Skip to content
Part 11 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Wace Irin Uwa Ce Ni?

Amshi:

Wace irin uwa ce ni?

Wace irin uwa ce ni?

Wace irin uwa ce ni

Na saka ‘yata a baɗala.

01.

Ana gudun karuwai,

Ina renon karuwai, 

Wace irin uwa ce wai, 

Da ke renon karuwai.

02.

Bana kwaɓar ‘yata, 

Bana ko zaginta, 

Bare ma in doke ta, 

Bani duba da halinta.

03.

Bana damuwa da fitarta, 

Balle in duba dawowarta, 

Ba ruwana da ƙawayenta, 

Balle kuma samarinta.

04.

Na maida ita ‘yar gata, 

Bana son ɓacin ranta, 

Tana shigar sangarta, 

Ba na kuwa kwaɓarta.

05.

Ashe halinta na lalata, 

Ya fi shekarunta, 

Kanta tuni ta lalata, 

Ni ko ban hango ba.

06. 

Cikin shige ta yiwo, 

Ga cikinta na ciwo, 

Bayan mun je awo, 

Daga nan sai wayyo.

07.

Abin takaicin asali,

Bayan na yi su’ali,

Akan wanda yai aikin,

Bata ma fa gane ba.

08.

Bayan wata uku, 

Yayarta ta dawo, 

Daga karatu ta dawo,

Ina murna ta dawo. 

09.

Bayan kwana biyu, 

Ita ma ciki sai ciwo, 

Kai ana yin gwaji, 

Ita ma cikin dai ta yiwo. 

10.

Wayyo ni ni kaico,

Kaina na mini ciwo,

Zuciyata tana kuka,

Na ɓata ‘yar ‘yata.

11.

Ina za na sa kaina,

Da wannan abun kunya,

Lallai na yiwo wauta,

Na gane laifina.

12.

Allahu nai sakaci,

Har ma da sakarci,

Na ga tarbiyyar,

Ɗiyana da ka bani.

13.

Allahu sarkina,

Ka yafe ni laifina,

Ka goge zunubaina,

Ka shafe ainun. 

14.

Iyaye ku yo duba, 

Hali da tarbiyya, 

Na ‘ya’yanmu kui duba, 

Kar ku bi layina. 

15.

Wallahi na yi nadama, 

Na gane duka aibuna, 

Gani yau ina kuka, 

Ina tuba a gareka. 

Amshi:

Wace irin uwa ce ni?

Wace irin uwa ce ni?

Wace irin uwa ce ni

Na saka ‘yata a baɗala.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tambaya 10Tambaya 12 >>

2 thoughts on “Tambaya 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×