Yau ma duk canopies ɗin da aka kafa cike suke da mutanen da Dawud yasan duk don Labeeb suka taru. Haka rayuwa take dama. Kyawawan halayanka za su ja maka addu’ar neman rahama daga mutanen da ko kalar fuskarka basu taɓa sani ba.
Tunda ya leƙa ya dawo abinshi, Labeeb ne da Tayyab suke can, tunda aka yi mishi allurai jiya, da safe kuma ya ɗan sha tea da magani ya ce zazzaɓin ya sauka.
Sai dai kukan da yake y akai akai. Shi kam nan ya zauna cikin gida yana kula da su Khateeb. Kamar yadda Labeeb ya ce ‘yar aiki zata zo, nayan sallar Azahar suka shigo ita da Labeeb , babbar mace ce, duk da Ummi zata girmeta, akwai wani abu a tattare da ita da ya yi wa Dawud kwarjini.
“Dawud gashi ta zo, bansan ya abu zai fi muku ba, tana da nisa da nan ɗin sosai, if you don’t mind her sleeping here in ta yi yamma……”
Ɗan ɗaga kafaɗa Dawud yayi, don a yanzun bai damu da abubuwa da yawa ba. Ko falo zata iya kwanciya abinta, baida matsala da hakan.
Yarda da ita shi ne babbar matsalarshi.
“Ba matsala in sha Allah.”
Dawud ya faɗi a sanyaye, inda ya ga idanuwan Labeeb kafe ya maida kallonshi, Sajda ce zaune ta saka hannuwanta duka biyun ta dafe kanta ta runtse idanuwa tana girgiza kanta.
Da sauri Dawud ya sauko daga kan kujera ya riƙo ta jikinshi. Cikin tashin hankali yake faɗin,
“No…. No…. Please no….Sajda……”
Tirje-tirje ta soma yi. Zulfa kam gefe ta ja jikinta ta saka hannuwa duka ta rufe idanuwanta da su. Bata son ganin Sajda tana wannan abin. Tsoro take ji.
Tsoro take ji sosai da sosai. Ihu Sajda ta fara tana ƙoƙarin ƙwacewa daga riƙon da Dawud ya mata, sai da Labeeb ya ƙaraso ya taya shi riƙe ta.
“Yayaaaa kaina…… Yaya kaina zai fashe…….”
Dawud kamar zai fashe da kuka ya ce,
“Sajda bansan me zan miki ba…. Bansani ba wallahi, dan Allah ku taimaka mun…. Bazan iya mayar da ita wajen nan ba….. I can’t!”
Labeeb kanshi hankalin shi ya tashi, don ya ga yadda wannan ciwon na Sajda yake mata. Abin sai addu’a, mai aikin da take tsaye da ‘yar ledar kayan ta ta ajiye gefe.
Ƙarasowa ta yi wajen da suke, ta tsugunna dai dai kan Sajda da ke ihu tana faɗin kanta zai fashe, hannunta ta ɗora a saman kan.
“Me kike haka?”
Labeeb ya tambaya.
“Ka barta in zata iya taimakawa”
Da idanuwa taima Dawud godiya da ya barta. Ya dan daga mata kai kawai tare maida hankalinshi kan Sajda.
“Ku ɗan ɗibo min ruwa a kofi.”
Zulfa da ke gefe ta cire hannunta daga idanuwanta da ta rufe ta miƙe da gudu ta nufi kitchen ɗin. Ruwan ta ɗibo ta kawo.
Wajen bakinta ta kai kofin ruwan shi tana yin addu’a a ciki kafin ta ajiye a ƙasa, ta saka hannunta cikin kofin tare da yin Bismillah ta ɗibo.
Murza shi ta yi tana shafa wa Sajda a saman kanta, sannan ta ƙara ɗibowa ta shafa mata a fuska, da hannu ɗaya ta riƙe kan Sajda, ta ɗibo ruwan ta buɗe bakinta ta ɗura mata shi.
Furzo shi waje Sajda tayi, saitin kanta ta tsugunna. Cikin kunne take mata addu’o’i har jikinta ya soma sanyi. A hankali ta bar ihun da take yi.
Sake ɗiban ruwan tayi ta shafa mata tun daga kanta har wuyanta, sannan ta karɓeta daga hannun Dawud ɗin. Da mamaki suke kallonta su dukkansu.
Kama Sajda ta yi ta shafe mata jikinta da ruwan addu’ar gaba ɗaya, bacci mai karfi ya ɗauki Sajda. Cak ta ɗaga ta tare da miƙewa da ita.
Kan kujera ta mayar da ita ta kwantar, sannan ta kalli su Dawud da suke kallonta suma ta ce,
“Da ta tashi daga bacci shikenan in shaa Allah”
Cike da mamaki Dawud ya ce mata,
“Kinsan me ya ke damunta?”
Girgiza mishi kai ta yi tare da faɗin,
“Ban sani ba, kawai dai na san ba na asibiti bane, kuma ba zai taɓa gagarar ayoyin Allah ba.”
“Mun gode sosai.”
Dawud ya faɗi, yanajin abinda tai musu a yanzun nan ya samu wajen zama a zuciyarshi. Miƙewa labeeb yayi.
“Na koma waje nikam saboda mutane.”
Bai jira amsar Dawud ba ya fice. Kallon matar da ko sunanta bai sani ba yayi. Inda Khateeb ke kwance ya ga ta nufa. Da sauri ya miƙe yana riganta.
Kallonshi ta yi. Ya ɗauki Khateeb ya rungume a jikinshi, idanuwanshi ya ɗan ware akanta. Yana jin duk wani abu da zai taɓa Khateeb ba zai iya ɗaukar shi ba.
“Zan ɗauke shi ne kawai.”
Ta faɗi, yadda ta karasa maganar ya tsaya mishi a zuciya.
“Me yasa?”
Ya buƙata a taƙaice. Kallon Dawud take yi, yanayin shi kawai ya nuna mata ya ga rayuwa ta fanni mai wahala ma kuwa.
Idanuwanshi ɗauke suke da girman hakan. Don haka amsar da ta fito daga bakinta iya gaskiyarta ne.
“Saboda Allah bai bani ba, sai dai ya bani zuciyar ƙaunar su sosai. Tun da na shigo nake son riƙe shi ko sau ɗaya ne.”
Maganganunta sun sake taɓa shi, ɗazun nan yake jinjina ɗawainiya da Khateeb. Ga wata da bata haɗa komai da shi ba tana son ɗaukar shi. Allah kenan, mai kyauta ga duk wanda ya so.
“Zan iya komai akansu, ina tsoron halin mutane, taimakon da kika min da sajda yanzun nan wallahi bazai mantu a wajena ba.
Amma bansan ta yadda zan fara yarda da ke ba. Bana son komai ya taɓa su.”
Kallon yarintar Dawud take, ta tabbata da Allah ya bata haihuwa da tana da kamarshi. Cikin taushin murya ta ce,
“Ka gwada yarda da ni ka gani, ba kowane mutane bane kala ɗaya da saura. Tsoron sun da kake ji dai dai ne, sai dai karka taɓa bari hakan ya canza ka.
Kowanne mutum yana buƙatar dama ko da guda ɗaya ce a rayuwa. Bance ka yarda da ni lokaci ɗaya ba. Dama kawai nake so ka bani zan zauna da ku da amana da yardar Allah.”
Baisan me yasa maganganunta sukai mishi shige da na Ummi ba, lokaci ɗaya yardar matar nan da ko sunanta bai sani ba da girmanta suka cika shi.
Hannunshi na rawa ya miƙa mata Khateeb. Karɓarshi tayi ta zauna da murmushi a fuskarta. Dawud ya tura hannunshi cikin sumar da ke kanshi.
Yana jin nauyin da ke kanshi kamar wanda ya shekara talatin a maimakon goma sha shidda. Yana ganin zulfa ta koma wajenta.
“Sannu da zuwa.”
Dariya ta bata.
“Yauwa ‘yan mata, ya sunanki?”
“Zulfa….ke fa.”
“Aisha….”
Riƙe baki zulfa ta yi tana jin daɗi.
“Sunanku ɗaya da ummi na, Ummi ta ce ba a faɗar sunan manya. In ce miki Mami?”
Cike da jin daɗi Aisha ta ce,
“Yayi daɗi, na gode.”
Sauke numfashi Dawud yayi, ya wuce ɗakin ummi ya bar Sajda da Mami, mamaki yake yi. Girgiza kai yayi da mamakin yadda a zuciyarshi har ya fara kiranta da sunan da Zulfa ta maƙala mata.
Ko da bai santa ba, duk wata Aisha a zuciyarshi cike take da daraja da kima. Ko don mai asalin sunan da kuma Ummin shi.
****
Kwance yake kan gadon Ummi, baisan me ya kai hannunshi ya janyo drawer ɗin da ke gefen gadon ba. Litattafai ne hard covers a ciki. Miƙewa zaune yayi ya ɗauko su ya ajiye akan gadon sannan ya maida drawer ɗin ya rufe. Ɗaya ya ɗauka, yana buɗewa ya ga takardu a linke a ciki.
Da mamaki ya ɗauke su, guda biyu ne. Ɗaya sunan shi ne a jiki. Ɗayar kuma an rubuta AUWAL da manyan baƙi. Ajiye ɗayar yayi ya buɗe tashi.
Rubutun Ummi ne, a ƙirjinshi ya rungume takardar yana jin kewar Ummi kamar ya sa ihu. Kafin ya dawo da ita zuwa dubanshi.
Ya soma karanta abinda ke ɗauke a ciki kamar haka:
Assalamu alaikum.
Bansan me ma nake shirin rubutawa ba ko me zance maka. Ban kuma san me yasa jikina yake bani cewar wani abu mai girma zai faru dani ba.
Abu ɗaya na sani, lokaci baya jiran mu. Bansan sa’adda za ka ga wasiƙar nan ba, ko inma za ka ganta ɗin.
Abu huɗu nake son fada maka koda ban samu damar gaya maka da kaina ba.
Na farko shi ne, ka min alƙawarin duk sa’adda abbanku ya nemi ku koma wajenshi ba za ka yi musun hakan ba.
Ko baka faɗa ba nasan zaka cika min wannan alƙawarin.
Na biyu, ina son ka bashi wasiƙar da sunan shi yake rubuce a jiki ko da ban samu faɗa mishi abinda nake so ba da kaina ba. Ka ba shi lokacin da ka tabbatar ya dawo abban ku da kuka sani.
Na yarda da yardarka. Na yarda za ka bashi lokacin da zan so ka bashi ɗin.
Na uku, a ko da yaushe ka duba a cikin zuciyarka, komin ɓacin ran da ke ciki, ka duba Dawud, can wani waje ba zaka rasa wajen yafiya ba.
Duk girman laifi inka yafe shi yakan zame maka mai sauƙin ɗauka. Karka manta daga lokacin da ka yafe ko baka manta ba ciwon shi zai rage maka.
Na huɗu, wannan naku ne ku duka, ina ƙaunarku, ina alfahari da ku, samun kyautar ku a rayuwata shi ne abu mafi girma.
Ka kula da su, ka ƙaunace su, karka barsu su canza daga yadda suke in har za ka iya. Allah yai muku albarka a rayuwar ku.
Ku karanta littafin nan a yanayi ɗaya (Lokacin da kuke neman ƙaunar mahaifinku a zuciyoyinku kuka rasa, ku karanta zai tuna muku yadda take, saboda nasan ba bacewa tayi ba, mantawa kuke)
AISHA.
Numfashi Dawud yake fitarwa da sauri-sauri, yana jin kamar zazzaɓi ya rufe shi. Baisan ko yaushe Ummi tai rubutun ba saboda babu kwanan wata a jiki.
Da nauyi a ƙirjinshi ya linke takardar kamar yadda ya ganta, ya kwashe duka biyun ya mayar. Baida tabbas akan Abba ko kuma sake ƙaunar shi, sai dai yana da tabbas akan zai bi duk wani abu da ke cikin wasiƙar nan. Drawer ɗin ya janyo ya mayar da littafin ya koma ya kwanta.
****
Zai rantse rayuwa cikin kwana bakwan nan ta zo musu da sauƙi ne saboda kasancewar Labeeb da kuma Mami a tare da su.
Raguna har biyu ya siyo aka yanka ma Khateeb. A masallaci akai raɗin sunanshi. Ciwon da Dawud ke ji kan Abba yana ƙaruwa da ya duba babu shi a wajen.
Badon zuwanshi zai ƙara musu komai ba. Ammanl zai canza wani abu a rana mai tarihi har haka a rayuwar Khateeb. Sadakar da Labeeb yai a ranar ta ƙara wa Dawud ƙaunar shi.
Do ya tabbata ko da Momin Labeeb ce ta rasu iya abinda zai yi kenan. Mami ta sa aka yi wa Khateeb aski. Cewarta bai kamata a bar ƙarfin sunnar yin hakan ba.
Zuwa yanzun ɗakin Dawud da tunda suka dawo gidan bai kwana ciki ba ya bar wa Mami, to ya kula su Sajda rashin ummi yasa sun mannewa Mami kamar suna son fito da Ummin da suka rasa a jikinta.
Hakan sam bai dame ta ba. In akwai wani abu a zuciyarta bai wuce ƙaunar su dukkansu da ta shiga ranta ba. Ɗakinta suke kwana, Khateeb kam dawud baya bar mata shi.
Wanka kawai take mishi ta shirya shi, zai ɗauke shi ya goya shi a ƙirjinshi. Ta kula kuma ko fita zai yi babu abinda ya dame shi da Khateeb yake fita. Ko madara shi yake bashi.
Kayan Khateeb ɗin ma sai dai in ta riga shi wankewa. Yana bata girma sosai.
Tayyab kam har yanzun ko alamar warwarewa bai yi ba. Don ma Dawud na mishi nasiha da ban baki. Kullum da dare sai yai kuka yake bacci.
BAYAN WATA BIYU
Nasara ta farko da suka yi a watanni biyu da rasuwar Ummi shi ne rashin tashin ciwon Sajda ko sau ɗaya a kwanaki sittin ɗin nan.
Ta biyu kam fitowar WAEC ɗin Dawud ce, da yake da credit bakwai sai distinction guda biyu. Yana dubawa Labeeb ne mutum na farko da ya kira ya sanarwa.
Yayi murna sosai da cewar a satin zai zo garin in yaso sai suyi magana sosai.
*****
“Yaya mami ta ƙi dawowa.”
Zulfa ta faɗi tana turo baki. Kallonta Dawud yake yi.
“Ke kika ce ba za ki bisu ba ai. Za ki dame ni kuma. “
Shagwabe fuska tayi.
“Haka ka ce Ya labeeb zai zo yau.”
Girgiza kai Dawud yayi. Gidan ‘yan uwansu Mami ta tafi ita da Sajda tun wajen Azahar. Baisan dalilin daya hana Zulfa binsu ba sai yanzun. Ashe don ya ce Labeeb zai zo ne.
Khateeb ya gyara wa riƙon da yai mishi a cinyarshi. Yaron yayi wata irin ƙiba, duk sati yake kaishi asibiti a duba shi don ya tabbatar da lafiyarshi.
Tun bayan sunanshi ya rage rikici. Don yanzun in kaji kukanshi wanka ake mishi ko kuma yana jin yunwa. Tayyab ne ya fito daga ɗaki.
“Yaya ka ga I. D card ɗina na makaranta?”
Kallonshi Dawud yayi.
“Yana cikin jakarka. Baka iya ajiye abun da kasan kana buƙata waje ɗaya. Next time karka zo ka tambayeni…”
Ɗan sosa kai Tayyab yayi, ya samu waje ya zauna. Hannu ya kai zai ɗauki Khateeb, dawud ya janye shi.
“Za ka zo kaita jagula shi sai yayi ciwon jiki.”
Riƙe baki Tayyab yayi yana faɗin,
“Chaiii yaya anya za ka bari a ɗauki babynka kuwa, wai! Ƙaƙumuna kenan!”
Pillow ɗin kujera Dawud ya ɗauka ya kwaɗa mishi.
“Ka rainani ba….”
Dariya Tayyab da Zulfa suka yi, Dawud ya harare su. Duk da har ranshi yake jin daɗin ganin yadda Tayyab ɗin ya warware, ya canza sosai. Don bayajin zai taɓa komawa yadda yake da.
Rayuwa na maka wannan sauyin, sai dai za ka iya zama wani daban, duk ta fannin da zata bugaka in ka tashi sai ka zaɓi mutumin da kake so ka zama.
Ƙasa da wanda rayuwa ta wujijjiga, kalar shi, ko kuwa wanda ya fishi. Da alama Tayyab ya zaɓi ya zama fiye da yadda yake a da.
Ƙwanƙwasawa suka ji ana yi, tun kafin dawud yai magana Zulfa ta tashi da gudu ta buɗe tana ƙanƙame shi. Ɗaga ta yayi da faɗin,
“Zulfa ta bata kowa ba.”
Dariya ta kama yi tana ɓoye kanta a jikin wuyanshi. A dole kunya take ji.
“Yaya ka sauke ni.”
Sake riƙeta dam Labeeb yayi.
“Kin girma yanzun ko. Na ƙi in sauke ki ɗin.”
Harbe-harben ƙafa ta dinga yi. Jin tana neman kayar da su yasa Labeeb ya sauke ta yana ja mata kunnuwa.
“Shikenan yanzun Zulfan nan ba tawa bace ni kaɗai.”
Turo baki tayi.
“Taka ce mana.”
Ya girgiza mata kai yana haɗe fuska. Shirin kuka ta fara.
“Da wasa nake fa. Waye ma zai ce zulfan shi gani.”
Dariya tayi tana rufe fuska. Ya kama hannunta suka ƙarasa cikin falon. Zama yayi ya zaunar da ita a gefenshi.
Tayyab ya gaishe da shi. Da fara’a ya amsa yana ɗorawa da,
“Tayyab ya makaranta. Har an shiga aji biyar ko?”
“Kai… Da saura yaya, ai bamu daɗe ma da shiga aji huɗun ba fa!”
“Kamar gobe ne. Allah Ya taimaka Ya kaimu lafiya.”
Su duka suka amsa da amin. Dawud ya ce
“Ya aikin?”
Ɗan ɗaga kafaɗa Labeeb yayi.
“Gashi nan muna ta fama.”
Miƙewa Tayyab yayi.
“Yaya don Allah ka bani shi tunda magana kuke yi.”
Miƙa mishi Khateeb Dawud yayi tare da faɗin,
“Saura kaita daƙuna shi.”
Dariya kawai Tayyab yayi ya karɓeshi ya fice daga gidan. Key ɗin mota Labeeb ya zaro ya ba wa Zulfa.
“Jeki Tayyab ya buɗe miki, chocolate ɗinku na nan ke da Sajda.”
Karɓa ta yi ta fita da gudu. Nutsuwar shi Labeeb ya tattara ya mayar kan Dawud.
“Really ya kake? I mean da komai da komai.”
“Komai lafiya. Nima am okay.”
Kai Labeeb ya jinjina.
“Good. Result ɗinka yayi kyau sosai. Gaskiya na ji daɗi, na ce za mu yi magana ne saboda bansan me kake son karanta ba.”
Jim Dawud yayi, tun tasowarshi yake cema abbansu yana son zama Biochemist, Abban ke ƙara ƙarfafa mishi gwiwa. Yanzun kam tunanin wani abu wai shi zama Biochemist kawai juya mishi ciki yake yi.
Ya tsani course ɗin da dukkan abinda yake da shi . Cikin sanyin murya ya ce,
“Medicine… In zan samu ina son medicine.”
Da ya faɗa sai ya ji kamar dama abinda ya kamata yayi ne. Murmushi Labeeb yayi.
“Za ka samu in sha Allah. Ka bani takardunka gaba ɗaya….”
Kai ya ɗan daga kafinn ya ce,
“Da zan dakata da karatun ne saboda Khateeb.”
Sai da Labeeb ya gyara zama sannan ya kalli Dawud sosai ya ce,
“Karatun da ka zaɓa ba mai sauƙi bane, sai dai banda haufin za ka iya. Kana buƙatar shekaru bakwai ko ƙasa da haka.
Jannenka basu da wannan lokacin, karka ɗauka zan taɓa gajiya da kula da ku. Wallahi bazan gajiya ba muddin ina da shi.
Saidai lokaci zai zo da za ka buƙaci son kula da su da kanka, kana buƙatar tsayawa da ƙafafunka. You are what? Sixteen ba, ka ƙara shekara bakwai akai.
Za ka gama karatunka da wuri, ka zama stable, lokaci baya jiranmu Dawud.”
Yafi kowa sanin lokaci baya jira, ya ga hakan akan rayuwar shi. Yaso ya dakata ne da Khateeb ya kai ko shekara biyu. Amma ya fahimci abinda Labeeb yake faɗa mishi.
In Allah ya taimake shi, ya samu gama karatun shi da wuri hakan zai fi. Zai samu aiki da kuɗin da zai wa su Sajda duk abinda suke so. Tunanin irin ranar zata zo kawai ya kusan saka murmushi ya ƙwace mishi.
“Nasan baka son ina cewa na gode. Kalma ce ƙarama El, banda abinda zan taɓa baka a rayuwata.”
Murmushi Labeeb yayi.
“‘Yan uwa basa taɓa rasa abinda za su ba wa ‘yan uwansu. For now ka yi karatu, shi ne kawai buƙatata.”
Jinjina kai Dawud yayi.
“Bazan baka kunya ba in sha Allah.”
A ranar ya haɗa gabi ɗaya takardunshi ya ba wa Labeeb ɗin ya tafi da su. Tayyab ne ya shigo gidan da leda a hannunshi da Khateeb.
“Ina zulfa ɗin?”
Dawud ya buƙata.
“Kaima ka sani ai. Ga chocolate ɗin duka ta barma Sajda.”
“Ko kayan sawa bata ɗauka ba, ga uniform ɗinta ma, har na Islamiyya duk suna nan.”
‘Yar dariya Tayyab yayi.
“Anjima sai in je in kai mata in sha Allah.”
Hannu Dawud ya miƙa mishi alamar ya bashi Khateeb, maƙale kafaɗa Tayyab yayi yana rugawa.
“Allah karka kayar da shi, Tayyab…. Wai ina wasa da kai…. Ka zo ka bani yaron!”
Tayyab na dariya ya ce,
“Yaron mu. Mu duka… Saboda haka dole a dinga sharing ɗaukarshi, time table zan zo in yi.”
Harara Dawud ya watsa mishi.
“Fine. Ka riƙe shi kafin anjima.”
Ɗaki Tayyab ya wuce abinshi. Labeeb ya dawo ya zauna. Lumshe idanuwanshi yayi yana ɗora ƙafafuwanshi akan kujerar ya kwanta.
Zuciyarshi cike da kewar Ummi bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi.
****
BAYAN SHEKARA BAKWAI
Tsaye yake yana kallon Sajda cike da alfahari a fuskarshi. Ƙaunarta na cika zuciyarshi kamar zata fashe. Yanayin sautin muryarta da ƙira’ar karatun ta na nutsar da shi.
Ya kasa zama saboda farin cikin da yake ciki. In da ance mishi zai iya shekarun nan babu Umminshi babu Abba zai musanta. Ya sake yarda cewa duk abinda kake cewa ba zaka iya ba a rayuwarka bai sameka bane ba.
A yanzun Mami ta zama wani ɓangare a tare da su cikin yarda da amana. Ta basu ƙauna da dawud ke da yaƙinin abinda ta Ummi zata nuna mata ɗaya ne.
Shi ne Ummi na son su fiye da rayuwa da kanta. Sai dai ƙaunar Mami mai girma ce duba da ko jini basu haɗa da ita ba. Ta basu shekaru har bakwai na rayuwarta.
Abu ne da ba zai taɓa mantuwa ba. Da idanuwa fiye da biyu yake kallon Sajda. Ji yake kamar ya je kusa da ita ya sanar da duk wani wanda yake taron cewar ƙanwarshi ce.
Ƙanwar shi ce yau ta yi saukar Alƙur’ani, kuma hadda, Sajda ce ɗauke da Al-Qur’an gaba ɗayan shi a cikin kanta. Hannu yasa yanajin yadda hawayen farin ciki ke cika mishi idanuwa.
Rabonshi da farin ciki irin na yau har ya manta. Muryarshi ɗauke da wani yanayi mai nauyi ya ce,
“Ummi da kina nan yau zata zame miki rana mai cike da farin ciki. Allah ya kai rahma kabarinki……”
Yana ƙarasa addu’ar Sajda na idar da ƙarshen aya cikin Suratul Al’Imran. Gaba ɗaya wajen aka ɗau kabbara. Murmushi yake har kuncin shi ya soma ciwo.
Tayyab ya hango, sun fi kowa haske shi da sajda a gidan, kamaninshi da Ummi ya sake fitowa da girman da yayi. Hannu Tayyab ya ɗago mishi yana murmushi.
Zuciyar Dawud ta doka da ƙarfin gaske, sosai Tayyab ke kama da Ummi, komai nasu iri ɗaya ne. Da hannu Tayyab yai mishi alama da ya taho.
Takawa yake yi, har lokacin yana duba irin sauyin da rayuwa ta zo musu da shi, su ne a wannan matsayin yanzun. Shi ne shekara ɗaya ta rage ma a matakin karatun shi.
Tayyab kam yana level two a KASU shima inda yake karantar Computer Science. Har inda Tayyab ke tsaye da sajda Dawud ya taka.
Hannuwan Sajda ya kama cikin nashi ya sumbata, sannan ya sumbaci goshinta. Muryarshi na rawa saboda yanayin da yake ji yace.
“Allah ya sanya miki albarka Sajda. I am so so proud of you….”
Dariya Sajda ta yi har dimple ɗin da ke fuskarta ya fito.
“Amin Yaya. I am proud to have you as my brother.”
Gyaran murya Tayyab yayi.
“Sajdaa.”
Ya faɗi muryarshi ƙasa – ƙasa. Dariya ta yi ta ɗan yi jim kamar tana tunani. Ware mata idanuwa Tayyab yayi.
“Haba mana….”
“Dakai ma….”
Ta ƙarasa tana dariya. Dariya suka yi su dukansu, har da dawud wannan karon.
“Yaya ina su Mami wai? Su zo ai mana hotuna.”
Juyawa Dawud yayi, Mami ya hango riƙe da Khateeb da ya ƙwace hannunshi yana rugowa da gudu wajen dawud.
“Don…”
Khateeb ya faɗi. Ɗaga shi Dawud yayi yana juya idanuwanshi, tun yana ƙarami bakinshi baya iya faɗin sunan Dawud. Ba kuma yadda Mami bata yi ba akan Yaya sam ya ƙi.
Tun yana faɗin abu mai kama da dawn har don ya fito. Shi kaɗai yake kiranshi Don ɗin nan, yanzun har ‘yan makarantarsu, saboda kusan ko yaushe yana tare da Khateeb.
Ko su sajda in suna jin tsokanarshi za su fara Yaya don. Zai yi ƙarya in ya ce sunan baya mishi daɗi. Kawai saboda Khateeb ne ya ke kiranshi haka. Ƙaunarshi da yaron abu ne da babu kalaman da zasu misalta yadda ya kamata.
Rungume Mami sajda tayi.
“Mami….”
Tana dariya ta janyeta.
“Sajda maza karya ni.”
Dariya Sajda ta kama yi, ta sakin Mami tare da faɗin,
“Hotuna za a yi mana.”
Hotuna aka soma ɗaukarsu, ta baya Dawud yaji an zagayo da hannuwa an shaƙo mishi wuya, yasan ba mai mishi wannan haukan sai Asaad.
Hannun ya cire yana zagayo da Asaad.
“Ranka zai ɓaci Asaad….”
Dawud ya faɗi yana haɗe fuska, dariya Asaad yayi.
“Come on Don, hoto za ai mana.”
Ture shi gefe Dawud yayi. Yanayin halayyarsu kaɗai yake bambancewa da Anees. Amma in su duka suka jera ba gane su yake ba.
Anees kam yana gefen Sajda, magana yake amma Dawud baya jin me yake cewa. Gani yai Sajda ta yi dariya tana rufe fuskarta.
In suna tare kallonsu kawai za ka yi ka gane ƙaunar da ke tsakaninsu ta wuce ta ‘yan uwantaka. Gyaran murya dawud yayi.
Da sauri Sajda ta bi ta gabanshi ta koma wajen mami. Kan Anees a ƙasa ya ce,
“Ina wuni.”
Da murmushi Dawud ya ce,
“Lafiya ƙalau Anees. Ya makaranta?”
“Alhamdulillah!”
Fatan alkhairi Dawud yai mishi kafin ya juya. Daga shi har Anees ɗin ba masu hayaniya bane ba. Kuma ya kula Anees na jin kunyar shi sosai da sosai.
Ya kuma san ƙaunar Sajda ne yasa hakan. Har ranshi fatan alkhairi kawai yake musu, duk da Anees ɗin level 3 suke. Ita kanta Sajdar yanzun ta kai zata shiga aji uku Secondary.
Motar Labeeb Dawud ya hango, ko parking bai ƙarasa ba ya ga an buɗe murfin kofar ta gaba an fito, Zulfa ce, jikinta sanye da doguwar riga ta shadda.
Tai rolling mayafinta a saman kanta, Dawud na kallon yadda wasu daga cikin samarin da ke wajen suna kallonta, baya so ko kaɗan.
Sai dai gaba ɗayan su babu mai kyawun Zulfa. Hakan kawai na saka maza binta. Don ma tana shakkar dawud ɗin.
Labeeb ya ga ya fito ya doka murfin motar, a fusace ya zagaya inda Zulfa take. Baya jin mai suke cewa ya dai san ko me Labeeb ɗin yake cewa faɗa ne yake ma zulfa.
Kallonshi kawai ta yi sosai, ta juyo ta soma takowa inda suke ba tare da ta ce komai ba, kai ya ga Labeeb ya girgiza ya biyo bayanta.
Ko a jikin Dawud, don zai iya rantsewa Labeeb ya fi shi kusanci da Zulfa. Ƙaunar su babu wanda yake gane kanta. Faɗansu babu wanda yake shiga don kunya za ka ji.
Dawud na kallon yadda kallo ya tashi daga kan Zulfa ya koma kan Labeeb. Yana kallon dalilin da yasa labeebY bai cika yawo babu masu gadin lafiyarshi ba.
Da yawan mutane hankalinsu ya koma kanshi, wasu harda hannu suke nuna shi. Ko ya nuna ya ga abinda suke yi baiba balle hakan ya dame shi.
Asali ma murmushi ya ɗora akan fuskar shi yana ƙarasowa inda suke. Mami ya gaishe da, Sajda kam rungume Zulfa ta yi da ta ture ta tana faɗin,
“Sajda mana. Sai kin min squeezing ɗin kaya.”
Ta ƙarasa maganar tana jan rigar ta da Dawud baiga abinda ya sameta ba. Sake maƙaleta Sajda tayi tana dariya.
Dariya Zulfar tayi.
“I am proud of you little sis. Gift ɗinki sai mun je gida.”
Sosai sajda ta ji daɗi, sumba zulfa ta manna mata a kunci, wannan karon Sajda ce ta ture ta tana goge kuncinta.
“Yaya zulfa sai kin shafa min jan bakinki ɗin nan da sai ka saka sabulu yake fita. “
Dariya Zulfa tai mata. Hotuna suka sake yi. Labeeb bai jima ba ya ce zai tafi saboda yadda mutane suka soma zagaye su.
Zulfa ya kalla, ta kauda kanta gefe, buɗe baki yayi zai yi magana. Da sauri ta janye Sajda tana faɗin,
“Zo ki ji…”
“Ehemm…. Trouble upstairs”
Asaad ya faɗi yana ɗaga girarshi duka biyun.
“Buzz off Asaad.”
Dariya yayi.
“Mu tafi tare”
Hararar shi Labeeb yayi.
“Da ni ka zo? Saboda me zamu tafi tare.”
Langaɓe fuska Asaad yayi.
“Kasan Anees tunda ya ga Sajda ba za mu tafi yanzun ba.”
Fitar da numfashi Labeeb yayi.
“Fine. In ka dameni in sauke ka a hanya. Don sai mun yi waya.”
Kai Dawud ya ɗan ɗaga mishi.
“Ba matsala. Be safe.”
“In sha Allah.”
Sai da yai ma mami sallama sannan suka wuce shi da Asaad. Basu daɗe da tafiya ba Zainab ta zo. Tana ƙarasowa wajen su ta juya idanuwanta da suka fi komai kyau a jikinta tare da faɗin,
“Hey couz.”
Kamar yadda take kiran Dawud ɗin. Murmushi yai mata.
“Zeezee sai yanzun? Sajda ta yi fushi.”
Shagwaɓe fuska tayi.
“Ta yi haƙuri, na je gyaran gashi ne, ba ma ayi ba na taho. Ga traffic a hanya…”
Bata ƙarasa maganar ba Sajda ta riƙeta ta baya tare da faɗin,
“Anty Zeezee.”
Murmushi Zainab tayi.
“‘Yan mata. Congratulations, Allah ya sanya albarka, sorry na yi missing ko?”
Amsawa Sajda ta yi da amin tana ɗorawa da.
“Haba bakomai, amma kinyi kyau.”
Ɗan ware idanuwa Zeezee tayi. Kamar yabon da Sajda ta yi cewan ta yi kyau tasan tayi ɗin ko ba a faɗa ba. Kama hannun Sajda tayi tana faɗin,
“Muje ki karɓo gift ɗinki.”
Binta Sajda ta yi suna hira har suka ƙarasa wajen motarta, akwatine ƙarami, Sajda dai ba zata iya faɗa ba. Handle ɗin kawai da ya fito take iya gani.
Saboda anyi wrapping ɗin shi gaba ɗaya.
“Nagode sosai Anty Zeezee. Allah ya bar zumunci.”
Daƙuna mata fuska Zainab ta yi.
“Am ok with the prayer. Banda godiya. What are sisters for? Beside you are my favorite cousin.”
Dariya Sajda ta yi kafin Zainab ɗin ta ce,
“Zan wuce Sajda. Sai wani lokaci kuma.”
Godiyar dai sajda ta sake mata, motar Zainab ta shiga ta ja murfin ta tayar ta wuce abinta. Sajda tai murmushi. Ita kam duk yadda ake faɗin halayyar Zainab kirkinta kawai ta sani.
Da ƙyar take iya ɗaga akwatin. Anees ne ya zo ya ɗaukar mata yana faɗin,
“Mutum ba ƙarfi sai rigima.”
Dariya tayi.
“Ko baka zo ba Yaya Anees zan ɗauki abuna lafiya ƙalau.”
Ɗan kallonta yayi kawai bai ce komai ba.
“Yaya duk sun tafi sun barka.”
Dariya ta bashi.
“Kin gaji da gani na ne sajda?”
Da sauri ta girgiza kai, kafin kunya ta rufeta ta sadda kanta kasa. Murmushi yayi, yana son kunyar nan ta Sajda kamar yadda yake son komai nata.
Rakata har wajen da su Mami take yayi da akwatin. Take faɗa musu Zainab ce ta bata, suka tayata godiya duk da Zainab bata wajen tare da mata addu’a.
Sallama Anees yai musu, da idanuwa yake tambayar Sajda ta rakashi. Kai ta ɗan girgiza tana nuna mishi su Mami na wajen.
Bai ce komai ba ya juya. Zulfa ta ce,
“Gulmammiya, me yasa ba zaki raka shi ba?”
Kanta Sajda ta ɓoye cikin hijabin Mami, kamar zata nutse take ji don kunya. Tana mamakin Yaya Zulfa da kunyar su Yaya da Mami bata dame ta ba.
Dukkan kyautukan da Sajda ta samu suka tattara aka zuba a motar Dawud ɗin da Labeeb ne ya bashi ita cewar shi saboda hidima yana buƙatar mota.
Suka wuce gida abinsu.
****
Yanayinta Dawud ya kalla bayan sun dawo gida ya ce,
“Ya dai Sajda?”
Kai ta girgiza mishi alamar babu komai. Daf da ita ya ƙarasa, yasa hannuwanshi ya tallabi fuskarta.
“In banji damuwarki ba wa zaiji Sajda? Menene?”
Idanuwanta cike taf da hawaye tace.
“Bana son ranka ya ɓaci.”
“Raina ba zai ɓaci ba, faɗa min menene?”
Sai da ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a wuyanta sannan ta ce,
“Na so Abba ya ganni yau, ƙila ya maida mu gida. In ya ga yadda nai kikari sosai.”
Runtsa idanuwanshi Dawud yayi ya buɗe su, kafin ya fara ƙirga ɗaya zuwa ashirin cikin kanshi, saboda yadda maganar sajda ta ƙona mishi rai.
Ta kasa gane cewar Abban nan da take nacin so har yanzun bai damu da su ba, basa gabansa. Ba ta su yake ba sam-sam.
Ji yake kamar ya girgiza ta ya sake faɗa mata ta cire shi a ranta, ta yi rayuwarta kamar yadda yake tashi babu suba ciki.
“Yaya ka ce ranka ba zai ɓaci ba. Ka yi haƙuri.”
Girgiza mata kai yayi, yana danne abinda yake ji a zuciyarshi.
“Bakomai da kake so bane kake samu a rayuwarka Sajda. Lokutta da dama abubuwa suna faruwa da baka sanin dalilin su.
Ki koyi ci gaba da rayuwarki kamar babu shi. You are doing just fine duk da baya nan.”
Hawayen da suka cika mata idanuwa ne suka zubo. Hannu Dawud ya sa ya goge mata su. Yana sake jin wutar tsanar Abban na ruruwa a zuciyarshi.
Ko ba komai shi ne sanadin fitowar hawayen nan a idanuwan Sajda.
“Ina ƙoƙari yaya. Rashin shi ba zai canza matsayin shi a wajen mu ba. Wata rana rayuwar mu zata koma kamar da.
In bamu daina ƙaunar shi ba zata dawo da shi.”
Kai kawai ya iya ɗaga ma sajda. Baya son faɗa mata yadda ya daɗe da daina ƙaunar Abba. Yadda zuciyarshi ta jima da sauyawa daga ƙauna zuwa wani abu da yake jin ya girmi tsana.
“Je ki sake kaya. Ki zo mu buɗe gifts ɗin tare.”
Murmushi tayi tana janye fuskarta daga hannuwanshi. Da ɗan gudunta ta wuce ɗakinsu.
Ɗakin Ummi da ya mayar nashi ya wuce. Don nan suke kwana shi da Tayyab, da safe ne Tayyab ke komawa ɗakinsu na asali.
Har yanzun babu abinda ya taɓa cikin ɗakin. Zuciyarshi ba zata iya bayar da kayan Ummi ba. Zai ta ajiye su ko da za su yi menene. Ƙananan abubuwa kamar su takalmanta da ‘yan kunnaye boxes suka yi suka haɗa su waje ɗaya.
Suma suna can gefe cikin ɗakin a ajiye. Sai dai in sun yi ƙura ya kakkaɓe ya gyara musu zama. Da ƙarfi ya doka ƙofar yana huce haushin da yake ji a kanta.
Nan ya zauna har sai da Sajda ta ƙwanƙwasa mishi ɗaki cewar ya fito su buɗe gifts ɗin kamar yadda yace sannan.