Skip to content
Part 30 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Walida ta duba da ta ga ta ƙura mata ido sai ta ga Walidar ta taso ta kamata bayan ta rataya jakar Hamidar da ake ajiye.

Da taimakon ta suke takawa zuwa cikin Hotel ɗin, dan Hamida daf take da ficewa hayyacinta.
Wani ɗakin Hotel ɗin ta kai ta ta dire ta bisa gado bishi-bishi Hamida ke kallon ɗakin idonta na lumlumshewa, Walida ta kece da dariya “Sorry ƙawata, tun farkon fara ƙawancen mu nake fama da takaicin a komai kin fi ni, don haka da aka nemi in kawo ki za a ba ni maƙudan kuɗaɗen da ban taɓa mafarkin riƙewa ba sai ban yi wasa da damar ba.”

Usman Hamida ta ga ya shigo ɗakin yana wa Walida tafi, “Kin yi namijin ƙoƙari.” Ya faɗi yana duban ta, murmushi ta yi masa ta miƙa mishi hannunta “A ba ni balance ɗi na.” Ya ciro wayarsa “Zan miki transfer yanzu.”

Ya matso kusa da Hamida ya kama hannunta sai ya sake shi hannun ya tafi yaraf, dariya ya kece da ita sai ya ɗauke ta hoto.

Shigowar Brigadier ya ɗauke ji da ganin Hamida. Sara mishi Usman ya yi suka juya shi da Walida don barin ɗakin, Brigadier ya bi bayan su ya murza wa ƙofar key, ya dawo yana murza hannuwa yana ƙare wa Hamida kallo.

Ya zauna gefen gadon so yake ya cire komai na jikinta kafin ya gabatar da ƙudirinsa, amma matsuwar da ya yi ya ji shi cikin jikinta ya sa ya fara kwance zanenta, ya zare skirt ɗin da ke ciki kyawawan cinyoyinta suka ƙara ɗimauta shi ya ja fant ɗinta pad ɗin da ya gani ya sa shi janye hannunsa da sauri, sai ya dafe kai komai ya tsaya mishi, ɓacin rai ya maye gurbin farin cikin da yake ciki, tsaye ya miƙe sai ya zura kayansa da ya tuɓe ya bar ɗakin.

Ganin motar Usman a harabar Hotel ɗin ya ba shi mamaki ya isa ya ƙwankwasa glass ɗin, Usman ya fito yana sara mishi “Ya ba ka wuce ba? Ya tambayi Usman kame-kame ya hau yi don saƙe-saƙe yake yadda zai samu damar ɗaukar hoton Hamida yayin da brigadier ke kwance da ita da video yake so ya yi mata barazana ta ba shi kanta, don shi ba zai amfani da ita tana wata duniya ba ya fi so ta faranta mishi da kanta hakan zai sa ya samu gamsuwar da kullum yake mafarkin samu.

“Yallaɓai ka fito kuma? Usman ya tambaya yana wani sunkuyar da kai “Mance kawai, abin su na mata take zan jira har ta tashi, idan ta wuce sai in tafi.” “Ok Sir” Usman ya faɗi ya faɗa motarsa ya ja ya bar wurin jin Brigadier ba tafiya zai yi ba, don da ya san zai fito yanzu da ɓoyewa zai yi har sai ya wuce ya shiga ya rage zafi.

Awa uku Hamida ta ɗauka tana barci sai ta farka zaune ta tashi ta dafe kanta da ke sara mata. Ta ɗan jima a haka kafin abin da ya faru ya fara dawo mata zumbur! Ta miƙe tsaye salati take tana ƙarawa ganin zanenta da skirt a yashe tunanin sun keta mata mutunci ya sa ta fashe da kuka, sai dai tuna halin da take ciki na al’ada ya sa ta shafa wurin, fant ɗinta na nan haka pad ɗin, sai ta yi wa Allah godiya da ya kare ta.

Usman, Brigadier, Walida. Ta riƙa kallon hotunan su a cikin ɗakin da Walida za a haɗa baki a tarwatsa rayuwarta? Komai na ta ta ɗauka sai takalmanta ne ba ta gani ba, ba ta damu da tsayawa neman su ba ta fita dakin, sai da ta je gaban motarta ta lalubi key a jakarta, yana ciki da wayarta, tana tayar da motar ta fara kuka iya ƙarfinta.

Har ta kusa gida ta tuna da Abdurrashid, agogon motar ta kalla takwas saura na dare gabanta ya yanke ya faɗi me za ta gaya mishi yau? Ba ta son ce mishi komai har sai ta nutsu ta yi tunani, tana ajiye motar kusa da ta shi ji ta yi kamar kar ta fito,don shi ma tana jin tsoron abin da zai ce mata ta dai daure ta fita, a hankali take takawa har ta isa ƙofar falon ta yi sa’a ta ji ta a buɗe sai ta shiga da sauri ta miƙe zuwa ɗakinta “Ina kika tsaya sai yanzu kike dawowa? Cak ta tsaya jin muryar Abdurrashid cikin kanta wanda sam ba ta lura da shi a cikin falon ba. “Ban san sau nawa zan faɗa miki ba na son ki fita ki kai irin wannan lokacin matuƙar ba tare muka fita ba, amma kin raina ni, zan ɗau ki mataki a kanki.”

“Ka yi haƙuri.” Ta furta ba tare da ta waiwayo ba “Kar ki damu ki cigaba sai dai kar ki yi kuka da matakin da zan ɗauka kanki.”

“Don Allah dai na ce ka yi haƙuri.” Ta ƙara bada haƙurin cike da ƙosawa ta samu ta shige ɗakinta jin ya yi shiru ta san ba zai ƙara cewa komai ba sai ta wuce ɗakinta kamar ana tunkuɗa ta.

Gado ta hau ta rufe idonta takaici take ji kamar ta rufe kanta da duka, me ya sa ba ta tona mishi asiri maganganun banzan da ya gaigaya mata da yau ko me Abdurrashid zai yi mata sai ta faɗi abin da suka yi mata a yau shi da Walida, abin da zai taka mata burki Brigadier da ya shigo tsakiyar su, ba za ta so auren yar’uwarta ya mutu ba ɓullar maganar zai iya shafar zumuncin su har a can gida,
don haka ta yanke yin shiru kawai tana kammala karatunta ta bar garin.

Wayarta ta lalubo sai ta gan ta a kashe ta kunna tana neman sunan Walida sai saƙo ya shigo ta tsaya dubawa gargaɗi ake mata kan idan ta tona abin da ya faru a yau kiran sunan wani a cikin su ukun abu biyu zai faru mutuwar auren Aina da tsintar gawar Abdurrashid. Wani busasshen miyau ta haɗiya ta ci-gaba da neman lambar Walida sai dai ba ta shiga, goge ta ta yi gabaɗaya daga wayarta don wani abu da ke tokare ta idan ta ga sunan ta tuna cin amanar da ta yi mata.

Tana nan zaune cikin alhini da baƙin ciki ba ta ankara ba sai ta ga ƙarfe biyu da rabi na dare, ta shi ta yi ta shiga bathroom ta tsaftace jikinta sai ta fito ta tuɓe kayan jikinta ta kashe wutar ɗakin ta kwanta shiru cikin wani sabon tunanin.

Asubar farko barci ya yi awon gaba da ita wanda ya ja mata muguwar makara, sauƙin ta ma da ba sallah za ta yi ba shi ma bugawar da mai mata aiki ke yi ya tayar da ita, don Abdurrashid bai bi ta kanta ba saboda yana fushi da ita ya gama shirin sa ya bar gidan.

Ta buɗe mata suka gaisa sai ta koma ciki ta yi wanka, da fitowar ta wata doguwar riga ta zura ko mai ka sa shafawa ta yi.

Ta fito ta haɗa Tea zalla tana sha bakinta ba daɗi don yadda ranta ke ɓace, gamawar ta ɗaki ta koma tana ci-gaba da tunanin da ya fara addabar ta ta rasa wa za ta kira su raba wannan abu da ya faru da ita ko za ta samu shawara, Hanan da Mimi sune aminan ta amma kuma su ɗin dangin miji ne ita kam tana tsoron dangin miji komai daɗin ka da su.

Tana nan har ta ji dirin motar Abdurrashid ta miƙe ta fita tarar sa jakar da ya shigo da ita ta karɓa tana mishi barka da zuwa ya amsa fuska ba walwala, ko da ya ke fushi da ita yana mamakin abin da ya sa duk ta yamutse bai dai tambaye ta ba ko da suka zauna cin abinci yana kula ba wani na kirki ta ci ba.

Haka suka ɗauki kwanaki uku yana ta tunanin abin da ya same ta, don ya san hakanan yake fushi da ita ba ta bari a kwana za ta yi shigar da za ta ɗau hankalinsa ta sha turarukan da ƙamshin su ke kiɗima shi wanda jikinta ma da gidan sun riga sun riƙe ƙamshin,ta kawo kanta tana kukan kissa tana ba shi haƙuri shi kenan ya wuce.

Ya dawo aiki tana makaranta wanda tun faruwar abin a tsorace take fita sai ta ga kamar za su sace ta su idasa mugun nufin su a kanta, ji take kamar ta haƙura da karatun da aski ya zo mata gaban goshi ta tattara ta koma Kano.

Yana zaune ta dawo ɗakinta ta shige ta fito tana kankare jan ƙunbar da ta sanya a farcenta, kallo ɗaya ya yi mata ya faɗi a ransa ta samu tsarki kenan?

Don haka da daddare tana kwance a ɗakinta ya shigo a wannan daren Allah ya yi ikon sa rabo ya shiga a tsakanin su wanda da wata ya zagayo Hamida ba ta ga al’adarta ba hakan bai wani ɗaga mata hankali ba don ta sha yin haka sai sun gwada su ga ba komai.

Ba abin da ta canza na daga ɗabi’unta ma’ana ba ta wani laulayi kuma Allah ya ɓoye abin sa ko shi likita bokan turan bai gane ba.

A haka ta kammala karatunta ta shiga magiya ga Abdurrashid ya bar ta ta koma Kano shi kuma ya ƙi amince mata.

Wata safiya ta yi waya da mutanen gida mutum na ƙarshe da ta yi wayar da shi shi ne Malam da za su tashi zuwa ƙasar Singapore shi da Engineer, Malam ɗin na fama da ciwon sugar Engineer kuma zai je kan harkokin kasuwancinsa kuma shi ma za a duba shi kan ciwon shi na zuciya.

Engineer ne ya shirya musu tafiyar, zai tafi har da Aunty Karima.

Hamida ta yi wa Malam fatan nasara da dawowa lafiya. Har ta ajiye wayar sai ta ga ya kamata ta kira Daada kwana biyu ba ta kira tsohuwar ba, duk da dai idan ta ji shiru Hamidar ba ta kira ta ba sai ta kira. Sun gaisa ta ajiye wayar, Abdurrashid ya shigo ya dube ta yadda ta harɗe ƙafa tsakiyar gado “Wai me kike a ɗaki? Murmushi ta yi “Yan Daura na kira da Malam mai tafiya.” Shi ma ya murmusa “Ya yi kyau, ni fita zan yi, zan ga wani abokin aikina amma ba daɗewa zan yi ba wani saƙo zan karɓa.”

Ta diro gadon ta bi bayan shi sai da ya fita ta dawo, gadon ta koma ta ɗauki wayarta Whatsapp ta shiga bayan ta kunna data, shigowar wani saƙo daga wata baƙuwar lamba ya sa ta dubawa, wani ɗan short video ne sai saƙo a ƙasa video ta fara dubawa abin da ta ganin ya sa ta miƙewa tsakiyar gadon, sai kuma ta koma ta zauna gabanta na masifar bugawa zufa na wanke fuskarta.

Vedionta ne kwance shame-shame a ɗakin Hotel, har sunan Hotel ɗin ga shi nan ta dafe ƙirji tana karanta saƙon da aka turo ƙasan Video *”Ina neman haɗin kanki idan kina son rufin asiri wurin mijinki, in ba haka ba zan tura mishi vedio nan.”*

Wani baƙin ciki ya turnuƙe zuciyar Hamida, ko da dama ta san ba su ƙyale ta ba ba ta san Usman zai iya zuwa mata da wannan rainin hankalin ba, ita da kanta ma yau za ta faɗi ma Abdurrashid komai. Voice note ta yi masa ta dandanƙara masa magana kafin ta kwasa ta fito falo tana jiran dawowar Abdurrashid wanda take jin kamar ta bi shi don ƙosawar da ta yi ya dawo.

An samu kamar minti talatin ta ji dirin motarsa. Bugun da yake wa ƙofar shigowa falon kamar ba na lafiya ba ta ƙarasa ta buɗe sai dai yanayin da ta gan shi tuni ya sare mata gwiwa, tashin hankali take hangowa a tare da shi gaba ɗaya ya birkice. Zama ya yi a kujera ya cusa hannayensa cikin sumar kanshi kafin ya ɗago ya dube ta da idanuwansa da suka canza kala, take ta ji ƙafafuwanta sun ɗauki rawa.

Ya ciro wayarsa ya nuna mata “Meye wannan Hamida? Wane zance nake ji game da ke Hamida?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 29Shirin Allah 31 >>

1 thought on “Shirin Allah 30”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.