Skip to content
Part 13 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Bayan komawar Taufiq gida, yayi kokarin boye bacin ransa musamman yadda yaga mujaheeda har zuwa lokacin bata dawo yadda take ba.

Saida daddare bayan Taufiq ya gama komai na al’adar rayuwarsa yazo kwanciya .
Lokacin mujaheeda itama tayi Shirin kwanciya tana gefen gadon a zauna.
Alokacin ne Taufiq ya Kira sunanta, ta amsa ahankali, sannan yace ” mujaheeda me yasa kika sanar da mahaifiyarki abinda yafaru tsakaninmu, bayan kinfi kowa sanin cewa idan kowa zai iya yimin uzuri to banda ita, idan har kina son ni da mahaifiyarki mu samu kyakkyawan alaka bai kamata ki dinga kokarin kara tura mata tsanata ba bayan tsanar data riga tayi min.”

Mujaheeda ta girgiza Kai tace, ” ni ban gaya Mata komai ba,”, ya waigo Yana kallonta yace “to ta yaya ta sani idan har ba ke kika gaya Mata ba” ta gyara zamanta tace ” gidan ta zo ta Kuma taddani a halinda dole zata San ina cikin damuwa da matsala, hakan yasa ta matsa min har saida na gaya Mata abinda yafaru.” Ya girgiza Kai yace ” mujaheeda na aureki ne don ina sonki , ba Kuma na fatan ace awayi gari na daina sonki , don haka ina son kisani ya Zama dole ki gane cewa aure kikeyi don haka dole ki dinga yin abinda zai dinga nuna ke matar auren ce, haka zalika ya Zama dole ki mutuntani ki girmama ni a matsayina na mijinki”, ta gyada Kai tace ” naji” ya Kara kallonta yace ” Abinda Haj ta je ta aikata agidanmu da irin maganganun data kirani awaya ta gaya min sun bata mun rai, Amma duk abar maganar nan komai ya wuce bana son bacin rai da tashin hankali, kije kiyi aikinki Amma ki tabbatar kin tsare kanki kin katange kanki daga dukkan abinda zai biyo baya ki kuma sani ke matar aure ce.”

Tadan dubeshi tace ” Nagode insha’Allah Kuma Zan kiyaye.” To awannan dare dai komai ya dawo dai dai tsakanin Taufiq da mujaheeda.

*****
Ranar litinin mujaheeda ta Fara zuwa aiki duk abinda yakamata Haj murjanatu ta yi tayi mujaheeda ta hau kujerar manaja ayayinda Àlh jibrin ya koma mataimakinta Wanda hakan ba karamin bata masa rai yayi ba , sai dai ya danne bai nuna ba, amma zuciyarsa har kuna take, ta yaya za’ayi ace aba yarinya karama irin wannan babban mukamin Wanda ko babba saiya dage, shin mema tasani Akan aikin .
Karfe goma shabiyu na dare ne , Alh Mustapha labaran Yana zaune atsakiyar gado Haj murjanatu tana zaune a bakin gadon gaba dayansu fuskokinsu babu alamun kwanciyar hankali, Àlh Mustapha labaran ya cigaba da magana wacce da alama ya dade Yana yinta.” Tsawon wannan shekarun kinsa abu a ranki kin aje kin kasa yafe min kin Kuma kasa mantawa, kina hango katuwar illar da hakan ya janyoma aurenmu?, Kin kasa Kara yarda Dani kin fahimci bakincikin da zuciyata take ciki kuwa!”

Ta waiwayo tana kallonsa zuciyarta na dawo Mata da munanan abubuwan da suka faru shekaru masu yawa da suka wuce, Wanda harta koma ga Allah bazata taba mantawa ba . Tace ” Kai yanzu kana tunanin Zan iya manta abinda kayi min ko na yafe maka , aah asalima duk tsawon wadannan shekarun babu ranar da zata zo ta wuce ban tuna bakin halinka ba , shiyasa kullum Muke nesa da juna , na zabi na cigaba da zaman aure da Kai cikin ràshin yarda da nuna kauna.”

Ya dubeta sosai yace ” yanzu dai kina nufin ba zaki manta ki hakura ba mu karasa cikin mutuntawa da ganin kimar juna ba.”

Tayi shuru kawai ta maida kanta kasa ya cigaba da cewa ” meye acikin rayuwar da yafiya zata zamo me wahala, to Allah ya sani nayi lefi na nemi gafarar Allah sannan na nemi gafarar ki Amma kinki to kisani ko awajen Allah bani da lefi idan ke baki yafe min ba to Shi ya yafe min, tunda ke bakar zuciya kike da ita.”

Bata ce uffan ba ta tashi ta shige bandaki.zuciyarta cike da tunani Kala Kala.halinda take ciki Yana daya daga cikin dalilin dayasa take son ta kare mujaheeda daga fadawa kunci da cin amanar namiji Kuma duk yadda zatayi zatayi domin ganin hakan ya kasance, domin ko kadan bata son yarta ta dandani daci da tashin hankalin data dandana arayuwarta.
*****
A can kauyen Durmi ta jahar jigawa, kauye ne da bai mallaki komai ba na game da ababen more rayuwa ba , kauye ne Wanda Baisan akwai wata Kalma ba wai ita romon dimukuradiyya, domin kuwa basu da hanya ba su da asibitici basu da makarantu basu da komai na jindadin rayuwa.

Acikin wani matsakaicin gida na kasa Wanda ko kofar kirki babu domin dai galan galan akasa aka sakaya kofar da ita.

Kwata kwata dakuna uku ne agidan Suma kanana ne sosai yadda babu wani wajen walawa,

Sai garken jajayen awakai atsakar gidan guda uku. Tsakar gidan kuwa babu komai sai gurbayar kasa , atakaice dai gidane daka kalla zaka tabbatar cewa gidan takakawa ne kwarai da gaske wadanda Basu fi karfin komai ba na bukatun rayuwa.

Ande Dije ce zaune Akan dutsen data Saba Zama akai kusa da dabbobinta ta cika ta batse kamar atabata ta fashe.

Dai dai lokacin Hajara ta fito daga daki rike da tsintsiya da alamar Shara zatayi, Ande Dije ta watsa Mata harara ta Fara maganganun da tunda ta zauna take yinsu sai dai idan ta gaji tayi shuru.

“Ai dole tunda ta riga ta tsotsa a nono Saita nuna ita wacece barewa zatayi gudu ne danta yayi rarrafe ni dai Allah ya dora mana masifa da ni da dana bansan Kuma ranar da zai yaye mana ba.”

Kamar koyaushe idan Ande Dije tana irin wadannan mugayen maganganun nata Hajara takan ji tamkar zuciyarta zata fita waje saboda bakinciki, tasan idan da sabo yakamata ta Saba amma da yske baa sabo da bakinciki yasa kullum abin yake sabo agareta.

Bata tanka ba kamar kullum, maimakon hakama Saita Fara share tsakar gidan Wanda hakan baisa Ande Dije tayi shuru ba ta cigaba da maganganunta ” shegiyar yarinya kamar taci kafar kare dazaran ta fita sai anganta, waye yasan abinda take aikatawa awajen tunda baayi gadon kamun Kai ba.”

Tana rufe baki, wata kyakkyawar yarinya wacce bata wuce shekaru goma sha takwas ba ta yi sallama cikin Kamala ta shigo gidan, wankan tarwada ce me cikar fuska da dogon hanci tana da matukar kyau na daukar hankali, kamar yadda Allah ya kawatata da diri kwarai.

“Inna sannu da gida” ta fada cike da nutsuwa , cike da fara’a tace ” yauwa muhseena , kin Samo ruwan”, ta wuce Kai tsaye wajen duron da take Tara ruwan , bata damu da irin mugun kallon da Ande Dije take watsa Mata ba tace ” na Samo Inna daker , mutane sunyi yawa wannan ràshin ruwa dai ya Zama masifa.”

“Ko kuma kece kika zamo masifar ba, fitinanniyar yarinya wacce bata huce takaici awa nawa da fitarki Amma ace sai yanzu zaki dawo saboda kin Zama ballagaza baki jindadin komai sai yawo ai da kinyi zamanki baki dawo ba kila da hakan yafi mana kwanciyar hankali.”

Muhseena ta juye ruwan acikin roba gami da maida bayanta ta jingina jikin garu ta runtse idonta, ta Dade bata ga tsana irin wacce Ande Dije take mata ba , duk kokarin da zatayi ba ta taba gani ba sai dai taga gazawarta,

Ande Dije ta cigaba da fadan duk abinda ya fito daga bakinta Kaida gani kasan dama can tana Jira ne. Zuciyar Haja data muhseena sai tukuki take Sam Sam Hajara bata son ta tanka Mata ko muhseena ta tanka Mata hakan yasa ta aje tsintsiyar hannunta ta dubi muhseena tace ” wuce daki”, ba tare da cewa uffan ba ta maida bokitin ta aje ta juya ta shige daki Hajara ta bi bayanta.Aysyinda Ande Dije ta cigaba jaraba sai kace wacce akayi ma wani gagarumin laifi.

Kan yar siririyar katifar dake yashe asaman dakin me kama da harshe Hajara ta zauna, yayinda muhseena ta jingina jikin bango ta runtse idanunta ta kasa tsaida hawayenta da suka Fara malala asaman kumatunta .

Cikin matsananciyar damuwa Hajara tace ” kiyi hakuri wannan jarfta ce, ina son ki sani ko wane bawa da irin jaraftar da Allah yake Dora masa , to mu dauka daga ni har ke wannan itace jarabawarmu.”

Muhseena ta bude idonta hawaye na fita tace ” jarabawa kuwa mummunar jarabawa Inna , na rantse Miki lokuta da dama nakan ji ina ma Allah ya dauki raina saboda Bana Jin Zan cigaba da jurar wannan masifar ba tare da wata Rana zuciyata ta buga ba, Inna ina cikin matukar damuwa , ina cikin damuwa” ta Kara rushewa da kuka Mai cike da ban tausayi ta zame kasa ta zauna dirshan tana cigaba da kuka sosai Mai taba zuciya.

Hakan yasa itama Hajara ta Fara zubar da hawaye, tana fadin ” kiyi hakuri muhseena,kiyi hakuri.”

Tace cikin kuka ” Inna ba maganar nayi hakuri bane , mummunar maganar da ake jifana da ita agari da wacce ake jifana agidan da yake matsayin gidanmu, sun isa su tarwatsa min duk wani farincikina balle ma Bani da farincikin , Inna babu me Sona , babu namijin dake son ya nemi aurena asalima aga mun tsaya ko da da gaisuwa babu namijin daya ke son haka, Inna meye laifina”.
Ta girgiza Kai tace ” Baki da laifi muhseena Sam Sam Baki da lefi.”

Tace ” to Inna Ki cireni a dubu ki warware min komai ki gaya min gaskiya ko da hakan zai Zama sanadiyyar mutuwata , ki gaya min gaskiyar maganar da ake yadawa akaina”.
Ta daga Mata hannu tace ” na gaya Miki ki daina min tambayar nan domin tana durkusar da guiwata tana lalata tunanina tana Kuma jefani cikin mummunan yanayi, ki rabu dasu duk Wanda zai fada abinda yake so ysyi ta fada, tsawon shekarun nan ahaka Muke babu wani abu dazai wanke mu “
Muhseena tace ” akwai mana Inna” ta dubeta tace ” menene Shi” mujaheeda tace ” gaskiya Inna , ita kadai zata wanke mu ki yi hakuri ki gaya min gaskiyar wacece ni don Allah Inna.”

Gaban Hajara yayi mummunar faduwa ta waigo ta zubama gudar jininta Ido, shin me zata gaya mata ta gamsar da ita wace gaskiya gareta da zata Kara yi Mata ado ta gaya ma muhseena.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 12Nima Matarsa Ce 14 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×