Skip to content
Part 9 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Kamar kullum momi ne da Afnan afalo Afnan na kwance akan cinyar momi ta na mata tsifa momi ne tace “wai ke bakisan kin girma bane se akwance za’a miki tsifa so kike ki karya ni”, “kai momi, a haka ne har na girma nidai yarinyace”, “Afnan wai kwana biyu kun rabu da waya da Abubakar ne?”, “Ehh bana samun Nombar shi”, “Afnan miye tsakanin ku da Abubakar”, “Afnan tashi ta yi ta zauna tace “kuji tsohuwan nan da tambaya miye kuwa idan ba mutunci ba”, dariya momi tayi tace “nice tsohuwa ko?, kinsan Dad ku ze had’a ki aure da Abubakar d’in”, Dariya Afnan ta yi tace “a’a ni yayana ne kawai”, Momi ne tace “Afnan mubar maganar wasa dad ki ze had’a ki aure dashi don har ma an bashi rana kawai za’a sa, Kina son shi ko kuwa nace a fasa”, murmushi Afnan tayi kawai momi ne ta ‘kara tambayan ta rufe fuska ta yi ta tashi da gudu ta nufi d’akin ta tana dariya, murmushi momi tayi itama.

Yau kwanan Abubakar Hud’u da dawowa yau ne kuma ya shirya zuwa gidan su Afnan ya gama shirin shi tsaf ya nufi gidan su koda ya isa horn yayi mai gadi yabu bud’e mai ya shiga da motar ciki, kai tsaye falon gidan ya shiga momi ne zaune tana kallo gaishe ta yayi ta amsa da murmushi tace “su tsoho an zo zance ne?”, kunya sosai ya rufe Abubakar sunkuyar da kai yayi yana murmushi yace “a’a nazo gaishe da kaka na ne, ke kad’ai nazo gaishar wa” murmushi momi tayi sannan ta tashi tana fad’in “bara na kira maka ita”, “to” yace ita kuma ta shige d’akin Afnan domin kiran ta tana zaune tana game awayar ta don yanzu dad ta ya siya mata waya babba iphone13 saboda karatu, Momi ne tace “to kije kin yi ba’ko”, d’agowa tayi tace “waye ne granny?”, “Abubakar” kawai tace mata murmushi tayi sannan ta shirya kawai yau se taji tana jin kunyar sa ta dad’e da shiryawa amma ta kasa fita momi ne ta dawo d’akin tace “wai me kike yi ne kin wani zunbula hijabi kamar me shirin yin sallah”, “to garanny ki raka ni na kasa fita”, dariya momi ta yi tace “to ki zauna kar ki fita ni na wuce d’aki na ma”.

Da’kyar Afnan ta iya fitowa falon ta nufo d’auke da sallama tun da ya d’ago ya kalle ta yake dariya don wani Hijabi da ta zumbula daga gani ma na Granny ce yace a ran shi, ‘karasowa ta yi ta zauna a d’ayan kujerar ta gaishe shi ya amsa sannan su ka cigaba da hirar su ko ince yayi ta suruntun shi don Afnan sarkin surutu yau shiru tayi Bayan sun gama firar ne Abubakar ya nufi gida.

Bayan Wata Biyu

Soyayya mai ‘karfi ne ya shiga tsakanin Afnan da Abubakar har an saka rana wata 3 duk da ba ya zaman garin amma kullum ne sai sun yi waya.

Bayan wata biyu, shiri sosai su ke na bikin duka familyn guda biyu, Abubakar ya fara had’ad’d’en ginin shi a cikin garin Adamawa gida ne sosai ake yi mai na gani na fad’a.

Abangaren Afnan ma yau su ke yin graduation na Ss3, Baban ta yaje mata da ya ke ya shigo garin, sai maimuna itama taje Abubakar ba ya garin shi waya kawai su ka yi yayi mata fatan Alheri.

Yau bikin su Abubakar saura sati2 ayau ne kuma Abubakar ya diro Nigeria tare da abokin shi ummar don Abubakar ne ya matsa mai da yace se saura sati 1 ze zo, Apart d’in Da yake sauka anan ya sauka ya sha gyara sosai part d’in domin dad shi ma ya fad’a mai anan Afnan za ta zauna kafin Ya ‘karasa ginin shi, aranar da yamma bayan sun ci abinci sun huta su ka nufi gidan su Afnan.

Girki sosai Afnan ta yi musu don tasan da zuwan su sun ci sun sha sannan su ka yi hirar su sosai har da Ummar don har sun saba ma da Afnan don su na yawan gaisawa da ita ko awaya ne, nan Abubakar ke tambayan ta ko akwai abun da take bu’kata, tace mai ba komai murmushi yayi sannan ya sa hannu a aljihun shi ya ciro kud’i dubu d’ari uku ya aje mata yace “gashi idan kina bu’katar wani ki min magana”, “Nagode!” kawai tace sannan su ka mik’e su ka nufi gida.

Yau biki saura kwana biyar amarya Afnan Sosai ta ke shan gyara awajen grannyn ta. Abangaren Abubakar yau ne aka had’o kayan lefe don momin shi ya bawa da wasu ‘yan uwan ta su ka had’o akwati goma ne kuma ko wanne cike yake da kaya masu masifar tsada, yau ne kuma za’a kai lefen gidan su Afnan ‘yan uwan momin shi ne su ka kai lefe da dubu d’ari biyar akai kowa ya ga lefe sai san barka don kaya sun had’u sosai.

Ahmad ne zaune a gaban momin shi yana tambayan ta kamar nawa ne ze isa a had’o ma Afnan kayan kicin da na funiture, momi tace “ko nawa ka bayar nima zan had’a da nawa ga kuma na ‘yan uwa kasan ko ma baka bayar ba ba wata matsala”, Atm card d’in shi ya mi’ka mata yace “ga shi momi ki ciri duk abun da ze isa kawai”, “to” momi tace sannan ta dube shi tace “Ahmad ka ga gashi har zaka aurar da ‘ya amma kai ka’ki fitar da mata har yanzu ka yi aure, yau shekara sha 17 kenan da rasuwar khadija amma ka kasa manta wa da ita ka yi aure Ahmad me kake so ne?” d’agowa yayi yace “momi ni idan na ce ma zan yi aure bansan wacce zan aura ba, momi to ki nemo min matar kawai”, dad’i sosai momi ta ji tace “ko kai fa Insha Allah zan nemo maka daga bikin Afnan se naka” “to momi” yace sannan ya mi’ke ya fita momi ne ta kira maimuna ta mata bayanin kayan da za’a siyo wa Afnan sannan ta bata kud’i.

Maimuna ce da wata ‘kawar ta Halima su ka siyo wa Afnan kayan kicin na gani na fad’a masu kyau ga su da yawa don idan ka gani za ka ce wani babban shagon siyar da kayan kicin za’a bud’e, kayan furniture kuma Al-amin sun yi magana da Ahmad yace kar a siya domin zai sa ayi mata na shi gudunmawar kenan ya so ma ya yi fiye da haka don shi ne amatsayin dangin uwarta amma da ‘kyar Ahmad ya yarda yayi furniture d’in, Ahmad ya samu yarinyar na shi ya tambayeta ko akwai wani abu da take bu’kata na bikin tace mai ba komai kawai walima za suyi da ‘kawayen ta na Islamiyya se kuma dinner da ummar ya shirya musu, wasu kud’in shima ya ‘kara mata ga na Abubakar da ya bata ma suna nan momi ta samu ta bata kud’in, momi tace bazata ‘karba ba ta saka su a account d’in ta a account d’in ta zuba su ga kuma wanda ƙawayen ta su ke bata gudunmawar biki.

A yau ne aka d’aura auren Sadiya Ahmad, da angon ta Abubakar Al-amin akan sadaki dubu d’ari biyar don Ahmad yace kar ya bada wani kud’i mai yawa, Buhari ma ya zo shi da matar shi Jamila sun zo biki tun ana gobe, Jamila ta sauka d’akin momin Abubakar, saboda tsabar sanin bariki irin nata se bata nu na musu komai ba har ‘kasa ta ke du’kawa ta gaisar da su, musammam ma Inna safiyya.

Bayan d’aurin aure ne misalin ‘karfe uku aka fara walima a gidan su Afnan yayin da kowa ya halar ta har Jamila ba’a barya abaya ba sosai ta ke manakin irin dukiyar da Dangin Buhari su ke da shi shine su ka musu d’an wannan gidan, bata gama mamaki ba se da su ka isa gidan Su Afnan ta ga irin kud’in da ake narkawa awajen walimar nan abinci iri-iri se wanda ka zaba, anci an sha amarya ta yi kyau sosai kamar ma ba ita ba, sannan an raba kyautuka sosai awajen Abubakar se jan d’an uwan shi yake yi ajiki kamar abokin shi, don tun da ya yazo komai tare su ke yi.

Bayan an tashi walima ne kuma bayan magrib aka tafi dinner da ummar ya shirya musu, sosai shima ya ‘kayatar sosai, da ya ke ba yau za’a kawo amarya ba ad’akin amarya su Jamila su ka kwanta bayan an dawo dinner don sauran d’akunan cike ya ke da mutane Jamila kasa bacci ta yi se kallon irin had’uwar da d’akin yayi take yi su hud’u ne su ka zauna ad’akin suma ba’ki ne sauran ita ma kawai sun karrama ta ne don, d’akin ya had’u ba ‘karya don ma falon kawai aka bud’e musu banda kicin da sauran d’akunan, kujeru ne lafiyayyu kawun ta Al-amin ya zuba mata.

Washe gari wanda su ka kwana sun ci mai kyau sun sha yayin da wasu kuma su ka nufi gidan su wasu kuma sunce se sunga amarya, da yammaci Abubakar ya tura da motocin d’aukan amarya guda goma10.

‘Karfe bakwai amarya Afnan ta iso d’akin ta cikin lubbu’bi don har yanzu kuka ta ke yi, sosai mutane su ke ta shiga ganin amaryar Abubakar, amarya ta yi kyau sosai se san barka son kowa ‘kin wanda ya rasa.

Amarya sun kwana da ‘kawayen ta yayin da Jamila yau a d’akin momin Abubakar ta kwana don mutanen da yawa sun tafi, koda gari ya waye Abubakar ne zaune da d’an uwan sa suna hira, Buhari ne yace “yaya ance ka fara gini ga shi har zan koma baka nuna min bin ba” murmushi Abubakar ya yi yace “kayi hakuri ‘kanina na manta ne kasan abubuwan sunyi yawa ginin ma har an gama kasan ba na zama ne shiyasa Dad yace kawai na barta agida zata fi jin dad’i, amma ka tashi ka shirya se mu je na kai ka”, mi’kewa yayi ya nufi gidan a lokacin kuma ummar ya ‘karaso don yaje raka sauran abokan su da su ka zo musu biki, ‘yan uwan Ummar ma sun zo ma Abubakar biki tun daga kaduna, jiya su ka koma.

Ko minti 5 ba ayi ba Buhari ya fito tare da Jamila don tun da taji inda za shi tace itama se ta bishi.

Su hud’u su ka tafi zuwa gidan ko da ganin anguwan ma kasan na manyan mutane ne sosai ‘kofar wani gida su ka tsaya horn ummar ya yi mai gadi ne ya fito ya bud’e suka shiga da motar cikin gida, fitowa su ka yi Jamila suman tsaye ta yi ganin gidan kamar ma sun bar Nigeria ne tsabar had’uwar shi ga girma sosai kamar wani d’an ‘karamin anguwa tun daga waje kenan, mukulli ya ciro ya bud’e falon shima sosai ya had’u har sama seda su ka hau gida ya had’u sosai duk da ba komai aciki se Kujeru ne kawai masu masifar kyau, sosai su ka zazzaga gidan kafin su ka fito su ka nu fi gida.

Bayan sun dawo gida ne Buhari su ka fara shirin koma wa Jigawa, zuwa ‘karfe Uku su ka fito kud’i ma su yawa Abubakar ya ba shi yayi na mota tsabar mutuwar zuciya kuma ‘kar’ba ya yi, Ba abun da ya kawo mai na gudunmawar biki, amma Abubakar be ce komai ba amma be ji dad’i ba bawai don yana bu’kata ba amma ko ba komai Idan na ka ya baka ai zaka ji dad’i ko ba yawa ne ma.

Su Buhari sun kama hanyar Jigawa yayin da Abubakar da Ummar da su ka je yimai rakiya su ka nufo gida, su na tafiya su na hira, Umar ne yace “nima dai mu koma na had’a ka ya na Nayi gaba”, “ai wallahi ba ka isa ba se gobe” dariya Ummar ya yi yace “lallai ma me ye ya rage to, anjima nan d’akin amarya za ka shige ka kyaleni”, dariya Abubakar ya yi yace “to baza ka raka ni ba”, “ai akwai abokan ka na nan garin”, dariya Abubakar ya yi yace “hakan ma Nagode” “ai to kar ma ka gode mana”, dariya su ka yi dukan su, Umar yace “kai ma idan kazo biki na sati za kayi”, “Ehh mana me ze hana” “ai nasan hali ne shi yasa na ke maka tu ni”, “nima fa na kusa don da na ko ma ma zan ta da maganar”, “yayi kyau to, Bilkisun ce?”, “Ehh mana” “Allah ya sanya Alkhairi” “Ameen nagode sosai”, haka su ka cigaba da hirar su har su ka iso gida Ummar kayan shi ya had’a ya yi wa su momi sallama, ɗakin amarya ma ya je su ka yi Sallama sannan ya wuce garin su Kaduna, sosai Abubakar ya ke kewar abokin na shi don wani irin shakuwa ke tsakanin su tun daga yarin ta, duk da yana da wa su abokan amma Ummar ne aminin shi.

Jigawa

Ko da su Buhari su ka koma gida sosai Jamila ta dinga tsinewa Abubakar tana fad’in “yanzu masu kud’i ba su da imani ace d’an uwan ka na da wannan kud’i amma ji gidan da kake zaune aciki amma shi ji gidan da ya gina had’ad’d’e kamar ma ba’a Nijeria ba ga kud’in da aka kashe ko kai ya bawa ka ja Jari ai amma tsabar almubazzaran ci ne kawai hakan.”

Shi dai Buhari bece komai ba tunani yake a zuciyar shi lallai kuma gaskiya ta fad’a hakan yasa ya kira Abubakar ya ce mai jarin shi ya yi ‘kasa don Allah ya turo mai, Abubakar be yi musu ba ya turo mai kusan 2millon ranar da ya fad’a wa Jamila ta’be baki ta yi tace “ina lefi ma ya gina maka babbar super market ne kawai wannan to wani sana’a zaka yi da shi?”, Buhari be ce mata komai ba don ba ta san ‘karyar da yayi wa dad shi ba na ya fara sana’a ya turo mai kud’i, har da Abubakar d’in ma ga shi basu san be da komai ba.

Ya tura wa Bilkisu dubu d’ari biyar itama, ya kuma tura wa mai gidan da su ke haya na shi don kud’in su ya ‘kare, har yanzu gidan haya suke, yayin yafi shekara rabon shi da zuwa Sokoton.

‘Yan kawo amarya sun watse yayin aka bar amarya da angon ta.

Washe gari Bayan sun tashi momin Abubakar ne ta aika musu da abinci don Afnan bata fara girki ba bayan sun karya ne Afnan ta yi wanka ta shirya ta fito waje ta gaida momi ta shiga d’akin Inna ma ta gaishe ta, da rana ma Momi ta aiko musu da abinci.

Bayan wata d’aya da Auren Abubakar sosai momi ke jin dad’in zama da Afnan don ta na rage mata kewa gashi sun yi sabo sosai tun tana jin kunyar ta yanzu ma ta daina don momi tana janta a jiki sosai, ita kuwa Inna tun ta na share ta tsabar ba’kin ciki yanzu ma ta na d’an sake mata ba lefi, yayin momin Ahmad ta zo gidan sau biyu kenan, maimuna ma ba’a barta a baya ba Ahmad ne dai tun da ya zo yaga d’aki be sake zuwa ba, amma su na waya sosai da shi.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yayin da yau Shekara d’aya1 da auren Afnan Abubakar ya koma wajen aikin shi, Anyi bikin Umar ma su na zaune lafiya da amaryar sa Bilkisu.

duk da Abubakar baya zama Hakan be sa Afnan rashin jin dad’i ba kullum tana cikin farin ciki sosai Al-amin yayi mata maganar komawa gidan su amma tace tafi son nan, haka aka barta su ka cigaba da zaman su Lafiya.

Abubakar bayan wannan gidan ma ya kuma yin wa su gidaje kusan guda uku kuma du ka sun had’u don guda biyun ma sun fi na farkon girma da had’uwa yayin da ya sayi wani gidan mai ma don sosai yanzu kud’i su ka zauna mai, awannan shekarar ne kuma su ka shirya zuwa aikin Hajji, Abubakar da Afnan se kuma Bilkisun sa Umar kasancewar Dad shi yaje sau biyu ma mom shi ma taje, har Inna shiyasa dad yace su je kawai don da da su yayi niyar zuwa.

Sun je sunyi aikin Hajji Sun dawo gida Lafiya.

Koda Buhari ya samu labarin zuwa Hajjin da ya yi ga kuma wasu gidaje da filaye da da gidan man da ya siya sosai hankalin shi ya ta shi ba shi da burin da ya wuce yayi kud’i tun yana yaro amma gashi se d’an uwan shi ne yayi shi yana nan, Hakan yasa su ka kwashi kayan da su ke bu’kata a gidan su kai gidan Saleh da taimakon shi su ka saka wa gidan wutan wai don ace sunyi gobara sosai gidan ya kama ya ‘kone sosai har ya fara ta’ba gidan ma’kotan su abu kamar wasa gidan ya kama sosai ga shi masu gidan basa nan yara kawai su ka bari a ciki su Uku wuta sosai yake ci ihun yaran kawai akaji acikin gidan masu ‘ko’karin kashe wutar ne wani ya kira matar gidan don mijin ta ya rasu ya barta da yara se gidan da su ke ta’kama da shi cikin sauri kuwa matar ta zo mukullin gida ta bada wani ya bud’e baza ta iya bud’ewa ba yanda hankalin ta ya ke tashe, a tsakar gida ya samu yaran guda biyu sun fito lolacin wutan ma ya fara kama tsakar gidan don ya cinye d’akin, ina d’ayan ‘kanin naku ya tambaye su, nu ni su kayi mai da d’akin da sauri ya kwaso so su ka fito maman na ganin su ta rungume yaran nata tana fad’in “ina shahid d’ina?”, Babban ne yace “momi yana ciki” kuka sosai ta sa ka mai tsuma rai ta na fad’in “shikenan Shahid ya ta fi ya barni, ba’ a samu nasarar kashe wutan ba seda ya cinye gidan du ka sannan masu kashe gobara su ka zo lokacin ma har ya fara kama gida na gaba an yi nasarar kashe wutan, su Jamila da tunda su ka had’a wannan masifar su ka shiga garin a zuwan wai basu nan ma wutar ta tashi, ba su san me akeyi ba yayin da yaron matar nan ‘karami ko gawar shi ba’a fitar ba ya ‘kone du ka sosai matar ke kuka don ta na matu’kar ‘kaunan yaron nata.

Se yamma su Jamila su ka dawo su na kukan munafur ci, mokota se ba su hakuri ake, ana se hakuri, ranar ma se gidan Saleh su kwana.

Washe gari tun da safe Buhari ya kira wayar Dad shi ya fad’a mai sunyi gobara hakan yasa cikin tashin hankali Dad na shi da Abubakar su ka nufo jigawa don ganin halin da su ke ciki ko da suka zo sun ga gidan ya ‘kone sosai sun tarar da su ma a gidan Saleh ne, hakan yasa hankalin su ‘kara tashi, su kace ma Buhari ya shirya shi da matar shi su koma Adamawa, buhari yace to amma su tafi za su zo haka su Abubakar su ka nufo Adamawa su ka barsu.

Bayan sati1 da faruwar abun su Buhari su ka shirya zuwa Adamawa gobe yayin makota se zuwa musu ake jaje kowa yazo kuma baze tafi hakanan ba se ya bada wani abu, kud’i su ka tara sosai a hakan, gidan kusa da su da ya ‘kone tun da Abubakar ya ji gidan marayu ne ya kashe kud’i sosai an gyara musu gidan su, tsaf har da wani kud’in kuna ya bawa matar.

Su Buhari sun sauka a Adamawa jiya, yau kuma da safiya, Abubakar ya samu Dad shi yace yana so ya bawa d’an uwan shi gida d’aya a cikin gidajen shi, to Abubakar ni me zance se dai nace Allah ya ‘kara zumunci cewar Dad su. Ameen dad, sannan ya samu, Buhari ya fad’a mai murna acikin shi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha, sun je sunga gida shida Jamila, sosai gidan ya had’u gashi katon gaske, bayan kwana3 su ka tare a gidan su don, Dad shi ya zuba mai kayan sosai a gidan kamar an saka su a aljanna haka su ka ji duk da Jamila bata so zaman su a Admawa ba amma hakanan ta hakura ganin daulan da su ka shiga, Saleh ma yazo ganin gidan sosai shima yaji dad’i, su na zaune suna hira a makeken falon shi da yaji maka-makan kujeru, Saleh ne yace abokina mafarkin ka na zama shahararren mai kud’i ya kusa cika fa kai kake ganin haka don in banda gidan nan wallahi banda kud’i se abun baza su gaza dubu d’ari biyar ba a account d’ina, to lallai yaushe zamu koma wajen mallam ne, ku ma fa ya kamata mu je don wallahi ina son samun kud’i, to ka shirya gobe muje, To daman ina son zuwa Sokoto ka ga na dad’e ban je ba, Ehh se mu je tare to,Allah ya kai mu.

Sokoto

Bilkisu ce ke zau ne a kan kujera gefen ta kuma, Baba Lami ce ke cin abinci, kallon ta ta yi tace, “Baba inajin dad’in zama da ke don Allah kiyi min al’kawarin ba za ki ta’ba bari na ba, don ke kad’ai na ke da ita yanzu” “ki dai na fad’in haka, Ga mijin ki nan”, “Baba wannan kawai dai muna zaune da shi ne amma da shi har gara ba bu”, “a’a Bilkisu ki dai na fad’in haka ke dai ki cigaba da hakuri Allah be manta da ke ba”, “to Baba nagode”, wani yaro ne ya fito da ga d’ayan d’akin yana murje ido da alama bacci ya tashi, Bilkisu ne ta kalleshi ta yi murmushi tare da cewa “yaron mama an ta shi ne?”, “Ehh momi yunwa na ke ji ma”, “to zo muci abincin”, cewar Baba Lami, ma’ke kafad’a ya yi yace “ni kad’ai zan ci”, “to bara na zu bo maka” cewar Baba Lami ta na mi’kewa ta nufi kicin d’in abincin ta zu bo ta kawo mai, ba shi ta yi ta na fad’in Abbas kenan sarkin rigima ba ka san ka girma ba ne shekar hud’u ba wasa ba, banza yayi kamar be jita ba se cin abincin shi yake, yi, knock su ka jiyo daga kofar gidan, Baba Lami ne taje ta Bud’e, mamaki ne sosai ya kamata ganin Buhari da Saleh, ga kuma mota da alama a ita su ka zo, “sannu da zuwa” tace tana nufar cikin gidan “yawwa Baba ya ‘ko’kari”, “Mun gode Allah” tace lokacin Baba Lami har ta shige falon, ta na fad’in Abbas ga Dad ka Ajiye abincin yayi da sauri ya na fad’in oyoyo ya yi hanyar fita, Bilkisu ne ta kàlli Baba lami tace “da gaske ki ke Baba?”, “Ehh mana”, Abbas da gudu ya ‘karasa ya rungume Dad shi tare da cewa “Dad wai ina ka ke zuwa ne, Dad ba na ganin ka”, shiru Buhari ya yi don be san mai ze ce mai ba d’aukan shi ya yi su ka nufi falon shi da Saleh, “Sannu da zuwa” Bilkisu tace mai “yawwa mun same ku lafiya?”, “Lafiya lau”, “to sannu my wife” cewar Buhari yana nufar d’akin Bilkisu ta shi ta yi ta nufi d’akin yayin da ta bar Baba Lami ta shiga kicin don had’a mu su ainci don ba su san da zuwan na su ba.

A d’aki ta same shi ya zauna shi da Abbas se surutu ya ke yi mai, Abbas je ka ta ya Baba Lami aiki cewar Bilkisu ta samu waje ta zauna. Da gudu Abbas ya fita, Kallon Buhari ta yi ta ce “ya hanya?”, “Alhamdllh ya na sa me ku?”, “lafiya lau” cewar Bilkisu ta ‘kara da cewa “Baban Abbas lokaci ya yi da ya kamata ka da wo gida ka zauna kullum Abbas se ya tambaye ni Dad shi tun ina ba shi amsa yanzu ban san me zan ce mai ba”, “Bilkisu kenan baza ki ga ne ba, nace miki aiki na ke da shi acan to wani irin aiki ne ba baza ka dawo da shi nan ba”, “ke malama ya isa haka tuhuma na ki ke yi ko zargi na, a can na ga damar yin aikin ki na da matsala da hakan ne, indai wannan za ki tambaye ni to kar ki ‘kara tambaya na kin ji ko” ya na kai nan ma ya bar d’akin, mamaki ne sosai ya ka ma Bilkisu na wannan lamari kamar ma ra gaskiya ha ka dai ta bar abun aranta ta fito don ta ya Baba aiki.

Bayan kwana biyu da zuwan Buhari har yanzu fushi ya ke da Bilkisu, ta same shi ta ba shi hakuri sannan su ka shirya, yace mata kuma gobe ze tafi amma ba ze dad’e ba ze dawo, ba abun da tace mai se dai Allah ya tsare hanya.

Washe gari kuwa su ka kama hanya su ka nufi Zamfara wajen malamin su, jeji ne sosai su ka shiga kamar yadda su ka saba.

Shiga su ka yi tare da gaishe shi, amsawa ya yi cikin muryar shi mai razanarwa, sannàn yace “an fad’a min zuwan ku, da kuma abun da ke tafe da ku amma ina so na ji daga bakin ku”, Sakeh ne ya gyara zama sannan yace “boka wannan aboki na ne da mu ka ta ɓa zuwa nan da shi, kuma ba shi da burin da ya wuce ya ga ya yi kud’i, amma hakan be samu ba”, cikin razananniyar murya yace “yanzu me ku ke so ayi ne”, “Duk abun da ka ga ya da ce boka” cewar Buhari “zan ba ku za’bi guda uku, na d’aya1 ko a kwace dukiyar yayan ka a mallaka ma ka, shi kuma a talauta shi, ko kuma a kashe shi gaba d’aya a ba ka dukiyar, na uku kuma ko a mai asirin da ko nawa ka tambaye shi ze ba ka kuma ba ze tambaye ka me za ka yi da su ba”, “Boka na ukun dai za’ayi, don sauran inajin tsoro” “to shikenan kafin ku isa Adamawa za’ayi mai da ka isa ma ka gwada tambayar shi ka gani” “to an gode sosai”, “sannan kuma akwai wa ni, kasan ina da mata a Sokoto to yanzu kuma na ‘kara wata, to ta na da ba’kin kishi, d’ayan kuma ta na zargi na, to ina so d’ayan ‘kar ta ta’ba sanin da d’aya”, “wannan mai sau’ki ne baza su ta’ba sani ba, ko daga gare ka, duk ranar da d’aya tasan da d’aya za ka fuskanci mummunar tashin hankali”, “ba za’a ta’ba ji a baki na ba”, “shine zaman ka lafiya.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wata Rayuwa Ce 8Wata Rayuwa Ce 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×