Skip to content
Part 57 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Safiyar Monday Mustapha ya wuce Abuja, inda ya tabbatar wa da Fatima lallai ba zai kara zuwa Katsina ba, kuma hutun wannan semister ta yi shi Abuja.

Ta amsa mishi da to ne kawai, ba wai tana da tabbacin zuwa din ba, don sosai take kewar Sandamu musamman Mama da yayyunta mata.

Sannan ita Sam ba ta saba da wannan hannun amsa hannun mayarwar da suke a kanshi ba. Ta fi jin ta da kwarin gwiwarta, idan ya zo ya mata dan satinshi ya wuce. Maimakon ta rika kallon shigar wata da kuma fitarta.

Yanzu kam a kan abu biyu ta fi mayar da hankalinta, tukin da take koyo da kuma exam din da take jira.

A kullum su kan fita koyon driving din sau biyu, safe da kuma yamma.

Kuma tuni ta fara kwarewa, yar tafiya mara nisa dai a wurin da babu cunkoso tana zuwa lafiya ta dawo lafiya, wani lokaci ma har makaranta ta kan shiga da motar musamman ace Umaima na kusa da ita, tun da ta fara koyon tukin ba ta taba fadawa kowa ba, jira take ta ba kowa mamaki tun ba Mustapha da Jamil ba.

Yau Alhamis tashi suka yi da labarin haihuwar Zainab namiji, sai dai dan bai zo da rai ba, doguwar nakuda Zainab ta yi, ta sha wahala sosai .

Shi ya sa Misalin karfe hudu na yamma suka shirya cikin doguwar riga ita da Umaima pitch color da adon bakar fulawa, sosai sun yi kyau kamar tagwaye, duk da Umaiman fara ce sol, sabanin Fatima da ta ba ta kai ta haske ba, kuma ta fi Umaiman budewa sosai, amma shekarunsu zasu iya kamawa daya.

Beauty kuma riga da wandon blue jeans mai kwalliya hade da farar shirt aka sanya mata na mata, gashinta gida biyu aka raba shi gami da daure shi da Light pink din ribom, ta yi kyau musamman yadda tafiyarta ta nuna yanzu, kafafunta sanye da takalma pink sai igiyar takalmin da ta kasance fara.

Napep suka tara zuwa unguwarsu Zainab din, saboda motar Umaima na wurin gyara, sakamakon dan buga tan da Fatima ta yi wajen koyon tuki.

Wani farin ciki ne a kasan zuciyar Fatima, kasancewar an fada mata Mama ta iso ba da jimawa ba, shi ya sa ma ta kosa su isa, ji take yi mai keken ma baya sauri.

Dakin Zainab suka fara yi wa tsinke, ba laifi ta dan warware ba kamar jiya ba, ita ce ma ke shaida musu Jamil na dakin Mama, lokacin da Fatima take tambayarta ta ga mota a waje kamar ta shi.

Daga yadda suka same shi a tsugunne a gaban katifar Mama ta san fada ake mishi, ganinsu ne ya sanya Mama yin shiru.

Cike da girmamawa Umaima ta gaishe da Mama, sannan ta juya kan Jamil wanda yake niyyar fita, a ciki ta ce “Ina wuni?”

Shi ma a cikin ya amsa hade da karasa ficewa daga dakin.

Bayan gaishe-gaishe da tambayar mutanen gida, suka shiga hira, wanda har ya kaisu biyar da rabi na yamma, a lokacin ne Umaima ta ce za ta je wurin mai gyara, idan ya gyara motar za ta karɓa daga nan ta wuce gidan Aunty Halima.

Fatima ta yi mata rakiya har sai da ta samu napep, inda Beauty ta saka kuka dole ta tafi da ita.

Lokacin da ta dawo gidan kai tsaye dakin Mama ta shiga, hade da zama a kan sallaya tana fadin “Wai laifin me Ya Jamil din ya yi?”

Bayan Mama ta canja fuska zuwa damuwa ta ce “So yake ya koma wannan Indiya din, ni kuwa ba na so Sam.”

“Mama ci gaban shi ne fa”

“Ina ci gaban yake a nan, gida ba ta ƙoshi ba a kai da wa, da bakinshi ya ce likitoci irin shi sun yi karanci a nan Kasar , shi ne kuma zai kwashe zuwa wata Kasar daban.”

Mikewa Fatima ta yi daga kwancen da take tare da fadin “Mama! Aiki a Kasar nan tamu fa sai mu din kawai, amma idan kika yi comparing da aiki a kasashen waje gaskiya ba kowa ne zai iya ba, musamman Ya Jamil da ya dandano na wata kasar ya ji, dole ya ji na nan ba dadi. Kin ga ba kayan aiki, kuma babu albashi mai tsoka, babu wani dan alawus, albashin ma wasu sai su kwashe watanni ba a biya su ba. Idan ba a nan Kasar ba, ina kika taba ji an ce likitoci na yajin aiki?”

Shiru Mama ta yi alamun nazari kafin ta ce” Ya yi hak’uri da nan din Fatima, ni dai ba na son tafiya nesan nan. Idan ma ya zama dole sai ya tafi din, to ya tafi da matarshi. Ba na son auran ba’indiyar nan, kuma tun da ya dawo nake mishi maganar aure amma fir ya ki. So yake ya kara samun dama ya gudu Indiyar ya kuma kwaso min wata, ya tara min mutane dole in hakura in karba. “

“Ni kuwa kin san ina yi mishi sha’awar auran wata. “cewar Fatima tana yar dariya.

“Wacece?” Mama ta yi saurin tambaya.

“Umaima, wacce ta fita yanzun nan” cike da kwarin gwiwa Fatima ta fadi hakan, kafin ta dora da.

“Wlh tana da hankali Mama zasu dace sosai, kuma kin ga irin aikinsu daya, ita ma ba ta da hayaniya. Don Allah ki mishi magana ya neme ta Mama.” a shagwabe ta karasa maganar.

Inda Maman ta zuba mata ido, ba tare da ta ce komai ba.

Dalilin da ya sa Fatima ta kuma dorawa,” Allah Mama tana da hankali sosai. “

“To ai lamarin ne Fatima naku na yaran zamani sai a hankali, bar shi dai ya nemo da kanshi.”

“Don Allah Mama kisa ba ki ya neme ta” cikin shagwaba Fatima ta kuma fada.

“Ba zan sanya ba ke, ke lokacin da na sanya baki, ki aure shi me ya sa ba ki aure shin ba, sai shi ne zan takuramawa ya auri kawar ki, ke ma ki ji yadda na ji a can baya.”

Kafin Fatima ta yi magana Jamil ya shigo dakin, hakan ya sa ta mike zuwa dakin Zainab.

A can ta yi sallahr magariba, kafin Jamil ya ce ta fito ya sauke ta.

Ji ta yi kamar ta yi kwanciyarta, amma tuna Beauty na wurin Umaima dole ta fito suka wuce.

Bayan ya yi parking ne ta yunkura da nufin bude kofar ta fita, maganarshi ta dakatar da ita.

“Me ya sa kike son haɗani da yarinyar can ne wai?”

Duk da ta fahimci ina maganarshi ta dosa, hakan bai hana ta fuskewa ba ta ce “Wace kuma yarinyar?”

Kallon da yake mata ne ya sanya ta kawar da kai gefe tana kumshe dariyarta.

“Kar ki kara fadawa Mama komai a kaina gami da wata, kawarki can, ke har kin san abin da ya fi dacewa da ni?”

Shiru ta yi cikin nazarin kalamanshi, kenan Mama ta yi mishi maganar Umaima, alamun ta matsu ya yi auran. To menene laifin Umaima? Idan a da can baya ita ya ki ta ne, saboda rashin nutsuwarta, Umaima kam a nutse take, ga kyau, ga kuma ilmi.” shi ya sani, ana nuna mishi annabi yana runtse idanu” a badini ta yi maganar, a zahiri kuma cikin kasa da murya ta ce “Allah Ya ba ka hakuri.”

Tsoki ya ja hade da fadin “Jiranki nake yi tafiya zan yi” Ya fada a fusace ganin ba ta da niyyar fita.

Yunkurawa ta kuma yi a karo na biyu, jiki a mace zuwa waje, ta na kokarin rufe mishi kofar ne, motar Umaima ta danno kai, hakan ya sa dole ya dakata da fitar da yake shirin yi, hade da gyara parking don ba ta damar Parker tata motar.

Ta fito sabe da Beauty ba tare da ta kalli inda suke tsaye ba ta wuce daki abun ta.

Shi ma ficewa ya yi daga gidan, ba tare da ya kara cewa komai ba.

A wani kasalance Fatima ta karasa dakin Umaiman, don ta san tana ciki, a lokacin kuwa har ta zare kayanta, sai towel ne a jikina iya gwiwa, yayin da Beauty ke kwance a tsakiyar katifa tana bacci.

Bin jikin Umaiman ta yi da kallo, subul a goge, sambal ba wani tabo ko makusa. “To ina laifin wannan halitta? Shi ya samu wannan halittar ai gata ta yi mishi” ta fada a zuciyarta lokacin da take zama gefen mattress din.

Umaima da ke kokarin hada tea ta ce “Ya na gan ki jiki a mace ko jikin Zainab din ne ya tashi?”

Girgiza kai Fatima ta yi alamar a’a, kafin ta ce “Ina ma ki daure, ki aje komai ki farauto min zuciyar Ya Jamil, ya kamu sosai irin sai yadda kika yi da shi din nan, Lallai da a duniya Umaima kin gama burge ni.”

Ta dakata da juya tea din da take yi kafin ta ce “Me ya sa?”

“kawai dai hakan nake so ya faru.”

“Saboda kin kai masa tallata bai karɓa ba?” Umaima ta tambaya hade da zama kan kujerar karatunta tana sipping din tea din a hankali.

Harara Fatima ta aika mata, ba tare da ta ce komai ba.

“Na fa sani Mom Beauty, kin yi Jamil maganata, wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa yake sha min kamshi. Ni ba ki kyauta min ba.” cewar Umaima bayan ta dakata da shan tea din.

Warware veil din da ke kanta fuskarta ta yi kafin ta ce “Ban kai mishi tallarki ba wlh, ki yarda da ni, amma har a zuciyata ina son shi da ke, shi nake so da ke, ba wai ke da shi ba, saboda idan ya aureki, na tabbata ya yi dacen matar da Mama take fatan ya samu, ke ma kuma na tabbata kin dace miji. Shi ya sa yau da Mama ta tayar da maganar auran shi na yi mata gulmar abin da ke zuciyata. “

“Shi ne sai ya ce baya so? “Umaima ta tambaya idanunta zube a kan Fatima.

“Bai ce ba ya so ba, sai dai kawai yana kallon na yi kankanta ni in zaba mishi matar da nake ganin ta dace da shi. Ni kuma shi ya sa nake so, ki aure shi, ko ya gane bambancin gayan fura da na gumba.”

Baki Umaima ta tabe, kafin ta ci gaba da sipping din shayinta a hankali ba tare da niyyar kara cewa komai ba.

Dalilin da ya sanya Fatima gyara kwanciyarta a kan katifar sosai, hade da zaro wayarta da ke vibration a cikin jaka.

Ganin Mustapha ne, kwanciyar ta kuma gyarawa, hade da manna wayar a kunnenta bayan ta daga.

“Ya kike?” ya fara tambayarta, bayan ya amsa sallamarta.

“Alhamdulillahi. Fatan kuma haka”

“Ya karatun?” ya kuma tambayarta ba tare da ya amsa tata tambayar ba

“Muna fama”

“Mama ta koma?”

Sai da ta yi murmushi kafin ta ce “A’a.”

“Amma ba anan za ta zauna ba, har Zainab ta yi arba’in ko?”

“Me ye damuwarka ne?” ta tambaya, lokacin da take kunshe dariyarta.

Ya dan bata fuska kamar mai niyyar shagwaba tare da fadin “Ai ke ma kin sani”

Dariya ta yi kafin ta ce “Sati daya kacal za ta yi, ai gida za a mayar da Zainab din.”

“Yauwa. Kin san na ce ba zan zo ba, idan Mama za ta yi arba’in kam, na tabbata sai na zo, don za ta fara fada, na yada mata Auta ko zuwa ba na yi. Ba Ta san Autar tata ce ke ta ban wahala ba. Yanzu Mama sam ba ta ganin laifinki, ko irin yar karar nan ba ta min.”

Dariya Fatima ta yi, hade da fadin “Ta gaji da yi ma ne.”

“Da gaske kam yanzu tare miki fada take yi.” cikin dariya shi ma ya fada

“Yaushe Exam din ma?” ya tambaya bayan ya dakata da dariyar.

“Yau saura sati”

“Please Fatima, don Allah ana gamawa ki taho nan.”

“Ina son zuwa gida Ya Mustapha, na rabu da zuwa.”

“To wa za ki gano a gidan, ina Mama? kuma ba ga ta nan kuna tare ba. Su Aunty Aisha ne na tabbata suma suna hanyar zuwa.”

“Ina son ganin ƴata ta ruwan sanyi Ummi” cikin siririyar dariya ta fada.

“Oho! Ni dai na fada miki ba zan zo ba. Ina Beauty da Auntynta?”

“Beauty na bacci, Auntynta kuma tana jin ka. Fada muke yi ma. “

“Wa ke shiga tsakaninku, ki gaishe ta.”

“Za ta ji.” ku san a tare suka yanke wayar.

Umaima da take sauraron wayar tasu ta ce “Kin ga irin kalar mijin da nake son aure, muna wasa da dariya cikin nishadi, ya rika ririta ni kamar sarauniya, amma ba mutum kullum fuska kamar bala’i ba, yana wani shan kamshi kamar wani sarki. “

Dariya Fatima ta yi kafin ta ce “Ya Jamil mutum ne mai saukin kai.”

“Kin san da haka me ya sa to tun farko ba ki aure shi ba?”

“Gori za ki min?”

“Eh.” Umaima ta amsa gami da harararta.

“Sha Allah ke da Ya Jamil, sai kun zauna a karkashin inuwa daya ta ma’aurata.”

“Ba mamaki, idan ya sauke girman kanshi ya roki hakan “

“Lokaci yana zuwa, kuma zai yi hakan sha Allah.”

Ganin Umaima ta shige toilet,, ita ma sai ta mike zuwa nata dakin.

A cikin kwanakin kullum Fatima sai ta je gidan Zainab saboda Mama, sai take jin kamar tana Sandamu, musamman dasu Aunty Sadiya suka zo, kwana suka yi, ita ma a ranar sai ta kwana a gidan aka sha hira, wanshekare suka tasa Zainab zuwa Sandamu. Ita ma ta dawo gida don shirin fara exam gobe Alhamis.

******

Yau kam da wuri ta shirya saboda tana son kai Umaima asibiti ba ta jin dadi, kuma a ranar ne take rubuta exam din ta, ta karshen 1st semester 300L.

Misalin karfe goma na safe tsaye take jikin mota, sanye da doguwar riga golden yellow , yanayin rigar sai ya kusan sajewa da hasken fatarta .

Musamman yadda ta nada veil din a kan fuskarta.

Umaima take jira su wuce asibitin, saboda karfe shadaya za ta shiga exam.

Ita ma Umaiman sanye da army Green din doguwar rigar ta fito, ba ta nada veil din ba, dorashi kawai ta yi a Saman kanta.

A hankali take takowa, har zuwa inda Fatiman take tsaye.

“Ina Beauty din?” ta tambaya dakyar.

“Na mika ta gidan Baba. Ya jikin naki to?”

“Akwai sauki.”

“To aike matsalarki ba kya shan magani ba kya son allura, ban san ta ya kike son ki warke ba, kuma ke kin iya matsawa mutum ya sha.

Bata rai Umaima ta yi, amma ba ta ce komai ba.

“Shiga mu je” Fatima ta ba ta umarni, lokacin daya kuma tana shiga driver seat. Rai bace, saboda sosai Umaiman ta bata mata rai daga jiya zuwa yau, saboda rashin shan maganin nata.

A hankali take tukin, suka fice daga gidan, asibitin da Umaima ke zuwa casual ta fara sauke ta, kafin ta dawo makaranta bayan ta jaddadawa Umaima lallai ta ga likita kamar yadda suka tsara tun farko.

Misalin karfe 4:30pm suka fito papern karshe, ga yunwa hade da gajiya sun rufarwa Fatima, wani ma irin ciwo kanta ke yi, sallah kawai ta yi, ta nufi asibitin, yadda hankalinta ke kan Umaima baya kan Beauty haka, saboda ta san Beauty ƙalau take, kuma tana samun kulawa.

A farfajiyar da aka tanadar don yin parking, ta Parker motar, ba tare da ta fito daga ciki ba, ta shiga kiran layin Umaima.

Ba jimawa kuwa ta daga.

“Kina ina?”

“Pediatric” Umaima ta ba ta amsa a hankali

Sai da ta rufe ko ina, sannan ta fito sabe da karamar jakarta, a hankali take taka wa saboda gajiyar da ta yi.

A nurse station ta samu Umaima kwance.

“Wai har yanzu jikin?”
Ta yi saurin tambaya, ganin yadda Umaima take kwance kudundune cikin farin bedsheet din gadon.

“To ba ta son magani ai” wata daga cikin nurse din ta ba ta amsa.

“Ba ta ga likitan ba?” Fatima ta kuma tambaya cike da jimami.

“Ta ki zuwa, kuma an ba ta magani ta ki sha. Test ma ta ki yarda a yi mata. ” wata daga cikin nurse din ta kuma ba Fatima amsa.

Cike da jin haushi Fatima ke kallon Umaima kafin ta ce” Wlh kina da matsala, ke kam kin iya matsa ma wani ya sha, amma ke ba ki son sha, ai sai ki tashi mu tafi gidan ki kwanta, ni kuma ina yi miki sannu tun da haka kike so, kuma kar ki manta gobe dai kina da jarabawa. “

Babu wanda ya yi magana, illa zubawa Umaima ido da suka yi, tana sakkowa daga kan gadon dakyar.

“To ina za ki kai musu zanen gadon? “Fatima ta tambayi Umaima ganin ta mike lullube da zanen gadon kuma tana niyyar tafiya.

Wasu daga cikin nurse din suka dan murmusa, yayin da wasu kuma suke mata sannu.

Nade a cikin bedsheet din suka fito, Fatima na rike da ita.

“Ina ne office din Ya Jamil?” Fatima ta tambayi Umaima a lokacin da suke tafiya.

“Oho!” Umaima ta amsa a hankali.

Hakan ya sa Fatima saurin kallon ta, saboda ta tabbata ta san inda office din yake.

Da tambaya aka kwatanta mata office din, lokacin mutane uku ne a waje, alamun suna jira a duba su.

Wayarta ta fitar hade da shaida mishi tana kofar office din shi.

Ya dauka da wasa take yi, dalilin da ya sanya shi fitowa, hannunsa rike da wayar. Ganinta a kofar office din da gaske sai ya dan fadada murmushinshi hade da karasowa kusa dasu.

Da Fatima suka gaisa, ya tambayeta Beauty da kuma exam.

Ta amsa mishi da Alhamdulillahi. Kafin ta ce “Umaima ce ba ta da lafiya, tun safe na rakota asibitin a kan taga doctor, idan na fito exam zan biyo mu tafi, ka ga har na fito daga exam din ba ta ga likitan ba.”

Ya mayar da hannayensa du biyun cikin aljihu yana kallon Umaima wacce take kunshe cikin zanen gado, ta kwantar da kanta a kan daya daga cikin kujerun da ke kofar office din Jamil din.

“Me ya sa ba ta ga likitan ba? ” ya tambaya a hankali, wannan karon idanuwansa a kan Fatima.

“Wai ba ta son allura da shan magani” cike da haushi Fatima ta amsa.

Tabe baki ya yi, kamar ba zai tanka ba, sai kuma ya ce “To me kike so yanzu?”

Ta dan marairaice “Don Allah ka duba ta”

“Ni ma abu biyun zan yi mata, kuma ba ta so”

Karon farko da Fatima ta kalli Umaima, ganin har lokacin idanunta a rufe ne, a hankali ta ce “Ka yi mata jan ido, tsoronka take ji”

Da alama bai san murmushin ya subuce mishi ba, dalilin da ya sanya shi juya zuwa office din tare da fadin “I’m coming.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 56Daga Karshe 58 >>

1 thought on “Daga Karshe 57”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×