Sunan Littafi: Bakar Tafiya
Sunan Marubuciya: Amina Abubakar ‘Yandoma
Inda aka Buga Littafi: Hikaya
Shekarar Bugu: 2023
Yawan Babi: 17
Mai Sharhi: Hajara Ahmad Oum-Nass
Tarihin marubuciyar a takaice
Aminatu Abubakar ‘Yandoma, an haife ta a garin Katsina, ta yi karatu a cikin garin katsina, ta fara rubutu bayan ta kammala makarantar secondary school a shekarar 2019, ta rubuta litattafai da dama waɗanda suka haɗa da na zamantakewa sai kuma na barkwanci da kuma na aljannu.
Wannan shi ne tarihin marubuciyar a taƙaice.
Tsokaci kan littafin
Sanadi ko kuma ace sila wasu abubuwa ne da suke faruwa ga ɗan adam, a wani lokacin ma sai mutum ya ƙirƙirarwa kansa faruwar abin daga baya ya ambace su a matsayin kalmar ƙaddara duk da shi ne ya ƙirƙirarwa da kansa faruwar su.
Kamar dai yadda Rabson, Salma, Basma, suka zama silar wanzar da mummunan ƙaddara ga Jafar da Biba, wajen kwasar romon zunuban su.
Na san da yawa za su ce ƙaddarar wani ba ta taɓa shafar wani, amma kuma idan Allah ya so jarrabaka sai ya ɗora ma nauyin zunuban wani don ya gwada imaninka. Labarin zai fi kama da films ɗin horaye da masu shan jini, ta wata fuskar kuma ya fi kama da na hatsabiban aljannu ko kuma fatalwa da aka saba gani a fina finan indiya. Sai dai duk da haka ya samar da kyakkyawan darasi na illar taurin kai ga mutane, da bijirewa umarnin miji da iyaye.
A taƙaice dai labari Baƙar Tafiya labari ne na wasu matasa guda biyar da suke da buri mabambanta na zuwa wani gari, kwatsam kuma suka yi karo da mummunan ƙaddara ta silar mutuwar Direbansu a tsakiyar jeji ba tare da sun san dalili ba. Hakan ya sa suka bazama suka nausa cikin jejin da tunanin hanyar dawowa gida suka nufa, ashe mahallakarsu suka tunkara.
Abubuwan birgewa game da littafin
Akwai abubuwa masu yawa sosai na birgewa a cikinsa. kaɗan a ciki su ne Jigon da aka saƙa labadin da yadda marubuciyar ta fito da illar bijirewa miji, da kuma rashin bin umar ni mahaifi.
Tasirin addu:a ga musalmi a duk halin da ya tsinci kansa.
Warwarewar labari bayan an nuna kamar ba za a rayu cikin sa ba.
Tasirin addu’ar Uwa ga yaranta.
Jigon littafin
An gina labarin ne akan Jigon kuskuren ƙauracewa umarnin miji da kuma na iyaye, sai tasirin addu:a ga bawa.
Zubi da tsari
Tun daga farko marubuciyar ta yi nasarar riƙe mai karatu, ta yadda ta ja zaren labarin nata, ta saƙa shi ta kuma kai shi ƙololuwa wajen wanzar da matsala, har kuma zuwa a ƙarshe ta yi nasarar warware shi cikin salo mai armashi da gamsar wa.
Halayen taurarin labarin
Rabi’u (Rob son): Ɗan gayu ne da ko a kalamansa da shigarsa yake bayyana ɗabi’arsa ta irin guy ɗin da ya yi wa makarantar arabi da ta zamani gudun famfalaƙi.
Jafar: Yaro mai ladabi da biyayya da nema wa mahaifansa mafita, mai tsananin ruƙo da addini da ƙaunar iyayensa.
Salma: Shagwaɓaɓɓiyar yarinya ce da mahaifiyarta ta sangarta ta, take kuma nuna mata cewar za ta iya komai saboda suna da kuɗi da wadata.
Basma: Marar haƙuri da fatali da duk wasu sharuɗɗa na zaman aure, bijirarriya a wurin miji mai girmama al’amarin ƙawayenta sama da na mijinta.
Biba: Mai sanyi hali da dogaro da kai ta ɗauki kalmar babu maraya sai rago ta duƙufa wajen gina rayuwar ƙannainta don su yi karatu, tana kuma girmama al’amarin mahaifiyarta.
Garba Kisa, Audu Gwarama, Nura Shila: Su dukansu ‘yan fashi ne, manyan ƙwauraye masu haddasa ruguntsumi da faɗan banga a siyasa.
Ɗarsau
Akwai Ɗarsau da yawa a labarin, wanda ya haɗa da na addini, tausayi, al’ajabi, tawakkali, da sadaukarwa.
Ɗarsau Na Addini: A shafi na 30 in da Jafar ya ke cewa Biba “Biba yanzu ba lokacin kuka ba ne, mu sa mu mafita, ni fa gani nake mu haƙura da dajin nan mu zauna cikin gidan nan kawai in Allah ya yi za mu fita shi zai kawo mana ɗauki da kan shi, saboda faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam da ya ce “Idan annoba ta samu gari to na ciki su zauna a garinsu na waje kuma kar su shigo garin.”
Ɗarsau Na Sadaukarwa: Lokacin da Biba ta fara magana, “Sanin haɗarin da muke ciki yasa daga yanzu ko wani bala’i ya samu ɗan uwanmu kada wanda ya ƙara ƙoƙarin guduwa ya rabu da sauran.” Anan duk sun amince da shawarar Biba na su rayu tare su mutu a tare.
Ɗarsau na Tawakkali: A shafi na 47 Jafar ya faɗa musu “A halin da muke ciki yanzu ba mu da mafita face mu dogara da Allah mu yi Basmala muci abubuwan da muka samu, Waman ya tawakkalu Alallah, Fahuwa hasbuhu.”
Ɗarsau na Nadama: A shafi na 39 Basma kuka take tana sambato ita kaɗai, “Allah sarki masoyina kuma mijina habibina, da na bi shawararka da yanzu ina gida amma haka na nace dole sai naje bikin ta gaban goshi, Allah ya isa tsakanina dake ta gaban goshi ke ki kai ta tura ni, ina ma Habib rashin mutunci, yanzu ga shi nan na baro ɗana, mijina yana fushi da ni na san mutuwa zan yi.”
Ɗaursau na Imani ga Allah: A Shafi na 41 muryar Aljana ta bayyana tana mai yi musu gargaɗi “Kun yi kuskure bil adama masu taurin kai da gadara, yau kwananku ya ƙare, a sannu zaku baƙunci lahira.”
Jafar yayi ƙarfin halin fara magana.
“Ƙarya kike ya ke wannan la’anannar halitta, ke baki isa ki kashe mu ba sai dai in kwanan mu ya ƙare, Ubangiji ya rabuta zamu mutu yau, amma ba dai ke ba.”
Ɗarsau Na Shawara: Tasirin Addu’a ga bawa a shafi na 52 in da wani dattijon aljani yake ba su shawara da su riƙe addu’ar LA’ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN, domin ita kaɗai ce za ta cece ku.”
Darsau Na Tsoratarwa: Lokacin da direbansu ya mutu muryar Aljana ta bayyana “Kun yi kuskuren shigowa DAJIN KAI KAZO!! Ku masu taurin kai Dukkan ku babu wanda zai fita da rayuwar shi. Za mu riƙa yi muku ɗauki ɗai-ɗai har sai mun ƙarar da ku” Hahahaha.”
Ɗarsau na Barkwanci. : A shafi na 53 bayan ɓacewar Aljani Rabson, ya maƙalƙale Basma dake kusa da shi.
“Ba ka da hankali? Ina matar aure za ka rinƙa shige mini?”
“Ke da auren na haɗa ku a turmi na Ƙulƙule. Kina matar aure tsabar gantali me ya fito da ke wannan tafiyar?”
Da dai sauransu.
Kurakurai
A tashin farko marubuciyar ta datse alaƙar ƙauna tsakanin mai karatu da jarumanta, ta yadda sakin layi ya yi yawa matuƙa. Misalin farkon labarin an fara hasko gidan Basma, da yadda take ta musayya da mijinta. Kafin mai karatu ya fahimci wainar da ta toya aka yi tsalle aka faɗa gidan su salma. A haka dai aka yi ta sakin layi har aka sada mu da jaruman da ba mu ji mun shaƙu ba har sai da tafiya ta miƙe. Ko me ya sa haka?
Tun daga farkon labarin har zuwa ƙarshensa marubuciyar ta yi watsi da ƙa’idojin rubutu. kamar yadda aka haɗe kalmomi masu yawa waɗanda ya kamata a ce a rabe suke, kamar su :
Baka madadin BA KA
Isaba madadin ISA BA
Dani madadin DA NI
inje —- In je
yayi —– ya yi
bada — ba da
abinda — abin da
dani — da ni
nayi, banga, jeki, zaki, kinyi, zani, barshi, yimashi, zakaje……
Da sauran su dai. Ko me yasa haka?
Akwai Hausar baka sosai a labarin kamar su : Mani, madadin mini, fah madadin fa.
hajara madadin Hajara.
Shin marubuciyar ta manta ana sanya farkon suna da babban harafi ne?
Abubuwan da suka faru a jejen da matsalolin da suka haddasu ga jaruman ba su yi kama da abubuwan da ke faruwa a gaske ba. Amma ban sani ba ko marubuciyar ta shiga jejin ne.
Shin labarin na gaske ne, ko kuma dai almara ne?
A ƙarshe ina jinjina da fatan alkhairi ga fasihiya ‘yar baiwa Allah ya ƙara basira da fikra.
Ko ban faɗa muku ba kun san; Labarin ya cancanta ta kowacce kusurwa idan aka yi duba da shi ne Bakandamiyar marubuciyar, wanda mutane da dama sun so shi har kuma a gobe suna kan ƙaunarsa.
Kuna iya karanta littafin Bakar Tafiya a Hikaya kyauta.