Skip to content
Part 29 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Ina Aunty Aina? Ta kuma maimaitawa “Ni na aika miki da saƙo ba Aunty Aina ba.” Ki nutsu Hamida na daɗe ina mafarkin wannan ranar, sai yau Allah ya cika min burina na samu damar kaɗaicewa da ke.

Tun ranar da na fara ganin ki sha’awarki mai tsanani ta kama ni, ki bani haɗin kai in kauda kwadayinki da ke azalzala ta.”

Hamida ta toshe kunnenta “A’uzubillahi billahi minash shaiɗanir rajim. Ka rufa min asiri ka buɗe min ƙofa ni matar aure ce kai kuma mijin yar’uwata ne.”

“Sai me? Zan mallaka miki komai a duniyar nan matuƙar za ki mallaka mini kanki.”

Ya fara nufo ta tana ja baya hawaye na sauka daga cikin idonta “Sai na gaya wa Aunty Aina.”

Ya noƙe kafaɗa yana ci-gaba da shafa cikinsa “Sai me idan kin gaya mata? Ranar da kika gaya mata ranar zan mata saki uku. Ki ba ni haɗin kai ta lalama, ƙin amince min zai sa a tsinci gawar mijinki don ba zan bar shi ba.”

Jikin Hamida ya shiga wata sabuwar rawar ta saki kuka gaba ɗaya.

Ya ci-gaba da nufo tana ja baya yana faɗin “Gaya ma wani wannan maganar zai sa ki rasa mijinki, da auren yar’uwar taki da take riritawa.”

Har ya ritsa ta ƙarshen bango matse ta ya yi ta shiga kiciniyar hankaɗe shi yana kiciniyar raba ta da rigarta, ihu ta ƙwalla ya tura ta gadon ta faɗa ya yi azamar bin ta zai danne ta ƙwalla ƙara ta miƙe ta dira gadon ta nufi ƙofa ganin ba key ya zare shi ya sa ta faɗa wa bathroom ta danna key sai addu’a ta Allah ya kuɓutar da ita daga wannan fasiƙin take.

Kukan wayar Aina da ya tura mata text ta jiyo, hankalinsa ne ya tashi ganin Aina ke kiran. Sai da ya saita kansa ya ɗaga kiran “Yaya lafiya? Ya ce mata “Gani nan dawowa, ka fita office ne? Gaban shi ya buga “Na fita na dawo, mantuwar wasu files na yi.”

Ok ni ma mantuwar na yi, sai da na fita na duba ɗayar wayata ban gan ta ba, kuma cikin ta lambar matar take.”

Ya ce “Ok sai kin ƙaraso.”

Ya matsa saitin ƙofar bathroom ɗin “Ga Aina nan, ki fito ni fita zan yi, amma ki sa a ranki haɗuwar mu ta biyu sai na samu abin da nake so, barin wata alama kuma da Aina za ta gane yana nufin mayar da ita har ke zawarawa.”

Gaban Hamida ya kuma tsananta bugawa, ko da jin shiru ta kuma leƙawa ta kafar makulli ba ta gan shi ba hakan bai sa ta fito ba har sai da ta ji maganar Aina.

Wanke fuska ta fara yi don yadda ko’ina na jikinta ke zubar da gumi,ta ɗan daidaita kanta sai ta fito “Haba ni dai na ga motarki ashe kina ciki?

Hamida da ta kasa haɗa ido da ita ta isa gaban dressing mirror “I na shigo Aunty Aina, ina kika je?
Takowa ta yi inda Hamida ta zauna tana murza ma fuskarta mai hannunta ta riƙe” Me ya faru da ke Hamida na fuskanci kina cikin damuwa? Ta sunkuyar da kanta don duk yadda ta so ta ware kar Aina ta fahimci komai abin ya gagara, hawaye ta fara hankalin Aina ya ɗaga “Kun yi faɗa da Abdurrashid ne?

Ta girgiza kai tana kai hannunta tana share hawaye “Damuwar rashin haihuwar ne ko auren na shi da Gwoggo ta ba ni labari? Ki yi haƙuri Hamida,gara kishiyar gida da ta waje. Ni nan yanzu kowa kallona yake ina ba shi sha’awa ina cikin daula, amma zaune dai nake ina haƙuri, Brigadier kamar bunsuru yake shi da mata.”

Hamida ta yi saurin duban ta “Wallahi Hamida, kin san dai duk yaransa maza ne suna Turai ya tura su karatu yana holewarsa, har gabana waya yake da karuwai, in taƙaice miki har gidan yake shigo da mata in ba na nan.”

Hamida ta dafe ƙirji,” Wallahi na yi nadamar irin auren da na yi Hamida, a gani na kuɗi sune jin daɗin duniya sai na ga saɓanin haka, ga dai daula ina ciki amma wannan matsala ta sha min kai a halittata ta yaya mata matan da ke yawo bisa titi me suka fi ni? Amma ban ishi Brigadier kallo ba, ya gwammace ya bi har waɗanda ba su ko kama ƙafata ba. Ba abin da ban yi don ganin ya daina amma kamar ina zuga shi, kullum ina cikin nadama na son duniya irin nawa ga shi nan na tsinci kaina a halin kwaɗayi mabuɗin wahala.”

Ku godewa Allah da kika auri saurayi matashi kyakkyawa ba ya neman mata yana son ki, auren da suka dage sai ya yi ke kuma ki dage roƙon Allah akan haka, haihuwar ma yaushe aka yi daren da za a tsangwame ki kan ba ki haihu ba? Ni zuwa na yi aka cire min abin da na sanya wa mahaifa ta, kin ga yanzu ina da cikin fata nake idan na haihu yaron da zamu samu ya kusanto min da Brigadier kusa da ni don mutum ne shi mai tsananin son yara.”

Kallon ta Hamida ta ƙara yi ashe ƙara harƙewar da ta yi kamar za ta fashe ciki ne, ta hura iska sai ta cigaba “Domin duk yadda nake ganin munin halin shi ban kuma so aurena ya mutu, ina komawa gida ƙasƙanta zan yi, aure komai watsewar shi daraja gare shi.

Yanzu ma tun fita ta na ji hankalina ya ƙi kwanciya da rawar da na ga yana ta yi da fitar da zan yi na kuma duba jakata na ga ba wayata ɗaya, na yi zargin shi ya cire ta duk da na kasa tuna mai zai yi da ita, na kira shi don ma idan yana tare da wata ya sallame ta kafin zuwana don ban shirya ganin tashin hankalin da zai yamutsa min tunani ba.”

Ta ja ajiyar zuciya “Na taho gabana na ta faɗuwa sai dai ganin ki a gidan ya kwantar min da hankali, duk da dai akwai alamar yana da plan na kawo wata daga yadda na zo na samu ya fasa masu aikina.”

Hamida ta girgiza kai “Ki yi haƙuri Aunty Aina.”

Ta dafa ta “Haƙuri ya zama dole Hamida, ƙarshen duniya muke kowacce da kalar haƙurin da za ki ga an manna mata a gidan aure, wata yanzu tana can ƙwaƙƙwaran abinci babu ba kuma sutura kuma yana bin matan.”

Hamida ta gyaɗa kai “Allah ya ba mu mafita.” Ta amsa da “Amin me za ki ci a kawo miki? Hamida ta miƙe zuwa gado “Ba komai Aunty Aina.” Ta kwanta ta rufe idonta.

Ainar ta fita can sai ga ta ta dawo “Kin ga wayar da na bari Abdurrashid ya kira.”

Ba tare da ta ɗago ba ko ta buɗe idonta ta ce “Na ce mishi ba ki jin daɗi ne Aunty Aina, don kar ya ce na cika zuwa.”

Kai ta gyaɗa “Ok kira ya yi ya gaishe ni kenan? Ta zauna gefen Hamida sai dai duk yadda ta so su yi hira Hamida lumshe idanunta ta yi kamar me barci.

Kwanciyar awa ta yi sai ta miƙe “Zan koma gida Aunty Aina.” Ta ce wa Ainar da ta samu a falo tana cin Tuffa “Haba dai tun yanzu? Ki zauna mu yi hira kin ƙi.” “Bari in je Aunty Aina.” Suka jera har inda ta adana motarta ta shiga ta tashe ta sai ta bar gidan.

Tana isa gida bedroom ta faɗa ta kwanta rub da ciki kuka ta shiga yi sosai na baƙin cikin jarabtar da aka yi mata da maza waɗanda suke makusantanta suke bibiyarta, bayan Usman aminin mijinta yau ga mijin yar’uwarta. Ko dai ta faɗi ma Abdurrashid take ta ayyanawa a ranta, wata zuciyar ta kwaɓe ta “Ki rufa wa kanki asiri.” Ko na Usman da ta yi niyyar ta faɗa mishi sai tunanin wata ƙawarta da suka yi karatu tare ya faɗo mata ita wani lacturer ne ya so ya haiƙe mata ta gaya wa mijinta, bayan sammaci da ya yanko wa lacturer ita kuma abu kaɗan za ta yi ya yi mata shaguɓe.

Haka ta yi ta kwanciya ko girki kasa tashi ta yi ta yi sai mai taimaka mata ta sanya ta yi. Ko da Abdurrashid ya dawo ya gan ta sukuku ya tambaye ta ce mishi ta yi kanta ke ciwo amma ta sha magani. Haka ta kwana cikin damuwa.

Da safe tana zaune gefen gadon Abdurrashid yana ɗaura takalmi, ziyarar aiki za shi Maiduguri. Ko da take cikin waccan damuwar tafiyar shi zuwa Maiduguri sai ta ji ta yi mata tsaye,gani take wurin Anisa za shi don tun barin ta Kano ta samu labari sun koma Borno.

Har wurin mota ta raka shi sai da ya ɗaga ta koma ciki ta fara shirin makaranta.

Haka ta ci-gaba da rayuwa cikin damuwa da ta sa a ranta a tsorace take fita zuwa makaranta don sau biyu tana lura ana biye da ita dukkan su ta sha da ƙyar.

Tana ta gaya wa Abdurrashid ita Kano za ta koma da zarar ta kammala karatunta, shi dai jin ta kawai yake yana mamakin ta ya rasa me za ta yo a Kanon da ta dage za ta koma ita kaɗai babu shi da ya kawo ta.

Ranar wata Alhamis da ba za ta taɓa mance ta ba a tarihin rayuwarta. Tana ta sauri makaranta za ta tafi wayarta da ke kan mirror ta yi ƙara, ta kai hannu ta ɗauka tana barin ɗakin, ganin sunan Walida ya sa ta murmushi “Manyan gari kuna nan? Hamida ta furta tana gota mai aikinta da ke mata a dawo lafiya, hannu ta ɗaga mata ta wuce cikin sauri “Haba dai ka ji zolaya, mutanen birnin tarayya ai kune da garin, ya kwana biyu? “Hamida ta ce “Sai alheri.” “Na shigo Abuja ki turo min address mu yi zumunci.” “Ah lallai ai wallahi ba ki da kirki Walida, duk daɗewa ta a garin nan wai sai yau za ki zo gidana.”

“Ba gara ni ba ga shi na zo ke ba sai dai a ji kin shigo Kano ba? Hamida ta buɗe baki daidai tana barin gidan “Duka zuwana nawa ni da ke karatu, akwai san da na je na je gidanku Umma ta ce min ba ki nan.” “An yi haka alhuda huda ni dai ina sauraren ki.” “Ok. Hamida ta ce ta sauke wayar tana ƙoƙarin tura mata sunan barrack ɗin.

Tana dawowa sai ga Walida ta yi mamakin yadda ta ga Walidar ta canza mata duk ba wannan ƙibar da ta narka.

Tara sosai ta yi mata suka zauna suna hira ta ce biki suka zo na yaron Aunty Saratu,da yake nan ya samu aiki(Yayarta da mijinta ya ɗauki nauyin karatun su Walidar) Hamida ta ce “Don rashin kirki ɗan Aunty Saratu na aure ba za ki faɗi min ba.”

Ta ce “Na ga garinku za a yi bikin don har su Aunty Saratun ba wanda ba za ki gani ba, akwai liyafar da za a gudanar gobe na san ai za ki halarta? Hamida ta ce “In sha Allah, yaushe za ki bar garin?
Ta ce “Sai jibi.” Kafin tafiyar ta ta yi ta jaddada wa Hamida tana fa jiran ta ta zo mata wurin liyafar.

Da Abdurrashid ya dawo suna cin abinci take ba shi labarin zuwan Walida da bikin da suka zo. Taɓe baki ya yi bai yi magana ba, murmushi ta yi don ta san da ma za a yi haka sanin ba wani haɗuwar jini ke tsakanin shi da Walidar ba. Ta roƙe shi za ta je ma Walidar Dinner ya ce “A’a.” Magiya ta yi sosai sai da ya ja ranta ya bar ta.

Washegari ta samu wayar Walida ta yi biyar tana jaddada mata tana fa jiran ta. Ta ce tana nan zuwa.
Kwalliya sosai ta yi da duk wanda ya dube ta sai ya kuma ga ƙamshi na musamman tana fitarwa,ta fita a motarta.

Ta kusa isa unguwar da Walida ta ce mata an kai amaryar don ta san unguwar nan ɗiyar Momi Binta ke aure sai ga kiran Walida ta ce “Ki ƙaraso View hotel anan za a gabatar da shagalin bikin, yanzu haka ina wurin.”

Tsaki Hamida ta ja “Wallahi kin wahalar da ni.” Ta karya kan motar sannan ta faɗi mata daidai inda take ta ce “Sai ki faɗi min ta inda zan bi, don ban san inda hotel ɗin yake ba.”

Ta ce “Kin ji ki kina yar gari ma ba ki sani ba ina ga ni baƙuwa. Bari in tambaya. Muryar wanda Hamida ta ji ya yi magana kusa da Walidar sai ta ji kamar ta san muryar, ta ɗan zurfafa tunani sai kuma ta watsar don ba ta ga abin da zai kai wanda ta yi tunani wurin ba.

Tana tafiya Walida na mata kwatancen har ta kai, ita ta zo ta tare ta sun jera bayan ta adana motar “Gaskiya matar nan kin samu duniya, kin ga yadda kike sheƙi.” Walida ta ce wa Hamida Hamidar duka ta kai mata suna dariya har suka kai inda aka ajiye kujeru kusa da sweeming pool don zaman jama’a.
Walida ta ja mata kujera ba ta zauna ba ta ce “A’a ya da zama kuma anan? Ta dafa kafaɗarta”Yanzu ake gyara wurin,mu zauna mu ɗan sha lemo kafin a fara.”

Amma shi ne maimakon ki bari in fara zuwa gidan bikin.” Hamida ta faɗi tana zama “Kar ki damu ba wanda ba za ki gani ba har Aunty Saratu.” Ba ta zauna ba ce ma Hamida ta yi tana zuwa, Hamida ta ciro wayarta tana dannawa har Walida ta dawo wani cikin masu aikin hotel ɗin na biye da ita da babban tray ya dire shi gaban Hamida sai ya juya, Walida ta zuba mata lemon sai ta zauna suna hira tana maimaita ma Hamida ta sha lemon, har dai ta ɗauka ta sha kurɓa ta uku sai ta ji kanta ya sara take ta ji ba ta yi, kanta ta dafe da ta ji yana juya mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 28Shirin Allah 30 >>

2 thoughts on “Shirin Allah 29”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.