Skip to content
Part 33 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Dukkan mu mun shagala sosai a cikin tadin soyayya mai ratsa zuciya, bamu san lokaci ya ja har sha biyun dare ba. Sai gyaran muryar Young Abba muka ji a bakin kofa. 

“Mr & Mrs Mawonmase, zan rufe gida na haka, na ga alama baku san zuru ba.”

Dariya yayi, nikuwa na sunkuyar da kai, “Tuba nake Abba yanzu zan tafi dama, amma don Allah ka roka min Siyam ta cigaba da kira na da sabon sunan data saka min yau. Oh me!” 

Ya fada yana rungume hannayen sa a kirji. Young Abba ya kai masa rankwashi a tsakar ka, ya ce “zan sa kafar wando daya daya da kai Hamzah, idan baka maida min matsayi na na suruki ba, Hamzah, i’m not your friend wai don muna sa’annin juna, but an in law.”

Ni dai tunda na samu Young Abba ya dauke masa hankali na sulale na gudu. Ba jimawa na ji tashin motar sa ya bar gidan. Na daga labule ina kallon sa yana fita daga harabar gidan mu, tamkar tare da tsokar dake tsakiyar kirji na yake tafiya.

A yau barci gagara ta yayi, sabida farin ciki da kuma doki, dokin garin Allah ya waye in dangana da Ya Omar, ba shakka hanyar shiryawa ta da Abba ta zo min in dai da gaske Hamzah Omar ya gani ya kuma sani ba wai mai kama da shi bane. 

Washegari da safe muna shirya kalaci na gayawa Aunty komai amma na roke ta kada ta gayawa Young Abba tukunna sai mun gan shi yau, mun tabbatar shine. Ni kuma ina da plans, shi kuwa Young Abba yana jin an ga Umar zai doka waya ya gayawa Abban Abuja.

Aunty kusan ta fi ni dokin karfe goma na safe tayi, don haka abincin ma bamu tsaya cin sa ba, a food warmer muka zuba muka tafi dashi da niyyar in mun samu nutsuwa sai mu ci.

Karfe goman kuwa ina zaune gaban kujerar dake fuskantar Aunty a ofishin ta. Lokacin da Mr. Hamzah ya murda kofar ya shigo da sallama dauke a bakin sa, Young Abba ya gaya masa ko’ina zai shiga yayi sallama maimakon yace “Hello”, haka a cikin waya. Is better ya ce “salamu alaykum warahmatullah” maimakon “Hello”. Shi din kuma sai aka yi sa’a mai kiyayewa ne kuma mai saurin daukar duk abinda Young Abba ya gaya masa.

Ya gaya masa again ko yayi sallama kada ya shiga waje sai an fara yi masa izini, duk yadda yake da mutum din da ya zo wajen sa, don haka yanzun ma da ya yi sallamar bai shigo har sai da Aunty ta ce masa. 

“Wa alaikumus-salam warahmatullah. Come in Sir”.

Kodaya ya shigo da korafi ya fara, a kan “Sir” din da Nasara ta ce masa, “ni fa yanzu ina kasan ki, tunda a wurin ki nake nema, girman naki ne, da girman kujerar ki Aunty Nasara”. Ya fada yana russunawa a gaban tebirin ta, alamar ya karya mata hula. “Sabahul khair Umman mu”. Duk sai ya bamu dariya.

Harara ta yayi, wata irin harara cikin zallar SO, wadda ba ni kadai ta baiwa kunya ba har Aunty Nasara saida ta kauda kai kamar ta nitse a wurin. Kallon dake cikin idanun sa means a lot; korafi ne? Soyayya ce ko kuwa fushi ne? Don jiya tun rabuwar mu ban kara kiran sa ko amsa nasa kiran ba), ko kuwa hararar ta Soyayya ce zallah? Ko ta kyawun dana yi masa cikin Egyptian Jilbaab dana sanya ne? Koko tsananin yadda ya matsu garin Allah ya waye yayi tozali da Siyam ne? Shi kadai ya bar ma kan sa sani.

Barcin daren jiya baki daya wahalalle ne a gare shi. Ga kadaici, ga maraici, ga soyayyar data kara yi wa zuciyar sa katutu, a dan zaman fahimtar junan da suka yi a ranar. 

A wani bangaren, tsananin sha’awar Siyam din da ya kwana da ita. Har yake ganin ba zai iya hakurin wadannan watanni ukun da Young Abba ya dibar masa ba kafin ya samu annual leave su tafi Najeriya neman auren Siyam. Dole ya nemawa kan sa alternative.

“We can go now (zamu iya tafiya yanzu)”. Na dauki jakar Anty sannan na dauki tawa muka rufa masa baya. 

Shine a gaba, motar mu na bayan tasa. Muna tafe Aunty na fadin “Mr. Hamzah is amazing! Na yi miki murnan samun miji daya da daya diyata, Allah ya tabbatar mana da dukkan alkhairin da ke ciki, ya kade fitina yasa ku abokan rayuwar juna na har abada ne.

A baya kam, ko kusa ban yarda zai yi miki irin son da na fahimta a tare da shi yanzu ba, in na yi la’akari da cewa wayewar ku da tarbiyyar ku ba iri daya bace. To amma Shi Allah haka yake shirya al’amarin sa, baka taba sanin wanene mijin auren ka sai lokacin yayi. 

Har yanzu kuma ina iya hango gagarumar rigima a gaban mu daga Ummati, ta fannin Abban ki bana jin zai yi wani action tunda dama ba wai ya yafe bane.”

Idanuna suka cika da kwallah, ina ji a rai na idan aka hana ni auren Hamzah babu makawa karshen rayuwa ta ya zo. Ban san ina son sa ba sai yanzu da ya musulunta, ya ke kwaikwayon attributes da dukkan dabi’un musulmi yadda ya kamata, koda yake dama can a baya kusan cikin su yake.

Hatta sallama da Young Abba ya koya masa ya gaya masa cewa akwai koyarwar christianity da yawa da take kamanceceniya da koyarwar musulunci, kamar neman izni kafin shiga waje sai dai ba ta hanyar sallama da musulmi ke yi ba suma suna knocking wato kwankwasa kofa.

Mun isa daya daga branches na bankin JP Morgan a can hanyar fita cikin City, Hamzah yayi parking a bayan Anty, sannnan ya fito ba tare da ya kulle motar ba yace mu jira shi, kawai kiran sa zai yi ya fito sai mu tabbatar idan shi ne ko kama ce.

A wannan lokacin kada ki so ki tona yadda zuciya ta ke azalzala da anxiety (zullumi da taraddadi). Kafin Hamzah ya dawo tare da wani bakin mutumin Cameroon, wanda tun daga nesa na san ba Ya Omar bane. Haka damuwar data nuna a fuskar Hamzah ta kasance abinda ake kira “labarin zuciya” hausawa suka ce wai “a tambayi fuska”. Ko dai bai samu Omar ba, ko kuma wani mummunan al-amari ya faru da Omar din. Na yi maza na damki hannun Aunty wadda ke zaune a gefe na. Ta rike yatsuna cikin nata tana fadin “cool down Siyama, khair zamu ji insha Allah”,

Daidai nan Hamzah ya karaso, sai kawai ya bude bayan motar mu ya shiga ya zauna yana maida numfashi cikin damuwa, mutumin da suka zo tare yana tsaye daga waje, ya ciza siririyar fatar bakin shi kafin ya ce “I’m Sorry Siyam. Faruk Gidado ya bar (JP Morghan) wai, ya koma aiki da wani banki a England wanda su duka abokan aikin sa basu san ina ne ba.”

Kawai sai na rushe da kuka ina fadin “Ya Omar, meyasa? Ashe Allah bai yi zan gan ka cikin sauki ba alhalin mun rayu a muhalli guda?” 

Daga shi har Aunty Nasara hakuri suke bani kuma hakika sun tausaya min, sun gayamin inda rabo zamu gana ba da jimawa ba, kuma tunda har Omar yana lafiya irin haka amman yaki neman kowa in rabu da shi kawai, in sanyawa zuciyata salama a kan sa, akwai abinda yake nufi da kin dawowar yana da target din sa na yin hakan.

Amma na kasa hakuran, Omar shi kadai ya rage min a matsayin tsanin da zai gyara tsakani na da Abba gashi ya kara yi min nisa.

Don haka ban koma ofis ba gida nace Aunty ta maida ni. Sai da ya rako mu har gidan a tashi motar tamkar wani mai tsaron lafiyar mu. Na fito zan shiga gida shima ya fito da motar shi yana taku da sassarfar shi zuwa gare ni. Saura bai fi taku biyu ba mu hade ya ja birki yana fadin.

“Take it easy Habeebty, komai kika ga Allah ya tsara yana da manufa, kada kije ki kulle kan ki agida kisa damuwa a ran ki. I’m sure Omar is more than fine and absolutely healthy. Na fi kyautata zaton Omar yafi son sai kin yi aure kafin ya dawo, kada ya dawo Abba ya sake tursasa ku a karo na biyu.

Don haka Siyam kin yi min iznin neman auren ki? Na yi miki alkawarin ba zaki nadamar zabe na a matsayin miji ba.

Kawai sai naji kuka na ya karu, na yi ta yi a fili har da sheshsheka. Aunty ta karaso tana ce da Mr. Hamzah da ke neman sakin layi cikin matsananciyar damuwar kada rashin ganin dan uwa na yasa na ce na fasa auren sa, in hakan ta faru baya jin zai kara yarda da soyayyar diya mace. 

“Kyale ta kawai mu shiga gida zan rarrashe ta Mr. Hamzah, tana bukatar nutsuwa”. A zafafe ya ce “ai lallashin nata nake yi aunty. Ko kina ganin akwai wanda zai iya lallashin ta sama da ni Aunty? Ki bar ni ta gaya min rashin ganin Omar zai hana tabbatuwar auren mu ne? Ban gane dalilin wannan kukan fitar ran data ke yi ba don bamu samu ganin Omar ba, da na sani ban gaya mata na san shi ba.

Ina ce dai Omar ba yaro bane, kuma  a kan karan kan sa ya tafi sabida shi raggo ne ba zai tsaya ya fuskanci challenge ba?” Aunty ta fahimci ba komai ke damun Mr. Hamzah ba face kishin ganin yadda na damu da Omar fiye da kima, kowanne irin bayani zata yi masa mai nuna girman zumuncin dake tsakanin Boddo da Omar ba ganewa zai yi ba. Sai kawai ta wuce cikin gida ta bar mu.

Hamzah yace “dalilin kukan tashin hankalin nake son sani Siyam, ko dai kina son Omar? Zan yi shigar sauri a tsakanin ku?”

Ya gaya min cewa dama yana da riko, in banda haka ban ga abin bacin rai a kukan rashin nasarar ganin Ya Omar dana ke yi ba alhalin na riga na saka ran ganin sa a yau. Shiyasa ban tsaya yi masa bayani ba nace bari kawai in shaqa masa. 

“Eh din, ina son dan uwa na yadda baka zato Mr. Hamzah.”

Hamzah da kyar ya ke iya bude idon sa a wannan lokacin sabida kishi, ya ce “kin san haka don me zaki bar shi ya tafi ba tare da kin aure shi tun a wancan lokacin ba? Kin ga da kin aure shi tun a lokacin da ba zan san ki bama balle in saka rai na a kan ki.” 

Ya farfadi maganganu son ran sa wadanda zasu sa ya ji sanyi, yana fadin Omar din rago ne, don an ce ba’a son sa ya bar gida, maimakon ya tsaya yayi yakin neman soyayyar, sai ya bige da nuna ragwantaka, yayi har ya gaji ban tsinka masa ba kafin ya shige motar sa ya ja da mugun gudu ya bar ni a wurin.

Murmushi nayi, na share hawayen fuskata sannan na shige cikin gida. Na tuna sanda Ya Omar din shima yake fadin Dream Husband dina raggo ne. Ya kasa bayyana sai ta cikin mafarki. Na wuce daki na ina fadin, “ka kwana cikin kunci kaima irin wanda nima yau zan kwana cikin sa. Omar bai yi kishin ka ba shi da na gayawa baki da baki ban iya auren sa sai kai, gara in mutu ta hanyar shan fiya-fiya akan in aure shi, sai kai ne zaka yi kishin rashin dalili a kan sa.

A falo na tadda Aunty tana waya sai na wuce ta zuwa nawa dakin. Aunty ta bi ni da kallo tana murmushi. Salon kulawar da Hamzah ke min tana gamsar da ita, irin mijin da take min fata kenan tunda ta fahimci ni din ma’abociyar son soyayya ce. 

“In ba Hamzan ba wai zai iyawa Siyama – VOA? Siyama-Soyayyah!”

Aunty ta fada a fili kuma ina jin ta. Har zan bata amsa da cewa “na fasa soyayya da VOA din, tunda shi bai iya lallashi ba sai tuhuma da neman fada, inna tuna dariyar da zata yi a kai sai naga gara in yi mata shiru kawai.”

Sai na zobara baki kawai ba tare da na bata amsa ba na wuce ta.

Ko abinci ban iya na ci ba a duka yinin yau saboda damuwar data yi min katutu, damuwa biyu ce ta tarar min; rashin nasarar samun ganin Ya Omar, da kuma damuwar Hamzah na fushi da ni. Amma na yi alkawarin ba zan neme shi ba.

Can da dare wajen karfe takwas sai ga kiran sa ya shigo min. Wani murmushin samun relief ya subuce min. Nayi kewar sa cikin awannin nan.  Amma sai na ki dauka. Ya kira har sau uku ban dauka ba. Sai yayo sako (text).

“I’m at the entrance…”

Wato yana kofar shigowa gidan mu. Nan ma ban bada amsa ba. 

Ba jimawa sai ga aunty ta shigo tana fadin “Siyam, baki ga sakon Hamzah bane ko kiran sa?” 

Zumbura baki nayi nace na gani. Don me zai sa min rai da ganin Ya Omar alhalin ba shi da tabbacin inda yake?” Sai kuka.

Aunty tace “ayya Siyaman VOA, shima bai san da maganar canjin wajen aikin nasa ba, wannan bakin mutumin da kika gan su tare dazu shi ya sanar da shi. Amma tabbas tunda ya ce shine kuma ya ambaci sunan sa exactly Faruq Gidado to tabbas shi din ne. 

England da fadi, kuma bankunan ta yawa gare su da mun je neman Omar ko don hankalin ki ya kwanta”. 

Haka tayi ta rarrashi na da kalamai masu dadi har na ware na yarda zan fita wajen sa.

“To dan gyaggyara ki canza kaya, kin ga tun kayan safe ne a jikin ki, ki kuma fente fuska ki sawa idon kohl  ki dan ja wa giran ki brow pencil.”

Dariya ta bani sosai sai da na murmusa. Na kuma kafe a kan ban yin ko daya, shi ai bai min wannan lallashin data yi min ba, sai bade ni da iskar motar sa da yayi. Wanda da ace akwai kura a wajen ba abinda zai hana ta taba jiki na”

Aunty na dariya ta fita tana cewa “kun fi kusa, ke da Dream Husband din ki, wai kashi da zawayi.”

Makeken jilbaab dina na zumbula na tadda shi a falon Young Abba. Kallo daya na yi masa na fahimci ya HUCE (sunan wani litttafin Takori).

Hannayen sa duka biyu zube cikin aljihu, ya dau sabon wanka, ya dauki kaftan na sabuwar filtex, sai walainiya yake, koda yake dama shi din ma’abocin iya daukar wanka ne, ta yadda zaka yi tsammanin babu namijin da ya kai shi iya tsafta, iya ado da iya sanya hula. Ta wannan fannin kam ya yi wa sauran maza zarrah.

Ina alfahari da kasancewar wannan tsalelen matashi zai zamo min miji, yana tattaki a kaina yana kuma yin abubuwa sabida soyayya ta, duk da ban same shi a yadda na yi tunanin samun shi ba; wato shima yana mafarki na kamar yadda nake mafarkin sa, na same shi ne a bai sanni ba, sai lokacin da ya ganni. Allah ya tainake ni ya saukaka min komai ta hanyar jefa soyayya ta farad daya a ran sa.

“Nazo in bada hakuri, tunda kin ki daukan waya ta. Zuwa da kai ya fi sako. I’m very sorry Siyam for how I reacted dazun. Ki sa a ran ki sai da SO a ke KISHI. Sai bayan NA HUCE na fahimci I’m wrong, ba da kowa a ke kishin ba”.

Ya karaso gaba na ya hada hannayen sa biyu pleadingly, yace “forgive me Siyam”. Sai na samu kai na da durkusawa a gaban sa sabida kafafuna da suka yi min rauni da ganin weakness din sa. Da na tuna waye Hamzah a idon duniya amma ga shi ya kaskantar da kai yana bani hakuri.

“Allah ya yafe mana Habeeby, I…..I…..” sai na kasa karasawa, sai shi ya karasa min, yace da rawar murya “……I LOVE YOU SIYAM, WITH ALL MY HEART. I LOVE YOU!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 32Sakacin Waye? 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×