Skip to content
Part 58 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Shi da kansa ya san hakan, yana bukatar ilimin addini tunda yana son addinin musuluncin da zuciya daya, yana kuma son ya mutu musulmi, musulmai su binne shi a maqabartar musulmai. Ba ya son tuna irin burial din jahilcin da Beroms suka yi wa kaka.

Har A/Cwato Air-Conditioner aka saka mata a kabari wai don kada ta ji zafin kasa. He has been asking himself cewa wannan ba jahilci ba ne? Ta ina za’a sami electricity a cikin kasa? Har da kudin guzuri  duk suka hada mata. Ta ya ya wanda ya mutu babu ruhi a jikinsa zai mafana da wani abu na amfanin gidan duniya. Haka ya wuni cikin wannan tunanin na shaguben Siyama wanda a bisa ma’aunin hankali gaskiya ta fada masa. He needs islamic school.

Tun zuwan mu Istanbul ba ma ga maciji ni da Hamzah, abin dai da Aunty Nasara ta hana ni ba ni da zabi ban da shi din, don ta shi ne kadai zan iya kuntata masa in jefa shi a bacin ran da ni ma ya jefa ni, wato (sex denial). Abin da na san ya fi kuntata shi fiye da tsiwa ta ko kalaman baki na marasa dadi wadanda ba sa kara masa komai sai nishadin yin cece ku ce da ni kawai, har sai na gaji na sakar masa.

A satinmu na biyu a Istanbul ne ya kasa hakurin da yake yi, ya shigo dakina a lokacin na fito daga wanka, ban ji shigowarsa, ba don na juya baya a wardrobe ina neman kayan barcin da zan saka. Daga bayana kawai na ji an zare tawul din da ke jikina.

Na juyo a fusace sai bakina cikin na Hamzah, ya soma wani soft kissing very gently, in the way and manner da ya san ko ina na kai da fushi da taurin zuciya zai samo ni.

Amma ina! Wankin hula yau ke neman kai shi dare, don sosai nake fighting dinsa, na kuma rantse babu ni babu shi a shimfida balle in samu cikin ‘ya’yan da ya ke ikirarin sai na haife su ne zan koma ga mahaifana.

Kokawa sosai muke yi, har ya fara gajiya, ni ban gaji ba, ya ce, “Siyam, are you…” Maganar ta makale a makoshinsa sakamakon ya samu galabar kai ni bisa gadon aurenmu. Rana ta farko da Hamzah ya gwada min karfi don samun biyan bukatarsa. A wannan daren ni da shi duka har kuka mun yi, domin mun gane no matter what bambancin ra’ayi da akidar da ke tsakaninmu ba za mu iya rayuwa ba tare da juna ba.

Amma na zabi daga wannan ranar ba zai kuma jin komai daga bakina ba. Na daina magana na daina cewa komai, ko talabijin bana kunnawa. Daga daki sai daki, abincin ma na daina ci sam.

Ruwan lipton nake cikawa a tea flask in shiga daki da shi in wuni ina sha babu ko sukari. Watakila in ya ga zan mutu ya yarda ya maida ni gaban iyayena, tunda ya ki ya zama irin musulmin da nake buri. Na yarda yanzu, ba komai ka ke mafarki ko buri ka ke samu ba. In kuma ka yi nasarar samun su ba lallai su tafi a yadda ka ke so ko ka tsara ba. Na maida hankali na ga tilawar karatun alqur’ani a dakin barci na, kuma daga ranar duk lokacin da ya nemi tarayyar aure da ni bana fighting dinsa, kyale shi dai nake ya yi kidansa da rawarsa shi kadai ya gaji, wanda wannan ya fi komai bakanta masa rai, don har ya gwammace muyi cikin kokawar yafi samun yadda yake so, don haka cikin bacin rai da zafin zuciya yake yin komai kamar dole, kamar in bai yin ba zai rasa ransa ne, ba don haka ba na tabbata da tuni ya hakura ya sallama ni. Hamzah kenan.

A haka muka kwashe wata guda a Istanbul kafin in fahimci ya fara fita daga karfe takwas na safe sai shidda na yamma yake dawowa gidan, kuma kullum zai fita sai ya kulle ni ta baya. Bai sani ba cewa idan ma bai kulle ni din ba ina za ni?Alhalin ban san inda ya kai passport dina ba, kuma ba ni da kudin jirgi?

Wannan shirun da nake masa wanda yake kira “silent punishmentfor coming to Istanbul” ya fi komai bakanta masa rai, ya kuma sa ya koma ga rungumar giya fiye da baya don a ganinsa wurinta kawai yake samun sanyi.

Watan Azumin Ramadhana mai girma ya kama, na fahimmci hakan ne rannan da na zauna a falo ba ya nan, na kunna TV sabida kadaici ya dame ni, na ji ashe gobe za a dauki azumin ramadhan, har masallacin makkah sun fara sallar tarawih. Don haka na mike na shiga kitchen don in samar wa kaina abin da zan yi sahur da shi. Kullum da ‘take away’ dinsa yake shigowa gidan, ganin cewa asara yake yi in ya saya don zai zo ne ya tadda abinsa ya sa ya daina sayowa da ni, ya bar ni da shan ruwan lipton dina. Gabadaya na zuge na kare a tsaye, yau kuma da na ji an ga wata za’a dauki azumi washegari don haka na yanke shawarar yin sahur, domin Annabi (S.A.W) ya kwadaitar da mu da yinsa ya ce, “Domin a cikinsa akwai albarka”.

‘Fried sphagetti’ wadda ta ji kayan lambu sosai na yi, na zauna a kan dan karamin dining din kitchen din mai cin kujeru uku, ina ci a hankali da fork. Daga can falo na ji rufe kofa alamar ya dawo gidan. Ba jimawa kuma sai ga shi ya shigo kicin din yana sanye da shirt da trouser na DKNY, ya yi kyansa kamar kullum, dogon da gaye mai aji na musamman ma’abocin tsafta ta ban mamaki, amma kuma ya rame sosai sabida damuwar rashin samun kan uwar gida, ya yi matukar mamakin ganina a wurin a daidai wannan lokacin ina cin lafiyayyen abinci. Farin cikinsa ya kasa boyuwa a kan classy fuskar da a yanzu ta daina burge ni, don ba zan ce na daina sonta ba, amma ko me ya yi yanzu Hamzah ya daina burge ni.

Ya shigo kicin din ne da zummar shan giyar da ya jera a karamin firjinsa na musamman ya rufe shi da makulli sai zai sha kawai yake zuwa ya bude ya sha. Yanzu ma abin da ya kawo shi kicin din kenan ya sha yayi wanka ya kwanta, ya tadda ni unexpectedlya kicin din. Kwarjinin musulunci da na yi masa shi ya hana shi bude firjin, ya ja kujerar da ke fuskantata ya zauna yana zuba murmushi.

“Madame, wato ita yunwa da ma ba kanwar uwar kowa ba ce”.

Ban tanka masa ba. Ya sake cewa, “What a delicious!”. Ya sa ka fork din gabana ya diba ya kai bakinsa. Sai da kunnensa ya yi motsi. Rabon shi da cin girkin Siyam tun a Washington. A fili yace, “Yaushe rabon duniya da ayyaraye? Yaushe rabona da daddadan girkin Siyamata?”

Mikewa na yi zan bar masa wajen da abincin duka. Ya riko ni idanunsa a wahale, “Siyama don Allah, Siyama VOA please, ki saurare ni. Ki zauna mu yi magana ta fahimta ni da ke, wallahi na gaji, na gasu, na soyu ke har na kone!”.

Nan ma ban yi magana ba na dai juyar da kai na wani gefen daban, idanu na suka ciko da kwallah. Idan na tuna bani da ranar ganin Abba balle in nemi gafarar sa sai in ji na kara tsanar sa kan yaudarar da ya yi min.

Hamzah ya zaunar da ni a kan cinyoyin sa, ya rungume ni sosai, muna shaqar kamshin numfashin junan mu muna jin yadda zuciyar kowannen mu ke bugawa da sauri da sauri tabbacin dukkan mu mun wahala, sai hawayen bakidaya suka balle min. Ina sonsa har gobe, amma ya kasa zama nagari irin yadda nake so ya koma.

Ban san lokacin da na kwantar da kai bisa kafadun sa ba, na yi kuka, na yi kuka har na ji babu dadi, Hamzah sai rarrashi na yake yi yana ba ni hakuri, the apologizer Hamza Mawonmase bada hakuri ba abu ne mai wuya a gare shi ba, balle a inda ya tabbatar ya yi laifi. Laifi mai girma irin wannan. Shi ma nasa idanun sun yi rau-rau ya ce, “Siyam, ki yarda don ina son ki ne ina kuma son rayuwa da ke na zabar mana hakan, wanda ke son ka shi ke son rayuwa da kai har muddin rai, shi ke kwadayin hada jinin sa da naka. Wallahi wanda ba ya son ka ba zai taba son jinin ka cikin jikin sa ba. Ina so in haifi ‘ya’ya da ke Siyama koda zan kare sauran rayuwa ta gabadaya a cikin jinyar su. In dai a kan dawowar mu kasar nan ki ke wannan mummunan fushin da ni na amshi laifi na, believe me a kan ba yadda zan yi ne. Suna son ki, ni ma ina sonki…!”

Ban san lokacin da na katse shi ba.

“Kana so na za ka rabo ni da su, ka hana ko gaisuwar waya tsakani na da su? Wanda ka ke so ba za ka juri ganin sa cikin kunci ba Hamzah. Yana zabar naka farin cikin ne a kan nasa…”

Ban rufe baki na ba ya ba ni amsa, “Ba wani farin ciki a gare ni da ya fiye min rayuwa da ke, ke ma ba wani farin cikin da ya fiye miki rayuwa da ni. Ina tausaya miki kamar yadda nake tausaya ma kaina ranar da na biye miki muka koma gaban Abba, kuma dan sa Omar yana nan bai yi aure ba, aka ce masa kuma ni AS kema AS. To be at the safest side, shi ne mu je tare da bataliyar ‘ya’yan mu”

Mikewa na yi daga cinyar sa na nufi daki, don na gaji da jin tatsuniyar sa irin ta kwararrun mashayan barasa, wadanda basu yarda Allah ke tsara komai ba a’ah wayon su ne da dabarar su. Duk abin da suka yi amanna da shi a matsayin daidai babu mai saka su babu mai hana su.

Bayan shiga ta daki har key na saka na rufe kofar na kuma bar shi a jiki ban zare ba, don ma kada ya bude da nasa spare din. Na yi alwala na dasa sallar Taraweeh ta daren farko na wata mai alfarma, ina rokon Allah ya kawo min mafita ta alkhairi ba da jimawa ba.

Na ga ya kamata in masa magana a kan ya dau azumi tunda dai yana ta fadin shi bai yi RIDDAH ba, sallar ce ta ke masa nauyi a jiki, da kuma mantuwa. Wani zubin kuma ko ya saka alarm domin ya tunatar da shi sai ya ji kamar kafafun sa ba za su iya tsayuwar sallar ba.

Lokacin da ya gaya min hakan rasa me zan ce na yi, a karshe na gane cewa lamarin Hamzah cikin addinin islam ya fi karfin hannu na ni kadai kamar yadda Anti Nasara da Young Abba suka ce, cewa ba wata makarantar addini da Hamzah zai shiga wadda ta wuce tawa, ni din ba ni da fasahar koyar da addini kamar yadda ya ce. Sai dai in ta fushi, fushin da ba ya saka shi, ba ya hana shi sai abin da ya yi niyyah.

Washegari na tashi da azumin farko, da safe ina kitchen ina wanke tukunya da plates din da na bata jiya da daddare, Hamzah ya shigo kitchen din cikin shirin tafiya office. Ban juyo na kalle shi ba, ya ce, “Good morning Ma’am”. Sannan ya ja kettle ya zuba ruwa ya jona.

Ina kallon sa ya yi wa shayin sa hade-haden da ya saba da liptop din ‘Tetly Tea’ din ‘cinnamon’ ya zauna a dan karamin dining din zai fara sipping. Ban san lokacin da na kira sunansa da karfi ba.

“Ba ka azumi Hamzah???”

Dakatawa ya yi da kofin a kusa da bakin sa, shi bai sha ba shi bai aje ba, kafin ya ce,

“You mean fasting?”

Na gyada kai a hankali, sai ya aje kofin bisa table din ya yi shiru, ya ce, “I don’t know about it at all, da na dauka, even in christianity we do fast”.

Tsaki na yi na ci gaba da wanke-wanke na, ni kaina ban san na yi tsakin ba, wai cikin addinin almasihu ma suna yin azumi, to ina ruwa na?

Dole ya hakura da shan shayin ya dawo kusa da ni yana taya ni jera plates din a mazaunin su, yana tambaya ta, “Azumin da wuya ne? Damuwa ta ba cin abinci ba ne…”.

“Barasa ce!”. Na yi maza na karasa masa.

Ya kama kai ya ce, “Oh! Kya bari ki ji me zan ce ko? Gaskiyar magana har da ita, kuma dai yunwa da wahala”.

Kamar in fasa ihu na ce, “Hamzah! Hamzah!! Ka ji tsoron Allah! Addini ba abun wasa ba ne, azumi yana daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, be careful, kai ba sallah ba, ka ce azumin ma ba za ka iya ba, alhalin kana ikirarin kai musulmi ne a yanzu, ga shan giya kai abun ya yi maka yawa wai shege da hauka. Ina jiye maka zama makamashin wutar jahannama….. Sa’irah wallahi!”.

Hamzah dariya ma na ba shi, ya dara sosai kafin ya ce, “Amma tare za mu shiga wutar da matar da ba ta taimaka wa mijin ta a shimfida, sai dai ta zame masa kamar jikakken tsumma, ba ta yi masa biyayya har da tsaki, kullum burin ta ta daga masa hankali, a hakan kuma tana ikirarin ta fi kowa tsoron Allah, in kuwa aka bincika nata laifukan na hakkin aure sai a ga sun fi nawa zunuban kazanta, tunda ni kullum ina addu’ar Allah ya yaye min, idan shaidan ne a tare da ni, Allah ya raba ni da shi, ke fa? Kin taba neman in yafe miki daga azabtarwar da ki ke yi min?

Kada ki manta aljannar da ki ke tunanin za ki riga ni shiga sai na daga duga-dugaina ni da ki ke gani kafirin za ki samu damar shigarta, so ki bi ni a hankali, ki kuma koyo manner of approaching sabon mutum a cikin addini”.

Da kyar na iya daga kafa zuwa daki na, ina mai tambayar kaina da gaske yake biris din da nake yi da shi da hakkokin sa za su iya hana ni shiga aljannah?

Sosai na zage ina shirya mana abun buda baki don a tunani na ya kai azumin. Amma me? Karfe hudu na yamma na fito daga sallar la’asar na gan shi a falo ya hada quaker oat yana ta shan abunsa babu ko kunyar Allah.

Sakin baki na yi galala cikin mamaki da bakin ciki sai ya ce, “Excuse me Madam Siyam, actually… actually I… I’m very much hungry, na yi miki alkawarin gobe zan yi, kin ga ban yi niyya ba, kuma ban shirya ba tukunna…”.

Juyawa na yi na koma daki ina kuka sosai. Ya zan yi ne? ya zan yi Hamzah ya rungumi addini da gaske?

Kukan da ya ga na kwana yi yau shi ya sanya washegari ya dauki azumin, ya kai da qyar da sidin ludayi, amma maimakon ya yi buda baki da dabinon Ajwa da na ajiye mana a kan dining wanda shi da kansa ya sayo mana a supermarket, wai ya ga musulmi a garin suna ta saya yau, shi kam Mr. Hamzah da tsadaddiyar barasa (wine) ya yi buda bakin sa.

Abin da ban sani ba, bai kuma zaunar da ni ya yi min bayani ba, sakamakon rashin kwanciyar hankali da rashin fahimtar junan da muke ciki, aiki ya samu da “TRT WORLD”, sabon gidan radio da talabijin na kasar Turkiyya, wato (Turkish Radio and Television Corporation) da suke broadcasting awanni 24 da harshen turanci dana Hausa da ke da matsugunni a birnin Istanbul. TRT na bayar da World News (labaran duniya da dumi-dumin su da kuma harkoki na yau da kullum (current affairs) a kan kasar Turkiya da sauran kasashen Europe, Africa, Western and Southern Asia.

Wannan hammshakin sabon gidan radiyon Hamzah ya yi nasarar samun aiki da su a matsayin sa na mai experience din aikin jarida na kusan shekaru goma da International Media. Dalilin sa na neman aikin kuwa, ba don ba ya son VOA ba ne a yanzu, sai don yana neman hanyar barin kasar Amurka da Siyama zuwa inda ba su da kowa, don su yi rayuwar su su kadai cikin kwanciyar hankali a dalilin tsoronsa na kada iyayen Siyama su raba su.

Wannan kenan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 57Sakacin Waye? 59 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×