Skip to content
Part 18 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Wayar ta ɗauki daƙiƙu a caji kafin ta ɗauka. Har ya ɗaga ƙafa zai wuce, sai kuma ya yanke shawarar kunna wayar. Ya san ba ƙananun kira ya rasa ba a cikin kwanakin da wayar ta shafe a kulle. Ga kuma rasuwar da aka yi mishi, abokan arziki da yawa za su kira a waya, wasu kuma za su turo saƙonni don yi mishi gaisuwa. Da waɗannan dalilan yasa shi kunna wayar, da niyyar bayan ya kunna ya barta tana caji saƙonni na sauka a hankali.

Abu ɗaya da ya manta shi ne saka wayar a matakin shiru ta yadda ƙarar shigowar saƙonni baza su hana shi sukuni ba. Karatun Alƙur’ani yake so yayi, tun bayan da suka ziyarci kabarin Ummee da jin labarin yadda har ta bar duniya tana kewarsa da mararin ganinsa ya ɗaukar ma kansa alƙawarin sauke mata Alƙur’ani a cikin kwana bakwai. Don haka yini yake ya kusan kwana yana karatu.

Ko a ƙofar gida yake zaune gurin karɓar gaisuwa za’a same shi da Alƙur’ani a hannunsa yana karantawa a hankali. Himma ba ta ga rago, cikin kwanaki biyu da dawowarsa kwanaki uku da rasuwar Ummee har ya karanta Izufi goma sha biyar.

Ƙarar shigowar saƙonni a wayarsa ce ta dame shi, duk yadda yake sharewa ya kasa jurewa, a dole ya ajiye Alƙur’anin ya matsa kusa da wayar da niyyar saka ta a silent. Yana buɗewa karaf idanunshi suka sauka kan sunan Rufaida, ko da yayi scrolling kan saƙonnin sai yaga saƙonninta sun fi na kowa yawa.

Haka kawai zuciyarsa ta kwaɗaitu da son duba abinda za ta faɗa mishi bayan duk wannan tashin hankali da ya shiga ita ce sila. Saƙonninta ya buɗe tun daga ranar da ya tafi, ya fara karantawa ɗaya bayan ɗaya. Saƙonnin farko-farko duk na ban haƙuri ne kan yadda a sanadiyyarta yabar gida, don tana da labarin su Ibbu sun neme shi sun rasa. Daga baya kuma duk saƙonnin da ta aika ɗauke suke da kalaman soyayya, tana faɗa mishi irin matsanancin son da take mishi ba tare da ita kanta ta san tayi nisa a cikin son shi haka ba.

Taɓe baki yayi, ko kusa saƙonnin basu ɗaɗara shi da ƙasa ba. Shi fa daman Allah ya sani bawai yana wani irin bala’in sonta bane can can har cikin ransa. Kawai dai ita ɗin ta yi kalar matar da yake burin yin rayuwar aure da ita ne, ɗari bisa ɗari. Yana tsananin son mace mai masifar yanga da ƙwalisa, balle idan ta haɗa da shagwaɓa cikin ƙanƙanin lokaci za ta tafi da imaninsa. Abubuwan da ita kuma Ziyada ta rasa kenan.

Faruwar wannan lamarin na nemanshi a hallaka shi kan Rufaida yasa shi jin gaba ɗaya ta fice masa arai. Da farko ko da mahaifiyarta ta aika da kashaidin ya rabu mata da ƴa, ya zaci kurari ne kawai za’ayi a gama kamar lokacin da ya fara neman Ziyada. Amma sai yaga wannan zazzafan al’amari ne da ya girmema wancan nesa ba kusa ba, don haka shi kam ya rabu da ita har abada.

Ko da ya gama karanta saƙonnin taɓe baki yayi, ya haɗa da jan tsaki ƙasa ƙasa ya cigaba da duba saƙonni, waɗanda daga na kamfanin layukan waya, sai na ƴanmatansa da ko da yai aure bai daina kula su sama-sama ba, sai kuma na abokansa da jama’ar unguwa suna mishi jaje da addu’a kan rasuwar mahaifiyarsa.

Ko da ya gama duba saƙonnin maimakon ya ajiye wayar sai ya kunna data ya shiga kafafen sada zumunta. Ko da ya leƙa whatsapp yaga saƙon gaisuwa sun fi yawa sai ya fita ya koma Facebook.

Ƙirjinsa ya buga daram, ba don komai ba sai don posting ɗin da ya fara arba da shi a facebook ɗin. A tsugune yake yana duba saƙonni, saboda tashin hankali bai san sa’adda ya zauna ba.

Kyakkyawan hoton Rufaida ne tana murmushi a ƙasan hoton aka sanar da rasuwarta kwanaki uku da suka wuce. Jikinsa na kyarma ya latsa posting yana bibiyar comments na mutane kan rasuwar, ga tsammaninsa zai ga ana ƙaryata batun rasuwar, sai yaga fiye da comments dubu biyu duk addu’a ake Allah ya gafarta mata. Hankalinsa ne ya ƙara tashi da ya lissafa yaga ai rana ɗaya ne rasuwar da na Umminsa.
_’Za’a rasa rayuka biyu, da na wanda kake matuƙar so, da na wanda kake yiwa soyayya sama-sama.’_
Ya tuno maganar da Malaminnan ya faɗa mishi.

Nan take ƙwaƙwalwarsa ta buga ɗaya bisa biyu ya gano abinda yake faruwa. Ran wacce yake matuƙar so Ummee ce. Ran wacce yake yiwa soyayya sama-sama Rufaida kenan. Ashe duk su biyun mutuwarsu ba na Allah da Annabi bane? Ashe shi ne sanadiyyar mutuwar Ummeensa da yake matuƙar ƙauna? Bai san kuka yake yi ba sai da yaji ɗanɗanon gishiri-gishiri na hawaye ta gefen bakinsa.

Kiran da ya shigo cikin wayarsa da baƙuwar lamba shi yasa shi sassauta kukan da yake yi, daƙyar ya iya ɗaga kiran ya kara wayar a kunnensa. Ya kasa magana, sai sauke ajiyar zuciya da yake yi akai-akai.

“Hello, Hello”
Aka faɗa daga can ɓangaren.

Shiru yayi bai amsa ba, sai da aka sake cewa
“Khamis? Kana ji na?”

“Ummm”
Ya amsa daƙyar, kamar mai ciwon haƙori.

“Ka gane mai magana kuwa?”
Aka tambaya daga can ɓangaren da murya mai bayyana mamaki. Kafin ya amsa sai kuma aka sake cewa
“Duwan ne, na san baka gane ni ba shi yasa baka amsa ni dakyau ba. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya?”

“Lafiya ƙalau.”
Ya sake amsawa a cije.

“To ya haƙuri? Mun samu labarin ka tafi kaduna. Ashe Allah yayi ma Mahaifiyarmu rasuwa, Sorry! Allah ya gafarta mata yasa ta huta.”

“Ameen.”
Ya sake amsawa daƙyar, zuciyarsa cike da jin haushin Duwan ɗin, saboda duk shi ne Ummul-aba’isin faruwar lamarin, da bai kai shi gurin hatsabibin malamin nan ba, da bai amince ayi aikin nan ba, da yanzu Ummee tana raye. Da bai jefa kanshi a cikin wata iriyar rayuwa da da can ba’a kan turbar yake tafiya ba. Tuno irin manyan matsalolin da ya gamu da su a dalilin haɗuwa da Duwan da Hadi yasa shi kasa cigaba da amsa wayar. Sai kawai ya katse kiran ba tare da sunyi sallama ba.

Daga can ɓangaren haɗa idanu suka yi su uku suka kwashe da dariya.

“Yi sauri ka tura mishi saƙo, ka tunasar da shi tunda ya shigo cikinmu fa ya shigo kenan. Ba komawa baya, babu ɗaga ƙafa, babu tuba, babu zancen sai sa’adda na so zanyi aiki. Duk sa’adda aka neme shi kawai zai zo ne, don daman aikinsa kenan.

Abinda bai sani ba shi ne tunda yasha ruwan bunu ko ya ƙi ko ya so aiki dole ne tsakaninmu da shi. Kuma tunda na kasa hajarshi manyan matannan suka saka rububi ya lashe jarabawar da aka yi mishi kenan, aiki tsakaninmu tabbataccen abu ne da ba yadda za’ayi ya fasu matuƙar ba mutuwa yayi ba. Ka faɗa mishi yana da ƙarin kwanaki biyar ne kacal a gaba, su ma kwanaki biyar ɗin na ƙara mishi ne kawai saboda mutuwar gyatumarsa. Ka jaddada mishi lallai duk abinda yake yi ya tabbatar a rana ta shida ya dira Abuja gurin Hajiya, tana can tana zaman jiranshi.”

Kakkauran mutumin da yake matsayin Oga a gare su ne ya faɗi haka idanunshi akan Duwan.

“Angama Oga, yanzunnan zan aikata kamar yadda ka ce. Har ma da ƙarin kalaman da zai san lallai fa duk abubuwan da ya ji, ya gani ba da wasa ake mishi ba.”
Duwan ya amsa a ladabce yana murmushi.

Mintuna biyar ya ɗauka wajen tura ma Khamis saƙon, ɗauke da maganganu masu firgitarwa da kaɗa hanjin wanda bai saba shiga cikin manyan cakwakiya ba. Sai da ya tabbatar saƙon ya shiga sannan ya ajiye wayar ya mayar da hankali kan Ogan suka cigaba da tattauna abubuwan da ke gabansu.

*****

Kwanci tashi ba wuya. Yau Ummee ta cika kwanaki bakwai da rasuwa. Anyi addu’a a masallaci, sa’annan anyi a ƙofar gida. Tun cikin dare Ummanmu da sauran dangi kwana sukai suna soye-soye abin sadaka da za’a raba na addu’ar bakwai.

Bayan anyi addu’a a masallaci kuma akayi raɗin sunan Babyn da Ziyada ta haifa, Nauwara sunan Ummee ne. Don haka Yusuf ya raɗa ma Babyn suna Khadija, sunan Ummanmu.

Har a ran Khamis ba sunan da yaso ba kenan, sunan Rufaida yaso saka ma yarinyar, amma sai bai furta ba. Ya ƙudurce a zuciyarsa in sha Allah kafin a gama mishi haihuwa zai saka sunan Rufaida, bazai taɓa manta ƙaunar da yarinyar ta gwada mishi ba.

Kafin la’asar ƴan’uwa da abokan arziki gaba ɗaya sun koma gidajensu, Hajiya matar Alhaji Bashir da tun da suka zo bata koma ba sai da aka yi bakwai, zuwa ƙarfe uku har ta kira a waya ta sanar da su ta isa gida lafiya. Wacce ta rage kawai Innarsu ce da tayi jinyar mahaifiyarsu.

Ita kam za ta zauna har sai anyi arba’in, saboda Ziyada mai jego, idan ta gama wanka za ta koma gidanta, ita kuma Ziyada za ta cigaba da zama a gidan har zuwa sa’adda Yusuf zaiyi aure, a lokacin za su yanke shawarar cigaba da zama tare ko kuma za su koma gidansu.

Bayan magriba gaba ɗayansu suna zaune a falo, ɗan tattaunawa suke kan rayuwa da yadda lamurar rayuwar ke tafiya cikin daɗi da rashin daɗi.

Kwatsam Khamis ya ce
“Gobe idan Allah ya kaimu zanyi sammakon tafiya Abuja…”

“Abuja? Lafiya dai ko?”
Suka haɗa baki su ukun gurin tambayarsa. Kafin ya amsa Yusuf ya ƙara da cewa
“Me za ka je yi a Abuja?”

Yasan zai fuskanci waɗannan tambayoyin daga gare su, don haka tun kafin ya faɗa musu zaiyi tafiyar ya shirya duk amsar da zai faɗa musu.

“Lafiya ƙalau ne fa. Ku kwantar da hankalinku, in Allah ya yarda tafiyar alkhairi ce. Watanni huɗu da suka gabata akwai wani abokin Oga Mu’azu (Ogansu a hukumar alhazai, inda yake aiki.) da muka haɗu da shi anan gurin aikinmu, ina gyaran wasu takardu a Ofis ɗin Oga ya shigo, sanadiyyar haɗuwata da shi kenan. To kun san dai ikon Allah da haɗuwar jini, da kuma idan Allah ya tsaga da rabonka a jikin mutum.

Tun a lokacin yace na burgeshi saboda yadda na karɓeshi cikin haba-haba da girmamawa. Ya kuma hangi zafin nama da kazar-kazar a tare da ni. Umrah zai tafi a lokacin, sai ya karɓi lambata ya ce idan ya dawo zai neme ni in je Abuja in same shi. Idan ina da rabo za’a duba a cikin kamfanoninsa a samu inda za’a cilla ni da yafi wannan ƙaramin aikin da nake yi a hukumar Alhazai.

Ko da ya dawo bai neme ni ba don haka ni ma na manta da al’amarinsa, sai shekaran jiya kwatsam ya kira ni wai in je da gaggawa, bayan na faɗa mishi rasuwar Ummee sai yayi min gaisuwa yace idan anyi bakwai in tafi washe gari. Kun ji abinda zai kaini kenan, don haka ku taya mu addu’a in da rabo sai kuga mun samu wani babban harka da za mu maƙale ma.”

Da fara’a a fuskokinsu suke mishi addu’ar dacewa da fatan alkhairi. Inna Saude da Yusuf suka ƙara da yi mishi nasihar ya riƙe gaskiya da Amana, indai ya riƙe waɗannan abubuwa biyun to da yaddar Allah duk inda ya shiga zai ɗaukaka, kuma maƙiya da mahassada baza su taɓa cin galaba a kanshi ba da yaddar Allah.

A daren ya harhaɗa kayayyakinsa cikin ƙaramar jaka. A yadda ya tsara, bazai wuce kwanaki biyu ba idan ya tafi. Amma saboda sanin halin tafiya kafin kayi kai ke da ita, idan kayi tafiyar sai yadda tayi da kai sai ya ɗauki kayan da za su ishe shi ya kwana huɗu.

A daren ya shiga gidan Ummanmu yayi sallama da ita. Ita kam babu wani ɓoyo ko jin kunya ƙarara ta fito fili tayi mishi nasiha kan irin harkar neman matan da yake jefa kanshi, a matsayinsa na yaro ƙarami.
“Ni bazan hana ka ƙara aure ba don kana auren Ziyada, idan kaga yarinyar da kake so, kuma ka tabbatar iyayenta za su baka aurenta kazo ka faɗa min. A matsayina na Uwa zan shige maka gaba sai inda ƙarfi na ya ƙare, in Allah ya yarda. Amma don Allah ka nutsu Khamis, ka ga ko baka tara shekaru ba girma ya kama ka, ƴaƴanka biyu, ga shi kun fara da haihuwar ƴaƴa mata da suke tsananin buƙatar kulawa da taka-tsantsan wajen tarbiyyah. Don girman Allah ka kiyaye ka ji Khamis? Kar ka kuskura makamancin abinda ya faru har yayi sanadiyyar ƙara ruruta rashin lafiyar Marigayiya ya sake faruwa nan gaba.”

“In sha Allahu zan kiyaye Ummanmu. Ayi haƙuri, a taya mu da addu’a. Da yaddar Allah bazan sake ba.”
Ya faɗa a kunyace. Kanshi a ƙasa, ji yake ina ma ƙasa za ta tsage ya shige don kunyar munanan tabban da yayi ma kansa da kansa.

Tun bayan tafiyarsu Kano Nauwara tana gurin Ummanmu, har yanzu. Duk da tayi barci, haka ya buƙaci a taso mishi ita ya ganta suyi sallama, ko da ya dawo garin tashin hankali da damuwar rashin Ummee bai sa shi neman yarinyar ba.

Sun rabu lafiya. Ummanmu da dattako har da ƙara mishi dubu biyar wai yasha ruwa a hanya, duk da ya faɗa mata yana da isassun kuɗi sai da ta takura mishi ya karɓa. Godiya sosai yayi mata kafin ya fice daga gidan, zuciyarshi cike da farin ciki.

Tun ana gobe zai tafi an saya mishi ticket na jirgin ƙasa, gurin zaman manyan mutane. Jirgin da zai hau na safe ne, don haka ƙarfe takwas na safe a filin jirgin tayi musu shi da Yusuf.

“Yanzu idan ka tafi sai yaushe kenan?”
Yaya Yusuf ya tambaye shi yana kallonshi da idanu masu cike da ƙauna.

“Ban sani ba Yaya. Amma dai duk yadda ake ciki ina sa ran bazan wuce jibi ba. Ko ma dai menene zan ke sanar da ku halin da ake ciki ta waya.”

“To shi kenan! Allah yasa a dace ya tabbatar da alkhairi.”

“Ameen ya Allah”
Ya amsa fuskarshi na bayyana jin daɗin addu’ar.

Sallama suka yi, Yusuf har ya juya zai wuce sai ya dawo gurin Khamis ɗin ya riƙo hannuwansa guda biyu.
“Ƙanina abin ƙaunata, ina roƙonka don girman Allah duk inda ka shiga kuma duk abinda za ka aikata ka dinga tuna mu biyu ne kacal muka rage ma junanmu a duniyar nan. Ka tausaya min, Ummee ta damƙa min amanar ne ba tare da ta san ni ɗin ba ni da faɗin ƙirjin da zan iya ɗaukar duk rikicin da za ka ɗakko ba. Ina maka nasiha kaji tsoron Allah, ka guji haram duk yawanta. Ka riƙi halal komai ƙanƙantarta, ka guji duk abunda kasan akwai shubuha a cikinta. Ka taimaka min ka taimaka ma matarka da ƴaƴanka, ka kawar da idanunka daga kan duk wata ƴa mace da ka san ta fi ƙarfin ajinka, don Allah Khamis ka rufa mana asiri mu rungumi maraicinmu mu zauna lafiya.”

Da Yusuf da yake nasihar, da Khamis da ake yima nasihar duk idanunsu cika suka yi da hawaye. Jikinsa a sanyaye ƙwarai ya ƙarasa jikin Yaya Yusuf ɗin ya rungumeshi.

Ya kasa magana, zuciyarsa cike da tsanar kansa da kansa. Tsawon wasu daƙiƙu suna rungume da juna kafin ya zare jikinsa a hankali. Hannu ya ɗaga masa alamun bye bye sannan ya juya da sassarfa ya shige can cikin filin jirgin, ko waiwayen Yusuf bai ƙara yi ba.

“Wannan tafiyar ita ce Mafari, mafarin buɗewar duk wasu munanan harkoki da shi kanshi Khamis da yasan farkon faruwarsu bazai ce ga ƙarshensu ba. Mafarin da ya jefa rayuwar zamantakewar auren Ziyada cikin walagigi da bala’in tashin hankali. Ƴaƴa uku da ta ƙara haifa bayan biyun da take da ta haife su ne cikin firgici da rashin nutsuwa. Mafarin buɗe sabbin matsalolin da Yusuf bai taɓa shafe watanni shida cif ba tare da an kira shi kan wani rikici da Khamis ɗin ya ɓallo ba. Kuma har yau da aka shafe shekaru takwas da farawar al’amarin tsakanin Ziyada da Yusuf babu wanda zai ce ga tsayayyiyar harkar Khamis. Ya daina aiki a hukumar alhazai tuntuni, amma yana samun kuɗi sosai fiye da yadda ake tsammani, wai don ma garin banza a farau-farau ɗin banza yake ƙarewa. Abu ɗaya zuwa biyu dai da idan aka ritsa Ziyada za ta iya bayar da tabbaci akai shi ne yana neman mata, sa’annan kuma yana taɓa harkar Kawalci. A bayan wannan abu biyun bata san komai ba, da suwa yake harƙallah? Bata sani ba. Me ke kai shi Abuja duk bayan sati biyu? Bata sani ba. Me ke kai shi kano duk ƙarshen wata? Bata sani ba. Wacece Big Aunty da take yawan kiranshi itama yake yawan kiranta? Bata santa ba. A cikin waɗannan shekarun, Yusuf yayi aure, yana da yara biyu duk maza. Bayan gama karatunsa harkoki sun buɗa ya samu babban aiki a gwamnatin jiha, ya gina gidansa babba mai kyau sun tare da iyalansa. Shi ma Khamis ya sayar da wancan gidan da babansu ya siya masa, ya sayi wani a unguwar sunusi, nan suke zaune yanzu tare da iyalansa. Gidan gadonsu sun zuba ƴan haya a ciki. Ummanmu ta rasu shekaru huɗu da suka wuce, Aunty Kareema da Aunty Ruƙayya duk suna gidajen mazajensu, Ruƙayya tana Abuja inda aiki ya cilla mijinta. Ita kuma Kareema tana kano, daman mijinta ɗan can ne.”

Cigaban labari…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 17Lokaci 19 >>

1 thought on “Lokaci 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×