Skip to content
Part 57 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Jirgi ya daga, yayin da at the same time zuciyata ma ta luluka cikin memories na zamana shekaru takwas a kasar Amurka, ta kuma dawo ga kissime-kissime na abinda zan tarar a gida. Tunanin Ummati, Anti Wasila da kannena da ta ke ta haifa mun ko wacce irin karba zasu yi min? na san dai su Maryam-Jamilah zuwa yanzu duka sun manta ni. Na tabbata haduwarmu will be very emotional. Na kuma shiga harhada kalmomin da zan yi wa Abba amfani da su wajen ban hakuri. Na yanke shawarar ba zan boye masa komai ba a game da Hamzah, da ayar fushin da na gani a cikin aurena da shi in dai har zan samu ya saurare ni. Na kissima abubuwa da yawa masu dadi a raina na yadda haduwata da iyayena za ta kasance idan sun yafe mini sun kuma karbi zabi na. idan kuma ba su karba ba zan ba su zabi ne a kan aurena da Hamzah duk abin da suka yanke da shi zan yi amfani, har shan giyarsa ba zan boyewa Abba ba.

Yanzu na yarda na amince soyayyar ba ita ce priority din rayuwar dan Adam ba. Idan kuma ka ba ta priority to kuwa watarana za ta kayar da kai kasa warwas, cikin tafkin nadama. Iyaye ba abin wasa ba ne.

Yau dai gani ni Siyama Mamman Gembu na tafi duniyar soyayya na kuma dawo kamar yadda na je ta shekaru masu yawa a baya, bayan dandana jin dadin dake cikin ta, as well as dacin dake cikin ta, na gane komai da ke cikinta mai iya canzawa ne ta inda mutum bai zata ba daga wanda ki ka mallaka wa soyayyar, hope din ki da dukkan burikan ki sama da mahaifi, shi da kan sa in ya san ciwon kan sa ya kuma san abinda kika aikata watarana zai iya goranta miki, ya canza miki, ya murde miki ko ya wulakanta ki kamar ba’a taba halittar kalmar soyayya a tsakanin ku ba, ko da kuwa kin yi sa’a kamar yadda na yi ya mallaka miki tasa soyayyar cikin sauki.

Na dubi Hamzah Mawomase da ke gefena yana buga game a wayarsa, ba abin da ya dame shi. Ni kadai ce cikin damuwa da zullumin haduwata da Abba na. Na tuna ko yau na fadi na mutu Hamzah zai auri hudu na, ni kuwa idan ya mutu wajen Abban dai zan koma. Abban dai.

Na rasa jin dadi a zuciyata ko kankani sabida tunanin Abba da yadda zan shawo kan sa ya yafe min, a haka muka sauka a Istanbul duk da yadda Hamzah ke ta tsokanata wai yau zan yi kwanan kasar Turkawa ban iya tanka masa ba. Hankali na ya yi Abuja.

Saukar dare muka yi a Istanbul. Amma abin da ya ba ni mamaki Hamzah drop din taxi ya daukar mana zuwa wata kebantacciyar unguwa a cikin kwaryar Ulus. Zan yi magana in ce ba a hotel za mu kwana ba, washegari mu sake hawa jirgi mu wuce Nija? Kafin in furta abinda nake tunani Hamzah ya ce, “Siyam ba ni aron wayarki”. Ina ba shi ga mamaki na sai ya bude ta ya zare sim card din, sannan ya karairaya shi ya watsa ta window ya jefa wayar a aljihunsa.

Kallon tsoro da mamaki na yi masa, sai ya lumshe min kyawawan idanun sa ya ce, “Don’t question me pls, da sannu za ki fahimci abinda nake nufi”.

Muka iso kofar gidan mai lamba (170) cikin rukunin gidajen (Taksim Square) na kasar Istanbul. Shi ne gida na kusan karshe a cikin Estate din. Mai taxi ya sauke mana kayanmu a kofar wani kyakkyawan apartment wanda duk estate din irin gini daya ne, Hamzah ya shigar mana da su. Mamaki da tsoro sun hanani cewa komai. Har ya dawo ya kama hannuna ya sakalo ni a kugunsa zuwa ciki, ban yi musu ba na bi bayansa.

Muna shiga gidan ya maida kofar ya rufe da mukulli, ya zare key din ya saka a aljihun sa, ya kunna fitila falon ya gauraye da kyakkyawan haske  sannan ya karaso inda nake tsaye ya rungume ni tsam ta baya.

“Siyama, ki yi hakuri ba ni da zabi ban da yi miki wannan azancin. Don in na gaya miki zamu dawo wata kasar da zama bazaki fahimce ni ba, amma na taba gaya miki cewa zamu koma inda bamu da kowa daga ni har ke, don na fahimci kawunki da gaske yake ba zai bari ki haihu da ni ba.”

Imagine har cewa ya yi ya samo mana yaron da za mu rike daga dangin mahaifiyarki Gashaka in je in karbo mana. Abban ki na nufin ni ba zan ga Dana a duniya ba ko me? Don kawai jini na mai bada sikila ne? Ko ya dauka shi zai tsara min yadda zan rayu?Sabida kawai ya ba ni aure? Auren da sadaki na biya ba sadaka ya ba ni ba, ba kuma auren yarjejeniya bane ba na bashi ba ne?

Siyam mun bar kasar Amurka daga yau, mun bar kusa da su Young Abba kin sha yin addu’a Allah ya bayyanar da ni domin mu rayu tare cikin soyayyar juna, ke da bakinki kin sha gaya min haka. To ga mu a nan, a inda za mu rayu tare, ba tare da saka ido da takurawar kowa ba.

In ba ki manta ba, na gaya miki ai za mu koma inda ba mu da kowa mu ci gaba da rayuwa mu biyu kika dauka wasa nake,na ce miki inda ba mu da kowa. Inyaso mu yi ta haifar ‘ya’yanmu sikila muna kula da su da lafiyar mu da gumi na. Zan yi ayyuka na neman halak da dukkan karfi na, ilmi da lafiya ta don ganin ke da ‘ya’yan ki baku rasa komai ba ta fannin ci da sha ba, baku rasa sutturahr daurawa da ilmi ba. Ki sa a ranki yadda ba ni da kowa a duniya sai ke, ke ma yanzu ba ki da kowa a duniya daga yau sai ni…sai yaran da zamu haifa in sha Allahu”.

Ya karasa muryarsa na shaking kamar yadda jikinsa bakidaya yake rawa da wata tsumammiyar sabuwar soyayya. Zai sumbace ni na kauce. Na soma tunanin ko barasa ta taba kwakwalwar Hamzah na ne? Abin da yake yi din nan wato desperation a kan son haihuwa bai yi kama da na mai cikakken hankali ba.

Fincike jikina nayi daga nasa, na ce, “What do you mean Hamzah? Ba Najeriya za mu karasa ba?”

Muryata na rawa da karkarwa kamar yadda jikina ya dau bari. Ya ce, “Forgive me Siyam, ba ni da zabi ban da in yi miki wannan azancin don in na ce ki biyo ni Istanbul ba za ki yarda ba ta ruwan sanyi. Amma tabbas baza mu je ko ina ba daga yau har zuwa sanda Allah ya nufa. Ban san masifar da ta same ni ba kan son haihuwa da ke ba, amma jiki na na bani muddin muka je gun Abbanki, a ka ce masa ni ba musulmi bane tun haihuwa tachristian ne kuma ina shan barasa ba zai bar ni dake ba. And I can’t live without you Siyam”.

Jikina duka bari yake da tashin hankali na ce “wallahi-wallahi Hamzah ko zamu mutu ba haihuwa sai ka kai ni gaban iyayena”. Na fara kuka ina rantsewa ba zan zauna ba.

Hamzah ya yi murmushi, ya ce, “Shi dan Adam naturally haka Allah ya halicce shi da son kansa, kuna son kanku ni ma ina son kaina.

Daga ke har iyayenki na gama gane take-takenku a kan aure na da ke, in ba haka ba me ya hana Young Abba ya ce mu je Nigeria tare, ya gabatar da ni ga mahaifinki ya kuma saita komai da ke tsakaninku?”

A wannan lokaci hakurina ya kai intiha, na ce, “Say it cleary kawai Mr. hamzah, ka rabo ni da iyayena yanzu saboda son kan ka da biyan bukatar zuciyar ka na in yi ta haifa maka ‘ya’ya, ba ka kuma da niyyar sake mayar da ni gare su, sabida bukatar kanka da kanka…”.

Kuka ya ci karfina na ce, “Wallahil azeem Hamzah ka ci amanar mai kaunar ka (Young Abba), you totally misunderstood him, ka ci amanar soyayyar da na karar da rayuwata ina yi maka in ka yi min wannan yaudarar. Ka san buri na daya yanzu a duniya shine saduwa da Abba na da Ummati shine zaka yi min swannan yankan kaunar.

Ka tuna Hamzah ka yi alkawarin saka ni farin ciki har karshen rayuwarmu amma wadannan abubuwan da ka ke yi yanzu ba inda suke kai ni sai ga bakin ciki da nadamar auren ka da shigowar ka cikin kaddara ta”.

Hamzah ya ce, “Ke ki ka so hakan ta kasance Siyam, idan kin bi duk abin da nake so kin daina takura min da matsanta min lafiya za mu zauna. Kina nufin sai in zauna ban ga kwaina duniya ba saboda wani genotype? Su sauran iyayen da ke haifar yaran a wannan halin suna dawainiya da su ba kya tunanin hakan zai zamo kankarar zunubai a gare su?

Ga mu a inda ba mu da kowa sai junanmu, yanzu ne zamu fara soyayyar da kike mafarki kina kuma roka mana, Allah kuma ya amsa, zamu rayu a cikin ta har karshen rayuwar mu in sha Allahu tare da ‘ya’yan mu, ina fatan in mutu cikin soyayyar ki da a kullum take kara kassara ni”.

“Hamzah kada ka yi min haka, za mu haihu cikin lumana ko a gaban iyaye na ne, ka yarda Allah ne ya hada mu babu mai raba mu, zamu haihu ba tare da ka raba ni da kowa nawa ba. Do not make such a wrong judgment like this. It will eventually backfired you with my parents…”. Na fadi, taurari na gilma min, na tafi luuu! Zan fadi ta baya.

Hamzah ya tare ni da dogayen hannayensa, ya rungume ni a kirjinsa, ina iya jinsa sanda yake cewa, “Ki yi hakuri, ba da son rai na na yanke mana wannan hukuncin ba, ba ni da zabi Siyam, in ba haka ba za su raba ni da ke ne”.

Daga haka ban kara fuskantar me ke faruwa da mu ba. Hayyaci na ya gushe saboda tashin hankali.

Sai farfadowa na yi na gan ni a kan gado, wani lallausan gado wanda katifarsa ta ruwa ce, wato (water mattress) lullube da wani lallausar Duvetpink colourda zane-zanen baki a jikin sa.

Hamza na manne da ni yana barci a gicciye, Allah kadai ya san lokacin da ya dauka yana kula da ni kafin ya samu wannan azababben barcin.

Na dade ina kallon kyakkyawar bakar fuskarsa ta cikin hasken dim light, na shiga dora abin da ya yi min a sikeli na hankali da tunani, soyayya ce ko kuwa mugunta ce?

Na kasa bambance cikin biyun wanne Hamza ke nufi a kaina. Idan soyayya ce ba zai taba son ganina cikin kuncin rashin iyaye da albarkar su ba. Don wai in haifa masa ‘ya’ya marasa lafiya. Idan kuwa mugunta ce sai in ce ya so kansa da yawa, kuma ya ci amanar Young Abba.

Na tuna cewa a kasar Istanbul nake yanzu, kuma passport dina da wayata duk suna hannun Hamzah, sai ranar da ya ga dama zan koma ga iyayena,in kuma Abba ya riga ni mutuwa shikenan ya tafi yana Allah wadai da haihuwata.

Wannan tunanin ne ya saka ni fashewa da kuka wiwi.

A dole Hamza ya tashi daga barcin da ya samu, ya soma kokarin zai lallashe ni na dakatar da shi, na ce, “Haihuwa dai ko? Don in haifa maka yaro ka yanke wannan danyen hukuncin?”

Ya kama kansa da ke sarawa yana fadin, “Boddo ba ki fahimce ni da kyau ba. Wallahi raba mu za su yi daga irin take-taken Young Abba. Ni namijine na fi ki hankali da tsinkaye raba mu iyayen ki zasu yi”.

“Sai ka ga gara ka cuce su ka raba su da ‘yarsu tun kafin su su raba mun, don biyan taka bukatar?”

Hamzah ya kama kai, ya ce, “Siyam don’t judge me wrong mana, za mu koma gida na miki alkawari, amma bayan mun haifi yara ko biyar ne. I want to build my family here, my own extended family tunda ba ni da kowa, ba kuma zan iya haifarsu da kowacce mace ba sai da ke kadai. You are my island, believe me I did it for our survival”.

Duk ta inda na billo don in nuna masa ya zalunce ni, sai ya kare kansa da kwararan hujjoji. A haka muka kwana ba tare da kowanne ya yarda da hujjojin dan uwansa ba.

Kwananmu uku muna tafka wannan rigimar, bai fita ko ina ba haka bai yi sallah ba, babban abin da yake kara daga min hankali ke nan, Hamza ya daina sallah kwata-kwata.

Ba ni da hanyar communicating da kowa nawa tunda ya kwace min waya da sim card baki daya. Wannan shi ya fi komai daga min hankali, na yi kuka, na yi kuka har na ba uku lada, Hamzah ya yi rantsuwa ni da sake rike waya sai ranar da na haihu, mai yiwuwa darajar ‘ya’yansa Abba ya ji tausayinsa ya karbe shi a matsayin miji na uban ‘ya’yana, mai yiwuwa idan na haife sun ba lallai su zo da cutar ko su zama carrier ba, shi ko a ya ya na haifa yana so, a cewar sa son da yake min da wanda nake masa ba zai bada kowacce irin cikakkiyar ma’ana ba sai mun haifi yara tare, masu lafiyar ne ko marasa lafiyan.

Wani lokacin zuciyar so da ta karfin son da nake yi wa Hamzah kan so ta rinjaye ni in ji tausayinsa, ganin yadda tashin hankalin dana ke masa duk ya ramar da shi, wani lokacin sai in kuma ga kamar da gaske ba shi da zabin ban da abin da ya yi din. So- so-so ne, amma masu iya magana suka ce son kai ya fi dabi’ar dan adam ce son kai. Amma a kullum zuciya ta ta kusa yarda da hujjar sa ina tunawa kaina ba za ka so ganin masoyinka cikin maraicin iyaye ba alhalin suna raye. Da fushin su a kanka. Da haka nake concluding da cewa, Hamza Mawonmase ya fi son kansa da abinda zan haifa masa a kan yadda yake ikirarin yana sona.

Rannan na kasa shiru, yana breakfast da ruwan lipton a kan dining din gidan na fito daga daki zan wuce kitchen, Hamzah sai cewa ya yi bayan ya aje cup din hannun sa bisa tebir, “Siyam, wannan wace irin rama ce ki ke yi haka? Ki rufa min asiri ki dinga cin abinci, don Allah ba don ni ba”.

Wata muguwar harara na sakar masa, na ce, “Ina ruwanka da rama ta Hamzah? Ba ni ba kara ce maka Shaheed ko Habiby don duk ba ka cancanci wadannan sunayen ba.

Shaheed na nufin shahidi wanda ya yi shahada ya rungumi Allah da ManzonSa da salloli biyar. Kai kuwa fa? Ba zan gaji da cewa kai ba shahidi ba ne yanzu, ko da za ka yi ta cewa ina tutiya da addini.

Habiby kuma na nufin masoyi na, shi kuwa masoyi ba zai taba son ganin masoyinsa cikin kunci da fushin iyaye ba…”.

Na fashe da kuka na ce, “Hamzah ka yaudare ni da yawa, addu’ar mace ga mijinta karbabbiya ce, Allah ya dandana maka irin kuncin da ke cikin zuciyata a yanzu”.

Hamzah ya zaro ido ya ce , “Ya Subhanallah. Siyam! Ki yi wa Allah ki maida addu’arki, idan kuncin rayuwa ya same ni na rantse ke ma ya same ki.

Ki kwantar da hankalinki mu yi rayuwar da ki ka rayu kina roka mana rayuwa da masoyin ka ta fi komai, musamman in ku ka samu sanyin idaniya a tsakaninku (‘ya’ya) kuka cika gidan kuda hayaniyar su.

Har yanzu ban karya alkawarina ba, zan kai ki wajen Abba da Ummati amma bayan mun samu ‘ya’yan da zan ci albarkacinsu a idanunsu”.

Da sauri na ce, “Idan kuma Allah ya hana mu ‘ya’yan fa? Idan ban haifa ba fa? Kana magana kamar mu za mu bai wa kanmu haihuwar, Hamzah ilmin addini bai ishe ka ba, ko kadan babu imani a tare da kai, na rantse kana bukatar shiga islamiyya”.

Na wuce kicin na bar shi a nan, na bar shi cikin zuzzurfan tunanin da furucina ya jefa shi.

“Kana bukatar shiga islamiyya.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 56Sakacin Waye? 58 >>

2 thoughts on “Sakacin Waye? 57”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×