Skip to content
Part 3 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Gudu suke ba tare da sanin in da suke nufa ba.

Iya gajiya sun gaji, tsayawa sukayi suna mai da numfashi, su Mandiya kuka kawai take tan ƙara tsinema magajiya da tun farko i ta ce sanadiyyarta shiga karuwanci.

Su Rabson guy abun ba magana zama yayi ya miƙe ƙafafu shame-shame yana mai da numfashi, yana jin wata sabuwar nadama nashigar shi, da dana sanin bijirewa maganar Kaka.

Ranar nan suka wuni, ga ƙishirwa ga yunwa, sallah ma da suka auna lokaci aransu suka ga yayi nan suka yi taimama su kayita nan.

Ƙara nausawa cikin dajin suka yi naiman ko ƴa’ƴan itatuwa ne su sanyama cikinsu.

Sunyi tafiya mai nisa suka isa wani wuri mai matuƙar kyau, korayen fulawowi ne ko ina ga wata ƴar ƙorama ruwa na gudana cikin ta, bishiyoyin kayan marmari ne duk in da ka duba sunyi bul_bul gwanin sha’awa.

Kallon_kallo suka hauyi ma junan su, suna mamakin wannan Baƙin daji tunda suka shigoshi basu taba ganin wuri mai kyau irin wannan ba, gashi dai a halin da suke ciki babu abunda suke matuƙar buƙata kamar ruwa da abinci, sai gashi sun samu amma suna shakkar cin shi.

Jafar lura yayi basu yadda da wurin ba, dan haka ya fuskan ce su ya fara masu jawabi;
“A halin da muke ciki yanzu bamuda mafita face mu dogara da Allah muyi Basmala muci abubuwan da muka samu, Wamanyatawakkalu Alallah! Fahuwa hasbuhu.”

Har cikin zuciyoyinsu sunyi na’am da maganar Jafar.

Ida isa sukayi wurin bishiyar Mangwaro Jafar na tsinkowa Audu na tsincewa.

A haka sun tara kayan marar mari mabanbanta masu yawan gaske.

Zama sukayi zasu fara sha koya bakinshi dauke da Basmala.

Alhamdulillah sun sha sun ƙoshi babu abinda ya faru dasu.

Nan suka yada zango suna hutawa, Basma sai yanzu ta lura babu gyalenta ya faɗi sana diyyar gudun da suka sha, ga suturar jikinta ba ta kirki ba duk ta matseta, dubanta ta kai ga Salma wadda ita ma hakan ta kasance gareta dan figaggen gyalenta ita ma tun suna cikin wannan gidan ya faɗi.

Duk cikin su Biba Ita kaɗai ce shigarta har yanzu hijabinta bata cireba sai dai cukuikuyewa da ta fara saboda wahalar da suke sha.

Abinda su Jafar basu sani ba tunda suka fara gudun nan wata ƴar ƙaramar barewa ke biye dasu.

Ba zato ba tsammani suka ga barewa ta nufo inda suke gadan_gadan.

Miƙewa sukayi a matuƙar razane suka dun ƙule wuri ɗaya.

Rike ɗewa barewar tariƙayi har ta koma wani farin tsoho mai cikar kamala da kwarjini.

“Ku kwantar da hankalinku ni taimakon ku nazo yi ba cutar daku ba, nima da kuke gani musulmi ne ɗan uwanki, abunda nike buƙata ku dogara da Allah ku zauna in sanar daku abinda baku saniba game da tafiyar da kuke.

Jikinsu kyarma kawai yake sun kasa zama sai da Jafar da Biba suka ƙara masu tuni akan su dogara da Allah su zauna.

Mai da hankalinsun sukayi ga wannan tsoho.

“Kamar yadda na faɗa maku a baya ni ba mutum bane, kamarku ni Aljani ne, suna nana Ammar bin asad, basai na sanar daku yanayin dajin nan ba nasan yanzu kun fara sanin yadda yake, wannan daji da kuke gani tun asali ya kasance wani irin shu’umin jeji wanda ko dabba ce ta shigo cikin shi da wuya ta fita araye, asalin fara zaman wannan daji wasu turawa ne ma’aurata bayan aurensu suna binciken inda keda abubuwan mamaki domin su Allah yayi su da son abubuwan al’ajabi, nan suka binciko wannan daji, sunyi ƙokarin zuwa dan ganema idanunsu abinda ke faruwa ana hana su zuwa amma suka nace, daga ƙarshe suka sulale suko yo Nageria, bayan zuwansu Nageriya basu yadda sun shiga wannan daji kai tsaye ba gida suka kama suka zauna suna hulɗa da hausawan mu har suka iya hausa abakunan su, Alƙawari mijin yayi in matarshi ta haihu ɗiyar tayi shekaru biyu lokacin ne zasu nausa cikin dajin dan gane ma idanusu abunda ke faruwa.”

“Ba’a ɗauki wani dogon lokaci ba Matar wannan Bature ta haihu, ranar da ɗiyarshi ta cika shekaru biyu ranar suka ɗauki hanyar wannan daji da duk guzirin da suke buƙata, Sanin halin wannan daji yasan ya direban dazai kai su dajin yace sai dai ya ajesu nesa da dajin su ida isa da ƙafafunsu, idansu ya rufe ga son shiga wannan daji dan haka basuji komi ba suka amince , gurinsu ya cika sun samu damar shiga cikin wannan daji daya kasan ce shine zai zama ajalinsu, tun shigar su dajin suke murna ganin dajin ko ƙasashen su basu taba ganin daji mai duhuwa da manya_manyan duwatsu, dajin kallonshi kaɗai abun tsorone amma su a wurinsu wannan shine kaɗan daga cikin abubuwan mamakin da suke naima,itatuwa mijin da matar suka hau sarewa suna haɗa katakan yin gidan da zasu zauna, sunyi aiki natsawon watanni biyu iya wahala sun wahala kafin suyi nasarar hada gidan, har yau babu abinda ya firgita su koya tsorata su tun shigarsu dajin, rayuwa suke tajin daɗi acikin dajin nan suna ɗiyarsu, ranar da bazasu taba mantawa ba ita ce ranar suna daga wajen gidan ɗiyarsu na nesa dasu tana wasa su kuma suna zaune suna hirarsu, wata irin ƙara kunnuwan su suka Jiyo masu, a firgice suka kwalama ɗiyarsu kira dake wasa nesa dasu baban ya ruga ya ɗauko ta suka nufi gidan, sai dai mi! Suna buɗe gidan suka ga ɗiyarsu nata wasanta ita ɗaya cikin gidan, dagowa tayi ta kallesu tana sakar masu murmushi, sakin wadda ke hannunsu sukayi suna nunata da yatsa suna ja da baya, su duka tare biyu da ta cikin gida da ta hannunsu nufo su sukayi suna momy ni ce Lara ɗiyar ku waccen ƙarya take, ruɗewa sukayi sun rasa gane ainahin ciki wacece ɗiyarsu, Lara ta ƙarya ta shago wuyan ta gaskiyar ta ɗagata sama ta wujijjigata ta wullata gefe, juyowa tayi kan iyayen tana dariya idanunta na zubda jini, nuna su tayi da hannu take wata iska ta yi sama dasu tana bugasu da bishiyoyin wurin tun suna ihu suna kiran abun bautar su har suka daina numfashi, bacewa. Basu farfaɗo ba sai da marece yayi sanyi bugesu sannan suka farfaɗo kan ɗiyarsu sukayi da gudu suna kiran sunan ta, kayansu suka haɗa suka nufi haryar da suka shigo dajin, abun mamaki haka suka ƙaraci yawonsu har duhun dare ya fara amma hanyar ta bace masu, dole suka haƙura suka dawo gidan suna tunanin abunda zai same su nadamar shigowa dajin na shigarsu , dare ya raba babu abuda kunnuwanka ke jiyo maka illa kukan tsuntsaye da ya haɗe da Iska yake bada wani firgitaccen sauti, ƙofar da suka kulle sukaji tana budewa da kanta ɗiyarsu suka jawo suka ƙara rungumewa, wani baƙin wayaƙi ya Cika ɗakin, a hankali ya fara haɗewa wuri ɗaya yana komawa doguwar halittah mai suffar mutum, ko ina jikinta hannuwa ne, idon ta guda a tsakiyar goshi, dariya ta kece da ita “ku masu taurin kai yau kwananku ya ƙare,yau zaku bar duniyar nan sakamakon ganin ƙwaf daya kawoku dajin nan,” tana rufe baki ta chafko miji ta wullashi sama ya fado ƙasa kanshi ya fashe ko shurawa bai yi ba ya mace, matar ta nuna da hannu take wani hayaƙi ya fito ta hannunta ya shigajikin matar da ɗiyarta take jini ya riƙa ambaliya ta hancinsu da baki suka sulale ƙasa matattu, atare gawawwakin su suka bace tare da wannan halittar, wannan shine abunda yafaru da waɗan da suke shigowa ɗakin nan, taimako ɗaya zaniyi maku shine kada kusake wannan addu”ar ta fita daga bakunan ku, *LA’ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTUMINAZZALIMIN*, sam koda wasa kada kusake ku rabu da abokan tafiyarku, ƙarfina bazai iya fiddaku daga dajin nan ba addu’ar ku ita zata taimake ku, nabarku lafiya Allah ya fitar daku, ya bace.”

Jikinsu sanyi yayi dajin wannan bayanin, basu ankara ba wurin da suke ya fara duhu bishiyoshin na komawa baƙaƙe flower ɗin wurin suna bacewa, Basma tsalle tayi ta faɗa jikin Biba jikinta na kyarma, Rabson Basma dake kusa dashi ya maƙalƙale.

“Bakada hankali? Ina matar aure zaka riƙa shigemani?”

“Ke da auren na haɗaku a turmi na Ƙulƙule, kina matar aure tsabar gantali miya fito dake wannan tafiyar?.”

Kafin ya rufe baki duhu ya ida rufe idanunsu, ji sukayi an shure su anyi sama dasu…

<< Bakar Tafiya 2Bakar Tafiya 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.