Skip to content
Part 8 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Biki na ta matsowa yau saura kwana goma, su Buhari ana ta shiri ya kama wani gida mai masifar kyau haya, wajen dubu d’ari biyar, shekara d’aya, iyayen Bilkisu sun je sun ga gida yace musu ma na shi ne, Bilkisu bata da aiki se kuka don har ga Allah bata son Buhari ko kad’an a ranta.

Abu kamar wasa yau an d’aura auren Buhari da Bilkisu akan sadaki dubu d’ari biyar yayin da aka kai amarya d’akin ta ba tare da wani bincike akan Buhari ba shi ma ba tare da sanin iyayen shi ba.

An kai amarya gidan ta da ke, cikin garin Sokoto, yayin da tashin hankali ya yi wa rayuwar ta Sallama.

Bayan wata biyu da auren Buhari su Saleh sun dawo gidan da zama don akwai d’akuna sosai a ciki, Ya d’auko mata mai aiki, wanda take kiran ta Baba lami, ita ce kawai ke d’auke mata kewa.

Bayan wata uku da auren su, Bilkisu na zaune ita da Baba lami a d’akin ta bakin labari ya same su cewa gidan su ya rushe, kuma iyayen ta na ciki duka sun mutu, kad’an ya rage Bilkisu batayi hauka ba don ciwo sosai ta yi na mutuwar mahaifan ta, bata da kowa yanzu a duniya se Allah se kuma wannan da aka ‘ka’kaba mata a cikin wata na uku da bikin su ne Buhari ya ce mata ze je Jigawa don yana sana’a ne acan, bata ce mai komai ba don ba ta ma son ganin shi.

Ya gama shirin shi tsaf shi da abokin shi Saleh, waya ya siya mata babba ce amma mai sau’kin kud’i ya ‘kar’bi number ta da na Baba lami.

Daga Sokoto Jigawa su ka nufa garin su Saleh, ko da su ka isa gidan yayi mamaki sosai yadda ake murna da zuwan saleh Sun manta ma da maganar makarantar da su ka tura shi, yayin da ya gabatar da Buhari yace abokin shi ne ya zo ziyara ne. Gidan su saleh gida ne na masu matsakaitan karfi gida ne da su ka gada awajen iyayen su daga shi se yayan shi da matar yayan shi da yaran shi se kuma kakan su, sosai Buhari ke jindad’in garin yana zaune a garin har wata biyu2 agarin don yanzu ko gida baya son zuwa ma.

*SOKOTO*

Tun da Buhari ya tafi Bilkisu ke fama da matsanancin ciwo, Baba lami ke kula, da ita, abu ya ‘ki ci ya ‘ki cinyewa hakan yasa su ka je asibiti, ita da Baba Lami in da aka tabbatar mu su ciki ta ke da shi, Bilkisu ta yi kuka sosai in da ta so ma a cire cikin amma Baba Lami ta yi ta bata hakuri da mata nasihohi haka nan ta hakura, Baba Lami ta kira Buhari ta fad’a mai, ba yabo ba fallasa ya ce “Allah ya sauke ta lafiya”. Sannan ya turo musu kud’i mai yawa.

*ADAMAWA*

Al-amin kuwa ya manta ma yana da wani d’a buhari yayin da kuma yau ne Abubakar ya shigo garin don an basu hutun wata d’aya1 sosai Abubakar ya yi kyau kai idan ka gan shi zaka ce bature ne don sosai hutu da jin dad’i ya zauna mai bayan kud’in da gwannati ta sakin musu, Al-amin na tura mai kud’i masu yawa lokaci zuwa lokaci, kwanan shi Shida da zuwa ya shirya zuwa gidan Uncle d’in su Ahmad don ya gaishe su, ko da yaje kyakykyawar tarba akayi mishi, Afnan ne ta zo ta gaishe shi, mamakin girman ta yayi don yanzu tana sheka na Sha uku13 kenan sosai tayi girman don tana da d’an kiba zaka ce ma ta wuce wannan shekaru, Azuciyar shi yace ba abun mamaki ba ne gani nima yanzu na shiga ashirin da shida26.

Sosai su ka zauna su ka sha fira da Afnan don yarinyar akwai surutu nan da nan sabo ya shiga tsakanin su yayin da har nombar wayar shi ya bata, bata da waya amma wayar momi kamar nata ne don d’auka take yi tayi ta game abun ta, be bar gidan ba se da akayi la’asar, su kayi sallama ya tafi gida, bayan magrib se ga kira ya shigo wayan Abubakar da ba’kon nomba ya na d’agawa ko yaji muryar Afnan gaishe shi ta yi su ka sha fira sannan tace mai “yaya don Allah gobe ka zo ka kai ni gidan anty maimuna”, “to” yace sannan su kayi sallama.

Washe gari kuwa Abubakar ya shirya, ya nufi gidan su Afnan d’in momi ya tarar a falo ya gaishe ta sannan tace “wato Afnan seda ta kira ka ko, tace min zata gidan anty maimunat nace ta bari dad ta ya dawo se ya kaita don yayi tafiya india, shine tace to zata kira ka ka kaita da fatan bata takura ka ba ko”, murmushi Abubakar yayi sannan yace “a’a momi nima nazo hutu ne to ba abunda ma nakeyi”, Afnan ne ta fito tayi wa momi sallama sannan su ka nufi gidan maimuna, har cikin gate d’in gidan su ka shiga yayi perking sannan su ka fito baze iya tuna yaushe ne yazo gidan nan ba don ya ta’ba zuwa sau d’aya, Shiga falon su kayi tare da sallama maimuna da ke zaune ta amsa musu da gudu Afnan ta je ta fad’a kan maimuna ta na fad’in “imiss u my anty na”, dariya maimuna ta yi tace “ke baki san kin girma bane ko so kike ki karya ni”, “a’a baza ayi haka ba,ina su anty ikram da ya mustapha?” su na ciki da gudu ta shige ciki yayin da ma ta manta da Abubakar tana son zuwa gidan maimuna ko don su sha wasa da yara don yanzu yaran maimuna shida mustapha shine babba se Ikram, khadija, Ummar, Madansir, se autar ta Aisha, tana zuwa kuwa duk suna d’akin su na fira ita ma ta shiga su ka cigaba da yi.

Maimuna ce ta kawo wa Abubakar Abinci ga kuma drink da snak, kad’an ya ci ya ce ze tafi anjima ze zo ya mayar da Afnan gida.Haka akayi da yamma yazo ya mayar da ita gida sannan ya mata sallama don zuwa jibi ze koma England kawai se ta ji bataji dad’in hakan ba.

Abubakar ya koma makaranta domin saura wata shida ma su gama karatun su gaba d’aya.

*SOKOTO*

Wata tara dai-dai Bilkisu ta haihu inda ta haifi kyakykyawan yaron ta, ya ci suna Abbas har lokacin Buhari be zo ba duk da Baba Lami ta kira shi ta fad’a mai, se cewa ya yi aiki ne ya yi mai yawa.

Bayan shekara biyu Abubakar ya gama karatun shi yayin da Su ka d’auke shi aiki acan Don likita ya karanta yana cikin jerin manyan likito ci kasar yayin da yakw d’aukan Albashin millon 30 duk wata, ban allowes da ake ba shi sosai ya zama mashahurin mai kud’i.

Buhari yanzu shekarar shi Biyu ba ya gida kuma be je Sokoto ba, don ya na jin dad’in garin sosai gashi ya samu wata yarinya da suke soyayya da ita sosai Jamila, kuma auren ta yake son yi, don ba haka su ka bar shi ba domin tun da jamila ta hanga ta ganshi kuma tasan Baban shi mai kud’i ne ta kwallafa rai da taimakon uwar ta ya fara son ta don da baya sonta duk da shige mai da takeyi kuma be bata labarin Bilkisu ba.

Se da ya cika shekara biyu baya gida sannan kuma ya yanke shawarar komawa gidan, ya shirya tsab ya nufi garin su, Ko da ya isa Al-amin ya tare shi ba yabo ba fallasa sannan ya tambaye shi ya karatun nashi yace mai ya gama karatun ma yanzu sana’a yake yi, Haka Baban na shi ya yarda da abun da ya fad’a mai. Da’kyar ya zauna yayi shekara d’aya agarin don kamar a ‘kaya yake, yayin da Baban shi yazo mai da maganar ya fito da mata yayi aure, yace ai akwai wacce yake so a can garin, Baban shi yace be yarda ba yarinya mai hankali da tarbiya ze aura mai, yace wacce yarinya kenan, ya ce mai Afnan yarinyar ‘yar uwar shi anan Buhari ya daga tsalle ya shafa wa idon shi to ka yace shi baze aure ta ba wallahi, Al-amin beyi mamaki ba don yasan za’a runa, kuma yace ya fad’a mai yarinyar da yake so asatin nan za’a je aneman mai nan ya basu adireshi, kafin su tafi ma ya kira jamila ya shaida mata iyayen shi za su zo, yayin da ta fad’a wa nata iyayen.

Ranar laraba akayi sammako wajen zuwa jigawa don nema wa Buhari auren Jamila sosai Al-amin yayi mamakin irin gidan da buhari yaje neman aure, gashi ba Hausawa ba ne hakan nan dai ya bar abun aran shi.

*SOKOTO*

Buhahi shekarar shi uku rabon da ya je sokoto se dai ya dinga tura musu kud’i ayau ne kuma ya shirya zuwa Sokoton, ya je ya same su lafiya ga yaron shi ya yi wayo sosai don yanzu yana da shekara Uku3 Bilkisu bata ma so zuwan shi ba don hankalin ta har tashi yake idan ta ganshi, yayi musu wata d’aya1 sannan ya koma Adamawa.

An saka ranar biki Wata3 don Kowa yace ashirye yake Buhari yasan dole su yi mai aure don bai tare ko biyar ba, har lokacin da aka saka biki yayi Al-amin da Abubakar su ka had’u su kayi wa Buhari auren yayin da yace a jigawa ze zauna don yana sana’a acan, Al-amin be yi mai musu ba, yabar shi ya tafi, tun da akayi bikin wata biyar kenan amma Buhari be zo gida ba daga shi har matar na shi.

*****

Bayan wata shida da auren Buhari, Maman shi safiyya ta matsa mai ya zo ya ga gida, ya kawo mata surikarta ta ganta amma ya’ki se ya ce mata yau, ya ce gobe se wasa ya ke mata da hankali, hakan ya sa ta ce ya yi mata kwatance ga ta nan zuwa yau, ta ga ma shirin ta tsaf! Na zuwa Jigawa Yayin da Al-amin ya ‘kyale shi, yasan kowa ya bar gida, gida ya bar shi, yana ta yiwa yaron na shi addu’a.

‘Karfe 2:00 Maman Buhari ta sauka a Jigawa, Buhari ne ya zo ya ‘karaso da ita har d’an madaidaicin gidan da Abubakar ya gina mai, ko da su ka shiga Jamila na zaune ta na jin suna sallama ta share su ta na kallo, Buhari ne yace “Haba my sweety ba ki ji muna sallama”, ji yo wa tayi ta yatsina fuska ta ce “kasan idan ina kallo ba wai ko wani irin magana na ke so ba, kawai ga guri ta zauna bara na ‘karasa”, baki safiyya ta saki ta na kallon ikon Allah, shi ko gogan naku cewa yayi “yi hakuri my sweety ban lura kina kallo ba ne, amma ki kawo wa Inna ruwa mana”, juyowa ta yi ta da ka mishi tsawa, “wai miye haka ne kai ruwan kawai baza ka d’ebo mata ba dole se ni, ko baka san inda yake ba ne”, juyawa yayi ya nufi kicin ya d’auko mata goran faro da lemo ya zo ya ajiye mata, inna safiyya da har yanzu mamaki ta ke yi tace “bana sha, ka wuce ka mayar da shi”,

“Inna kiyi hakuri Don Allah”

yace sannan ya fita, Inna da taga ba sarki se Allah ai tuni ta d’auki ruwan ta fara sha don kishi ta ke ji sosai ga yunwa da ta ke ji tana kallo Jamila ta tashi ta shige d’akin ta barta awajen, ga shi Buhari be dawo ba ga yunwa da ta ke ji.

Buhari be dawo gidan ba se wajen 3:30 lokacin Inna har ta fara baccin wahala, ya na shigowa ta tashi, “sannu inna yace mata”, hararan shi ta yi tace “sannu mijin tace, se ka samo min abinci idan ba kashe ni ku ka shirya yi ba kai da matar ta ka mai zubin aljanu”, “Inna bata kawo miki abincin ba?”, “idan ta kawo zan tambayeka ne?”,

‘Dakin Jamila ya nufa Ya sameta ta na sharar baccin ta fitowa yayi yace “inna gashi bacci ta ke yi”, tsabar takaici inna ta rasa ma mai zata ce se kawai ta bishi da kallo, fita yayi yace “Inna bara na samo miki abincin”.

Gidan Abokin shi saleh ya nufa don shima yayi aure yau wata uku, Suna yi sosai da amarya me suna salamatu se de ita kawai Allah ya sa kaddarar ta ne auren Saleh amma halin su ya sha bam-bam don mace ne mai hankali, nutsuwa, kawaici.

Koda ya shiga gida. saleh ma bayanan da yake gidan nasu ba nisa, bayan sun gaisa yace “amaryar mu kinyi mana girki kuwa?”, murmushi ta yi tace “Ehh mana”, yace “wlh momi na ne ta zo daga garin mu gashi ‘yar ganin daman matar tawa bata dafa komi ba”, “to bara na zubo mata, kace ina gaisheta kafin na le’ko mu gaisa”,

“to”

abinci mai rai da lafiya ta zubo mai akula ta bashi.

Koda ya isa gida Inna ta na inda ya barta don ba’kin ciki ta kasa tashi ma, sallam yayi sannan ya ajiye mata abinci yace “gashi inna” bud’ewa ta yi ta fara ci ya shiga kicin ya kawo mata ruwa da lemo, duk yawan abincin Inna se da ta kusa cinyewa don kad’an ta bari.

Bayan ta gama ne Buhari ya kaita wani d’aki yace anan zata sauka se lokacin Inna ta samu sukuni yin sallah ta kwanta don huce gajiya.

Washe gari koda inna ta tashi bata ga jimila agidan bama Buhari ne yake fad’a mata ai ta tafi garin su biki se tayi sati d’aya ma zata dawo, mamaki ya hana Inna magana tace “lalle wannan akwai shaid’aniyar yarinya ko da baza ta fasa tafiyar don zuwana ba ai ta zo tayimin sallama ko?”, kallon shi tayi tace “yanzu ko gaisawa bamuyi ba ta tafi”, wayan shi ya d’auko ya kira Jamila d’agawa ta yi ta ce “yĆ  akayi kuma?”, yace “haba sweety ba ku gaisa da momina ba kika tafi”, “to ai naga ba gaisuwa ta zo yi ba, gida tazo gani nabar mata gidan ma ita kad’ai ta ‘kare mai kallo, amma ka sani idan nadawo naga wani abu ba dai-dai ba kan ka ze dawo”, “sorry sweety amma kinsan ta zo ganin gida ne da matar gidan ko”, “to bata ganni bane!?, Idan bata ganni da kyau ba ka nuna mata hoto na se ta kalla ko”, “amma swee……!” dif! Ta kashe wayar yayin da shi bega laifin ta ba Inna ce tace “na zo naga gida bara to nazo na koma”, “haba inna kwana d’aya fa kika yi” “Ehh yau d’in nan zan koma Yanzu ma” jakar kayan ta ta d’auka ta nufo kofar gida shima biyo ta yayi ya rakata har tasha ta hau mota se Adamawa ko sisi be bata ba ita da tazo don ta samu wani abun daga wajen d’an nata da kuma surikar ta.

‘Karfe 4:00 Inna ta isa gida Maman Abubakar ta na part d’in ta tana aiki ta jiyo sallamar safiyya da sauri ta fito tana mata sannu da zuwa ba yabo ba fallasa safiyya ta amsa domin bata so a san komai da ya faru, khadija tace “ya amarya?”, “tana lafiya, tace agaishe ku”, “to muna amsawa, kin ga da ace Dad Abubakar ya bar Ni da tu Ni tare muka je” “Ehh da” Inna tace tare da nufan Part d’in ta ta d’ora girki, don Al-amin ya musu gida had’ad’d’e inda yayi part uku a ciki gidan ya had’u sosai kuma agarin na su yayi shi don yanzu Al-amin kud’i sun zauna mai sosai ga Abubakar da kullum shima cikin taimakon Baban nashi yake, Part d’in su komai na more rayuwa akwai aciki.

Al-amin koda ya dawo be yi mamakin ganin Safiyya har ta dawo yau ba don yasan gidan baze zaunu mata ba, da da khadija za su je ya hanata don yasan za’a rina.

Bayan Sati 1 da dawowar Safiyya Jigawa, Yau kuma ake shirye-shiryen taron Babban ba’ko wato Abubakar khadija farin ciki sosai take da dawowar yaron nata guda girki had’ad’d’e ta yi masa da misalin ‘karfe 12:00 Abubakar ya iso Jigawa abun ka da tafiyar jirgi sosai ake murnar dawowar Abubakar inda ya sauka a d’akin Mahaifiyar shi Idan kaga Abubakar baza ka taba cewa khadija ta haife shi ba don inda yayi tsayi sosai gashi yana da jiki sosai kuma bashi da ‘kiba ko kad’an ga shi fari ne sosai kamar balarabe gashi ya tara gashin shi d’an dai-dai wanda yaji gyara sosai.

Bayan kwana2 da dawowar Abubakar Al-amin ya same shi da maganar yayi mai mata Abubakar be yi musu ba tun kafin ma yaji matar, tambaya yayi yace “amma dad a ina take?”, murmushi yayi sannan yace “Afnan ce yarinyar ‘yar uwata da ita naso Buhari ya aura don ina tunanin ze shiryu amma kuma se ya’ki nima kuma se na sake tunani don ko na aura mai ita ba lallai bane ya shiryu kila ma ya cutar da ita, shine yanzu na ce na zaba maka don nasan baza ka watsa min ‘kasa a ido ba, don har nayi wa mahaifin ta magana ma ya amince ya baka ita yanzu rana za’a sa kawai”, “to dad, Allah yasa hakan ya zama Alkhairi”, “Ameen” Dad nashi yace sannan ya mi’ke ya nufi part d’in da ya kasance kamar nashi don idan yazo anan yake sauka, wayar shi ya lalubo ya kira abokin shi ummar, kira d’aya ya d’auka yace “aboki na yane naga kiran ka awannan lokaci ya hutu?”, dariya Abubakar yayi wanda har seda ummar yaji yace “kai dai bari wallahi ina cikin farin ciki ne”, “to fad’amin mana”, “hm ina yarinyar da nake baka labari ina sonta”, “wanda kace min maman ta ‘kanwar baban ku ne ta rasu”, “Ehh mana, to Dad har yaje nenan min auren ta kuma an bashi yanzu ku shirya shan biki”, dariya ummar yayi yace “saura mu kenan” “Ehh ayi zuciya afito da mata dai”, dariya su kayi dukan su sannan su kayi sallama, Abubakar se tunanin Afnan yake don ya dad’e yana son yarinyar.

Ahmad kuwa tun ranar da Al-amin yayi mai maganar Had’in auren yaran na su be yi musu ba don yasan waye Abubakar dama ya dawo hutu ne ya fad’awa momin shi ita ma ta yi farin ciki sosai don yaron yana da hankali sosai yace ta fad’awa Afnan.

Tun sannan ma ya koma don yanzu baya wani zaman Nigeria don damuwa taruwan mai yake idan yana nan shiyasa aikin shi ma ya koma can yayin da momi har yanzu maganar aure take yimai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wata Rayuwa Ce 7Wata Rayuwa Ce 9 >>

1 thought on “Wata Rayuwa Ce 8”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
Ɨ