Skip to content
Part 14 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Hajara ta kara kallon yarta cikin matukar tausayawa, tace ” na rokeki muhseena kibar wannan maganar, kamar kullum bazan gaji da gaya Miki ki dauke kanki daga Jin maganganun mutane ba, komai lokacine ranar da duk lokacin aurenki yayi babu makawa Allah zai baki Mijin da zaki aura, don haka don Allah ki sama kanki hakuri da dangana duk abinda kike ji nima ina ji tashin hankalin da kike ciki na shiga Wanda ya fishi ina Kuma ciki har yanzu.

Ke kadaice sanyin idaniyata, saboda ke kadai kawai nake rayuwa idan Kuma kikace zakisa kanki acikin irin wannan yanayin to yaya kike son nayi da Kaina.”

Muhseena tasa hannu tana share hawayenta, shin ta yaya zata fahimtar da mahaifiyata cewa duk duniya babu abinda take bukata sama da amsar tambayar da tayi Mata, shin wacece ita? Meyasa ake jifanta da mummunar Kalmar da ta gurbata rayuwarta?, Meyasa mutane suke kyamatarta?

“Idan kun gama zaman dakin AI sai Ki fito ki daukar min tallan goron , idan Kuma bakincikin ne ya motsa irin na uwarki sai kibarni da kayana.”

Hajara ta Kara kallon muhseena kallo me cike da tausayi tace ” kiyi hakuri ki tashi kije ki daukar Mata goron, kafin ta maida abin babban al’amari, kinsan dai halinta Sarai.”

Muhseena ta jinjina Kai tace ” toh”, daganan ta Mike ta wuce wajen ledar kayanta ta bude ta dakko dogon hijabinta har kasa Wanda Shi kenan Mata gaba da baya. Ta cire gelen jikinta ta maida hijabin tasa gami da Kara goge hawayenta sosai, ta dubi màhaifiyarta cike da tausayawa da kauna tace ” na tafu Inna.”

Ta gyada Kai tace ” Allah ya bada sa’a Allah ya tsare ki, ki kula don Allah”, tace tana kokarin fita ” Amin , insha’Allah Zan Kula”.
Fitarta wani kuka Mai karfi ya Kara kwacema Hajara, hakika tana daya daga cikin Matan da basuyi sa’ar zuwa duniya ba, irin bakaken abubuwan da suka faru da ita arayuwa Abu ne Wanda ya Zama babban kalubale agareta, tun faruwar al’amarin bata Kara riskar farinciki ba, rayuwa kawai take amma bata San inda ta dosa ba.

Muhseena tana fita da farantin goro akanta , sukayi kacibis da babanta mallam Umar , ya tsaya Yana kallonta harta karaso tana gaidashi, yace ” muhseena, Bana ce na hana tallar nan ba , meyasa kika dauka”, tace ” Ande Dije ba zata bari ba , dole na dauka matukar ina son Zaman lafiya agidan.”

Yayi shuru Yana Jin ràshin dadi acikin ransa, ya dubeta yace ” jeki” Kai kawai ta gyada ta wuce ta tafi ayayinda ya bita da kallo cike da zargin Kansa na ràshin sauke nauyin da ke Kansa Akan mujaheeda, baya jindadin yadda mahaifiyarsa ta dau kahon zuka ta Dora Mata ya rasa yadda zaiyi da ita ko ya shawo kanta ta daina nuna kiyayyarta ga muhseena.
Adamuwa ya shiga gidan har zuwa lokacin Ande Dije tana zaune awajen zamanta, lokacin Hajara ta fito ta cigaba da shararta.
“Sannu da dawowa” cewar Hajara ya amsa Yana kallonta cike da kulawa yace ” yauwa Hajara ya gidan” tace ” lafiya lau”. Ande Dije ta saki tsaki tace ” shashanci kayi ta lelen Mata sai kace akanka aka fara aure, Ka Zama shanyayye Baka da wani abu agabanka sai Hajara.”

Ya Matso kusa da ita yace ,” haba Ande meya kawo wannan maganar Kuma, don Allah ki dinga hakuri” ta watsa masa harara tace ” Anki a dinga hakurin, nace Anki a dinga hakurin , tunda ni babu damar na yi maganar gaskiya sai kace wai na dinga hakuri tunda dama Bani da hakuri ko.”

Ya durkusa kusa da ita cike da girmamawa yace ” Ande don Allah ina rokonki kamar yadda nake rokonki kullum ki cire abinda ke ranki agame da Hajara da yata muhseena,” ta watsa masa harara tace ” yarka aina, kadaina wannan maganar kadai cigaba da rukon wahala Amma har kullum ina gaya maka Ka daina alakanta kanka da muhseena.”

A gaggauce Hajara ta gama kwashe shararta, tayi saurin shiga daki jikinta na rawa kanta na Sarawa, ta koma Kan katifa ta zauna gami da takurewa.kukanta ya dawo sabo.

Komawarta daki yasa Mallam Umar ya Kara Jin ràshin dadi atare dashi, ya numfasa yace ” Ande kamar fa yadda kike ganin nayima Hajara halacci na taimaketa hakanan nima Hajara tayi min halacci ta Kuma taimaka min kema kinsan haka ba Kuma zamu taba mantawa ba, don haka ni duk banga dalilin wannan abubuwan ba, shekara da shekaru ana aikin abu daya ko yayane dai zuwa yanzu aiya kamata ki sakko ki rungumi Hajara da muhseena amatsayin naki.”

Ande Dije ta Kara sakin tsaki tace ” halaccin daka Mata aiyafi Wanda ta maka to ma har wane halacci tayi maka, har abada bazan taba son Hajara ba balle yarta” ya kama Kansa ya rike Yana jujjuyawa yace” saboda me Ande don me ba zaki iya sonsu ba ,bayan dimbin girmamawa da mutuntawa da suke Miki da Kuma yi Miki duk abinda kike so cikin ràshin nuna kosawa, don Allah Ande ki sassauta musu ko don su Sami natsuwa.”

“Bazan sassauta ba, duk abinda zaka fada kaje kayi ta fada.”

Yasan kafiyar mahaifiyarsa da ràshin daukar shawara , don irin wannan maganar yayi tafi dubu da ita aiya tsawon shekarun da aka kwashe.

Ya nisa yace ” to shikenan, Amma ina ganin lokaci yayi da ya dace ace kin daina dorama muhseena talla saboda tayi girma KO wane lokaci muna iya aurar da ita akalla zuwa yanzu yakamata ace ta Sami nutsuwa waje daya.”

Tayi masa kallon tsaf tace ” waye zai aureta? Waye kake tsammanin zai iya hada jibi da mummunan tsatso ko kuwa tunda kake tunda muhseena tayi girman tsayawa da samari Ka taba ganin anyi sallama da ita, babu me son hada zuria da ita, don haka idan saboda wannan dalilin kake son na daina dora Mata talla to bazan daina ba talla yanzu na Fara Dora Mata , Koko, kunu, Dan wake , goro Kai komai Naga damar dora Mata aciki Zan dora Mata tunda duk tana dauka don haka ki shiga taitayinka Ka fita harkata.”

Mallam. Umar ya yunkura ya tashi domin dai yayi Imanin cewa Ande Dije ba zata taba sauraron sa ba ballefa ta taimakeshi tayi abinda kullum yake rokonta tayi masa.
Asanyaye ya wuce dakin Hajara ayayinda Ande Dije ta cigaba da maganganunta marasà dadi daga bisani itama ta tashi ta kakkabe zaninta ta shige dakinta.

Hajara tana zaune inda take hawaye take sosai, ya tsaya Yana kallonta cike da matsananciyar damuwa ya zuba Mata Ido, Yana matukar Sonta amma yakasa bata farinciki ko daya arayuwarta.

Ya danyi gyaran murya yace ” nasha gaya miki kuka babu abinda zaiyi Miki bazai cire Miki damuwa ba sai dai ma ya Kara Miki ràshin nutsuwa kila Kuma ma har ya taba Miki lafiya, nasan babu dadi da zafi Kuma an dade anayi , ko yayane yakamata ace an rage wani abun ko baa daina Duka ba, Amma na rasa yadda zanyi na Gaza Hajara nagaza ki yafe min.”

Hajara ta goge hawayenta tace ” kadaina zargin kanka mallam, nasan da kana da yadda zakayi Ka hana abinda yake faruwa faruwa da tuni kayi , nasan Kuma kayi iya bakin kokarinka haka zalika Kai ubane Nagari ga muhseena Bani da haufi Akan irin son da kake Mata idan Kuma da ace abubuwa hannunka suke da duk hakan Bai kasance ba.”

Ya numfasa yace ” hakane Hajara Allah ya sani ina kaunarku ina kwadayin na Baku farinciki amma Bani da yadda zanyi ina da rauni.”

Hajara ta jinjina Kai tace ” nasani don haka Ka daina damun kanka , idan da sabo ai mun Saba sa halin Ande.”

Yace ” akullum ina adduar Allah yaba muhseena miji nagari tayi aurenta ko ta huta da irin wannan rayuwar da babu abinda take bata sai damuwa da tashin hankali “. Ta daga hannayenta sama tace ” Amin ya Allah nima shine burina kullum Kuma itace adduata”.
Mallam Umar yace ” baa Sami komai an sarrafa agidan ba ko.”

Ta girgiza Kai tace ” gari nadan samu na jikama muhseena Tasha saboda zata tafi bin layin ruwa nasan Kuma zata Dade hakan yasa na bàta Tasha” ya girgiza Kai yace cike da damuwa ” kiyi hakuri, bari na Kara fita insha’Allah Zan Samo abinda zaa ci” tace ” Allah ya bada saa, Allah yasa a Samo halal”,
Daga waje bakin kofa muryar Ande Dije ta amshe maganar “ko haram din ne ma ya zaayi ya samu bayan Yana tare da karfa”
Hannu ya dagama Hajara alamar Yana bata hakuri sannan ya wuce ya fita ya wuce Ande Dije tana kaiwa da komowa atsakar gida yace ” Na fita” tace ” adawo lafiya kasani kuma yunwa nake ji matuka” yace ” Allah zai bada yadda zaayi ” ya karasa magana Yana ficewa da sauri.
*****
Karfe takwas saura minti hudu na dare, mujaheeda ta tsaida motarta a harabar gidan. Cikin gajiya ta shiga gida.

Taufiq na zaune a falo yana kallo da alama shi ya dade da dawowa gidan, ya dago yayi Mata kallon tsaf ya raina guntun gelen dake jikinta ahankali ya dauke Kansa akanta.

Ta fada Kan kujera tana maida numfashi, tana fadin ” Ashe kadawo” yace ba tare daya kalleta ba ” tun karfe shida da rabi ni INA gida, aida alamu aikinki yafi nawa yawa, idan akayi laakari da irin lokacin da kike dawowa gidan kwana biyun nan.”

Sautin maganarsa Yana fitar da ràshin jindadin abinda yake magana akai.ta dubeshi sosai tace ” kasan karshen shekara aiki Yana cushewa to abinda ke faruwa kenan yanzu aikin yayi yawa” ya Dan gyara zamansa yace.

“A matsayinki na shugabar kamfanin kina da damar da zaki je office sanda kike so ki Kuma tashi sanda kike so meye na kokarin tskurama kanki ki Kuma takura ma wani, meye amfanin ki dinga dawowa gida da daddare ko a karkashin wani kike aiki amatsayinki na mace ai kya dinga kokarin dawowa gida Akan lokaci.”

Ta yaye gelenta ta aje akusa da ita tace ” idan har kana ganin don ina shugabar kamfani bai kamata na maida hankali Akan aikin ba da Kuma cigaban kamfanin ba to hakan ba dai dai bane, domin ya Zama dole na maida hankali na Kuma dage domin ganin na ciyar da kamfanin nan gaba.”

Taufiq ya girgiza Kai yace ” gidanki da mijinki sune Abu na farko da zakisa agaba kafin komai, amma fa bance dole ba kina iya zaben aikinki fiye da komai Wanda Naga kamar hakan kika zaba.”

Mujaheeda tayi shuru tana nazarin maganarsa data Fara fahimtar tamkar abin ya na taba Taufiq, bata son damuwa domin kwana biyu abubuwa sunyi sauki bata bukatar ko kadan wani sabanin ya shiga tsakaninsu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 13Nima Matarsa Ce 15 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×