Skip to content
Part 55 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Hawaye fal ido na, ba na zafin marin dana sha bane daga yatsun Hamzah, a’ah, na tunanin daga hannun da marin ya fito ne, hannun da kullum ke shafata, yake runguma ta yana tarairaya ta da sumbata na ne. Hawayen suna son bulbulowa amma ina kokarin rike su ta dole, ina gayawa kai na ban cancanci zubar da su ba, don zubar su ma rahma da cancanta ne. NI NA JAWO kuma sakaci na ne; zabar soyayya akan Baba na, so duk abinda soyayya ta janyo min in sa hannu in karba da godiya, in sa zani da majanyi in goya soyayyah. Komai Hamzah ya yi min daidainsa ne tunda na gama nuna masa ba zan iya rayuwa ba sai da shi, wato it’s my own NEGLIGENCE ba na kowa ba….ba na Abba bane sakacin nan nawa ne ni kadai, ni Aishatu-Siyama (Boddo).

As far as namiji ya fahimci mace na yi masa so irin nawa, irin wannan soyayyar da ta wuce kima kuma ya sani ko ya ji labari, watarana sai ta ga irin haka, yau na zama misalin kai na da kai na.

“Ni ce idiot yau a bakin ka Hamzah? Ni ce stupid Habeeby? Ni ka mara? Ni Aisha-Siyaman? Ni ka daka haka ina cikin jinin bikin haihuwa da radadin ta? Haihuwa fa nayi Hamzah bani da lafiya ko jinin haihuwa bai kai ga dauke min ba?

Har ni zaka gayawa zafin mutuwar Da, shin akwai wanda ya kai uwa jin ciwon rasa Dan ta? Wa ya kashe maka dan ba Kakar taka ba? Banda Allah ya takaita ya kuma kiyaye da nima ta kashe ni, ta yi wa iyaye na asara ta don ba zan ce ta yi maka ba, tunda zaka iya auren thousands of SIYAMAH masu shirin barin addinin su saboda kai, iyaye na kuwa bazasu kuma maida rashi na ba.

Amma ka ji ni na yi complaining a kan hakan? Saboda mene ban yi korafin ba? Saboda na yarda Allah shi ke bayarwa kuma shi ke karba ba sanadin ta na rasa nawa dan ba, Allah ya rubuta na amfanin can ne ba zai zo min da rai ba, ban bari Imani na ya samu nakasu a kan hakan ba, saboda banida tsatsar giya a cikin kai na, tunanina fes yake, ina iya banbance abubuwa, kai kuwa gaka nan tana tamaula da tunanin ka akan mutane mafiya kusanci da kaunar ka, har take neman haukata ka don kawai an baka shawara.

Kawai don Young Abba ya baka shawarar da yake ganin ta dace damu zaka bi ka fitine ni? Ni me ye nawa a ciki? Ko na ce na yarda da abinda ya ce din? Ko don kawai nace ka daina sabawa Ubangiji ka kuma bar shan abinda zai gusar da hankalin ka da imanin ka? Ka rike sallah da tsarki?

In baka bari don Allah da lafiyar ka ba, ya kamata ka bari haka a dalilin ka fara zama UBA (ka fara ajiye ‘ya’ya).

Ko ka san duk wannan haukan da kake yi ba cikin hankalin ka bane? Ko ka san kai da mahaukaci a halin yanzu baku da maraba?

Yana daga illar abinda ka rika a matsayin abinda zai baka kwanciyar hankali da saukin zuciya maida kai (partially mental) a yawancin lokutan da kake cikin mayen ta, a duk lokacin da ka sha ta, halakar da hankalin naka kawai kake yi babu wani sauki ko farin ciki da kake samu a cikin ta”.

Na fada wannan karon cikin radadin zuciya da hawayen bakin ciki suna zubo min. Na basu fili su sha sharafin su a kan kumatu na, ba don zafin marin Hamzah ba, sai don bakin cikin Hamzah ne da kan sa yau ya mare ni kuma ya daki banza, hakan bai sa na tsane shi ko na daina son shi ba, na daina takura musu da son mayar dasu inda suke bubbugowa, gara in bar su su yi ta zuba kuka rahma ne ga dan adam, duk wani weakness dina dana ke boyewa zuwa yanzu ya gama bayyana.

“Daga psychiatric na fito, ba partially mental ba, idiot kawai, wadda bata san halaccin wanda yayi sadaukarwa don ya rayu da ita ba, ya kuma cece ta daga azabar soyayya, wadda bata san martabar iyayen da suka haife ta ba a kan soyayya ina za ta san martabar auren shi kan sa? Shashashar Siyam kawai wadda bata da godiyar Allah.

Fisabilillah da me na raga miki a aure da kika hana ni zaman lafiya a gida na? Me na rage miki a soyayyar da kika aure ni domin ta? Ina ruwan ki da ingancin addini da dabi’a ta wai? Tunda kin samu abun da kike so da tabbatuwar mahaukatan mafarkan ki?

Ya kamata ki duba cewa nima na yi sacrifices masu yawa don na rayu dake, amma kin ki bari na in rayu da ke ‘in peace’, rigimar ki ta yau daban, ta gobe daban, ke gaki ma’asumiya (wadda bata sabon Allah) kullum cikin daga min hankali kike a kan maganar addini, baki da manner of approach ga wanda bai san addini ba.

Ya kamata ki san ba’a addini ta karfi da discipline, ba’a horon namiji da sex denial, wanda maimakon in yi abinda kike so saidai ya sa in kara fandare miki, komai nayi na ibada ban iya ba, komai na yi ki ce ban yi sallah ba, ki yi ta danne min hakki wai bana sallah.

Zuwa yanzu na gane neman rabuwa da ni kike, tunda kin gama da abinda kike so a jiki na, hankalin ki ya karkata yanzu gare shi kina hangen nasa, ……. nasa sweet sex and hot kisses din ko? Hummmmm. Nympho kawai……..!!!”

Ban iya na karasa jin wadannan munanan sharrin marassa dadin ji daga bakin sa ba, daga bakin wanda na fi so duk duniya sama da kowa, wanda na zaba akan inyi rayuwar duniya kacokam, wanda na zabi in bata da Abba na don in tsira da shi.

Kalaman Hamzah Mawonmase zan ce ko na giyar da ya kwana sha ta kai masa mugun karo, na juya da gudu nayi daki na ina wani irin zazzafan kuka wiwi.

Kaya na na shiga fiddowa daga wardrobe ina dannawa a trolley babu ninki babu kintsi, yau ko Hamzah tare “Asshe” ta haife mu ni da shi, na yanke shawarar daga yau zan gwada barin sa in koyawa zuciya ta hakuri da abunda ta nacewa komai son da take masa, in tafi gida ko da soyayyar zata yi ajali na.

Na zumbula jilbaab dina na janyo akwatin na fito. Amma ba Hamzah babu alamar sa a falon. Na kama kofar gidan da zummar in bude in fice sai na ji ta gadagau, wato ya kulle ni ta baya ya fice da mukullin gidan sa. Kamar ya san zan yi nufin tafiyar. Tafiyar da na tabbatar ba zai dawo ba nan kusa, tunda kuwa kasar Nigeria zai wuce da gawar Kakar sa.

Tsugunnewa nayi a kan kafafuna ina kuka. Kukan da bai taimaka ba ko kankani wajen rage min radadin zuciya da nadamar dake cin rai na na kin biyayyar Abba. Ina rokon Allah ya dauki rai na in huta.

Da na ga durkuso a bakin kofa ba zai min ba domin kafafuna ne suka fara ciwo sai na tashi na koma dakin barci na. Na dau waya ta da niyyar in kira Aunty Nasara in ce mata kada ta jira ni, zan zauna ni kadai har ya dawo. Don mun yi da ita ne inna raka shi airport ya tashi zuwa Najeriya daga can zan hau drop din taxi in wuce gidan ta har sai ya dawo. Ga jini naji alamar yana ta kara yawan zuba daga jiki na.

Kai tsaye na wuce toilet na hada ruwa mai zafi cikin kwamin wanka na shiga. Na gasa kaina sosai na kuma yi gashin tawul a gabban jiki na kamar yadda Nasara tace in dinga yi kullum sau uku a rana aka kuma koya min a asibiti. Ina zaune gefen gado na ina ta faman sharar hawaye bayan na canza pad na yi kyakkyawan ruwan zafi naji dan dama-dama na dawo bisa gado na zauna ina dan danne danne cikin waya ta ina kuma azkar da baki na, domin na kasa samun Anti na a waya, wayar ta na a kashe (switch off), kuma gara da ban same ta din ba, don tabbas na san ba makawa da ta ji muryata zata gane ina cikin wani hali na garari da tashin hankali. Wannan kuma na saka a rai na sirri na ne wanda daga ni sai Allah sai Hamzah zamu rike shi, na fasa tafiyar, dam aba wai zan iya bane koda kullum zai ke yankar naman jiki na ne don ya huce daga zafin zuciya marar amfani da ya dauka, bazan iya gayawa kowa irin gore-goren da yake yi min ba a kwanakin nan, don babu mai maganta min saidai ma a ce “Allah ya kara”.

Danne danne kawai nake cikin wayar hannu na in shiga nan in futa can don hana kai na damuwa da tunani. Ina kara yawan salatin da nake yi wa Annabi. Kamar an ce in shiga akwatin sakon emails dina sai na shiga akwatin yahoomails dina na bude.

Nan na ci karo da wani tsohon ajiyayyen sako wanda yayi watanni kusan uku da aikowa ban san da shi ba.

Sakon, wanda aka rubuta shi da harshen fulatanci daga wani adireshin email na wanda ya kira kansa da suna abandonedsoulgembu@yahoo.com ga fassarar abinda ya kunsa;

“Boddo na, Azumin Ummati, Siyaman Abba, daughter of my late mother, Ashshe.

Koda yake yanzu BODDON HAMZAH MAWONMASE ce. SIYAMAN VOA ko?!!!

How is life with you here in America? Na san zuwa yanzu rayuwa ta zama cikakka, yadda kike burin ta. Na tabbata zuwa yanzu kin gamu da DREAM MAN din ki, VOA Media Celebrity, “Hamzah Mawonmase”.

And life is moving as it was supposed to, with him aside.

Na san zuwa yanzu dukkan MAFARKAN nan da ake damun mu da su sun zamo reality kamar yadda na dauki tsahon duka shekarun nan ina rokon Allah ya bayyanawa Boddo DREAM HUSBAND din ta,

Surprised ko? A in ana san HAMZAN VOA? Don’t panic! Ya Omar yana biye da duk wani takun-sakar Boddon sa a rayuwa. Tun daga DAAR AL ULOOM AL-MADANIYYAH har zuwa George Washington University, har kuma zuwa Internship a gidan rediyon VOA. Da kuma haduwa da Hamzan VOA.

Boddo ‘yammatan Anti Wasila, na ga sakon email din ki once in a while, a lokacin da kike roko na in dawo gida. Amma a lokacin ban shirya baki amsa ba kuma ban shirya dawowa ba sabida a lokacin daga ni har ke bamu kai ga samun abinda muke so ba, ni ban samu sauki ba daga ciwon kiyayyar Boddo na, ban samu sauyin rayuwa ba daga ciwon abandonement, ina fighting ne da kaddara ta, ke baki kai ga samun Dream Husband dinki ba shiyasa ban dawo ba.

Zan zo kusa

Zan zo soon

Zan zo ba da jimawa ba!

ABANDONED SOUL.

Na kusa in yi dan karamin haukan farin ciki ni kadai a daki na. Dana gane daga inda sakon nan ya fito. Babu ko tantama Yaya na Omar ne yau ya fara hucewa ya neme ni ta yanar gizo.

Tuni na manta da damuwar da Hamzah ya assasamin da kulle ni da yayi a cikin gida ya tafi kasar Najeriya da mukullin. Na Fadi na yi wa Allah sujjadah na dawo na dauki wayar na soma rattabawa Ya Omar Sako.

A cikin sako na, na yi murna na kuma yi godiya da ji dana yi daga gare shi. Na nuna mamaki na a kan sanin da yayi na cewa na ga Dream Husband Dina, na kuma kara da appreciating din sa a kan cewa da yayi duk wani takun saka ta a rayuwa ya san da shi wannan ya nuna min har yanzu matsayi na na kanwa kuma ‘Boddon sa’ bai canza a zuciyar sa ba kuma bai daina kula da ni da rayuwa ta ba duk da laifin butulcin dana san na yi masa.

A karshen Sako na nace “Ya Omar actualizing dreams din ba shine kawai ba, a’ah, matsaloli da kalubalen da ke cikin reality din mafarkan sun fi dadin da ke cikin sa yawa. Ba zan ce komai ba sai ranar da ka zo din, ko Allah ya hada mu, ranar ne zan gaya maka cewa ban samu mafarkan a yadda na zace su ba”.

Ina turawa Ya Omar sako na karanta ayoyin karshe na suratul Hashri sannan na kwanta cikin kwanciyar hankali. Ko ba komai yau na ji daga Ya Omar. Na samu ragin dabaibayin dake zuciya ta.

Washegari dana tashi ban ga reply din sa ba. Na kira Aunty Nasara wannan karon na yi sa’a na same ta, ta ce “Siyama lafiya ban gan ki ba? Kina kula da kan ki kuwa? Ya zaki zauna ke kadai da danyen jego a jikin ki? Kina gasa jikin ki in ce ko, kina kuma shiga ruwan zafin yadda aka gaya miki? Kina shan tea mai kauri sosai da cin gasashshen nama da yajin dana baki? Ya kunun kanwan kina yi ko kuwa?” “Duk ina yi Anty kada ki damu, na fasa tahowa gidan ki saboda aikin project dina an bani deadline, zan cigaba da yadda kika koya min in sha Allah ba matsala kuma ina shan magunguna na a kan kari” Anti tace “ni dai nafi so ya zama kina gaba na ina kula da ke tunda haihuwar fari ce, in yaso kiyi aikin project din anan, Wasila ma mun yi waya ta ce ayi miki sannu, na gaya mata kin haihu dan ya koma, ta ce kiyi hakuri kada ki ga bata kiran ki yanzu, Abba ya hana ta ne amma in sha Allah abubuwa zasu yi daidai ba da jimawa ba, don tace jikin sa yayi sanyi da ta fada masa kin haihu dan bai zo da rai ba duk da bai ce komai ba, wai kawar ki Ka’oje ma ta haihu tana kuma zuwa gaida ta har yanzu, ta kawo mata dan da ta Haifa ma, kin tabbata ba matsala zaki iya din?” “Aunty tunda babu Baby kuma Hamzah baya nan ai babu hidima mai yawa tare da ni, ba zan kasa wadannan abubuwan na kula da kai da kika koya min ba, in da matsala zan kira ki in gaya miki” da wannan muka yi sallama da Anty Nasara.

Labarin da ta bani na Anty Wasila da Ka’oje ya hadu da farin cikin email din Ya Omar na jiya ya ya kara min kuzari da koshin lafiya. Na yi wankan tawul na gasa kasa na da jiki na duka, na ga gudun jinin ya ragu. Bayan fito toilet na shirya cikin kaya marasa nauyi na zaman gida. Sai naji ina son motsa jiki na kadan don na gaji da kwanciyar. Sai kawai na fada kitchen da karfin guiwa ta na hau gyaran sa, duk abinda ya fara baci na kayan abincin mu na fitar, na gyare koina na share tas. Na kalkale gidan nayi mopping koina kai baza ka ce ina da damuwa ba kuma jego nake yi. Lallai iyaye rahma ne Dan uwa Rahma ne. Balle dan uwa irin Omar Farouk Gidado Gembu. Doki na na son komawa gida ya kara ninkuwa. Kwana kusan biyar ina cikin kurkukun Hamzah ni kadai, ba waya ba sako, tunda ya tafi bai kira ni ba. Bai kuma kara bi ta kai na ba. Kadaicin ya saka na mayar da hankali ina karasa aikin project dina na kammala karatun digiri wata mai zuwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 54Sakacin Waye? 56 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 55”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×