Skip to content
Part 69 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Firr! Ummati ta ki russuna zuciyar ta a kan Hamzah, ta ki yarda a ko’ina ba’a rasa na kirki har a gidan Fir’auna, in everything there’s exception, ta ce sai dai na kara zaba ko shi ko su. Ba maganar auren Omar kuma har abada sun kashe ta, in har da gaske yafiya da afuwar su nake so ita da Abba kawai in zauna tare da su.

Shi ma Abba da ya zo washegari a bisa kiran mahaifiyar sa ya yarda ya saurare mu, amma ya ce shi da say, sai abinda Ummati ta fada, da shi da ita duka abu guda ne; ba su yi na’am da auren tubabbe ba, sun yarda har abada ba maganar Ya Omar tunda ni da shi duk mun hada kai mun ji auren juna mun zabo bare, to mu cigaba da zumuncin mu da suka san mu da shi amma dole Hamza ya sakar musu Boddo in ta haihu ta samu miji asalin musulmi ta yi auren ta.

“Na yafe miki duniya da lahira Aishatul-Siyama Boddo, bacin ran da ki ka sanya ni shekara da shekaru na yafe miki, na yarda rabon cikin dake tare da ke ne ya janyo komai don ban isa in hana dan wani shaqar numfashi da iskar duniya ba, amma na ba ki zabi ko cigaba da auren tubabbe ko ci gaba da zama da mu”.

Ina kuka Hamzah na yi na ce, “Duk abin da ka zaba min Abba b azan kara musu a kai bad aga nan har karshen rayuwa ta, na ba ka wuka da nama. Na gode bisa afuwar daka yi min Abba”.

Abba ya ce, “To kuwa ya sake ki ta ruwan sanyi mu yi sallama ta mutuntawa da fahimtar juna”.

Iyakar bacin rai ran Young Abba ya gama baci, Ya Omar kuma tausayin Hamzah ya sa ya zama kurma a falon ba ya iya cewa uffan.

Young Abba ya ce, “Ni ya bai wa sadakin ta, saboda na dauka nima uban ta ne da zai iya aurar da ita, ya biya ta sadakin warawaran zinare guda uku, kuma suna hannun ta, zata maido ne?

Yau Yaya ka nuna min ba ni na haifi Boddo ba, da ni na haife ta da ba a yi min wannan nuna iyakar ba”.

Ya juya ga Hamzah, wanda daga jiya zuwa yau kadai ya rame fit, idanun sa sun yi ciki sosai sun kuma kada saboda tijarar Ummati. Ga ta Abba kuma yau wadda ta dame tatan, tunda shi saki kacokam din sa yake bukata without a second thought.

Ya tuna cewa ya riga ya bai wa Allah zabi, ya fauwala masa komai don haka ya yarda duk abin da ya zaba musu shi da Siyama shi ne daidai. Hamzah ya tsugunna a kan gwiwoyin sa ya ce da Abban.

“Na bi Allah na bi umarnin ka Abba. Amma Boddo na da juna biyu na yara har guda biyu, ina rokon alfarmar ku barta ta haifa mun su, ta shayar ko na shekara daya ne kafin in sake ta, ya zama bata da iddata bayan haihuwar ta, in ya so sai a kirawo ni in dauke su in an yaye su in kawo takardar sakin, na barku lafiya, ina mai neman gafarar ku.

Ya juyo gare ni ina ta cizgar kuka cikin mayafi na, wai aka ce ba mutuwa akewa kuka ba SABO ne, ba soyayyar nakewa kuka ba SABO ne domin hakika na saba da Hamzah na kuma shaku da shi. Hamzah yayi murmushin karfin hali ya ce

Siyam, sai watarana, Allah ya yi miki albarka, Allah ya sauke ki lafiya. Za ki ga sako na cikin account dinki, kada ki manta a saka musu sunan Young Abba da Anti Nasara, idan duka mata ne a saka Siyama da Nasara, idan maza ne a sa Young Abba da sunan Abba…”.

Daga haka Hamzah Mawonmase ya bar gidan mu, tafiyar da ba ni da tabbacin zai dawo ko ba zai dawo ba. Ban kuma san inda ya nufa ba, fatan sa ya je inda rayuwa za ta koma masa cikakka, kuma ma ma’ana, ta kuma maida shi cikakken mutum a idanun iyayen Siyama.

Ita rabuwa da miji kowacce iri ce, ko da auren kiyayya ce sai ta kekketa zuciyar diya mace balle rabuwa ce ta auren SO tsantsa irin wanda ke Tsakani na da Hamzah Mustapha, rabuwa kuma bata saki ba, tun daga ranar da Hamzah ya bar ni a Mambillah muka dawo Abuja na rungumi Allah na rungumi ibada, na kuma ci gaba da rainon cikina na haihuwa yau ko gobe tare da kyautata wa mahaifi na wanda bashi da abin tattali yanzu iri na, da kyautatawa uwa ta Wasila da kanne na guda uku, Abba ba shi da abin tattali yanzu irina, komai nake so sai idan Wasila ba ta gaya masa ba. Tuni ya yi min sayayyar kayan haihuwa iri-iri da kayan jarirai (unisex) ba tare da damuwa da makudan kudaden ciyarwar da Hamza ke turowa account dina duk karshen wata ba.

A cikin bacin rai Young Abba da Anti Nasara suka koma U.S, Ya Omar da iyalin sa suka tare a gidan da Abba ya gina masa tuntuni da sunan ni da shi. Amma Aryan bai bi su ba, ya ci gaba da zama a nan gidan mu saboda sakonsa Hayatuddeen, Ya Omar kullum sai ya zo gidan mu ya kwantar min da hankali, ya kuma gaya min kada in taba nuna wa Abba gazawa ta a kan hukuncin sa. Hamzah kuma ya kira shi ya tabbatar masa yana nan lafiya, amma ya bar Turkiyyah.

Abin da bai gaya min ba shi ne, yadda aminci mai karfi ya kullu tsakanin sa da Hamzah, suna kokarin samo mafita ga auren mu ta hanya mafi dacewa. Abba bai kara tada zancen Mawonmase ba ko da wasa. Ummati ce dai sai in ba mu hadu ba, amma sai ta yi korafin zan haife mata tubabbun jikoki a zurri’a, ita bata taba zaton za a cakuda mata zuri’a da kabilu kuma tubabbu ba. Idan Ya Omar yana wurin shi kadai yake tare min, ya ce, “Bawa ba ya wucewa abin da Allah ya rubuta masa, kuma dukkan mu kabilun Najeriya ne tushen mu shi ne kasar Najeriya, da fulani da Hausawa da kabilun Jos da na kudancin Najeriya auratayya da cakuduwar mu in peaceful coexistance abune mai kyau (to make one GREAT NIGERIA). Shi tunda Hamza ya musulunta da gaskiya kuma ya yi sabuwar dammara cikin imanin da ya yi da Allah ba shi da kaico a kan aure na da shi.

Sai kuma ya ce, “A’a Ummati, ki yi wa dan Adam uzuri sau saba’in kafin ki kama shi da laifi, don Allah fulani mu rage kabilanci”.

Ummati sai dai ta zobaro baki, ta ce, “Kabilanci ko? Ai har kasa ta nade ba za mu daina shi a kasar Najeriya ba”.

Ni dai na daina kwakkwarar magana ma a cikin mutane, ba kuma cikin bacin rai ko takurar zuciya nake ba, amma na dade da sanin Hamzah ya tafi, tamkar tare da ruhi na. Tamkar gangar jikina ya bari a Mambillah da Abuja ya tafi da dukkan walwala ta inda ya nausa.

Amma kullum cikin godiyar Ubangiji nake domin Abbana da nake tare da shi a yanzu, kuma kullum zai fita sai ya sanya min albarka ya yi min addu’ar sauka lafiya, har ya kara min da ta gamawa da duniya lafiya.

Ba abin da ya kai soyayyar iyaye dadi, soyayyar miji daban ta ke, a kuma nata muhallin, tunda Ubangiji da kanSa shi ya assasa ta tsakanin Adamu da Hauwa’u, su kuma suka haife mu. Amma soyayyar iyaye da kulawar su ga ‘ya’yan su ba za ka taba hada ta in any way da soyayyar miji ba.

Amma soyayya gaskiya ce, domin na samu kaina da jin haushin Hamzah da tun tafiyar sa ko a waya bai neme ni ba, ko da a boye ne ta hanyar Ya Omar wanda kusan kullum suna tare a waya. Har a gabana Ya Omar kan amsa wayar Hamzah. Na kasa yi masa uzuri da cewa Abba ne ya kore shi bisa jagorancin bacin ran mahaifiyar sa, Ummati.

A ganina ko da suka kore shi ai auren mu yana nan, ba kudin da yake faman turomin duk wata nafi bukata ba, na cancanci ko lafiyata ya dinga tambaya, kudin da yake cika min a account ba su ne damuwata ba ko kadan, kuma na daina addu’a a kan komai ban da zabin Ubangiji, kamar irin in ce Allah ya sassauta zuciyar Abba ya barmu mu ci gaba da rayuwar mu tare, ko in ce Allah ya dawo da Hamzah gare ni, ko wata addu’a makamanciyar wannan, a’a, yanzu addu’ata ita ce Allah ya zaba min abin da ya fi alkhairi a rayuwata.

A cikin wannan yanayin na shiga EDD dina, Aunty Wasila kullum cikin shiri ta ke na tarbar haihuwa a kowanne lokaci, ciki ya yi tsiri ya kuma yi fadi ya yi tororo, ta gama tanadar duk abin da ya dace har yajin jego haka shi ma Abba, Ya Omar ma ba a barshi a baya ba don tabbatar da ba ni da matsala, kuma ba ni da damuwa har Allah ya sauke ni lafiya a asibitin Nizamiye. Yara lafiyayyu kyawawan gaske, black beauties irin dai yadda nake mafarkin yarana da Dream Husband su kasance, amma Hussainar ita ma kamar na farkon ko kuka ba ta yi ba ta koma, Hassanar Allah ya bar mana wadda tun a ranar Abba da kansa ya yi mata khutbah da sunan ‘NASRA’ don Ya Omar ya jaddada masa wasiyyar Hamzah na a saka sunan Anti Nasara. Abba bai yi musu ba, amma sai ya kira ta da Nasrah don shi ma ya yarda cewa Nasara Alkali ta taka rawa mai girma a rayuwa ta.

Tun kafin mu dawo gida daga asibiti Ya Omar ya kira Hamzah ya gaya masa, ban san me suka tattauna ba na ga dai Ya Omar yana ta daukar baby a wayarsa yana dariya yana fadin, “Na taya Aryan godiyar wannan zukekiyar mata. Allah ya sa rayuwarmu ta kai. Ga Boddon ko za ku gaisa?”

Ban san me Hamzan ya ce masa ba, ya ce, “shi ke nan babu damuwa, everything will be alright in sha Allah”.

Na ce, “Ya Omar, ka daina yi masa tayin gaisawa da ni, ni ma ba zan gaisa da shi ba bisa umarnin Abba ba, ya je ya yi ta tafiya shi sarkin masu zuciya”.

Ya Omar ya kama baki, ya ce, “Oh! Kada ki ce min kan sa za ki juye laifin su Abba? Bawan Allah, cewa fa suka yi ya sake ki, tafiyar sa ita ce mafi alkhairi a lokacin don in suka tursasa shi zuciya ba ta da kashi Siyama, karshen kyara da kyama Hamzah ya gansu gun Abba da Ummati, dole ya yi nesa da ke for the mean time da suke bukata din, don a samu zuciyarsu ta yi sanyi ta kuma fahimci ba laifi bane jihadi ne kuma kari ne ga addinin musulunci, tunda ba abin da lokaci ba ya canzawa a rayuwar dan adam”.

Ya Omar ya kawo wa Abba tikeken rago da tikekiyar tinkiya ya ce na radin sunan Nasrah in ji mijin ta Aryan. Ba kuma shi ya fada ba Hamzah ne ya yi wannan kyautar wa Aryan tun saukowar ta duniya. Da ma kuma tunda aka yi haihuwar nan Aryan ya tare a daki na yana taya mu raino da rarrashin baby. Abba sai da ya yi dariya ya ce, “Ni dai babu ruwana, idan ta yo halin uwar ta ta bar min Aryan da cizon yatsa”.

Kunya kamar in yi yaya, sai da na mike na bar wajen, Anti Wasila kuma ta ce, “Ai ba ta yar a kasa ba ita ma Boddon gado ta yi, ‘yar na gada ce ba ‘yar na koya ba. So a daina ganin laifin ta dukkan ku fulanin nan sai a hankali wajen kafiya da naci fa Abba”.

Abba na hararar Anti ya ce, “Ni dai ba ni da halin Boddo, can ta gado abinta wajen Adamu”.

Ya nisa ya ce, “Humm! Wai ni Adamu ya daina kulawa ya kuma daina daukar waya ta ko? Babu laifi don bare/kabila ya fi ni yanzu a wurin sa. Na rasa inda zai kai Hamzan nan saboda son da yake masa, ita ma Boddon kanta ta hakura ta bi umarnina sai shi? Ai shi ke nan ya je ya yi ta yi, ‘ya ta ce bas hiya Haifa mun ba kuma ta gama zama da tubabbe”.

Wani ikon Allah tun lokacin da Nasrah ta yi wani zazzabi Abba yakai mu asibiti da kan sa, likita ya tabbatar masa yarinyar sickler ce, wato tana dauke da SCD a jikinta Abba ya dauki son duniya da tausayin duniya ya dora a kan Nasrah. Naturally da ma ‘ya’ya sicklers akwai su da shiga ran iyaye da kakanni, musamman iyaye mazan. Ga yarinyar kullum kara kyau da wayo take, ga gyara da ado tana sha a hannun Anti Wasila.

A haka yarinyar ta soma dabo (tafiya). Abba kan zauna ya saka Nasrah a gaba in tana wasa da Aryan a gaban sa da kawunsu Hayatuddeen, ya kura mata ido cikin tausayi, in Wasila na wajen sai ya ce, “Who knows ko zan yi tsawon ran da zan ga girman ta? Ko ita za ta riga ni tafiya tunda ba sa tsawon rai?

Who knows ko Allah zai kama ni da laifin hana ta tashi a gaban mahaifin ta? Who knows ko za ta yafe min in ta ji na tsani Babanta na raba su don kawai ya musulunta?”

Ranar da Anti Wasila ta gaya min kalaman nan da ta ji Abba na fadi, I was shocked, very shocked, na soma tunanin ko dai Nasrah ce za ta zama tsanin gyara tsakanin Abba da Hamzah?

Sanda na yaye Nasra shekarunta biyu tana gudunta ko ina. Rannan na ga advert a LinkedIn BBC Hausa na neman ma’aikata, for the position of a broadcaster da za su ajiye a reshen su na birnin tarayyar Najeriya. Kamar da wasa na yi applying, kuma babu jimawa na samu suka dauke ni (as a George Washington University alumnae kuma mai first class degree) British broadcasting Corporation suka ba ni gurbi tare da su, na zama daya cikin BBC family. Na fara ayyuka na cikin madaukakiyar nasara na karanto labarai da shirye-shiryen BBC da harshen Hausa.

Kullum shirin safe nake yi, don kuwa ni ce nake bude gidan radiyon BBC kullum, muryata ta samu karbuwa wajen dubban jama’a, rana ta farko da aka haska ni a shirin talabijin kuwa BBC sun sha kira daga masu saurare, kai har da masu neman iri daga sassan duniya daban-daban, domin babu wanda ya yi min kallon matar aure balle UWA. Ni kaina na san Allah ya yi min halitta mai boye shekaru mai bayyanar da kuruciya da wadatar jini a jika. Ba jimawa na zama BBC Celebrity of the year “Aisha Siyama Mamman Gembu”.

Rannan Ya Omar ya zo ya samu Abba da wata muhimmiyar magana. Ban san dai me suka tattauna ba, wanda har ta kai ga Abba ya kwanta zazzabi. Wai ashe Hamza ne ya turo shi ya gaya wa Abba yana son daukar Nasrah, ya gama magana da asibitin da za su yi mata BONE-MARROW TRANSPLANT da wuri tun kafin ta cika shekaru uku.

Abba ya shiga damuwa matuka, don ya ce wa Omar in yarinyar nan ta mutu garin Bone-Marrow ba zai taba yafe musu ba. Don bai taba haihuwar dan da yake so kamar ta ba, ko Siyaman albarka.

Ya Omar ya yi ta lallashin Abba, ya ce, “Insha Allahu lafiya za a yi a kuma gama lafiya, don samar wa yarinyar rayuwa mai inganci a gaba. Da saukaka mata wahalar da za ta sha a rayuwarta. Ya gaya ma Abba, Hamzah ya sayar da dukkan gonakin sa na Jos, don ya samu kudin da za’a yi Bone Marrow Transplant din, da asibitin ‘Saudi-German’ yanzu ana neman ‘donor’ da zai yi matching ne.

Abba sai ya ce, “Ba ga ‘yan uwanta ba? Maryam-Jamilah da Shukrah-Nadiya? A duba cikin su in ya yi daidai a tafi da su a dauka”.

Hatta Anti Wasila was a bit shocked da wannan kauna ta Abba da Nasra, amma a hali na kirki irin nata ta amince dari bisa dari, ‘ya’yanta su ceci rayuwar diyar Azumi-Siyama tunda sune sibllings din ta.

An auna Maryam-Jamila sai aka samu AS ce. Shukra-Nadiya cikin kudurar Ubangiji AA ce haka Aryan, dukkansu AA. Don haka Aunty Wasila da Aunty Kausar ko sun firgita da zamowar ‘ya’yansu ‘donor’ ga Nasra Hamzah Mawonmase, to ko a fuska ba su nuna firgitar tasu ba, sun bada goyon baya da addu’ar fatan alkhairi dari bisa dari.

Sai shirin wadanda za su raka Nasra zuwa Saudi-German, ni dai na yi kawaici wanda kowa bai zata ba, na ce ba sai na je ba. Na wakilta Aunty Kausar din Ya Omar ta wakilce ni, addu’ata za ta tadda Nasra har inda ta ke.

Ba kuma don komai na yi hakan ba, sai don ban shirya fuskantar Mr. Hamzah Mawonmase ba, for the second phase na rayuwa ta ba ni da zabi ba ni da buri, tunda har gobe Abba bai furta komai a kan komen namu ba.

Dadin dadawa shi ma Hamzan yau shekaru uku kenan bai neme ni ba ko a waya, sai dai in ji Hamzah kaza-Hamzah kaza a bakin Ya Omar. Kai na fahimci yanzu ne ma Ya Omar ke son Hamzah har fiye da son da Young Abba ya yi masa a rayuwa. Sirrin amintakar tasu ne ban sani ba har yau.

A kullum Ya Omar ya shigo gidan sai ya rusuna ya sumbaci Nassy a goshi, sai ya ce, “In ji Daddyn ki”.

Rannan ina ji tana tambayar sa, “Waye Daddy na? Ni Abba ne Daddyna, Aryan miji na, Yetuddeen (Hayatuddeen) Babana…”.

Ya Omar ya hau dariya ya sure ta ya daga sama yana cewa, “Ni kuma fa?”

Ta ce, “Yayan Boddo”.

Ai kowa sai dariya. Aunty Wasila har da kyakyatawa.

Anyi-anyi Nasrah ta daina ce min Boddo ta ki dainawa, yadda ta ji kowa a gidan na fada ita ma hakan ta ke fadi ba ruwanta da wani Mama ko Mummy. Boddo-sama-Boddo-kasa kamar ita ta rada min sunan.

A kullum na dubi Nasra fuskar mahaifin ta nake gani a cikin tata, his dark complexion and his almond shaped eyes. Idan kuwa ta karkace ta tsaya a gab ana ko tana takun nan nata majestically, sai ka rantse Mawonmase ya yi kaki ya tofar ne, his gait (takun tafiya), his geniusness and his coolness duka Nasrah ta kwashe komai.

An saka ranar tashin su zuwa kasa mai tsarki, Nasrah, Aryan, Shukra-Nadiya, Ya Omar da maidakinsa Aunty Kausar Shettima domin yi wa Nasra Hamzah Mawonmase ‘bone-marrow transplant’.

Na kwana a kan goshi na a wannan ranar. Cikin sujjadah da ruku’i. Kamar yadda a can wani bangare na gidan malamai na jami’ar Ommul Qurah da ke Madinah, a daidai wannan lokacin, shi ma yana can cikin sujjadah, cikin rokon Ubangijin sammai da kassai ya sa a yi aikin diyar sa cikin nasara, ya tashi kafadun ta. Yayi masa tsawon rai da nisan kwanan da zai aurar da ita da hannun sa ga Muhammad Umar Farouq Gidado AKA (ARYAN).

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 68Sakacin Waye? 70 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×