Skip to content

Nazarin ka’idojin rubutun Hausa 2

A darasin da ya gabata mun yi bayani ne game da ma’anar rubutu da ma’anar ƙa’idojin rubutun Hausa da samuwar rubutun Hausa da kuma muhimmancin ƙa’idojin rubutun karɓaɓɓiyar Hausa. A wannan darasin kuma za mu yi duba ne kan baƙaƙe da wasulan Hausa, da kuma wuraren da ake amfani da babban baƙi.

Baƙaƙen Hausa

Baƙaƙe jami’i ne na baƙi, shi kuma baƙi shi ne harafin da ba wasali ba. Babban baƙi shi ne, baƙin da masana suka haɗu a kan cewa shi ne babban baƙi. Abajadin haruffan Hausa kowane yana da babba da ƙarami daga baƙaƙe, har zuwa wasula. Da farko, ga jerin haruffan Hausa manya da ƙanana domin sauƙin tantancewa.

1. Wasulan Hausa

– Manya: A E I O U

– Ƙanana: a e i o u

2. Baƙaƙen Hausa

– Manyan Baƙaƙe:-

B, Ɓ, C, D, Ɗ, F, FY, G, GY, GW, H, J, K, Ƙ, KY, KW, ƘY, ƘW, L, M, N, R, S, SH, T, TS, W, Y, ‘Y, Z.

– Ƙananan Baƙaƙe:-

b, ɓ, d, ɗ, f, fy, g, gy, gw, h, j, k, ƙ, ƙy, ky, kw, ƙw, l, m, n, r, s, sh, t, ts, w, y, ‘y, z.

Wuraren da ake amfani da manyan baƙaƙe

Akwai wurare da dama inda ya zama dole mai rubutu ya fara rubutu da manyan baƙaƙe. Ƙa’idar rubutun Hausa ta keɓe wurare masu yawa waɗanda ake amfani da manyan baƙaƙe.

Don haka, saɓa wa ƙa’idar a irin wurare zai haifar da gurɓatar rubutu, wataƙila har da gurɓatar ma’ana a wasu kalmomin. Wasu daga cikin wuraren da ake fara rubutu da babban baƙi sun haɗa da;

1. Sunaye Mutane:- Waɗannan su ne, sunaye waɗanda aka laƙaba wa mutane. Don haka, a wajen rubuta sunayen mutane ana fara wa da babban baƙi. Misali:

Daidai               Kuskure
Abdullahi        abdullahi
Sadik                sadik
Aminu              aminu
Isa                     isa
Hashim            hashim
Hassana           hassana
A’isha                a’isha
d.s

2. Sunayen Ubangiji:- Suna ne, mafi ɗaukaka wanda Ubangiji Ya ba wa kansa. Dole ne duk wanda zai yi rubutu cikin Hausa ko kuma wani harshe da yake da tsarin manya da ƙananan haruffa ya yi amfani da babban harafi wajen rubuta sunan Ubangiji. Misali:

Daidai              Kuskure
Allah                 allah
Ar-Rahman     ar-rahman
As-Salam         as-salam
Al-Hadi            al-hadi
Al-ƙudus         al-ƙudus
Al-Kaliƙ           al-kaliƙ
Al-Hayyu         al-hayyu
Al-Ƙayyumu   al-ƙayyumu
d.s

3. Sunayen Ƙasashe:- Shi ne, laƙabin da ake yi wa ƙasashe domin a gane su. A lokacin da za a rubuta sunan kowace ƙasa ana fara rubuta sunan da babban baƙi. Misali:

Daidai                  Kuskure
Najeriya                najeria
Rasha                     rasha
Faransa                 faransa
Nijar                      nijar
Saudiya                saudiya
Mali                      mali
d.s.

4. Bayan Amfani da Alamar Tambaya ( ? ):– Alamar tambaya kamar yadda sunan ya nuna alama ce wadda ke nuna tambaya a wajen mai magana. Murya takan sauya a duk lokacin da aka yi amfani da alamar tambaya. Ana amfani da babban baƙi bayan an yi amfani da alamar tambaya. Domin alama ce ta tsayawa. Misali;

“Babu shakka na tafka babban kuskure, me zan faɗa wa iyayena ranar da asirina ya tonu? Da wane ido zan kalle su? Wace hujja na riƙa don kare kaina a gaban Ubangiji?”

5. Bayan Amfani da Alamar Motsin Rai ( ! ):– Alamar motsin rai kamar yadda sunan ya nuna, alama ce wadda ke nuna motsin rai, ma’ana maganar da aka faɗa ta motsa rai. Murya takan sauya a duk lokacin da aka yi amfani da alamar motsin rai. Ana amfani da babban baƙi bayan an yi amfani da alamar motsin rai. Domin alama ce ta tsayawa. Misali;

“Wayyo Allahna! Na shiga uku ni Dije, me zan gani a gidan nan? Cikin shege! Wallahi gara na kashe ki kowa ya huta…”

6. Bayan Amfani da Aya ( . ):- Wannan na nufin ɗigo guda ɗaya wanda ke nuna kammalar zance ko jimla. Ana fara rubutu da babban baƙi a duk bayan amfani da aya, wato inda za a fara sabon zance ko sabuwar jimla.

7. Harufan Farkon Zancen Wani:– Duk lokacin da marubuci ya zo gabatar da zancen wani, wajibi ne ya bude zancen da harafin farko babban baki, misali;

Ran Suwaiba a bace ta diro daga motar, ta dubi Bello ta ce, “Iska ce take wahalar da mai kayan kara, Ba zan taba sauya ra’ayina ba…”

8. Harufan Farkon Jimla:- Kamar yadda yake a kowanne harshe, a kowace jumla ana fara rubutu ne da babban baƙi ko wasali, misali;

– Kowa ya zauna.
– Yara suna wasa da ƙwallo.
– Ina son na zama likita.

9. Harufan Farkon Kanun Magana:- Wannan na nufin kanun labarai ko maƙalu, a duk lokacin da aka zo rubuta su da babban harafi ake farawa. Misali;

• A Najeriya ana rantsar da shugaban ƙasa

• Hukumar KAROTA za ta sabunta lasisin masu abin hawa

• Matsalar yawaitar sace-sacen ɗalibai a jami’o’in Najeriya da yadda za a magance ta

10. Sunayen Watanni da Ranakun Mako:– Gabaɗaya sunayen watanni da ranakun mako na Musulunci da na Turawa ana fara rubuta harafin farkon kowanne da babban baƙi. Misali;

Ranaku                Watanni
– Juma’a                Ramadan
– Lahadi                Janairu
– Litinin                Yuli
– Talata                 Maris
– Alhamis             Safar
– Asabar               Shawwal
– Laraba               Rajab
d.s

11. Sunayen Littafai da Fina-finai da Shirye-shiryen Gidajen Rediyo da Talabijin:– Ana fara rubuta sunayen waɗannan abubuwa da aka ambata da babban harafi. Misali;

• Ƙur’ani
• Injila
• Jiki Magayi
• Ruwan Bagaja
• Tekun Labarai
• Daɗin Kowa
• Kulɓa na Ɓarna
• Ƙarshen Alewa…
• Gane Mini Hanya
• Inda Ranka…
• Kowanne Gauta
• Baƙon Mako
• Hangen Dala…
• Kwana Casa’in
• Ƙwaryar Ƙira
• Duniya Tumbin Giwa d.s

12. Jaridu da Mujallu:- Misali;
– Aminiya
– Gamzaki
– Leadership
– Rariya
– Nagartacciya
– d.s

13. Sunayen Bukukuwa Addini Da na Gargajiya:- Akwai bukukuwa da dama da ake aiwatar da su da suka hada da na addini da kuma gargajiya. Duk yayin da za sunayen wadannan bukukuwa to wajibi ne a yi amfani da babban harafi. Misali;

– Maulidi
– Babbar salla
– Karamar salla
– Takutaha
– Ista (Easter)
– Kirsimeti
– Ranar ‘Yancin kai (Independence Day)
– Hawan Daba
d.s

14. Sunayen Ma’aikatu da Hukumomi da Kamfanoni:– Misali;

• Hisba
• Hukumar ‘Yansanda
• Bakandamiya
• Gaskiya Textile
• Ashaka
• Ma’aikatar Ilimi
• Bayero University Kano
d.s

Waɗannan wurare da aka kawo a sama kaɗan ne daga wuraren da ake amfani da babban baƙi a rubutu. Ku ci gaba da wannan darasi a makalarmu ta uku.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page