Skip to content
Part 15 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Ruwa ta kawo mishi, ta sam waje ta zauna, jikinta sanye da atamfa, fuskarta ta sha kwalliyar da zata baka mamaki a shekarunta. 

Far ta yi da ido tare da kallon Abba ta ce, 

“Alhajina kana faɗa min yadda kuka yi da yaran nan.”

Murmushi Abba yayi, abincin da ya gama ci ya mishi daɗi sosai. 

“Taurin kan Dawud na nan, yaron nan baya jin magana Wallahi. Kin ga yadda ya rufe ido zai min fitsara, wai ni yake ce ma in fitar musu daga gida. 

Har Tayyab ma, yaran duk sun girma.”

Murmushi Hajiya Beeba ta yi duk da a zuciyarta tana jin kamar ta aika musu da mala’ikan mutuwa, saboda yadda ya faɗi duk sun girman nan cike da kewar ba a gabanshi ba ya ɓata mata rai. 

Saboda siyasar nan da yake son tsayawa ta Senator ne kawai yasa ta ce ya dawo da su, kamar wasa daga siyasar kasuwa Abba ya fara. 

A hankali rayuwar ke tafiyar musu da ci gaba. Tasan da bunƙasar matsayin shi a siyasa da ci gaba da surutan da za a yi akan ‘ya’yan shi. 

Hakan zai iya tauye shi sosai da sosai. Shi ne kawai dalilin da ya sa zata bari waɗannan ƙadararrarun yaran su shigo rayuwarta. 

Balle Sajda da tunda suka yi maganar dawowarsu data tuno ta da abinda ya faru shekarun da suka wuce sai gabanta ya faɗi. Burin da take da shi a rayuwa yake ƙara tunzurata da dawowar sun. 

Tana son ta fita ana nuna ta cewar matar wannan ce, don ta tsani yadda Yayan Abba ya fi shi kuɗi, har da gina gidan gulma suka dawo ciki. Don dai kawai tsarin gidan ya mata kyau sosai ne yasa ta bari suka dawo. 

Kuma ko ba komai ta gama da matan ‘yan uwan shi suma, da ‘yan uwanshi ma da kansu, dawowar ba wani abu bace ba. 

Hira suka ci gaba da yi kan dawowar su Dawud ɗin. 

“Ya dai ce za su dawo da kansu, idan basu zo ba gobe zan koma.”

Girgiza mishi kai tayi. 

“Ka bar su sai satin nan ya ƙare, ka basu kwana bakwai, in basu zo ba sai ka koma.”

Da fara’a ya ce, 

“Hakan zai fi ko?”

Ta ɗaga mishi kai tana wani ƙasa-ƙasa da ido. Kafij ta tashi ta koma kusa da shi tana ci gaba da abinda ta saba wato kissa da salo kala-kala. 

**** 

Haka suka kwana ranar, babu wanda ya sake tayar da maganar zuwan Abba, don kowa da tsoron da yake ji na makomar yin hakan. 

Haka su dukkansu suka fita makaranta washegari banda Zulfa da ko jarabawarta ma bata fito ba balle. Daga ita sai Mami aka bari a gidan. 

Ranar haka ta zo ta wuce ma Dawud, fahimtar karatun ranar ya mishi wahala sosai saboda tunanin da yai mishi yawa a zuciyarshi da kanshi gaba ɗaya. 

Abu biyu suka saka shi a tsakiya, lafiyar ƙannen shi da farin cikinsu, a ɗayan ɓangaren kuma alƙawarin da ya ɗaukar ma Ummi. 

Har a zuciyarshi yana jin yadda barin alƙawarin Ummi ya riga da ya gama yin nasara, yasan ta hango abinda ba zai taɓa gani ba kafin ta sa yayi mata wannan alƙawarin. 

Ummi bata taɓa saka su yin abu babba haka ba babu wani dalili, ya yarda da ita akan wannan, kamar yadda ya yarda da ita akan komai. 

Sai dai abu ɗaya ne Ummi bata hango musu ba, yana zaton bata hango musu nisan shekarun da Abba zai ɗauka bai nemi su koma wajen shi ba. 

Bata hango kalar canjin da za su iya samu da ba za su buƙaci Abba a cikinshi ba ko kaɗan. Yana tashi wajen shida bai bi takan Tayyab ba. 

Don ba koda yaushe suke dawowa gida tare ba. Da abokanshi yake dawowa, ranar da yake son su dawo taren da kanshi yake zuwa ya neme shi. 

**** 

Sai dai ga mamakin shi a gida ya samu Tayyab, su dukkansu sun yi jugum zaune a falo, baka jin muryar kowa sai ta Khateeb da Mami. 

Sallamar shi ma, Mami ce kaɗai ta amsa, ya ƙaraso ya samu waje ya zauna. Kafin Khateeb ya dawo kusa da shi ya zauna yana ɗora hannayenshi a jikin Dawud ɗin. 

Yau ba shi da zuciyar da zai ji da Khateeb, abubuwa sun mishi yawa. Kallon su yake, baisan kalar tunanin da suke ba su dukkansu. 

Yasan shi suke jira, abinda ya yanke suke so su ji, in ya tayar da maganar su yi ta, in kuma ya zaɓi suyi shiru su manta da Abba ya zo gidan hakan za su yi. 

Nauyin girma da matsayin da suka bashi yake ji yana danne shi fiye da ko da yaushe. Wannan karon zaɓin na hannunshi, kuma yana nufin har da farin cikinsu gaba ɗaya. 

Muryarshi kamar wadda aka shaƙe ya ce, 

“Zamu koma, zamu koma wajen shi.”

Murmushi ne ya bayyana a fuskar Sajda, da sauri ta taso ta rungume Dawud da yake zaune a wajen kamar an dasa shi tare da sumbatar kuncin shi. 

“Thank you Yaya.”

Ta faɗi tana sakinshi ta ruga ɗakinsu da gudu, kallon shi ya mayar kan su Zulfa da Tayyab. Yana jin zuciyarshi na ciwo da kalar kallon da suke mishi. 

Zulfa kallonshi take kamar hukunci da ya yanke babban cin amana ne a wajenta, idanuwanta cikin nashi ta girgiza kai ta miƙe kawai ta nufi ɗaki. 

“Zulfa!”

Ko juyowa bata yi ba. Ɗakin Tayyab ta nufa wannan karon ba nasu ba. Da alama bata son ganin Sajda kamar yadda ya ga bata son ganin shi, da ƙarfin gaske ta doko ƙofar.

“I can’t believe za ka yi mana haka.”

Tayyab ya faɗi cike da wani yanayi a muryarshi da ya ƙara wa Dawud zafin da ƙirjinshi yake yi. Shima miƙewa yayi ya bi Zulfa. 

Saukowa Khateeb yayi daga kan jikin Dawud shima ya bi bayansu, yana kallon shi ya tsaya yana tunani kafin ya wuce inda Sajda take. 

Hannuwanshi na ɓari ya kawo su kan fuskarshi ya rufeta, ciwo zuciyarshi take yi na gaske. Kafin ya buɗe fuskarshi ya kalli Mami. 

“Mami sun tsane ni, ba laifina bane ba, ya zan yi? Na ma Ummi alƙawari, babu yadda zan yi Mami.”

Ya ƙarasa maganar yana jin wasu hawaye masu zafi na biyo fuskarshi da baisan ta inda suka fito ba. Ita kanta Mami yanayin maganarshi da abinda ke faruwa yasa hawaye zubo mata. 

Tabbas in kana da rai za ka ga rayuwa. Hannu yasa ya goge fuskarshi tare da jan wani irin numfashi kamar yana mishi wahalar zuwa inda ya kamata. 

“Babu yadda zan yi. Me yasa ba zasu fahimta ba? Rayuwar mu daban take, bazan iya kare su daga wasu abubuwan ba.”

Mami ta rasa abinda zata ce mishi, gaba ɗaya kalamai sun ɓace mata. Tana kallo ya miƙe, wajen bango ya ƙarasa kafin ya dunƙule hannunshi ya kai ma bangon duka da dukkan ƙarfin shi. 

“Dawud!”

Mami ta faɗi tana miƙewa, don yanayin ƙarar da ta ji tasan ƙasusuwan ‘yan yatsun shi sun samu matsala. 

Shi kanshi azabar da ta ratsa shi ko ba aikin likitanci yake karanta ba yasan ƙasusuwan ‘yan yatsun shi sun samu matsala. 

Ko guda huɗu basu karye ba, wasu cikinsu sun karye, sauran kuma sun samu damuwa, sai dai yana welcoming wannan ciwon da yake ji don shi sabo ne. 

Sabon ciwo ne da ya fi na ƙirjinshi sauƙi, kamar daga sama Zulfa da Tayyab suka fito daga ɗakin da suke ciki, don sun ji komai, Sajda ce kawai bata ji ba. 

Ita ma earpiece ne a kunnuwanta suna can suna shiririta da wayar Zulfa da ta bari a ɗaki ita da Khateeb. 

Da sauri suka ƙarasa inda Dawud ɗin yake tsaye da hannunshi da jini ke ɗiga ɗis ɗis. Zulfa ta kama hannun, tana kallon yadda ya Runtsa idanuwa. 

“Yaya me hakan yake nufi? Kamar abinda muke ciki bai ishemu ba?!”

Tayyab yake faɗi cikin ɓacin rai. Dawud ya ji idanuwanshi sun sake cika da hawaye. 

“Yazan yi Tayyab? Ina buƙatar distraction, ga damuwarku, ga damuwar inda zamu koma, ga damuwar rashin sanin lokacin da rayuwar mu zata yi dai dai. 

Alƙawari na yi wa Ummi, alƙawari nai mata duk ranar da ya nemi mu koma wajen shi zamu koma, ku yafe min don Allah.”

Tsugunnawa Tayyab yayi yana jin hawaye masu ɗumi na zubo masa, shima Dawud binshi yayi, haka Zulfa ma da hannun Dawud ke riƙe a jikinta. 

Tunda ta fito dama da kukanta ta fito, mayafin da ke kanta ta warware, ta saki hannun Dawud ɗin tana son keta dankwalin ta kasa. 

Tayyab ne ya karɓa, ya raba shi gida biyu, ta kamo hannun Dawud ɗin shikuma yasa tsumman yana naɗewa, kuka kawai suke yi. 

Ƙwace hannunshi Dawud yayi yana riƙo su jikinshi, hawaye ke zubar masa, baisan ranar da zai iya kare su ba, ya yi alƙawarin kare su ya kasa. 

Cikin kunnenshi Zulfa na kuka take faɗin, 

“Mu yi addu’a… Addu’a za mu yi Yaya, da Ummi tana nan haka zata ce mu yi.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, Hasbunallah Wa ni’imal wakeel…!”

Tayyab ya soma faɗi a fili, kafin suka ɗauka suma, hannu Mami ta kai tana goge hawayenta kafin a hankali ta bar musu falon. 

Abu ɗaya ta koya a zamanta tare da su, ƙarfin zumunci da ƙaunar dake tsakanin ‘yan uwa tana nasara a kodayaushe. 

Ko da sun rasa ƙarfi, ko ta ina rayuwa ta gwarasu za su kama hannuwan juna, zasu haɗa ƙarfin su, za su nemi taimakon Allah, zasu sake miƙewa. 

Kuka suke suna roƙon Allah da Ya kawo musu sauƙi don basu da kowa sai Shi. Kuka suke suna riƙe da junansu. Muryar Tayyab na rawa ya ce, 

“Zamu koma Yaya, zamu tayaka cika alƙawarin Ummi, komai zai canza…..”

Girgiza kai Zulfa ta yi, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, 

“Ba komai ba….. Ba komai zai canza ba…. Abba zai iya ƙwace abubuwa a rayuwar mu, amma banda ƙaunar da ke tsakanin mu.”

Da ƙwarin gwiwar da Dawud ya rasa ya ɗago kanshi, ɗayan hannunshi yasa yana goge ma Zulfa fuskarta, kafin ya ƙarasa ya goge ma Tayyab tashi yana girgiza musu kai. 

A tare suka kai hannuwansu don su goge mishi nashi hawayen. Muryarshi a dakushe ya ce, 

“Kai bana so…..”

Yana ɗaure fuska. Basu san lokacin da dariya ta kufce musu ba. Riƙe shi Tayyab yayi Zulfa ta sa hannuwanta tana goge mishi fuska. 

Ya na ture su da hannunshi mai lafiya. Sun yi gaskiya, ƙaunar su ba zata taɓa sakewa ba, ko da komai zai ci gaba da zame musu sabo a kullum, suna da abinda yake familiar na har abada.

**** 

Rayuwa suka ci gaba da yi kamar Abba bai zo ba. Dawud na kula da Sajda, yadda take ware mishi idanuwa duk idan ya shigo tana son tambayarshi yaushe za su koma. 

Hakan yasa ya zaunar da ita ya faɗa mata cewa jarabawa zai fara, sai ya gama tukunna zasu koma. Cikin sati biyu dawowar Abba uku gidan. 

Yadda Dawud ya faɗa ma Sajda cewar sai ya gama jarabawa haka ya faɗa ma Abban. Amma da alama bai yarda da maganar da ya faɗa mishin ba.

Don yanzun haka da Dawud ke zaune a ƙofar gida da handout ɗinshi yana hango motar Abban tana tahowa, ya ja numfashi yana fitar da shi. 

Ba ƙaramin ƙoƙarin tsayawa yake yayi wa Abba magana cikin hankali da nutsuwa ba, bayan babu abinda yake so yayi daya wuce ya mishi ihun da yake jin yana taruwa akanshi har sai ya ɓace ya fita daga rayuwar su gaba ɗaya. 

Ganin shi da jin muryarshi bakomai bane a wajen Dawud sai takura da tsanarshi da ke ƙaruwa. Yana kallonshi yayi parking tare da buɗe motar ya fito. 

Har inda Dawud yake ya ƙaraso, hannu yasa ya taɓa wajen yana so ya ga ko da datti, kafin ya zauna, kamar wanda aka tsira ma wani abu Dawud ya ƙara matsawa. 

Abba na kallonshi da alama baya son jikinsu ko kaɗan ya haɗu, ya rasa me yaron nan yake ji da shi haka. 

“Kai baka iya gaisuwa bane?”

Kallon shi Dawud yayi da wani irin na yanayi, kafin ya maida hankalinshi kan takardun da ke hannunshi. In bai yi focusing kan wani abu ba matsala za a samu. 

Saboda Ummi kawai, don Ummi yake jure duk wannan abin. Haka ya ci gaba da faɗi a cikin kanshi da zuciyarshi. Ganin ba shi da niyyar cewa komai yasa Abba cewa, 

“Na ga shiru baku zo ɗin bane, yasa na ce bari inzo mu tafi.”

Muryar Dawud can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Bansan sau nawa zan maimaita magana ɗaya ba, zamu zo da kanmu, sai na gama jarabawa nan da sati uku masu zuwa.”

Sosai ran Abba ya ɓaci. Don Hajiya Beeba ta ce mishi Dawud ɗin raina mishi hankali yake shi yasa yau a 360 ɗinshi ya taho. 

“Dawud karka raina min hankali don ka ga ina lallaɓaka, zan iya maka ku kotu ku dawo dole. Zanbarka sati ukkun ne in ga gudun ruwanka. 

Da sharaɗin in baka dawo ba duk matakin da na ɗauka ka ɗora laifin hakan a kanka.”

Kallonshi Dawud yake cikin fuska yana mamakin alaƙar ɗa da Uba dake tsakanin su. Don babu komai a zuciyarshi banda tsanar mutumin nan da yake ji har bayan zuciyarshi saboda ta cika fal. 

“Ba kai kaɗai kake da sharuɗɗa ba. In zamu dawo gidanka zamu dawo har da Mami.”

Cike da rashin fahimta Abba ya ce, 

“Wacece Mami?”

So yake ya faɗa mishi itace matar da ta zauna tare da su lokacin da basu da kowa, lokacin da su Sajda suke neman soyayya ta uwa, lokacin da suke cikin ɗanyen maraici. 

Sai dai baida lokacin da zai yi asara yana wa mutumin nan bayani. Don haka ya ce, 

“Ka ganta ranar da ka zo, da ita zamu koma.”

Abba yasan da wuya Hajiya Beeba ta amince da wannan abin, Dawud na kallon rashin amincewa a fuskar Abban tun kafin ya furta hakan. 

“Babu inda za muje babu Mami. In ka shirya komawarmu ka shirya har da tata, in baka shirya ba ka aiko min lau yanka.”

Dawud na ƙarasa maganar ya tattara sauran takardunshi da ke ƙasa ya haɗa su da na hannunshi sannan ya miƙe ya shige cikin gida ya doko ƙofar kamar ita tai mishi laifi. 

Idanuwanshi ya sauke kan na Mami da ke zaune. 

“Lafiya dai Dawud?”

Ta buƙata, ƙarasa takowa yayi ya ajiye takardunshi kan kujera, daga tsayen ya dafe goshin shi. 

“Mutumin nan ne ya sake dawowa Mami, na gaji Wallahi.”

“Zauna.”

Mami ta faɗi, kallonta yayi, zai buɗe baki yayi gardama ta sake faɗin, 

“Dawud ka zauna…”

Zaman yayi yana sauke numfashi. 

“Ko da kake ganin shi a haka, mahaifinka ne, babu abinda zai canza hakan, ko da kaine da kanka. Na ji ka ya rasa wannan damar lokaci mai tsawo da ya wuce. 

Ka ce saboda Ummi kake komai da kake a yanzun ba? To haka za ka yi haƙuri da shi, wata rana komai mai wucewa ne. 

Ka daina barin abinda yake yana zauna maka a cikin kanka don Allah, jarabawa kake, karka sa damuwar komai a ranka. Kuma ma ba gani ba?”

A hankali ya ɗaga wa Mami kai, da idanuwanshi yake nuna mata yadda girman karamcinta yake a wajenshi. Murmushi tai mishi ya miƙe ya ɗauki takardunshi ya wuce ɗaki. 

Ruwa ya ɗan watsa ma jikinshi, jeans ya saka baƙi da riga fara kamar yadda shigarshi ke kasancewa yanzun kusan ko da yaushe sannan ya fito. 

“Mami na ɗan fita, ba daɗewa zan yi ba.”

“Allah ya tsare hanya, ya dawo da kai lafiya.”

Ta faɗi, ya amsa da amin. In takan mishi abu irin haka sai ya ji kama Ummi, murmushi yayi ya fice zuciyarshi cike fal da wata nutsuwa da tunanin Ummi kaɗai ke haifar da ita. 

**** 

Ba wani waje zashi ba, kawai yana son ya ɗan taka ne. Don in tunanin yai mishi yawa, haka yake yi yakan samu sauƙi ya kuma ji kanshi ya ɗan samu iska ko ya take. 

Earpiece ɗinshi ya maƙala a kunnen shi ya jona da wayarshi yana playing waƙoƙin Sahwa. Ya mayar da wayar a aljihu tare da saka hannayenshi duka. 

Ba zai ce ga inda yake zuwa ba, a nutse yake tafiya abinshi, waƙoƙin da yanayin sautinsu na ƙara tuna mishi Ummi, tana son waƙoƙin Sudanese sosai.

Ji yayi kamar ana magana, kasancewar ba wai ya ƙure gaba ɗaya sautin wayar bane. 

“Malam……. Malam…..”

Ya ji kiran na matsowa kusa da shi, kuma kamar da ƙarfi wannan karon, hannunshi ɗaya ya zaro daga aljihunshi ya cire earpiece ɗin kunne ɗaya tare da juyawa a hankali. 

Sai maida numfashi take, ba sai ya tsaya neman inda ya taɓa ganinta ba, don yanzun ganinta yasa wani ɓangare na zuciyarshi da ya rasa tunanin meye a wajen matsowa kusa. 

Ita ce ajiye a wajen, tunanin yanayin da ya gani a fuskarta da idanuwanta bai barshi ba, ya yi shiru ne saboda akwai abubuwan da suka fi shi girma. 

Zai yi wahala ta wuce sa’ar Sajda, ko zata girmi Sajda ba zai zama da yawa sosai ba, a daƙune fuskarshi take yayin da yake kallonta yana mamakin me take yi a wajen. Ko me yasa take kiranshi. 

Kayan da ke jikinta yake kallo, atamfa ce da ba zai ce skirt bane ko zani saboda hijabin dake jiki, sai dai takalman ƙafarta, silifas ne, sun suɗe sosai da sosai. 

Ji yayi sam bai ji daɗi ba, baya son ganinta da takalman ya kuma rasa dalili. Yana kallon yadda hannuwanta ke lalube jikin ƙugunta ta cikin hijab ɗin kafin ta ciro ko meye take nema. 

Ta fito da hannunta na dama, ta miƙa mishi, kuɗi ne sun cukwikwiye ba kaɗan ba. 

“Ina ta nemanka, ko budurwarka ban sake gani ba, dubu ɗaya da ɗari uku ne kuɗin awarar, yayi yawa, ina so in baka canjin ka ban ganka ba.”

Baisan lokacin da ya ce mata, 

“Ba budurwa ta bace, kanwata ce…” ba

Kuɗin da ke hannunta yake kallo, da yanayinta, ba zai iya tuna ko tun yaushe abun ya faru ba, zai iya kai wata biyu. Yanayinta ya nuna tana buƙatar kuɗin sosai amma tanata ajiyarsu. 

Ba kowa yake da zuciya irin tata ba. Burge shi tayi sosai. 

“Me yasa baki kashe ba?”

Ya buƙata, girgiza mishi kai tayi. 

“Ba nawa bane ba”

“Ki ɗauka nabar miki.”

Sake girgiza mishi kai tayi, tana ƙara miƙa mishi kuɗin. Idanuwanta cike da tsoro. Baya son ganin tsoron a cikinsu ko kaɗan. 

Ƙara miƙo hannun da tayi yasa shi kula da ciwon dake jiki. Da sauri ya ce, 

“Ciwo ne a hannunki? Dame kika ji wannan ciwon?”

Ya ƙarasa maganar yana ƙara matsawa yana kallon hannun sosai. 

“Buɗe in gani.”

Ya faɗi, dayan hannunta ta ciro ta riƙe kuɗin da shi tana buɗe mishi tafin hannunta sosai, ƙonewa ce sosai a hannunta, tun daga cikin tafin hannunta har ya sauka kan fata. 

“Wannan ai ƙonewa ce, ya akai a buɗe haka, ba a kaiki asibiti ba?”

Ya buƙata yana kama hannun ya duba sosai, da ƙyar in bai zama infected ba. Shirun da ya ji tayi ne yasa shi ɗagowa ya kalli fuskarta. 

Ga mamakin shi hawaye ya gani cike fal da idanuwanta da ya fi tsoron da ke cikinsu ɗazu taɓa mishi zuciya. Zubowa suka yi akan kuncinta, ta sa ɗayan hannunta ta goge su. 

Dube-dube dawud yake har ya hango wata bishiya can tsallakensu, hannunta ya saki, don har ranshi yake jin riƙe shin da yayi na mishi wani iri. 

Sanin ba halacci a cikin hakan, duk da yayi ne da niyya mai kyau. 

“Mu tsallaka can.”

Ya buƙata, bata yi musu ba ta bi bayanshi. Har suka ƙarasa wajen bishiyar da bulalluka birjik, saboda ginin da ake yi a kusa da wajen. 

“Zauna…..”

Ya faɗi yana nuna mata ɗaya daga cikin bulallukan. Babu musu ta zauna, tsugunnawa yayi a gabanta, idanuwanshi kafe kan fuskarta. 

“Garin yays kika ƙone?”

Yanayin tambayar da yayi babu wajen musu ko gardama a cikinta yasata tsura mishi idanuwanta itama, wannan ne karo na biyu da ta taɓa ganinshi. 

Amma wani abu a zuciyarta yana faɗa mata zata iya yarda da shi, a fuskarshi take ganin babu abinda yake so da ya wuce ya taimaka mata. 

Muryarta can ƙasa ta ce, 

“Mami ta ƙona ni.”

“What?!”

Dawud ya faɗi har sai da ya ɗan tsorata ta, hakan ya kula, ya ja numfashi yana fitar dashi. 

“Wacece Mami?”

Muryarta na rawa ta ce, 

“Matar Baba ce……”

So yake ya fahimci abinda yake faruwa a gabanshi, so yake tai saurin faɗa mishi ba abinda zuciyarshi ke faɗa mishi bane yake faruwa da rayuwarta. 

“Ina mamanki? Yayyenki? Da shi Baban har ta ƙona ki?”

Wani hawayen ne ya sake zubo mata, da sauri Dawud ya haɗe hannayenshi waje ɗaya yana riƙe su, saboda babu abinda yake so daya wuce ya goge mata hawayen nan dake zubo mata. 

“Baba baya nan, ko yana nan baya hanata. Mamana ta rasu, banda yayye ko ɗaya, ni kaɗai ce a gidanmu.”

Kai yake jinjinawa, magananganunta na taɓa shi har zuciyarshi, ya fi kowa fahimtar me take ciki, ya fi kowa gane halin da take ciki. 

Sosai yake kallonta yana jin ranshi na ɓaci da kalar rashin adalcin da take ciki, su Sajda na da shi amma har yanzun baya iya hana rayuwa daina taɓa su, balle yarinyar nan da bata da kowa. 

Tsanar Antyntan nan da ta faɗi ya cika mishi zuciya, yana jin da yana da wani ƙarfin iko zai sa aita nemo masa irin su ana kulle su, a kulle su can wata duniya da ba za su fito su cuci yara irin haka ba. 

Hannunta ya sake kallo, ba ƙaramin marar imani bane zai ma ko dabba abinda akai mata, balle ɗan Adam. Baya son sanin dame ta ƙonata ko ta yaya. 

Saboda ƙara bata mishi rai zai yi. Muryarshi a dakushe ya ce, 

“Ita kike siyar ma awara?”

Kai ta girgiza mishi, a sanyaye ta ce, 

“‘Yar unguwarmu ce, in ina jin yunwa ina roƙarta saita bani inyi ta ban abinci.”

Hannunshi yasa ya dafe fuskarshi, har da Baban yarinyar nan ya tsana, irin su ɗaya da Abba. Bai ga banbancin su ba, da shekarun yarinyar nan zata iya shiga wani hali saboda yunwa. 

Buɗe fuskarshi yayi ya ce mata, 

“Makaranta fa?”

“Soba nake, ta kwana, tunda na dawo hutu wancan term ɗin ban koma ba, uniform ɗina sun lalace, Anty ta ƙi faɗa ma Baba, kuma har da litattafai ba a siya min ba.”

Da duk kalma ɗaya da zata faɗi da yadda ranshi yake ƙara ɓaci da rashin adalcin da take ciki. Yadda ta ga fuskarshi na sauyawa yasa ta ɗorawa da,

“Anty ta ce da ta samu kuɗi zata siyamun, ta mayar dani kuma.”

Dabara ce ta faɗo ma Dawud. 

“Baba zai bari Antyn ta mayar da ke?”

Kai ta ɗaga mishi. Miƙewa yayi. 

“Muje ki rakani wajen Antyn.”

Babu musu ta miƙe. Tafiya suke shiru, yana jin yadda zuciyarshi ke zafi da labarin yarinyar nan. 

“Ya sunanki?”

Ya buƙata, sai da ta ɗan yi jim sannan ta ce mishi,

“Fatima. Sunan kakata ne, mamana tana cemun Yumna, yana nufin kyauta, ta ce saboda ni kaɗai ta haifa.”

Ya maimata sunayen nata duka biyun, sun yi mishi daɗi. Tafiya suka yi sosai da Dawud ba zai ce ga lungunan da Yumna take bi da su ba, sam tunanin shi ba akansu yake ba. 

Har suka kawo ƙofar wani ƙaramin gida, daga wajen gidan zai nuna maka cewar na talakawa ne sosai. 

“Shiga sai ki faɗa wa Antyn ina so mu yi magana.”

Wucewa Yumna ta yi ciki, hakan ya ba Dawud damar zaro wallet ɗinshi, ƙirga kuɗin ciki yayi, dubu takwas da ɗari biyar ne. 

Yasan yana da kuɗi a account ɗinshi, sai dai ba nashi bane shi kaɗai, nasu ne gaba ɗayansu, na hidimarsu ne da Labeeb yake tura mishi duk wata. 

Sai dai ciki ba zai rasa cirar wanda zai taimaka ma Yumna ba, da ba a taimaka mishi ba bazai taɓa kawowa haka ba. 

Mayar da wallet ɗin yayi, bayan ya kwashe kuɗin ya saka su cikin aljihunshi. Yumna ta fara fitowa sannan wata mata ta biyo bayanta, ba wata babba bace, saidai yanayi na rayuwa. 

Gaisawa suka yi da dawud cikin mutunci. 

“Lafiya dai ko?”

Ta buƙata a ɗan tsorace, don tunda Yumna tace mata wani ne suka zo tare yana son magana da ita taji ta tsorata. Numfashi Dawud ya ja ya fitar da shi. 

“Lafiya ƙalau, bansan ta inda zan fara ba, banma san me zance bane da ya wuce in faɗa miki nafi kowa fahimtar halin da Yumna take ciki.

Sai dai ni ina zagaye da mutanen da basu bari rayuwa ta kaini ƙasa ba. Ina son zame mata hakan, duk da ba lallai ki yarda da ni ba…..”

Da mamaki take kallon Dawud ɗin, hannu yasa ya zaro duka kuɗin, ya miƙa mata yana faɗin, 

“Ki fara siya mata abinda take buƙata na makaranta, in sha Allah zan dawo in ƙara wani akan wannan ɗin. “

Kuɗin tasa hannu ta karɓa, su duka ita da Yumna sun rasa abinda zasu ce. Daga yanayin Dawud Anty ta ji ta yarda da yaron, gashi da gani ba wani shekarun kirki ne da shi ba. 

Sai dai hankali da nutsuwar shi a bayyane yake. 

“Allah ya taimake ka kamar yafda ka taimaki marainiya. Allah ya sadaka da dukkan alkhairi…..”

Anty ke faɗi muryarta na rawa. Yumna kallonshi take itama, kuɗin ɗazu ta fito da su, ta sake miƙa mishi, girgiza mata kai yayi. 

“Ki ba Anty ta kaiki a sa miki magani a ciwonki. “

Kanta ta saddar ƙasa.

“Na gode.”

Kalma ɗaya ta faɗi, amma yana jin ma’anar godiyar da fassarori da yawa. Ɗan ƙaramin murmushi yayi. 

“Zan koma, saina dawo ko Yumna?”

Da sauri ta ɗago kanta, hakan yasa Anty yin sallama da Dawud tare da ƙara yi mishi godiya ta koma cikin gida. Kawai Yumna sai ta tsinci kanta da son kar ya tafi. 

Don zuwanshi ya bata wani irin yanayi na daban. 

“Zan dawo Yumna. I promise, mu haɗu inda kika ganni yau.”

Kai ta ɗaga mishi, ya ɗan mata murmushi yana wucewa. Da sauri ta ce mishi, 

“Bansan sunanka ba”

Bai juyo ba yace mata. 

“Dawud….”

Nanata sunan ta ci gaba da yi har saida ta daina hango shi. Sannan ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah da yau ya amsa addu’ar ta. Tana jin ya turo mata wanda zai taimaka mata. 

****

Washe gari banki kaɗai ya fita tunda wuri, ya ciro dubu goma, ya riƙe biyar yaje ya samu Yumna a inda yace matan. 

Basu wani jima ba don ta ce Anty zata mayar da ita makaranta a ranar, kasancewar an ci sati har uku cikin term ɗin. Gani na uku kenan yai mata, haka ya dawo gida zuciyarshi cike da kewarta. 

Yanayin maganarta, murmushinta, komai nata ya tsaya mishi a zuciya, yasan shi da ya sake ganinta kuma sai lokacin hutu. 

Miƙewa yayi daga kwanciyar da yayi, gaba ɗaya kasala yake ji ta babu dalili. Kitchen ya nufa inda Mami ke girki. 

“Mami sannu da aiki.”

Ya faɗi, ta amsa shi da murmushi. Maggi ta ɗibo ta miƙa mishi don ya ɓare mata. Tasan abinda ya shigo da shi kitchen ɗin kenan. 

Halin Dawud daban ne. Sai dai in baya gidan zata yi aiki. Zai tayata, duk da daga Sajda har Zulfa basu da ƙyuyar aiki indai suna nan. 

Amma dawud kan bata mamaki, yadda ko kwanoni take wankewa zai tayata. Tun tana ce wa ya bari har ta ƙyale shi. 

Dawud a nashi ɓangaren, yanayin nan ba ƙaramin tuna mishi da Ummi yake yi ba, yakan ji ya rage kewarta ba kaɗan ba. 

Hirarrakin su na dawo mishi sosai a lokuta irin hakan. Ƙwanƙwasa gidan suka jiyo. Dawud ya bar Ummi ya wuce falon ya ƙarasa ya buɗe gidan. 

Zulfa ce, fuskarta kawai da ya gani babu kwalliya yasan ba lafiya ba. 

“Menene?”

Ya tambaya yana jin zuciyarshi na dokawa. 

“Yaya Labeeb ne…..”

Wani abu Dawud ya ji tun daga ɗan yatsan ƙafarshi har cikin cikinshi ya yamutsa. Kallon Zulfa dake mayar da numfashi yake yi yana son ta faɗa mishi ko me ke faruwa. 

“Muna gida a zaune, ya shigo, bai fi mintina goma ba motar ‘Yansanda suka zo har biyu suka tafi da shi.”

Yama kasa fahimtar abinda Zulfa take son faɗa mishi. 

“Yansanda? El ɗin? Me yai musu?”

Wayarshi yake lalubawa a cikin aljihunshi ya rasa ta, juyawa yai yana duddubawa cikin falon ya hangota kan kujera. 

Ɗauka yayi, ya cire key ɗin daga inda yake yana faɗin, 

“Mami kin ji wai ‘Yansanda sun kama El.”

Da sauri Mami ta fito daga ɗaki tana salati. 

“‘Yansanda kuma? Me yake faruwa ne?”

Lambar Labeeb Dawud yake trying ta ƙi shiga. 

“Ban sani ba Mami, inata kiran lambarshi ta ƙi shiga.”

“Ka kira ko su Anees mana…”

Lambar Anees ya kira, har sau huɗu ba a ɗauka ba. Ya kalli Mami ya ce, 

“Bari kawai in je gidan.”

“Abinda zance kenan yanzun. Ka je gidan shi zai fi.”

Kai ya jinjina ya wuce ɗaki ya ɗauko mukullan shi, yana fitowa falon dai dai shigowar Tayyab.

Sallama kawai yayi bai ma jira sun amsa shi ba ya ɗora da. 

“Me nake ji yana yawo a makaranta? Matar Yaya Labeeb na neman saki saboda dukan da yake mata and…..”

Mami ya ɗan kalla yana kasa ƙarasa maganar saboda nauyinta. 

“And?”

Dawud ya buƙata yana son jin ƙarshen maganar, ɗan sauke murya Tayyab yayi. 

“And he is gay…..”

“Subahanallah, wanne irin magana ne wannan Tayyab?!”

Ɗan ɗaga kafaɗa Tayyab yayi yana rausayar da kai gefe. 

“Wallahi abinda yake ta yawo kenan a makaranta, shi ne fa na taho gida inji.”

Dafe kai dawud yayi, wannan abin babba ne. Gida suka bar Zulfa, shi da su Tayyab suka wuce gidan su Labeeb. 

****

Gaba ɗaya sati biyun da suka zo musu bayan ranar a birkice suka yi shi basu da kwanciyar hankali, ga zaman kotu da Zafira da Labeeb suke tayi. 

Sharri kala-kala, babu wanda bata liƙa ma Labeeb ba, mafi munin ciki shi ne luwaɗin da ta jefe shi da shi. Sai dai babu wata shaida. 

Sai rantsuwa da yayi wanda aka yi juyin duniya da Zafira itama ta rantse ta ƙi. Haka aka sallami ƙarar da tara mai yawan gaske kanta wanda Labeeb yace baya buƙata. 

Yanzun haka zaune suke a falon gidan su Labeeb ɗin, dashi da Mamdud, Dawud sai kuma su Asad. 

“Nifa banga dalilin da zai sa ka ce ba zaka karɓi kuɗin nan ba.”

Cewar Asad. 

“Ni kaina bangani ba, tunda bata da mutunci.”

Dawud ya faɗi yana gyara zaman shi cikin kujerar. Anees ya kalle su. 

“Kuɗi ba zasu taɓa wanke fentin da ta yi mishi ba, za’a kwana biyu kafin abin nan ya ɗanyi ƙasa, gogewar shi kam da wahala”

A gajiye labeeb ya ce, 

“Kawai bana son duk wani abu da zai sake haɗa ni da ita. Aurenta was a terrible mistake.”

“Wannan kalamaina ne, ka samu naka daban.”

Zainab da ke fitowa daga ɗaki ta faɗi tana wucewa abinta. Dariya Asad yayi. 

“Kuma gaskiyan Zeezee sai da ta faɗa maka, bata ga amfanin auren nan ba. Ka jira right girl ka ƙi yarda.”

Dariya Mamdud yayi, Labeeb ya harare shi yana miƙewa. 

“Nikam bacci nake ji. Na ga alama babu gajiya a jikinku.”

Ya ƙarasa yana wucewa ya bar su a nan falon. Dawud ma miƙewa yayi yai musu sallama ya nufi gida. 

<< Prev | Next >>

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 14Rayuwarmu 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.