita da shi sun zo a duniya daban-daban. 

“Ban sani ba, komai bashi da tabbas, amma inajin labarin samun soyayya sau ɗaya tak zai tabbata akaina. Bana jin zan sake soyayya kuma…. Amma zan cigaba da addu’a ke ki samu. Ɗaya daga cikinmu ya cancan ci farin ciki…”

Numfashi ya ja yana fitar da shi a wahalce. Jiri yake ji, ga wani zazzaɓi sabo da ya sake lulluɓe shi. Kukan ta na ƙara karya mishi zuciya. 

“Ina miki fatan alkhairi. Na gode da dukkan ƙaunarki. Bazan manta ba…”

Ya ƙarasa yana juyawa.

“Muneeb!”

Zafira ta faɗi cike da tashin hankali. Tsaye yayi cik, tsigar jikinshi gaba ɗaya na miƙewa da yadda ta kira sunanshi, yanayi ne da yasan fitar rai ne kawai zai mantar da shi. Bai juyawa ba ya ja ƙafarshi yana ci gaba da tafiya. 

“Muneeb karka tafi… Don Allah ka tsaya tukunna… Wallahi bansan ya zan yi ba. Innalillahi wa inna ilaihiy raji’un…. Karka barni tukunna ka tsaya in sake ganin ka….”

Zafira ke faɗi tana rarrafe don ta ƙaraso inda yake saboda ƙafafuwanta basu da ƙwarin miƙewa. 

“Muneeb…”

Ta faɗi lokacin da ya fita daga falon. Kwanciya ta yi a wajen tana sakin gunjin kuka, tana jin yanda ƙarshen duniyar ta ya zo da tashin hankali marar misaltuwa. Kuka take kamar zata shiɗe. Bata san shigowar Aroob ba sai ji ta yi ta ɗagota, ruƙunƙume Aroob ta yi tana wani irin gunjin kuka. Tana jin da wahalar gaske ta kai dare saboda yanayin firgici da tashin hankalin da take ji yana tabbatar mata ƙarshen rayuwarta ya zo. 

*****

Da ƙyar ya kai wajen motar shi, ya buɗe ya shiga. Kanshi ya haɗa da gaban motar yana maida numfashi, kafin ya saki wani gunjin kuka kamar mace. Inda an ce wata rana zai yi kuka irin wannan dariya abin zai bashi, amma komai na duniya ya daina bashi mamaki. 

Tsakanin jiya da yau ya shiga tashin hankalin da kalamai ba za su iya misaltawa ba. Zuciyarshi yake ji tana ciwo kamar zata faɗo daga ƙirjinshi. Ta ina zai fara rayuwa da sanin duka burin shi akan Zafira yana cikane a tare da wani namijin daban. Tari ya soma yi yana jin kamar zai sume. 

*****

Tsaye yake bakin ajin su Zafira. Murmushinta ya soma mishi maraba tana fitowa daga ajin. Farin mayafin da kanta yake naɗe da shi na sata yi mishi wani haske na daban. Da sallama ta ƙaraso inda yake tana jingina bayanta da motar shi tare da gaishe da shi. 

“Kin yi kyau sosai…”

Dariya tai a kunyace. 

“Kaima ka yi kyau…”

Tsayuwar shi ya gyara. 

“Ina ƙirga kwanakin shekarun nan a cikin kaina fa….”

Dariya ta sake yi sautin na dirar mishi a kunne da wani nishaɗi. 

“Kai Love…. Duka yaushe aka shigo shekarar?”

Ta buƙata cike da zolaya. Rausayar da kai ya yi. Ba zata gane yadda yake son ganin magana mai ƙarfi ta shiga tsakanin su ba. 

“Kinsan akan ki ne na yarda akwai soul mate? Ina jin kamar an halittamun zuciyata ne kawai don ta doka miki ke kaɗai…. Zafira da wahalar gaske in so wata macen bayan ke.”

Ɗan kallon shi ta yi kafin ta sadda kanta ƙasa. 

“In baka same ni ba fa? Ka daina faɗin hakan, zan so ka kasance cikin farin ciki ko da bana rayuwarka…”

Ware mata idanuwa ya yi yana jin wani irin hargitsi a zuciyarshi. Yanayin shi na sata dariya tare da haɗe hannayenta cikin alamun ban haƙuri. 

“Wasa nake…”

Numfashi ya sauke, har lokacin zuciyarshi na rawa. 

“Karki sake min wasan da zai zo da hasashen rayuwata babu ke a cikin ta. Kina sa ina jin kamar ni kaɗai nake haukan sonki…”

Muryarta babu wasa ta ce, 

“Da soyayyarka zuciyata ta buɗe idanuwa, bansan me zanyi in babu kai a rayuwata ba, tun bansan menene so ba zuciyata take doka maka. Ba kai kaɗai bane ba, bansan yadda kake ji a kaina ba, amma nasan yadda nake ji a kanka…”

Murmushin dayai mata har saida dimple ɗin gefen fuskarshi ya loɓa ciki. 

“Allah ya cika mana burin mu. Ina sonki wallahi. Sosai ina sonki…”

Dariya ta yi. 

*****

Dariyar da yake jin sautin ta har cike da motar shi yanzun nan. Dariyar da wani zai dinga ji har abada. Wani irin kishi da bai taɓa sanin yana da shi ba ya turnuƙe shi. Me yasa rayuwa bata da adalci ne, me yasa Daddy zai musu haka, kuka yake sosai. Ji ya yi kamar ƙarar mota, ɗago kanshi yayii da fuskarshi a jike da hawaye, Daddy ne zai fita da motarshi kuma yadda Muneeb ɗin ya yi parking ɗin tashi ba zai bari ba. 

Da sauri Muneeb ya fito daga motarshi ko rufe murfin bai yi ba yana zagayawa ya kama glass ɗin murfin motar Daddy, ganin shi yasa Daddy sauke glass gaba ɗaya yana son tuna inda yasan fuskarshi. 

“Don girman Allah Daddy ka taimaka mana…. Ka rufa wa rayuwar mu asiri ka bar mu mu yi aure….”

Muneeb yake faɗi hawaye na zubar mishi. Kallon shi Daddy yake cike da rashin fahimta. Hakan ya gani yasa shi faɗin, 

“Muneeb ne, abokin Rafiq… Ni nake son Zafira. Wallahi ina sonta sosai kuma zan riƙe ta tsakani na da Allah…”

Wani irin kallo Daddy yake mishi. Sai yanzun ya tuna inda ya taɓa ganin shi. Motarshi ya sake kallo tukunna ya kalle shi. Rafiq baya gajiya da kwashe-kwashe. Ko cikin motocin da ake zuwa cefane dasu a cikin gidanshi babu mai arhar ta Muneeb. 

“Auren ta ran asabar ne. Ka nemi yarinya dai-dai kai. Kar kuma in sake ganinka a ƙofar gidan nan… Ka janye motarka ina da abu mai muhimmanci kafin in sa security su janye min kai da motar…”

Hannu Muneeb yasa yana goge fuskarshi. Ko ba komai ba zai ji kamar bai yi wani ƙoƙari ba. Wucewa ya yi ya koma cikin motarshi yana yin gaba abin shi. Ko hanya baya gani sosai saboda kukan da yake. Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya. Sau huɗu yana kusan haddasa hatsari. Yana shiga ɗaki kayanshi ya soma haɗawa a akwati. Duk wani abu da hannunshi yakai sama kawai yake zubawa. 

Har lokacin kuka yake mai cin rai, gida zai tafi, ko bakomai in ya ga mahaifiyar shi zai samu sauƙi-sauƙi. Dama zai ɗauki hutun ƙarshen shekara ne, zai yi amfani da damar nan kawai ya ɗauka. In ya zauna a Abuja sanarwar ɗaurin auren Zafira da zata cika garin zai iya zama ajalin shi. Yanzun ma sama-sama yake jinshi. Tasha zai je yahau motar haya. Don ba zai iya tuƙii ba a halin da yake jin kanshi. 

Bayan Sati Ɗaya 

Kallo ɗaya za ka yi wa Zafira ka tabbatar babu kwanciyar hankali a tare da ita. Da ƙyar ta gama jarabawar da take da ita a ranar ta dawo gida. Inda Allah ya taimake ta bata barin karatu ya tarar mata, da babu abinda zata iya rubutawa. Kuma jarabawar tazo mata da sauƙi fiye da yadda ta fahimta. Kwance take cikin ɗaki, don yanzun ko abinci Aroob ce take kawo mata ɗakin. 

Bata son fita. Nuri bata yi mata magana ba, don tana tunanin bata san abinda zata ce mata ba. Hakan kuma ya mata daɗi. Wayarta kuwa tun ranar take a kashe har yau bata kunna ba. Ta roƙi Aroob da karta faɗa wa Fawzan. Ta barshi tukunna, yadda aka bankaɗo ƙofar ta san ba lafiya ba. Miƙewa ta yi babu shiri. 

“Kinsan lefenki ake karɓa a falo yanzun haka?”

Fawzan ya tambaya yana tsare ta da idanuwanshi da suka canza launi saboda ɓacin rai. Bata ce komai ba, idanuwanta ke zafi saboda babu sauran hawaye a cikinsu. Tayi kuka hartae gode wa Allah. Cikin ɗakin ya shigo sosai yana samun waje gefen gadon ya zauna tare da dafe kanshi da hannuwa. 

“Ya Fawzan don Allah karka wani damu… Ka ga kar ciwon ka ya tashi…”

Zafira ta faɗi hankalinta a tashe. Ƙarshen abinda zata so a yanzun bai wuce ciwon Fawzan ɗin ya tashi ba. 

“Saida na tambaye ki ko akwai abinda ya kamata ki faɗa min kika ce babu, ke kika amince Zafira?”

Fawzan ɗin ya ƙarasa tana ɗago kanshi ya tsare ta da idanuwa. 

“Ni na amince da kaina. Bawai zai zaɓi abinda zai cutar da ni bane ba…”

Miƙewa tsaye Fawzan ya yi yana kai kawo cikin ɗakin. 

“Me kike so in faɗa wa Yaya Rafiq? Zafira me kike so in ce mishi? Karo na farko daya bude bakinshi ya ce in kula da ku…me yasa za ki amsa Daddy baki sanar da ni ba?”

Kallon shi Zafira take yadda yake jan numfashi kamar yana ɗanɗana iskar. 

“Ni dai don Allah karka ɗaga hankalin ka. Zan faɗa wa Yaya nice na amince da kaina ba dole akai min ba…”

Jinjina kai Fawzan ya yi. 

“Yeah kin kyauta sosai. Gobe ɗaurin aurenki, za’ai sauran abubuwan bayan jarabawarki ta ƙarshe…”

Ya ƙarasa maganar yana ficewa daga ɗakin tare da doko kofar kamar zai karyata. Ƙafafuwanta Zafira ta ja ta mayar kan gadon tana kwanciya. Zoben da ke hannunta take wasa dashi. Zoben Muneeb da take jin dole ta cire shi daga gobe take wasa da shi. Zuciyarta ta riga ta gama bushewa, ta karɓi ƙaddarar da ta zo mata da hannuwa biyu. 

Bayan Sati Ɗaya 

Kallo ɗaya za ka yi wa Zafira ka tabbatar babu kwanciyar hankali a tare da ita. Da ƙyar ta gama jarabawar da take da ita a ranar ta dawo gida. Inda Allah ya taimake ta bata barin karatu ya tarar mata, da babu abinda zata iya rubutawa. Kuma jarabawar tazo mata da sauƙi fiye da yadda ta fahimta. Kwance take cikin ɗaki, don yanzun ko abinci Aroob ce take kawo mata ɗakin. 

Bata son fita. Nuri bata yi mata magana ba, don tana tunanin bata san abinda zata ce mata ba. Hakan kuma ya mata daɗi. Wayarta kuwa tun ranar take a kashe har yau bata kunna ba. Ta roƙi Aroob da karta faɗa wa Fawzan. Ta barshi tukunna, yadda aka bankaɗo ƙofar ta san ba lafiya ba. Miƙewa ta yi babu shiri. 

“Kinsan lefenki ake karɓa a falo yanzun haka?”

Fawzan ya tambaya yana tsare ta da idanuwanshi da suka canza launi saboda ɓacin rai. Bata ce komai ba, idanuwanta ke zafi saboda babu sauran hawaye a cikinsu. Ta yi kuka har ta gode wa Allah. Cikin ɗakin ya shigo sosai ya samu waje gefen gadon ya zauna tare da dafe kanshi da hannuwa. 

“Ya Fawzan don Allah karka wani damu… Ka ga kar ciwon ka ya tashi…”

Zafira ta faɗi hankalinta a tashe. Ƙarshen abinda zata so a yanzun bai wuce ciwon Fawzan ɗin ya tashi ba. 

“Sai da na tambayeki ko akwai abinda ya kamata ki faɗa min kika ce babu, ke kika amince Zafira?”

Fawzan ɗin ya ƙarasa yana ɗago kanshi ya tsare ta da idanuwa. 

“Ni na amince da kaina. Bawai zai zaɓi abinda zai cutar da ni bane ba…”

Miƙewa tsaye Fawzan ya yi yana kai kawo cikin ɗakin. 

“Me kike so in faɗa wa Yaya Rafiq? Zafira me kike so in ce mishi? Karo na farko da ya buɗe bakinshi ya ce in kula da ku…me yasa za ki amsa Daddy baki sanar da ni ba?”

Kallon shi Zafira take yadda yake jan numfashi kamar yana ɗanɗana iskar. 

“Ni dai don Allah karka ɗaga hankalin ka. Zan faɗa wa Yaya nice na amince da kaina ba dole akai min ba…”

Jinjina kai Fawzan ya yi. 

“Yeah kin kyauta sosai. Gobe ɗaurin aurenki, za’ai sauran abubuwan bayan jarabawarki ta ƙarshe…”

Ya ƙarasa maganar yana ficewa daga ɗakin tare da doko ƙofar kamar zai karyata. Ƙafafuwanta Zafira ta ja ta mayar kan gadon tana kwanciya. Zoben da ke hannunta take wasa da shi. Zoben Muneeb da take jin dole ta cire shi daga gobe take wasa da shi. Zuciyarta ta riga ta gama bushewa, ta karɓi ƙaddarar da ta zo mata da hannuwa biyu. 

Aroob ce ta shigo ɗakin jikinta sanye da doguwar riga ta material, sai wata irin hula saman kanta, fuskarta tasha kwalliya marar hayaniya.

“Ki tashi, su Asma sunata kiran wayarki a kashe tun jiya. Za su shigo ba sai kowa yagane me yake faruwa ba…”

Can ƙasan maƙoshi Zafira ta ce, 

“Don Allah ki kira su ki ce su yi zamansu. Ba sai sun zo ba. Ɗaurin aure ne kawai gobe in Allah ya kaimu. Ko me za’ayi ku bari sai na gama exam ɗina.”

Zafira ta ƙarasa maganar tana jin kamar ba ita ba. Kamar wata ce daban duk wannan abubuwan suke faruwa da ita. 

“Bansan me zan ce musu ba. Ki tashi ki shirya. Ina jin Fa’iza na maganar wani party ko meye….sa’adda kika cema Daddy eh baki yi tunanin duk wannan ba ai…”

Tashi Zafira ta yi ba sai Aroob ta ci gaba da faɗa mata kuskuren da ta yi ba, kamar yadda takan yi a duk satin nan. Gani take kamar laifinta ne duk abinda yake faruwa yanzun. Sai lokacin ta kula da wata milk ɗin riga a hannun Aroob ɗin da yanayin da take ciki bai hanata ganin kyawunta ba. Gefe Aroob ta ajiyeta tana faɗin, 

“Ki sake watsa ruwa. Ga riga nan…”

Miƙewa tayi, bata yi mamakin ganin rigar ba. Tunda dama sune abinda Aroob take ɗinkawa, tun tana aji uku a secondary ta ce tana son koya, Rafiq kuma ya goyi bayanta, shekara biyu da yake tana son abin ta zama ƙwararriya sosai, tana da ɓangare a cikin gidan da take da kekunanta. Sosai take ciniki a family ɗinsu, duk da sai ta ga dama ɗinkin nata. 

Wanka ta yi ta fito. Ta shafa mai, Aroob ta yi mata kwalliya mai nauyi saboda ta ɓoye duk wani alamu na rashin bacci da damuwa. Sannan ta fice tana barinta don ta sa rigarta. Dawowa ta yi da hular da ta fi tata ado tana tayata gyara gashin kanta da ba wani yawan kirki gareshi ba, don haka basu ɗauki lokaci ba. Ta saka hular. Ita kanta saida ta yaba da kyawun da ta yi, akwai wani gyale daga kafaɗar rigar ya ɗauka zuwa baya cikin yanayi na ƙayatarwa. 

Waje ta samu ta zauna. Tana jin yadda ƙirjinta ya yi wani irin nauyi, sai dai nauyin bai sa ta daina jin rashin wani ɓangare na zuciyar ta da zai kasance tare da Muneeb har abada ba. Sama-sama take jin ihun su Asma’u da suka shigo, dariyar su da duk wata magana da sukeyi. Murmushi ne kawai ta ɗora saman laɓɓanta, idanuwanta da wani irin nisantancen yanayi. 

Tana jin in wannan ya dafata sai wancen ya riƙota, hasken da take gani yana gilmamawa ta cikin idanuwanta kawai yake tabbatar mata da hotuna ake ɗauka. Bata san waya kamata ya miƙar da ita tsaye ba, sama-sama take jinta, hasken camera dai ta ci gaba da gani cikin idanuwanta, kafin ta ji kamar anason saka mata wani abu a ƙafafuwanta. 

Ɗaga ƙafafun ta yi Aroob ta taimaka mata tasa takalman. Kafin su fita, ko gani bata yi sosai, har lokacin murmushin da ta ɗora yana kan fuskarta, tana ji suka shigar da ita mota, Aroob da Asma na zama gefenta. Aka ja su inda bata san ko ina bane ba. Amma sanin zuri’arsu bazai wuce gajeran taro na tayata murna ba. 

*****

Basu dawo gidan ba sai bayan Isha’i, abinci ma Aroob ce ta matsa mata ta ci shi. Ba wai don ta so ba, ranar a ɗakin suka kwana ita da Aroob. Washe gari da sukai sallar Asuba ita bata koma ba, nan ta zauna kan kafet ɗin tana ɗora kanta a gefen gadon ta. Jikinta ya mata sanyi, juyawa ta yi ta buɗe drawer ɗin gefen gado ta ɗauko wayarta da ke ciki tana kunnawa. 

Ƙarfe takwas da rabi na safiya, an ce ɗaurin auren ta ƙarfe goma ne na safiyar ranar. Dubawa ta yi wani ɓangare na zuciyarta na fatan ko da saƙo ɗaya ne na Muneeb ta gani . Ga tarin saƙonni daga mutane da ke nemanta a kashe suna fatan lafiya amma babu nashi ko ɗaya. 

Inda hotunan kan wayar suke ta shiga, tana buɗe folder ɗin da hotunan shi ne kala-kala. Zuciyarta ta numfasa da wani yanayi da ko ina na jikinta sai da ya karɓa, ɗan yatsa tasa tana shafar fuskarshi.

“Allah ya baka farin ciki fiye da wanda nake tunanin zan iya baka…”

Ta furta kamar yana ganinta, hawayen da ta kwana biyu bata ji alamarsu ba suna cika mata ido da zubowa kan kuncinta da wani irin ɗumi, tana jin zafinsu tun daga zuciyarta ne. Bankwana take son mishi amma ta kasa furta kalaman ko a zuciyarta. Tana jin agogon da ke mata yawo cikin kai, agogon da yake ƙure mata. 

Kafin wani lokaci har goma saura, duka ta kai ea Aroob da ke bacci, a firgice ta miƙe tana kallon Zafira. 

“Saura minti sha biyar Aroob…..Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, wallahi saura mintina sha biyar…”

Zafira take faɗi wani irin tashin hankali da bata taɓa sanin shi ba yana lulluɓe ta, asalin abinda auren wani ba Muneeb ba yake nufi a tare da ita yana zauna mata a zuciya. Gunjin kuka ta saki da yake fitowa daga ƙarƙashin zuciyarta. Sakkowa daga kan gadon Aroob ta yi tana riƙe Zafira da ko’ina na jikinta ke kyarma. 

“Allah yasa hakan ne mafi alkhairi a duniyarki da lahirarki….”

Aroob ke faɗi hawaye masu ɗumi na zubo mata. Inda zata iya ko yayane zata ɗauke wa Zafira wani ciwon da take ji. Girgiza mata kai Zafira take yi tana kuka kamar zata shiɗe. 

“Bazan iya mishi bankwana ba, bansan ya zan rufe wannan ƙofar ta rayuwata ba….”

Zafira take maganar cikin kuka. Riƙeta Aroob ta yi sosai, tana rasa ta inda zata gaya mata ba sai ta yi ƙoƙarin rufe ƙofar rayuwar soyayyarta da Muneeb ba, ALKALAMIN ƘADDARArsu ya riga ya rubuta musu yadda komai zai faru, lokaci kawai suke jira. Wayar Zafiran da ke riƙe a hannunta ta fara kuka, da sauri ta duba, Muneeb ne. 

Ɗagawa ta yi ta kara a kunnenta tana sakin wani irin kuka. 

“Duk yanda naso kar in kira na kasa Zafira, yau kawai kafij goma ta cika ina son sake jin muryarki kafin ki zama mallakin wani…”

Muneeb ya ƙarasa tana jin ɗacin da ke tattare da sautin muryarshi ta cikin wayar, yanayin da ke ƙara gudun kukanta. 

“Ki ce min wani abu don Allah, saura mintina uku kacal halaccin magana da ke ya tsaya min…. Ki min magana…”

Girgiza kai take tana jan numfashi cikin son ko yaya ne muryarta ta fito, amma abin ya faskara, kuka take da bata taɓa irinshi a rayuwarta ba, bata ma taɓa zaton zata iya irin shi ba sai yau. Ta ɗauka ta haƙura ta gama kukan, amma muryarshi ta dawo mata da komai sabo. 

“Yaa Mu… Muneeb…. Muneeb….”

Ta samu furtawa numfashinta na wani tsai-tsaiyawa. 

“Na gode da komai. Na gode da soyayyarki duk da bata kaimu inda na hango mana ba. Saura minti ɗaya….”

Kuka ta sake rushewa da shi muryarta na sarƙewa take faɗin 

“Ina sonka sosai…. Wallahi ina sonka. Allah ya baka farin ciki…”

Tana jin numfashin da yake ja yana fitarwa a kunnenta. Muryarshi a sarqe shima yace

“Allah ya sanya miki alkhairi da albarka. Ki kasance cikin farin ciki…”

Ya ƙarasa yana kashe wayar, dawo da ita Zafira ta yi saitin fuskarta tanajin kamar ta ɓulla ta ciki ta ganshi na ƙarshe. Lokaci ta gani, ƙarfe goma dai-dai. Cilli ta yi da wayar tana haɗuwa da bango, ƙararta na ruguza sauran abinda ya rage a zuciyarta, da sanin cewa ta zama matar wani da ko sunanshi bata kai da sani ba, wani irin numfashi ta ja da fitar da shi na mata wahala. Kafin wani duhu ya gilma ta cikin idanuwanta. 

Can sama-sama ta ji Aroob ta riƙota tana faɗin, 

“Zaf! Zafira!!”

Kafin gaba ɗaya duniyar ta yi mata wani irin shiru.

ALHAMDULILLAH

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 10 Alkalamin Kaddara 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×