Skip to content

Nazarin ka’idojin rubutun Hausa 1

Gabatarwa

Harshen Hausa na daga cikin harsunan da suka ci gaba ta ɓangaren ƙa’idojin rubutu. Don haka harshe ne da ya ke da wasu tsayayyun ƙa’idoji waɗanda ake amfani da su bisa ƙa’idojin rubutun daidaitacciyar Hausa. Don haka, wannan rubutu zai yi bayanin muhimmancin da ƙa’idojin rubutu ke da shi wajen fahimtar harshe Hausa.

Ma’anar rubutu

Wani masani mai suna Xavier Pevret kamar yadda ya bayyana cewa, “Rubutu wata dabara ce ta yin wasu ‘yan alamomi da za su wakilci magana.” Amma a fassarar Ƙamusun Webster (1996) an bayyana cewa, “Rubutu shi ne alamta kalmomi ko wasu abubuwa da za su iya zama matsayin kalmomin, ko kuma wasu ra’ayoyi, ko fahimta da aka yi a wasu abubuwa, a kan ko takarda, ko itace, ko dutse, tare da amfani da fensiri ko wani burushi ko ta wasu dabaru daban kamar tambari ko ɗab’i ko huje-huje da zane-zane.”

Asalin rubutun Hausa

Masana sun nuna cewa rubutun Hausa ya samo asali daga ɓullowar Musulunci ƙasar Hausa, wanda ya haifar da rubutun ajami. A ganin waɗannan masana rubutun ajami ne na farko da aka fara rubuta Hausa da shi, da Bature ya bayyana ƙasar Hausa aka haifi rubutun boko. Don haka, waɗannan su ne hanyoyi biyu fitattu da ake ta kai kawo da su wajen laluben asalin rubutun Bahaushe.

Ma’anar Ƙa’idojin rubutu

Ƙa’idojin rubutun Hausa na nufin wasu dokoki da aka samar domin samun ingantacciyar hanya ta rubuta Hausa, wadda ba za ta ba da wahala wajen karanta rubutu da gane manufa ba. An daɗe ana rubuta Hausa da baƙaƙen boko ta hanyoyi daba-daban kafin a cim ma yarjejeniya wajen tabbatar da ƙa’idojin da ake bi a yanzu.

In aka yi nazarin rubuce-rubucen Hausa da aka yi a lokuta daban-daban a kan sami bambance-banbance kimanin iri uku kamar haka:

1. Hanyoyin sarrafa wasu muryoyi na Hausa a cikin abajadin boko, wato samar da wasu haruffa waɗanda za su wakilci muryoyin Hausa irin waɗanda babu su a harshen Ingilishi, misali muryar ɓ, ɗ, ƙ, ts, ‘y. Waɗannan duk babu su a harshen Ingilishi, don haka an samar da su ne sakamakon samar da ƙa’idojin rubutun Hausa.

2. Yadda ake haɗa wasu kalmomi na Hausa da yadda ake raba wasu a rubuce-rubuce, an sami gyara ta fuskar rubutu bayan an samar da ƙa’idojin rubutun Hausa.

3. Gauraya wasu keɓaɓɓun kalmomi na karin Hausar wurare daban-daban a cikin rubutu. Misali haɗa karin harshen Sakwatanci da karin harshen Kananci a rubutu ɗaya. Wannan yana haifar da rashin fahimta ga masu amfani da rubutun musamman waɗanda ba karin harshen su ba ne.

Muhimmancin Ƙa’idojin rubutu

Ƙa’idojin rubutun Hausa suna da yawa kuma suna da muhimmanci a rubutu. Wasu daga cikin ƙa’idojin sun haɗa da; yanayin rubuta baƙaƙe da wasula, da ginin kalmomi, da yadda ake raba ko haɗa kalmomin rubutu, da sauran makamantansu. Waɗannan abubawa su ne ginshinƙai a rubutu, don haka kula da su zai samar da inganci a rubutu. Yayin da rashin kula da su zai haifar da cikas a rubutu, saboda haka, yana da muhimmanci a yi amfani da su a rubuta.

Kaɗan daga cikin muhimmancin amfani da waɗannan ƙa’idoji a rubutu sun haɗa da:

1. Fito da ma’anar kalma ko jimla:– Ƙoƙari da masana Hausa suka yi na daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa ya ƙara fito da ma’anar kalmomi, musamman kalmomin da ke da sigar rubutu iri ɗaya, kafin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa ana yin rubutu ne barkatai, amma samuwar ƙa’idoji rubutu ya kawar da wannan matsala, don haka yin amfani da ƙa’idojin rubutu yana fito da ma’anar da ake son amfani da ita, kamar yadda rashin amfani da ƙa’idar rubutu kan rikita ma’ana duba da waɗannan misalai:
– A’i
– Ai

Kalmar farko da ta biyu iri ɗaya ne bambancin da aka samu kawai shi ne amfani da al’hamza a kalmar farko, kuma shi ne ya banbanta ma’anonin kalmomin. Kalmar farko na nufin sunan mace, amma kalma ta biyu na nufin ƙarin bayani a wata magana. Misali a jimla:

a) A’i ta tafi (an ambaci sunan wacce ta tafi)

b) Ai ta tafi (ba a ambaci sunan wadda ta tafi ba)

Don haka, za a ga cewa amfani da ƙa’idar rubutu ta alamar rubutu ta fito da ma’anar kalmar da ake son isarwa, da mai rubutu zai rubuta jimla ta biyu da nufin ya isar da saƙo da ke ƙunshe a jimla ta ɗaya, da mai karatu ya sami matsalar fahimtar saƙon.

c) Rabi
d) rabi

A waɗannan kalmomi an fara kalmar farko da babban baƙi wanda zai sa mai karatu ya fahimci cewa suna ne, domin ƙa’idar haka ta tanada. Amma kalma ta biyu an fara da ƙaramin baƙi, wanda hakan ya nuna ba suna ba ne, ana nufin wani kaso na ɗaya bisa biyu.

Amma idan mai rubutu ya yi amfni da kalmar farko a inda ya kamata ya yi amfani da kalma ta biyu, hakan zai ba mai karatu matsala wajen fahimtar saƙon. Ga misali a jumloli:

a) an ba ni Rabi (suna)
b) an ba ni rabi (kaso/kashi)
c) Rabin gidan Musa (suna)
d) rabin gidan Musa (kaso/kashi)

Waɗannan kalmomi sun bambanta ne ta yin amfani da babban baƙi domin dokar ta ce a fara rubuta suna da babban baƙi a duk inda ya zo a jumla.

2. Ƙa’idojin raba kalmomi da haɗe su abu ne sananne a Hausa:- Amfani da waɗannan ƙa’idojin na fito da ma’anar kalmomi, haka kuma ƙin amfni da su na haifar da rashin fahinmtar ma’ana ga masu karatu.

Ga misalin kalmomin waɗanda duk rubutunsu daidai ne, sai dai mai rubutu ya san inda zai amfani da wadda aka raba da inda zai amfani da wadda aka haɗa domin ma’anoninsa daban ne.

A haɗe              A rabe
itace                    ita ce
taga                     ta ga
yau                      ya’u
kusato                 ku sato
d.s

Waɗannan kalmomin suna kama da juna, amma wasu na yin kuskure wajen rubutu su a haɗe a inda ya kamata a rubuta su a rabe. Ga misali a jumla:

– taga aka buɗe  (a haɗe)

– ta ga an buɗe   (a rabe)

– itace ta kwaso  (a haɗe)

– ita ce ta kwaso  (a rabe)

– kusato ta            (a haɗe)

– ku sato ta           (a rabe)

A nan mun ga amfanin raba kalmomi ko haɗa kalmomi da yadda yake fito da ma’anar kalmomi don haka suna da muhimmanci wajen fahimtar rubutu.

3. Amfani da Ƙugiya:- Amfani da ƙugiya, wata ƙa’ida ce a rubutun Hausa, kuma amfani da wannan ƙa’idar na fito da ma’anar kalma haka kuma rashi amfani da ita na haifar da matsala ga rubutu. Akwai baƙaƙen da ake amfani da ƙugiya domin samar da sautukan Hausa na musamman, waɗanda babu su a tsarin abacada (abcd).

Ga misalan kalmomi masu gaɓoɓi iri ɗaya da tsarin rubutu ɗaya amma ma’ana ta banbanta sakamakon amfani da ƙungiya a wani baƙi.

Da ƙugiya          Ba ƙugiya
Ƙarya                    karya
Faɗa                      fada
Ɓari                       bar
Ƙara                      ƙara
Yaya                      ‘ya’ya

Idan aka yi amfani da baƙi mara ƙugiya a inda ya kamata a yi amfani da mai ƙugiya ko mai
ƙugiya inda ya kamata a yi amfani da mara ƙugiya, yin hakan zai haifar da saɓanin ma’ana. Ga misalai:

1. Fada ya tafi  (gidan sarki)
2. Faɗa ya tafi  (rigima)
3. Yayana ne    (ɗan’uwa)
4. ‘Ya’yana ne  (yara)
5. Kara ya yi    (kauwar da kai)
6. Ƙara ya yi    (ihu)

Wannan ya nuna irin muhimmancin amfani da ƙugiya a kalmomin da inda ya kamata da kuma inda bai kamata ba.

4. Kafa harshen Ƙasa:- Samar da ƙa’idojin rubutun Hausa da yin amfani da su ya bunƙasa harshen Hausa, har ya kai Hausa ta zama harshen ƙasa. Dalili kuwa shi ne, babu harshen da za a ɗauka a matsayin harshen ƙasa har sai yana da daidaitattun ƙa’idojin rubutu da masu harshen suka tanada aka kuma amince da su. Saboda rashin tsayayyar ƙa’ida zai haifar da mabambantan rubuce-rubuce a wurare daban-daban. Domin harshen Hausa na da ƙa’idojin rubutu tsararru waɗanda ake amfani da su a ko’ina tun daga makarantun firamare har zuwa jami’o’i. Kuma wannan ƙa’ida ita ce ake amfani da ita a gida da ƙasashen waje inda suke koyo ko koyar da Hausa.

Saboda haka, za a ce ƙa’idojin rubutun da Hausa ke da su, ya sa aka amince a yi anfani da  harshen a matsayin ɗaya daga cikin harsunan ƙasa, kuma ake amfanin da shi a fannin koyo da koyarwa a matakai daban-daban. Don haka, yana da muhimmanci a kula da ƙa’idojin rubutun Hausa a wajen rubutu tare da ƙara ƙoƙarin inganta su inda ya kamata a yi hakan.

Ku ci gaba da wannan darasi akan bakaken Hausa.

1 thought on “Nazarin ka’idojin rubutun Hausa 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page