Skip to content

Kadan daga ka’idojin rubutun Hausa domin marubuta

Marubuta da dama na fama da ƙarancin fahimtar ƙa’idojin rubutun Hausa, hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon mafi yawancinsu ba harshen Hausa suka karanta ba. Wasu sun fara rubutu ne kawai saboda suna da sha’awa, ba tare da sun san da zaman ƙa’idojin ba. Sanannen abu ne cewa da yawan mutane na yaudarar kansu ta hanyar tunanin za su iya amfani da kasantuwarsu Hausawa su yi rubutu da Hausa hakan nan ba tare da bin ƙa’idojin harshen ba. Irin waɗannan mutane da dama za ka same su cikin da na sani daga baya, domin da zarar tafiya ta fara nisa za su fahimci cewa dole su koma su fahimci waɗannan ƙa’idojin, matuƙar dai suna so su cimma nasara a rubutunsu.

Wannan dalili ne ya sa na yi wannan ɗan rubutu domin haskakawa ‘yan’uwana marubuta waɗannan ƙa’idojin.

Haruffan Hausa

Kamar sauran mafi yawancin yaruka, harshen Hausa yana da nasa haruffa da ake amfani da su wajen rubutun Hausar boko. Waɗannan haruffa kuwa an samo su ne daga haruffan turanci. Shi harafi ƙwayar sauti ne da ke ɗauke da wata magana cikakkiya kuma mai ma’ana. Shi kuwa sauti, a iya cewa shi ne duk wani amo da kunne ke iya shaidawa.

Haruffan Hausa sun rabu gida biyu, wato baƙaƙe da wasulla.

Baƙaƙe

Bb Cc Dd Ff Gg Hh Jj Kk Ll Mm Nn Rr Ss Tt Ww Yy Zz

Baƙaƙe masu goyo

Su irin waɗannan baƙaƙen wani lokaci akan kira su da baƙaƙe masu aure, gwamammu ko kuma tagwaye. Ga su kamar haka:

fy, gy, gw, ky, kw, ƙy, ƙw, she, ts, ‘y

Wasulla

Aa Ee Ii Oo Uu

Wasulla masu aure

Irin waɗannan wasullan, kamar dai baƙaƙe masu goyo, akan kira su da tagwaye ko gwamammu. Su ne kamar haka:

ai, au, oi, ui

Haruffa masu ƙugiya

Haruffa masu ƙugiya mun yi bayaninsu a baya, na ƙara kawo su a nan ne kawai domin fayyacewa. Wani lokaci akan kira su da haruffa masu tanƙwara. Dukkansu guda biyar ne. Ga su kamar haka:

Manya

Ɓ, Ɗ, Ƙ, ƘY, ƘW

Ƙanana

ɓ, ɗ, ƙ, ƙy, ƙw

Rashin amfani da waɗannan haruffa a inda ya dace na iya hana ma’anar kalma ta haƙiƙa fitowa fili, ko kuma ya sauya ma’anar kalma ko jimlar gaba ɗaya. Ga misalin yadda ake amfani da su:

 • ɓarawo ba barawo ba
 • ɗaki ba daki ba
 • ƙarfe ba karfe ba
 • ƙyaure ba kyaure ba
 • ƙwarya ba kwarya ba

Amfani da babban baƙi

Da babban baƙi ake fara rubutu a farkon sakin layi, da gaban aya, da farkon sunaye, da gaban waƙafi mai ruwa, aya ruwa biyu, alamar motsin rai, alamar tambaya da karan tsaye. Don haka wajibi ne mai rubutun Hausa ya kiyaye su sosai.

Sunayen yanka

Duk sunan yanka da babban baƙi ake fara rubuta shi.

Misali

 • Aisha ba aisha ba
 • Kamal ba kamal ba
 • Kano ba kano ba
 • Afirka ba afirka ba

Sunayen ranaku

Su ma sunayen ranakun mako ba a fara rubuta su da ƙaramin baƙi.

Misali:

 • Litinin ba litinin ba
 • Talata ba talata ba
 • Laraba ba laraba ba
 • Alhamis ba alhamis ba
 • Juma’a ba juma’a ba
 • Asabar ba asabar ba
 • Lahadi ba lahadi ba

Sunayen watanni

Duk sunayen watannin shekara da babban baƙi ake fara rubuta su.

Misali:

 • Janairu ba janairu ba
 • Fabarairu ba fabarairu ba
 • Muharram ba muharram ba
 • Rajab ba rajab ba

Kalmomin jama’u

Duk kalmomin jama’u haɗa su ake yi waje guda. Ga misalan kalmomin jama’u da yadda ake rubuta su.

 • kowaɗanne ba ko waɗanne ba
 • koyaushe ba ko yaushe ba
 • kowanne ba ko wanne ba
 • kowacce ba ko wacce ba
 • ko’ina ba ko ina ba
 • komai ba ko mai ba

Harɗaɗɗun kalmomi

Harɗaɗɗun kalmomi da karan-ɗori ake rubuta su, in kuwa ba a yi hakan ba, lallai an zaɓa wa Daidaitacciyar Hausa.

Misali:

 • gaya-wa-jini-na-wuce
 • a-kori-kura
 • bi-da-bi

Nuna mallaka

A ƙa’idar rubutun Hausa, akwai yadda ake rubuta mallaka. Mallaka iri biyu ne a nahawun Hausa, doguwa da gajeruwa. Sannan in ana maganar mallaka, akwai abubuwa guda biyu da ya kamata a lura da su, wato mai mallaka da kuma abinda aka mallaka.
Ga misalan mallaka:

Doguwa

 • riga tamu ba riga don mu ba
 • naki ɗakin ba na ki ɗakin ba

Gajeruwa

 • rigarka ba rigar ka ba
 • ɗakinki ba ɗakin ki ba
 • gidanku ba gidan ku ba

Harafin M ko N?

Wani lokaci marubuci kan kasa tantance harafin da ya dace ya saka a tsakiyar kalma, wato ya kasa tantance m ne ko n. To amma, harafin m ya kamata a yi amfani da shi idan har baƙin da ya biyo b, f, ko m ne.

Misali:

 • bambanci ba banbanci ba
 • ambato ba anbato ba
 • shimfiɗa ba shinfiɗa ba.
 • famfo ba fanfo ba

To amma kalmar da za a iya saka harafin n ɗin ba ɗaya suke da waɗancan ba.

Misali:

 • tankiya ba tamkiya ba
 • tuntuɓe ba tumtuɓe ba
 • santsi ba samtsi ba

Ƙarshen kalma

Harafin n ake amfani da shi a ƙarshen kalma ko da kuwa baƙin da ya biyo baya b, ɓ, f ko m ne.

Misali:

 • ‘yan fashi ba ‘yam fashi ba
 • yawan magana ba yawam magana ba
 • kejin zomo ba kejim zomo ba

Harafin R da D

Aikatau mai ƙarewa da (ar) da (d) su ne kamar su shigar da, fitar da, kawar da da dai sauransu. To in za a rubuta su, ba a haɗe su da kalmomin da ba su ƙare da (r) ɗin ba.

Misali:

 • Ta kawar da shi ba ta kawadda shi ba
 • Ya fitar da ita ba ya fitadda ita ba

Nanata baƙaƙe masu goyo

Mun mun yi magana game da baƙaƙe masu goyo a baya, yanzu kuma za mu yi bayani ne game da yadda ake rubuta su a cikin kalma ne. A ƙa’ida ba a maimaita asalin baƙin, ga yadda ya kamata a rubuta su:

 • tsattsaga ba tsatstsaga ba
 • fyaffyace ba fyafyfyace ba
 • Shasshaka ba shashshaka ba

Wato dai, harafin farko na harafin kawai ake maimaitawa.

2 thoughts on “Kadan daga ka’idojin rubutun Hausa domin marubuta”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page