Skip to content
Part 68 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Motar mu ba ta tsaya a ko’ina ba sai a kofar gidan Ummati. Wannan karon da Hamzah ya yi baya-baya sai Young Abba ya kamo hannun sa ya damke suka shiga tare. Shi kansa bai san tsoron me yake ji ba a kan iyayen Siyama, amma shin me ye laifin tubabben bawa?

Shi nasa tsoron ya san bai kyautata addinin yadda ya kamata ba a bayan karbar shi, and this is what’s haunting him today. Don bai san me zai je ya zo ba idan Siyam ta zabi abin da yake tsoron kasancewar sa.

Sai ya samu kansa da kama addu’a irin wadda bai taba yi a rayuwar sa ba.

“Na tuba Ya Ubangiji na tuba, na bi Ka Ya Ubangiji. Ya Ubangiji na bi umarnin Ka. Astagfirullah! Astagfirullah! Astagfirullah! Idan iyayen Siyam suka kwace ta na yi alkawarin ba zan bar addini na ba, na karbi addinin musulunci da dukkan zuciya ta, zan tsare dukkan iyakokin sa matukar iyawa ta. Idan sun dubi Allah sun bar min ita, na yi alkawarin kyautata mata, daga yau zan zame mata miji irin wanda ta ke mafarki (mai addini), kuma mai nagarta irin wanda iyayenta suke so ta samu kuma mijin marainiya. Kada Ka bar mu da zabin ran mu ya Allah, ka zaba mana mafita ta alkhairi ni da ita baki daya”.

Hamzah ya kalle ni, muna saka kai a rumfar Ummati, kamar kowannen mu ya san irin addu’o’in da dan uwan sa ke yi a zuciyar sa, muka yi wa juna kallon da idan ka gani sai ya yi matukar ba ka tausayi.

“Ummati… Ummati useini fu ummu daga balndi da hokka am kosam mi bofti velo”.

Tun daga tsakar gida Ya Omar ke fadi cikin Fulfulde. Yana nufin, “Ummati… Ummati tashi daga wannan kwanciyar taki ki ba ni fura da nono, yunwa na kwaso”.

Kishingide ta ke a kan katifar Dunlop dinta kamar yadda ta saba a kowane yammaci, tana sauraren shirin jakar magori daga ‘yar radiyon ta. Ni kuma na ce.

“Ummatin Mambillah, wai ke ba kya taba tsufa ne? Abba duk ya tsofe amma ke sai kara dawowa yarinya danya sharaf ki ke yi?”

Kamar daga sama Ummati ta ji wadannan muryoyi na Boddo da Omar, amma ba ta gasgata ba har sai da ta ji Boddo kwance cikin jikin ta.

Iya kaduwar da Ummati ta yi ya isa, kuma ta bi bakin fuskar da kallo, wato Hamzah, Aryan da Aunty Kausar suna zama a kujerun da ke fuskantar ta.

Ture ni ta hau yi daga jikin ta tana cewa, “Daga ni, kada ki karasa ni, ban shirya bin Dalhatu yanzu ba.  Ban ga ‘ya’yan ku ba.

Yaya ran ki don kin ganni danya Sharaf? An ce miki kowanne Da irin ki ne mai sa iyaye a damuwa da hawan jini? Da na dan albarka Mamman ke kula da ni baya taba bari na in yi kukan babu”. Ta dubi Young Abba ta ce, “Auta jabbama-jabbama, kun sha hanya, sannun ku da zuwa, wannan kidahumar sai yau ta ga damar zuwa? Ai na dauka sai zaman makoki na za ta zo”.

Ummati ta soma sharar hawaye nan da nan sannan ta ce, “Daga kawai an ce ki nemo Omar sai ki kwashe shekaru haka ba ki zo gida ba? Na yi na yi su yi miki aure sun ki ko bazasu dawo mana da ke ba, shi Omar din da yake soko ne na gaske, ai yana aiko mana da gaisuwa ta waya, dukkan ku kun bar gida ba waiwaye, in mun yi fushi ba za ku dawo ku yi ta bin mu da lallashi har sai mun huce ba?”

Ina kuka sosai na ce, “Wallahi Ummati kullum ranar Allah da ku nake kwana da ku nake tashi a rai na. Kaddarorin rayuwa suka rike ni”.

Young Abba ya zamo jikin sa daga cikin kujera yana gaida Ummati. Ta mike ta dauko tabarmar ta ta shimfida wa Hamza.

“Jabbama (lale maraba) abokin auta, kema bakuwa barka da zuwa”. Jabbama ya ki karewa daga bakin ta, Kausar kuma ta shimfida mata dardumar sallar ta.

Da man dai Ummati ba daga nan ba wajen karrama bako. Ta dubi Aryan da ke makale jikin Mamin sa ta ce, “Ya ka nan, zo nan mai kama da Gidado, Allah Kareem, kada ku ce min yaron Omar ne?”

Ummati ta janyo Aryan jikin ta tana hawaye, kamar Gidadon ta yana karami, jini ya yi magana da kansa ya gaya mata ko wanene Aryan ba sai an gaya mata ba.

“Faruku da gaske ne abin da idanuna ke fada min? Wannan jikan Gidado na ne?”

Ni da Ya Omar sai kuka ya kwace mana, kukan tausayin Ummati ga tsufa ya kara rufar mata ta ko ina. Yanzu ne muka san hakika duk mu biyun bamu kyauta ba. Hakika ba mu kyautawa Abba da Ummati ba dukkan mu.

Omar ya gurfana a gaban Ummati yana afi yana fadin, “Ban kyauta ba, ban kyauta ba. Na yi aure babu sanin ku Ummati, ku yafe mana ni da Boddo, kaddara da rabo ne mai karfi suka fitar da mu daga gaban ku, ba mun yi don mu bata muku ba ne. Boddo ma kin gani Young Abba ya yi mata aure har ta haihu dan ba rai, yanzu kuma ta kusa sake haihuwa.”

Sai falo ya koma tamkar gidan makoki, sabida koke-koken Ya Omar, Boddo, Ummati har da Anti Nasara ta shiga taya mu. Su ma Young Abba da Hamzah don maza ne na gaske karfin hali suke yi, amma idanun su sun kada. Hamzah ya ji ya tsani kansa a kan parental deprivation din da ya janyo wa Boddo da iyayenta.

And guilty conscience overwhelmed him. Me ya sa bai cika alkawuran da ya daukar wa Boddo a lokacin da ya kamata ba? Me ya sa bai kawo ta wajen Abban ta immediately bayan auren su ya cika alkawarin da ya dauka ba? Me ya sa bai taya ta nemo Omar ba kawai duk ya koma mata wani devilish rana daya bayan shi kansa ya san ba halayen sa ba ne? Abin da ya sani shi ne ya kudurta cika dukkan alkawuransa bayan ya samu ‘ya’ya tare da Boddo sabida tsoronsa na kada iyayenta su raba su in ya tuno background din sa. Abin da ya kamata kuma ya saka a ransa tun a lokacin shi ne, ‘ALLAH’ shi ke yin komai ba dabarar mu ba. Idan ka rike shi you have no fear of anything and anyone in life.

A wadannan ‘yan dakikan Hamzah ya yi wa kansa fada mai yawa tunda ya san ba shi da mai yi masa. Ya gaya wa kansa ya so kan sa, sannan ya dora buri mai yawa a kan son haihuwa da Boddo wanda watakila shiyasa Allah ya jarrabi ‘ya’yan nasa da zuwa da cuta. Ya yi wa kansa alkawarin idan Allah ya sake ba shi damar zama da Boddo zai gyara komai, zai gyara halayen sa.

Wata zuciyar ta tunasar da shi cewa, “Dama tana zuwar wa dan Adam ne sau daya a rayuwa, da kyar zai sake samun irin damar da ya samu a kan Boddo a baya, idan Allah ya yi maka baiwa to ka san ya yi maka, and make use of it a appropriatelyatappropriate time.

Hamza ya lumshe idanun sa, don ba ya son ganin irin kukan da Boddo ke yi a jikin Ummati. All because of him, all because of his love which he didn’t make use of it wisely.

“Boddo am, ya isa haka”. In ji Ummati, “Tunda har kin kawo min Omar da mata da dan sa mai kama da Gidado, to kin fita ko ba sabulu”.

Young Abba ya zakuda ya ce, “Boddo ba ki gabatar da Hamzah gun Ummati ba”.

Na sunne kaina cikin kirjin Ummati ina cewa, “Kai Young Abba… haba Young Abba ai kai zaka gaya mata”.

Ummati ta ce, “Wane ne Hamzan?”

Young Abba ya nuna mata inda Hamzah ke zaune daga can nesa da su sunkuye da kai, alhinin duniya, nadama da tausayin Siyama da family din ta suna ta daka tsalle a tsakar kansu.

“This is Mr. Hamzah Mawonmase Ummati, mijin mafarkin Boddo, wanda kullum ta ke gaya miki tana jira, tana kuma ganinsa cikin mafarki”.

Ummati ta yi sakale tana kallon Hamzah. Young Abba ya ci gaba da cewa, “Na yi musu aure tun da jimawa, gashi har sun samu rabo, na farkon ya koma, tun lokacin da Hamzah ya karbi addinin musulunci a dalilin son da yake wa Boddo na yi musu aure”.

Ummati ta dan daburce, “Ban katsi hanzarin ka ba Auta, amma ban gane me ka ke nufi da ya karbi musulunci ba, da ma can ba musulmi ba ne ko ya ya?”

Ba Young Abba kadai ba, hatta Ya Omar ya firgita da razanar Ummati, cewa ta ke, “Hande mi woni dume mi nanata do?” (Na shiga uku nikam, me nake ji haka?) Tubabbe ka aura mata saboda ba kai ka haife ta ba ko ya ya?”

Young Abba kunya ta yi bala’in kama shi ganin irin muzantar da ta bayyana a fuskokin mu ni da Hamzah, one thing da bana iya jurewa shi ne, a kira Hamzah ‘TUBABBE’ amma gaskiyar kenan, ina so ko bana so.

Young Abba ya shiga da ya sani da bai fada ba. Ya koma lallashi cikin kasalalliyar murya.

“Ummati, da wanda aka haifa cikin musulunci, da wanda ya shigo yau duka daya muke a wurin Allah, Ummati kari muka samu a cikin addinin Allah, kamata ya yi ki yi farin ciki sanadin Boddo musulunci ya samu kari”.

Inah! Ummati ta mike tana rawar jiki tana karkarwa tana cewa, “hande mi woni. Jikar Dalhatu Gembu ka aura wa tubabbe, auta? Ba ka taba bata min rai ba irin yau, ka bata min kyakkyawar zuri’a ta”.

Jiki na rawa ta dauko waya tana kiran Abba Mamman, yana dagawa ta rushe da kuka.

“Mamman da sanin ka auta ya aura wa Boddo tubabbe?”

Dr. Mamman Gembu a kwance yake amma sai ganin sa Wasila ta yi a bakin kofa yana fadin, “Iyeee? Na’am? Ummati me ke faruwa? Mene ne kuma tubabbe?”

A takaice ta yi masa bayani, wai ashe mijin Boddo da Young Abba ya aura mata a Amurka dan addinin Almasihu ne ya shigo musulunci saboda Boddo”.

Abba ya ce, “hasbunallahu wniima wakeel. Yo ni Ummati sanda ya kawo min zancen auren na ma tsaya na ji wa zai aura mata? Ina ruwa na ko bayahude ya aura mata su suka sani tunda shi ta zaba”.

Ummati ta ce, “Akul! Diyar ka ce Mamman, lallai ka zo gobe, fushi a nan gabar ba naka ba ne, ka zo mu ceci ‘yar mu, wannan karon dole a bai wa Boddo zabi, ko dawowa gida gaban iyayen ta, ko auren tubabbe…”.

Abba ya ce, “Ummati na daina tada jijiyar wuya na a kan Boddo, ni tunda ba ta auri Omar ba ko Fir’auna ta aura ba ni da matsala”.

Ummati ta ce, “Lallai-lallai gobe ka zo, ba zan yarda a bata min zuri’a da jinin kafirai ba, ka ajiye maganar fushi ka kama ‘yar ka, fushin naka ne ke ta walagigi da ita yake neman halaka ta. Idan itama ta yi riddah fa? Lallai-lallai ina jiranka gobe a Mambillah”.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Kawai muke maimaitawa a falon Ummati, ganin yadda ta dauki tafasar zuciya ta yi jajajir abinki da farar fatar tsohuwa. Jijiyoyin wuyan ta dana goshin ta duk sun mimmike. Ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba. Young Abba yana ta kokarin kiran Yayan sa don ya gyara kalaman daga yadda Ummati ta cabalbala su. Dr. Mamman Gembu, ya yi kememe, ya yi kemadagas ya ki daga wayar sa. Ko me ya faru da Boddo a ganin Abba Mamman Gembu Young Abba ne ya daure mata gindi.

A karshe ta ce mu fitar mata da tubabbe daga gidanta kada mu janyo mata fushin mala’ikun rahma, ta yi da fulatanci ta yi da hausa, ta yi har da larabci. Kunya, bakin ciki da takaici sun ishi Ya Omar da Young Abba har ma da Anti Nasara da ta san yadda ake mutunta Hamza a inda ya baro.

Ummati ta hada su su duka har Nasara ta yi musu wankin babban bargo da cewa ta yi dana sani da ta yarda ta ba su rikon Boddo. Kada su bari ta kyafta idanun ta ba su fidda mata tubabbe daga gidan Malam Dalhatu ba, tun kafin a nuna masa a kabarin sa.

Duk yadda muke zaton rigimar za ta kare cikin daren a fahimci juna da Ummati, abu ya faskara. Dukkan mu a rumfar Ummati muka yi kwanan zaune. Hamzah yana so ya yi hawaye ma ko ya ya ko ya ji sanyi a zuciyar sa daga zafafan maganganun Ummati na wulakanci da batanci da aibata tubabbe, hawayen sun ki disa ko sau daya a kan fuskar sa sai kirjin sa da ke kai kawo yana sama yana kasa. Shi dai ya san akwai alaqar aure tsakanin Beroms da Fulani, kuma addinin musulunci ya yarje wa wanda ya karbi shahada ya auri mata daga abin da ya yi masa dadi har hudu cikin matan musulmi, thenwhy this extreme hatred daga kakar Siyam?

Sai ya tuna shi tashi kakar hadiyar zuciya ta yi ta mutu ma gaba daya. Don haka na Ummati mai sauki ne.

Ko runtse ba ta runtsa ba tana ta zuba fada cikin fulatanci da hausa, ta kuma dora laifin kacokam a kan Young Abba. Babban abin da ya daga masa hankali cewa da ta yi, don ba shi ya haifi Siyama ba.

Young Abba ya dafe kai cikin kasalalliyar murya ya ce, “Ummati na rantse da Allah abin da zan yi wa Boddo na alkhairi ba zan yi wa dan da na haifa ba, ki tsaya ki fahimta Ummati.

A tarihin musulunci Annabi (S.A.W) ba ya kyamar Ahlil kitabi. Hijirar farko ma ai a wajen NAJJASHI musulmai suka tsere don neman saukin azabar Quraishawa wanda a karshe Najjashi ya musulunta ya zama daga cikin manyan sahabban Annabi (S.A.W).

Allah madaukakin Sarki ya halatta auren kamammun mata daga cikin ahlil kitabi, wato Yahudawa ko Nasara suna ma cikin addinin su kamar yadda ya yi bayanin haka a cikin suratul Ma’idah, aya ta biyar.

‘Al-yauma uhillulakumul dayyibat, wa da’amul lazeena utul kitaba hillullakum wa da’amukum hillullahum, wal muhsanati minal mu’uminati wal muhsanati minal lazeena utulkitaba iza ataitumu hunna ujurahunna, muhsinina gaira musafihina wala muttakhizee akhdan…’.

Har ila yau, an samu wasu daga cikin Sahabbai sun aure su kamar Usman dan Affan Halifa na uku a musulunci ya auri Ahlil kitabi, haka Dalhatu dan Ubaidullahi ya auri Banasariya. Shi ma Huzaifa masanin sirrin Annabi (S.A.W) ya auri Bayahudiyya Allah ya kara musu yarda. Duba (Ahkamu- Ahlizzimah, P2/794).

Balle shi Hamzah ya yi shahada Ummati, ya shaida Allah daya ne ya yi sallama da wancan addinin nasa faufau, kafin ya auri Boddo”.

Kwana Young Abba da Ya Omar suka yi suna yi wa Ummati nasiha mai ratsa jiki da kawo mata misalai na ahlil kitabin da suka musulunta ake kuma amfana da su. Ciki har da marigayiya Dr. Aisha Lemu ta jihar Neja. Da umarnin da musulunci ya yi na peaceful coexistence tsakanin mu da su. Ya kuma halatta mu aura daga tubabbu kuma kamammun cikin su.

Duka wannan dambarwar da ke faruwa yau a kan sa kuma a kan idanun sa, bata sa ya ji haushin iyayen Siyama ba (Ummati da Abba), hasali ma ba komai takun sakar da dambarwar da wulakancin ke saka masa ba sai wani irin zeal da kakkarfan determination a kan neman ilmin addinin musulunci ko a ina yake, in dai wannan shi ne kadai zai ba shi kima a idanun iyayen Siyama, su daina yi masa kallon kafiri duk da musuluntar da yayi, in har kuma ilmin addini shi ne abinda zai ba shi kima da lasisin ci gaba da auren Siyama to kuwa zai tafi har birnin Sin don nemo shi.

“Kanku ake ji”. In ji Ummati. “Haka kawai watarana a mayar min da jikoki ahlil kitabi, ai ba za ku hada abin da aka yi aka wanye lafiya a zamanin Annabi (S.A.W) da na wannan zamanin ba. Arnan Najeriya ne aka ce muku ban sani ba? Wadanda har kisan gilla suke yiwa musulmai saboda kabilanci?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 67Sakacin Waye? 69 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×