Skip to content

Rubutun batsa koma-baya ne ga dukkan marubuci mai kima – Haiman Raees

A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya Hikaya ke yi da marubuta na wannan zamani, a yau mun yi yi tattaki mun zaƙulo muku da fitacce kuma shahararren marubucin wake, da yake fassara wakokin Indiyawa gami da dan taba rubutun zube kansa, wato dai sha kundum a kowanne fanni, Jamilu Abdurrahman (Haiman Raees). Marubucin kuma mawakin ya bayyana irin gwagwarmayar da ya sha a harkar, dama sauran abubuwa da suka danganci rayuwarsa. Ku kasance damu domin jin ko wane ne Haiman Raees.

Tambaya: Malam Jamilu da farko dai za mu so jin cikakken sunanka da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarka in ba za ka damu ba.

Amsa: To, Assalamu Alaikum warahamatullah wa barakatuhu. Cikakken sunana shi ne Jamilu Abdulrahman, amma an fi sani na da Haiman Raees. An haife ni a ranar uku ga watan Maris shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in da uku (3rd March, 1993) a garin Gadan Gayan, wanda ke gundumar Fanshanu, ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a Najeriya. Na fara karatuna na boko da kuma na addini duk a garin Gadan Gayan ne kafin daga baya na dawo cikin garin Kaduna inda na ci gaba, kuma har yanzu dai ina ci gaba da karatun ne. Ina da aure kuma yanzu haka ina zaune ne a cikin garin Kaduna. Baya ga haka, ni marubuci ne, manazarci kuma mai sharhin litattafai da fina-finai tare kuma da fassarar waƙoƙin fina-finan Indiya.

Tambaya: A wacce shekara ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinka har ka fara rubutun?

Amsa: Gaskiya na daɗe da fara rubutu, domin tun ina aji huɗu a firamare na fara rubuta labarai, kuma har yanzu duk suna nan. Sai dai ban fara fitar da su a matsayin littafi ba sai a tsakanin 2022-23. Gaskiya tun ina yaro ni mutum ne mai son yawan karance-karance, domin tun ina aji uku a firamare na fara iya karatu kuma daga nan na dasa har yanzu. Shekera guda daga nan na fahimci cewa ina da labaran da zan iya bayarwa. To tun daga nan ne na fara rubuta labarai ina ajiyewa. In lokaci ya ja sai in kwafe su a cikin sabon littafi, ina kuma rubuta wasu sababbi. Baya ga rubutun zube, ina rubuta waƙoƙi, wasan kwaikwayo da kuma muƙaloli. Sannan ina rubutu da harshen Hausa da kuma Turanci.

Hira da Haiman Raees 1
Marubuci Haiman Raees

Tambaya: Wanne irin ƙalubale ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ka bi har ka tsallake?

Amsa: Babban ƙalubalen da na fuskanta a baya dai shi ne rashin damar fara fitar da labaraina duniya ta san da zaman su. Hanyar da na bi wajen magance matsalar kuwa ita ce haƙuri tare da ci gaba da rubutun ba tare da sagewar gwiwa ba. A yanzu kuma, babban ƙalubalena shi ne ƙarancin lokacin yin rubutu, domin ina da labarai masu tarin yawa da nake so in bayar amma babu isasshen lokacin bayar da su. Sai kawai in yi haƙuri da ɗan abin da ya samu kuma in yi abin da zan iya yi da shi.

Tambaya: Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.

Amsa: Gaskiya na rubuta littattafai da dama, za su kai guda goma sha ɗaya. Ga su kamar haka:

  1. Fasaha Haimaniyya
  2. Fatalwar Sinu
  3. Birnin Sahara
  4. Voice Of Love
  5. Ba’indiya
  6. Malam Jatau
  7. Baƙar Ƙaddara
  8. Warwara
  9. Falsafa
  10. Tambaya
  11. Mysterious Pen

Amma Falsafa da kuma Mysterious Pen ba ni kaɗai na rubuta ba, haɗaka ce muka yi ni da Mujahid Nuhu Yusuf (Matashi)

Tambaya: Wanne littafi ka fi so a duk cikin littattafan da ka rubuta, kuma me ya sa?

Amsa: Gaskiya na fi son littafin Birnin Sahara, saboda shi ne tubalin ginin duniyar labaraina na Duniyar Labaran Haiman (DLH).

Tambaya: Wanne littafi ne da ka taɓa karantawa kuma ya fi burge ka?

Amsa: Gaskiya na karanta littattafai da dama waɗanda suka burge ni matuƙa. A litattafan gida Nijeriya dai akwai Magana Jari Ce, Uwar Gulma, Fasaha Aƙiliya, Kundin Tsatsuba, Things Fall Apart, A Man Of The People da kuma From Fatika With Love. A litattafan ƙasashen waje kuma akwai Wizard’s First Rule, Origin, Twilight, A Game Of Thrones da kuma Harry Potter.

Tambaya: Idan za ka yi rubutu, shin ka kan tsara komai da komai ne kafin ka fara ko kuwa kai tsaye ka ke farawa?

Amsa: Gaskiya sau tari sai na tsara tukunna nake farawa. Amma akan samu lokacin da kawai farawa nake yi in ya so daga baya sai in gyara abubuwan da suka kamata.

Tambaya: Ya kake yi idan wani tunani sabo ya zo maka game da wani rubutu na daban alhalin kana tsakiyar rubuta wani. Ka kan saki wancan ne ka yi wannan sabon ko kuma sai ka gama da wanda ka fara?

Amsa: Rubutawa nake yi a gefe saboda gudun mantuwa, in na samu nutsuwa sai in dawo in duba. To amma da yake yawancin labaraina suna da alaƙa da juna, irin wannan sabon tunani na iya zama wani littafin daban ko kuma wani labarin da zai fito ta wata siga ta daban.

Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ka wahala daga cikin dukkan litattafan da ka taɓa rubutawa?

Amsa: Birnin Sahara, saboda shi ne tubalin ginin Duniyar Labaran Haiman (DLH). Baya ga haka kuma, littafi ne da ke ɗauke da saƙonni masu yawa da ke buƙatar bincike mai zurfi.

Tambaya: Wani lokaci kan marubuci kan cushe har ya kasa rubuta komai. Shin ka taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ka bi wurin magance hakan?

Amsa: Eh, gaskiya ina tsintar kaina a irin wannan yanayi a lokuta da dama. Kuma sau tari da zarar irin hakan ta faru bacci nake zuwa in yi. Ko kuma in kama wani abu can daban har sai na samu nutsuwa tukunna sai in ci gaba.

Hira da Haiman Raees 2
Marubuci Haiman Raees

Tambaya: Yanzu lokaci ya canza, haka zalika al’amura da dama na mutane su ma sun canza wanda na wasu yake zuwa a karkace, har ta kai ga yanzu rubutun littafin batsa abun so ne ga wasu mutanen. Shin wane kira za ka yi wa irin waɗannan marubuta?

Amsa: Rubutun batsa koma-baya ne ga dukkan marubuci mai ƙima. Domin kuwa, shi marubuci tamkar malami ne da ke koyar da tarbiyya, to idan kuwa aka wayi gari shi ya koma aikata ɓarna ai ya ci baya kenan. Kiran da zan yi ga masu rubutun batsa kuma shi ne, su guji rubuta abinda zai zamo musu bala’i duniya da lahira, su mayar da hankali wajen rubuta abinda zai amfane su da sauran jama’a duniya da lahira.

Tambaya: Ka samu nasarori da dama duba da irin littafan da kake yi irin waɗanda mutane ba sa gajiya da karantawa ne, kuma suna daga cikin waɗanda suka yi suna, kusan duk mai karatun litattafai na Hausa ya san su. Shin waɗanne irin nasarori ne ka samu wajen rubutunka?

Amsa: Babbar nasarar da na samu a harkar rubutu ita ce damar yin rubutun da mutane ke so, suke karantawa har ma su amfana. Nasara ta biyu kuma ita ce sanayya da na samu a wurin jama’a masu tarin yawa waɗanda ban san iyakar su ba. Sannan na samu lambobin yabo daga wurare da dama kuma na samu kyautuka na kuɗi da ban san adadinsu ba.

Tambaya: A naka ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi ma’ana da tsari?

Amsa: Rubutun bugu na hannu ya fi, saboda ana tsayawa a bashi haƙƙoƙinsa yadda ya kamata. To sai dai shi ma rubutun online yana da irin nashi muhimmancin, musamman duba da irin yadda zamani ya canza. Kuma duk da haka, a kan samu jajirtattun mutane da ke tsayawa kai da fata wajen ganin sun inganta shi. Wataƙila hakan na daga cikin dalilan da ke sa yake ta ƙara samun karɓuwa a wurin masu karatu.

Tambaya: Wasu mutanen suna tunanin cewa babu abin da rubutu yake jawowa sai ɓata tarbiyya. Shin wacce shawara yakamata a dinga ba irin waɗan nan mutanen?

Amsa: Wannan magana ba gaskiya bace, rubutu babbar hanya ce ta isar da muhimman saƙonni ga al’umma ta hanya mai sauƙi da za su iya fahimta kuma su ɗauka. Dalili na farko da zai tabbatar miki da haka kuwa shi ne, kaso casa’in da biyar da ɗigo biyar duk za ka samu mutanen kirki ne, in banda waɗansu ‘yan tsirarun da suka fanɗare. Kin ga kenan ba daidai ba ne a yi jam’in aiyukansu waje guda. Matasa da yawa a wannan zamani daga maza har mata suna amfana daga rubutun da ake wajen fahimtar al’amuran zamantakewa, kai har ma da na addini a wasu lokutan.

Tambaya: Shin ya kake ganin tafiyar adabin Hausa? Ma’ana, irin ci gaban da aka samu game da shi a yanzu?

Amsa: Gaskiya adabin Hausa na samun gagarumar nasara, musamman adabin zamani. Saboda yanzu zamani ne na ilimi da ci gaban zamani, hakan ya sa ilimi ya yawaita kuma kullum manazarta, marubuta da sauran masu sha’awar adabin ƙaruwa suke yi ba raguwa ba.

Tambaya: Wacce Karin Magana ka fi so? Kuma me ya sa?

Amsa: ‘Jiki Magayi, duka da ɗanyar kara.” Saboda ka ƙi jin gyara da baki, jikinka ya gaya maka. Saƙo ne a buɗe.

Tambaya: Shin ka na da wani maigida da yake nuna maka harkokin rubutu?

Amsa: Tabbas ina da shi, ba ma mutum ɗaya kawai ba. Da farko dai akwai Malam Mujaheed Abdullahi Kudan, wanda Malami ne a Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harsuna na Jami’ar Jihar Kaduna. Kuma ya taɓa kasancewa Mai Taimaka wa Shugaban Karamar Hukumar Kudan a Kan Bincike da Sadarwa ta Zamani (Technical Assistant, Research, Documentation and Social Media). Shi ne mutum na farko da ya fara yin nazarin rubutuna. Sannan akwai Jamilu Adamu Ɗanwayye, da Lawan Ɗalha, da Abubakar Sadik da ma sauran wasu da dama.

Hira da Haiman Raees 3
Marubuci Haiman Raees

Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ka ke rubutawa a yanzu haka da masoyanka za su yi tsumayin fitowarsa?

Amsa: Akwai litattafaina guda huɗu da nake sa ran duk za su fita a cikin wannan shekarar in Allah ya yarda. Su ne kamar haka:

  • Dandi Ƙaho
  • Tsibirin Al’ajabi
  • Kiahiyar Kwali
  • Keken Ɓera

Tambaya: Wacce irin shawara za ka iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?

Amsa: To duk da dai ni ma sabon marubuci ne, ina ba su shawara da su zamo masu kyakkyawar manufa a cikin harkar rutbutunsu, kada su ke yin abubuwa ba tare da tsari ba. Yawancin abubuwa marasa tsari ba sa tasiri.

Tambaya: Daga ƙarshe, me za ka iya cewa game da Hikaya?

Amsa: Hikaya ta zamo tamkar gida ne a wurina. Babu ranar da ba na shiga saboda irin amfanuwa da nake yi da ita ta fuskoki da dama. Ina fata wata rana Hikaya ta zarce kamfanin Amazon wajen samar da litattafai ga masu karatu.

Tsara tambayoyi da gabatarwa: Asma’u Abdallah (Fulani Bingel)

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page