Skip to content
Part 43 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Cikin dan lokaci kankani na kara amsa sunan MATAR HAMZAH. Cikakkiyar amsawa mai amo da sauti. Irin amsawar da ko wadanda suka shekara hamsin tare da junan su cikin rayuwar aure basu yi irin ta ba. Babu inda bai bi ya side ya tande a jikina ba. Lokacin da na fahimci Hamzah ya biya bukatar auren sa da ni (in a soothing way), mun kuma samu wata irin gamsuwa a ciki wannan karon fiye da duk yadda zan kwatanta, fiye kuma da lokacin baya.

Amma sai me? Duk da cewa gashi dai na samu cikar burika na da tabbatuwar dukkan mafarkai na, gashi dai na samu duk abinda nake so a auren Hamzah Mawonmase, na samu duk irin soyayyar dana ke mafarki da kintacen samu daga Dream Husband dina a tare da Hamzah, na samu mijin wato Hamzah a yadda nake so ya kasance. A fannin soyayya da farantawa matar sa ya zarta har fiye da mafarki da burika na, amma sai kawai Abba na ya fado min a rai, naji tamkar Abba ya san abinda nake nan ina aikatawa a bayan idon sa, wato abinda na zaba sama da in yi masa biyayya kenan! Abin nufi, zabar soyayyar Da namiji da jin dadin rayuwa ta a kan sa…..wannan ne abun da nake ganin bazan iya yi da Ya Omar ba sabida nauyin ‘yan uwantaka da respect din dake tsakanin mu, duk da Allah bai haramta yiwuwar aure a tsakanin mu ba.

Sai kawai na hau kuka wiwi, kukan da Hamzah bai san dalilin sa ba, kuka nake na karin son miji na da kuma damuwar tunanin mahaifi na rashin kyauta masa dana yi duka a lokaci guda, alhalin a lokacin ina manne cikin jikin sa, mun kasa rabuwa da juna tamkar an sa glue an manne mu cikin jikin juna. Ko kuwa ka yi tsammanin a haka aka halicce mu sabida yadda muka dunkule cikin juna tamkar curin alkaki. Kowannen mu shauki abinda ya faru ‘yan mintunan da suka gabata ya kasa sakin sa.

Lallashi da ban baki irin wadanda Hamzah ya rika yi min, kamar shima zai taya ni kukan sabida yadda kuka na ke luguiguita zuciyar sa, a wannan ranar mai dimbin tarihi cikin rayuwar auren mu na kasa manta su, sabida muhimmancin su da tasirin su gare ni. Lallashi ne irin wanda maza basa yi wa mata, shi kam daban yake da mazan hausawa.

Abubuwa da yawa na sawa mace ta kara son mijin ta a irin wannan lokacin, ni na kara son Hamzah ne sabida saukin kan sa, duba da yadda ya damu da damuwar dana ke ciki wadda shi bai san ko ta mecece ba har ya fi ni damuwa da kuma irin kalar lallashin da yake min in a soothing and romantic manner.

Sabanin ni da nake kukan damuwa da tunanin rashin albarkar mahaifi na na bibiya ta, da kuma tsananin kewar Abba na da ahali na, shi Hamzah kukan farin ciki ya ke yi a wannan lokacin.

Farin ciki irin na samun mace wadda ta zarcewa burin sa. Matan da ake kira “shu’arah” a harshen larabci wadanda daidaiku ne a cikin matan duniya.

A karo na biyu, Hamza ya sake neman kari, bai ko yi la’akari da kukan da na ke ta yi ba, tunda ya yi lallashin har ya gaji ban daina ba, kukan nawa ma sai ya zame masa tamkar ziga, sai dai this time around he is doing things very gently.

Kokarin Hamzah shine ya samu rangwame daga tarin ajiyayyar sha’awar sa ta shekarun rayuwar sa 38, wadda ya yi rantsuwa ya yi alkawarin sai ta hanyar aure kadai zai kawar da ita da kuma matar da ya tabbatar yana yi wa so na hakika har zuciya da bargon sa, daga bisani shi da kan sa ya tausaya min, ya kuma tausayawa kan sa for being insatiable….

Ya tabbatarwa kan sa yanzu kam ya gama sauke dakon samartakar sa, da gwaurantakar shekarun kuruciya. Daga bisani ya je ya sake yin wanka, ya sake shiryawa shirin tafiya ofis, ya shirya ne cikin kananan kayan da suka fi amsar shi fiye da na farko da ya canza. Ni ina daga kwance ina ta ‘yan koke koke na wanda zuwa yanzu ya ce sun koma na shagwaba kuma, har yanzu ban yi shiru ba har ya gama shiryawa, ya shiga kitchen da kan sa ya hado min tea ya dumama samosa ya kawo min, ya ja bedside ya dora a kai. Gashi ana ta kiran sa akai-akai a waya daga office din su (VOA).

Duk sun kasa masa hankali, ya rikice ya rasa da harshen da zai lallashe ni in yi shiru kuma, ya ce “ki yi hakuri Sweetheart, na san lamarin nawa is too much idan ni ne na yi laifin nan, amma babu yadda zan yi ne, ya kamata ki fahimta na wahaltu wajen rike kaina har zuwa wannan lokacin, amma hakan bai fi ba akan a ce wata ta riga ki samun wannan alfarmar ta hanyar haramun?

Ga lada mai yawa kina ta samu Boddo na Boddon Anti? In this aspect… Na karya miki hula, na lankwasa guiwata a kan ki, na rantse, bazan iya rayuwa ba tare da ke ba Siyaaama”.

Kukan nawa wanda babu amo ko sauti sai hawaye masu yawa da sheshsheka ya karu, hudawa yake har cikin ran Hamzah Mawonmase. Ganin ya kasa lallashin nawa in daina kukan kuma dabarar sa ta fara karewa ba tare da ya samu yadda ya ke so ba sai ya ce,

“Yanzu dai ki min izini in je office in dawo, kin ga dai duk basu san nayi aure ba, kin dauke hankali na daga kan komai Siyama-Boddo. Ko excuse ban bayar ba, shi yasa da basu ganni ba kwana da kwanaki yau suke ta kira na su ji ko lafiya.

Ina so in dauki hutu daga yau don in samu damar da za mu tafi Florida (Miami Resort), don haka bazan jima ba, in na dawo sai na amsa query, daga nan mu dora daga inda muka tsaya”.

Ya fada cikin tsokana da son saka ni magana dole.

Ai kuwa kuka ya kara kwace mini, ganewa da nayi ya maida ni abar tsokanar sa.       

Murya ta abin tausayi nace “me za’a dora din daga inda aka tsaya din? Kai fa sai ka koyawa bahaushe Hausa”

Hamzah ya kwanto a jiki na gabadaya yana murmushin tsokanar da bai gajiya da ita, ya sakar min dukkan nauyin sa da gangan, na yi ‘yar kara nace “Shaheed za ka balla ni”, ya kanne ido guda yana murmushin abinda zai fada, sai ya yi wani irin kyau a idanu na, cikin sigar jan fada kasa-kasa yace, “wai third round din mu na yau nake nufi ko ya kika gani? We’re going for the third round da zarar na dawo, ko Baby ya yi maza- maza ya shigo gidan Uban sa?”

Na yi maza na ture shi daga kai na ina fadin “ni ban isa haihuwa ba wallahi bazaka tsofar da ni yanzu ba.”

Sai lokacin ya tuna bai yi sallahr asubah ba. Ya yi tunanin in ya tsaya zai kara bata lokaci ne bari kawai ya je ya dawo sai ya hada ta da azahar yayi, in ya gayawa Siyam bai yi ba kuma ran ta zai sosu.

Ya koma toilet da sauri, yana daura alwala. Yana cewa ko kuma ya yi a office in ya samu sukuni. Walha dama wahala take bashi, in Siyam bata ce ya yi ta ba, a lokutta da yawa sharewa yake yi.

Har ya dau mukullan mota ya fita sai ya dawo kan gadon inda nake kwance, ya sa hannayen sa ya tallafoni ya dago ni daga kwanciyar ya aza bisa cinyoyin sa, yana min wani irin kallo kamar zai hadiye ni cikin cikin sa ya huta.

“Ko dai Babyn Mawonmase har ya samu muhalli ne? Irin wannan fresh da kika yi daga jiya zuwa yau bangane masa ba Siyam-Boddo. Ko duka ‘yan Mambillah haka suke very fresh a satin farkon su?”

Cikin kishi mai tsanani nace “akwai mata da suka fi ni kyau da yawa a Mambillah, in muka je zaka gan su fal, har in kana son kari ka kara da guda uku”.

Dariya yayi cikin matsanancin nishadi. Ya fahimci Siyamah akwai kishi. Ya ce “wa? Ni Hamzan wai? Yanzu in kara aure in bawa matar me?

Bayan saboda greadness (hadamar ki) kin kwashe komai dake cikin jikin Hamzahn, baki barwa sauran mata komai da ya danganci sperm daga Hamzah ba. I’m now empty.

Habeebty yau ji na nake wani irin sakayau! Fresh and reborn, kamar yau aka haifo ni. Thanks for the wonderful gift of love and and all the sacrifices Siyam. You know I LOVE YOU ko? To a yau na ninka wannan statement din zuwa sau trillion.

In tsaya ina ce miki “INA SON KI” will not be enough to express my gratitude to Allah and to you Aisha-Siyama. Insha Allahu zamu je gida Najeriya don nasan damuwar ki kenan, idan na gama mana shirin tafiya a sannu, in je ga Abba in durkusa in nemi albarkar sa, in gaya masa ya iya haihuwa, ya bani farin cikin duniya bakidaya sai fatan samun na kiyama.

Daga nan in ga tsaunin Mambillah (Mambillah Plateau), in ga garin Gashaka (bangaren surukaina na wajen uwa), in hau tsaunin Mayo Selbe in hango ko’ina na Gembu, in kuma ga Kakar mu abar son mu, Ummati”.

Wani murmushin dadi ya subuce min, ban san na yi kewar gida har haka ba sai yau da ya ambato tushe da asali na. Bahaushe yayi gaskiya da ya ce “KOWA YA BAR GIDA GIDA YA BAR SHI.”

Ko babu komai na dan ji sanyi a rai na, at least he cares, tunda ya yarda zamu je ga Abbana ya taya ni rokon gafara, ya kuma nuna damuwa da damuwa ta. Sannan ya bani dukkan kulawar data dace miji ya baiwa matar sa da ke cikin hali na damuwa.

Ka tsaya karantar halin da matar ka ke ciki ma soyayya ce mai zaman kanta, da ba duk maza ke yi ba, in dai sun samu biyan bukatar gangar jikin su.

Ina so mu je ga Abba kwarai don in nemi gafara ko in bashi dama ya yanke min duk wani hukuncin da zai wanke ni a wurin sa, in dai ba zai raba ni da miji na ba zan dauka, koda kuwa zai ce in fita neman Ya Omar kasa-kasa ne, amma bana son tuna ranar haduwa ta da Ummati, ba don komai ba sai don na san sai tafi Abba daukar zafi don mutum ce mai matukar kabilanci da wariya ga wadanda ba Fulani ba, musamman kuma a gaya mata asalin ko wanene Hamzah, a can baya ta kan bamu labarin arnan Jos da kiristocin cikin su kasancewar akan samu auratayya tsakanin Beroms da Fulanin jeji, ta sha gaya mana labarai a kan su da yadda sukewa musulmi da hausawa kisan gilla a yankin su, ban san hukuncin da zata dauka a kan aure na ba, idan ta ji ko wa aka aura min/wa na zaba ya zama miji na, ba kuma da sani da yardar ta ba. Kai bana zaton ma ta san da maganar auren. Tunda Young Abba yace sai gashi ga ta zai fada mata.  In ya so ya jurewa duk boren ta.

Na kuma tabbata yadda Abba ya ki tsayawa ma ya saurari zancen auren daga bakin Young Abba da kyar in zai yi wa Ummati zancen. Shi kuma Young Abba ya ce ba zai gaya mata a waya ba tunda ya kusa tafiya gida Najeriya sai sun hadu gaba da gaba zai mata bayanin Hamzah, asali da tushen sa zata fi fahimtar sa fiye da a waya. Amma tabbas ya san (she will retaliate). Hamzah na tafiya office bayan na ce “a dawo lafiya Shaheed”, ina so in ce masa baka yi sallahr walha ba, kuma sallahr walha ba’a farawa a daina, amma na yi shiru na barwa rai na, dole sai ana masa uzuri a hankali, amma na sa a raina zan cigaba da naci a kan sa kwarai da gaske, har zuwa ranar da Allah zai sa ya rike sallolin sa biyar da nawafil da da kyau da ikhlasi.

Fitar sa ba jimawa na tashi na yi wanka na shirya na yi tsaf da ni, gidan Hamzah Mawonmase dan karamin American-Condo ne, amma komai na bukatar rayuwar dan adam ya ji sharr a cikin sa. Fasalin gidan da komai da ya zuba a cikin sa ya yi min daidai da nawa tsarin rayuwar, ya yi daidai da yadda nake son gidan aure na ya kasance in dai a rayuwa ta diaspora ne. Perhaps sabida zukatan mu tare suke motsi, shi yasa hatta likes and dislikes din mu na tsarin muhalli ya zamo daya.

Ina son farar kala Hamzah na son fararen abubuwa. Shi ba tankareren gida ba, ba kuma gida ne mai yawan dakuna ba, a’a dan karamin apartment ne mai dakuna biyu daga nawa sai nasa sai study da babban falo. Babban madafi da toilets a kowanne daki. Na yarda na amince ni din, wato ni Aisha-Siyama Mamman Gembu, mutum ce mai sa’ar samun dace da samun burirrikan ta.

Hamzah Mawonmase ta wani wani fannin ya zo a yadda nake son sa, shi ba mai kudi bane, ba mai tarin arziki bane, amma babban ma’aikacin gwamnatin Amurka ne, sannan kuma babban manomin ‘Irish’ da ‘cocoa’ a gida Najeriya, ya mallaki komai na rayuwa daidai gwargwadon arzikin da dan adam mai wadatar zuci ke burin samu.

Domin duk wata bayan albashin sa na VOA, Hamzah Almutapha Mawonmase, yana da kudin da amfanin manyan gonakin sa na Irish da Cocoa ke badawa duk shekara a garin Jos. Don haka a fahimta ta, mijin nawa, wato HamzahAlmustapha, yana da rayuwa ta sukuni da rufin asiri dai-dai nasa, kwatankwacin bukatar kowanne kasaitaccen babban dan boko a irin rayuwa ta Diaspora.

Na bude firjin gidan babu nama da kifi sai express foods abinciccika na leda da na gongoni irin wadanda gwauro ke amfani dasu a yawancin lokuta, babu cefanen kayan abinci sam a gidan shiyasa tun zuwa na yake mana takeaway na abinci. Yau kam nasa a rai na zan fara girki miji na ya koma cin abinci na, na gaji da cin abincin kantuna.
Wayata na dauka na kira shi, kara daya tayi a na biyu ya amsa alhalin yana tuki, ina jin sa har da ajiyar zuciya kafin ya ce “Siyam ya aka yi? Kin tashi kin yi wanka in ce ko? Kin daina kukan ko? Na iso office yanzu. Kuma in an approximately two hours zan dawo in sha Allah.”

Mamaimakon in bashi amsoshin da ya bukata sai na zarce kai tsaye ga gaya masa makasudin kiran nawa, abubuwan da zai taho min dasu na cefane, na fara jerowa, sai ya katse ni ya ce “Afuwan Habeebty, afuwan Sweetheart, ban taba yin cefane ba, don haka bazan iya rike dogon list dinnan naki ba, yafi karfin brain dina, kin san ba kwakwalwar iya lissafi ke gare ni ba sai ta iya soyayya.”

Kunya ta kama ni na kama murmushi, sai yace “He who mastered in linguistics has no mathematlics, (wanda ya kware a iya harsuna bai iya lissafi ba) bari in dawo sai in dauke ki muje Walmert Supermarket kawai ki zaba cefanen ki da kan ki. Daga nan ma ki mike kafar ki da ke nade waje guda kwanannan, bana so ki fara kiba.”

Har ga Allah naji dadin fitar da yace zamu yi din. Ban san me yasa ba, a rayuwa ta ina son jerawa da Hamzah, a wasu lokutan can a baya, har mafarkin hakan nake yi, balle a ce a cikin motar sa ne, ina zaune (by his side), shi kuma yana tuka ni (like my chauffer). Sai in ji ni ‘on top of the world’

Bazan manta ba. Rana ta farko da hakan ta faru wato ranar haduwar ‘lifter’ da ya rage min hanya zuwa gida don kada ruwan sama ya doke ni, ni kadai na san abinda na ji a rai na.

Na ji kai na ya kumbura, na ji ni tamkar sarauniyar duk matan duniyar nan. Don haka cikin farin ciki na ce,

“sai ka dawo din Shaheed, can’t wait for you to come back!”

Da wannan ya karasa ofishin sa cikin farin ciki mabayyani, kai in ka ga irin takun da Hamzah Mawonmase yake yi yau a harabar VOA…tafiya yake gab-gab-gab cikin kuzari da koshin lafiya, far’ar da ke fuskar sa kadai in ka gani zaka tabbatar cikin matsanancin nishadi da madaukakin farin ciki yake. Wanda duk ya gamu da shi a hanya ko cikin ofis din sa sai da ya shaida hakan.

Da Director Philip ya tambayeshi dalilin wannan annurin na fuskar sa, da musabbabin wannan fara’ar, sai yayi dariya, daga bisani cewa ya yi yana farin cikin zagayowar ranar haihuwar sa ne domin yau ya cika shekaru 38, kuma wadda ta yi daidai da ranar angoncin sa.

Sai Director Philip ya gyada kai yace “in haka ne ya kamata ka dau hutu ko na sati biyu ne, don amarya ta samu lokacin ka sosai kai ma ka samu ka rage tsufa”

Hakan kuwa aka yi. Hamzah ya samu leave na sati biyu kamar yadda ya bukata da ya fada cewa yayi aure. Magana tun ana yin ta kadan – kadan, tsakanin masu aikin safen ranar, har kafin dare kowa a VOA ya san Director Hamzah Mawonmase yayi aure kuma wai musulma ce ba Christian ba. Kowa da abinda yake fada a kai. Wasu karyatawa suke yi don an san cewa ‘catholic’ ne, mai kuma farin jinin ‘yammata iri daban-daban na kasashe daban-daban, sun fi dauka cewa ba zai iya ajiye mace daya kwakkwara a gidan sa da sunan auren sunna ba, ganin yadda ‘yammata iri-iri ‘ya’yan gata ke sintiri a kan sa kasancewar sa media celebrity mai tashe da farin jinni a wurin al’umma, a gida ne ko office. Baka raba Hamzah da baki mata. Sai kowa da ke aiki tare da Hamzah ya zaku da son ganin wacece wannan lucky girl din, da Hamzah Almustapha Mawonmase ya zaba ta zama matar sa. Wasu kuwa tausaya mata suke, a ganin su ba zai taba maida hankali ga rayuwar iyali ba. Duk da haka, suna ganin ita din mai sa’a ce.

Sa’ar ta guda biyu ce, na farko ta samun miji broadcaster mai farin jini a cikin mutane ta fannin sana’ar sa, daya da daya ta fannin kyau da iya daukar wanka da iya dressing a cikin mazaje bakar fata ‘yan Najeriya, ta kasa ‘yammata bakar fata da farare har ba adadi, sannan gashi gwani a fannin barkwanci da raha, ko a radio da talbijin yake Magana zaka ji baka so ya daina, gwarzo kuma mai sa’a a kan duk abinda yasa gaba. Kowa dake tare da Hamzah a VOA ya san wadannan baiwarwakin da Allah ya yi masa.
Amma a iya tsinkayen su babu wanda ya taba kawo zai iya auren musulma, balle kuma a kai ga cewa shi din ma zai iya musulunta. Koda yake sabga ta addini (is a personal issue) su a wurin su.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 42Sakacin Waye? 44 >>

3 thoughts on “Sakacin Waye? 43”

  1. Assalamualaikum.
    Aunty Sumayya barka da dare. Inai Miki Fatan Alkairi Mai dorewa, Ina matukar son Littafin ki SAKACIN waye sabida yyi ma’ana game da tsarin al’adunmu Muslim and Christen

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×