Skip to content

Shawarwari 20 ga sabbin marubuta

Rubutu, kamar sauran sassan ilimi da ɓangarorin rayuwar yau da kullum yana da nashi irin tsarin da kuma dokoki. A matsayinka na sabon marubuci wanda yanzu zai fara rubutu, sanin matakai da dokokin da suka shafi rubutu na iya zama bambancin da ke tsakanin nasara da rashin ta a gare ka. A bisa wannan, ga wasu ‘yan shawarwari nan guda ashirin da za su taimaka maka wajen cimma nasara a harkar rubutu. Fatan alheri.

1. Manufa

A matsayinka na sabon marubuci, kana buƙatar ƙaƙƙarfar manufa kuma nagartacciyya matuƙar kana so ka yi nasara. Ya kamata ka yi wa kanka tambayoyi kamar haka:

  • Me ya sa ka ke son fara rubutu, shin za ka fara rubutu ne kawai don ka ga wasu na yi ko kuma don kana da nagartaccen labarin da ka aminta har cikin ranka cewa ya cancanta duniya ta ji?
  • Shin a matsayin nishaɗi za ka fara rubutu ko a matsayin sana’a?
  • Shin wane irin saƙo ka ke son isarwa a cikin rubutunka?
  • Wasu irin abubuwa ne ka ke fata masu karatu za su amfana da su cikin rubutunka?
  • Ya ya ka ke hango kanka nan da shekaru biyar ko fiye da haka a harkar rubutu?

Waɗannan tambayoyi da ma wasu ire-iren su na daga cikin tambayoyin da ya kamata ace sabon marubuci ya yi wa kansa tun kafin ya fara rubutu. Samun amsoshin waɗannan tambayoyi shi zai ba shi damar saita tunaninsa a bisa manufar da ta dace. Zaman tunaninsa akan manufar da ta dace kuma shi zai ba shi ƙwarin gwiwa a cikin tafiyar da zai yi daga wani mutum zuwa wani sabo yayin da ya shiga bigiren rubutu.

2. Ƙa’idojin rubutu

A matsayinka na sabon marubuci, wajibi ne ka san ƙa’idojin rubutu, ka kuma kiyaye su, matuƙar dai kana so ka samu karɓuwa kuma littafinka ya yi tasiri a zuciyar masu karatu. Sau tari sabbin marubuta kan ɗauka cewa tunda suna da labari mai daɗi, bari kawai su fara rubutawa kuma su sake shi duk yadda suka ga dama. Amma abin da suka kasa fahimta shi ne, rashin sanin ƙa’idojin rubutu na iya hana mai karatu fahimtar ainahin saƙon marubuci ballantana har ya amfana da shi. A matakin farko ma dai ba zai ji daɗin karatun ba ballanta ya maida hankali wajen fahimtar saƙon da ke cikinsa. Wasu makaranta, waɗanda suna da yawa, tun a shafin farko suke daina karanta littafin da suka ga bai cika ƙa’idojin rubutu ba, domin sau tari ciwon kai yake sa masu. Daga cikin abubuwan da sabbin marubuta ya kamata su kiyaye matuƙa game da wannan akwai;

  • Haruffa masu ƙugiya (ɓ,ɗ,ƙ)
  • Kalmomin da ake raba su da waɗanda ba a raba su (koyaushe ba ko yaushe ba)
  • Alamomin daidaita rubutu, su ne kamar haka:

– Aya .
– Waƙafi ,
– Waƙafi mai ruwa ;
– Ruwa biyu :
– Baka biyu ( )
– Karan ɗori –
– Alamar zarce ….
– Maganar wani ” “
– Alamar motsin rai!
– Alamar tambaya?
– Karan tsaye /
– ds.

  • Sanin baƙaƙe masu goyo (fy, gy, gw, ky,kw,ƙy,ƙw,sh,ts)

Ƙarin bayani

Akwai buƙatar sabon marubuci ya sani cewa, P,Q,V,X,CH ba haruffan Hausa bane kuma ba a amfani da su a cikin rubutu na yau da kullum. Sai dai wajen rubuta sunayen mutane, garuruwa da makamantansu. Misali; Bauchi, Qatar, Peter ds.

Sanin yadda ake amfani da waɗannan zai taimaka wa sabon marubuci ƙwarai wurin gyara rubutunsa ya fita da kyau.

3. Daidaitacciyar Hausa

Kusan kaso hamsin na sabbin marubuta basu san komai ba dangane da Daidaitacciyar Hausa har sai da suka fara rubutu. To me ake nufi da Daidaitacciyar Hausa? Daidaitacciyar Hausa samfuri ne na salon maganar da dukkan Hausawa suka yi tarayya a kansa. Wannan samfuri kuwa, kari ne da aka zaɓa aka daidaita masa ƙa’idojin rubutu da na nahawu, kuma aka adana su cikin litattafai da ƙamusoshi domin amfanin masu magana, rubutu da nazari a harshen Hausa. Kenan in mun fahimci hakan, Bakatsine ba zai yi rubutu da karin harshen katsinanci ba, haka Basakkwace da ma duk sauran kare-karen Hausa. Wannan ya sa lallai ne sabon marubuci ya san Daidaitacciyar Hausa da ƙa’idojinta domin ya zamana kowa zai iya karanta labarin da ya rubuta kuma ya fahimce shi.

4. Jigo

Jigo shi ne ƙashin bayan kowane labari, shi ne yake kasancewa muhimmin saƙon da labarin ke isarwa. To a nan, akwai buƙatar sabon marubuci ya zaɓi jigo mai nagarta wanda zai yi rubutu a kansa. Zai fi kyau sabon marubuci ya yi rubutu a kan abin da ya sani, hakan zai ba shi damar yin rubutu mai kyau da nagarta. Akan samu masu yin amfani da jigo fiye da ɗaya a rubutu. To amma, sabbin marubuta ya dace su sani cewa, akwai jigogi masu tarin yawa da suka shafi al’ummarmu ta fuskoki da yawa da za su iya ɗauka su yi rubutu game da su. Ba wai su ke ɗauko labaran wasu abubuwa da basu da jiɓi da su ba. Ɗauko jigo daga cikin al’amuran da suka shafe su zai ba su damar rubuta abin da mutanenmu za su fi karɓa kuma su amfana da shi. Alal misali, littafin da aka rubuta shi game da sana’o’in gargajiya na Hausawa tare da nuna al’adun Hausawa da suka jiɓinci waɗannan sana’o’in sai ya fi dacewa da al’ummar Hausawa fiye da littafin da aka rubuta shi game da wata Bahaushiya da suke soyayya da wani Balarabe.

5. Nau’in littafi

To bayan ka zaɓi jigo mai kyau da za ka yi rubutu game da shi, ya kamata ka zaɓi nau’in da za ka yi rubutu a kansa. Misali, nau’in litattafan soyayya za ka ɗauka ko na yaƙi, na siyasa ko na barkwanci. Sannan ya kamata marubuci ya zaɓi fannin da zai yi rubutu akai daga cikin fannonin adabin zamani. Wato rubutun zube (prose), ko rubutun wasan kwaikwayo (drama), ko kuma rubutacciyar waƙa (poem). Kowanne marubuci ya ɗauka daga cikinsu zai iya fitar da jigon da yake so. Sai dai ya danganta ga wanda ya fi ƙwarewa a kai ne.

6. Zubi da tsari

Wannan ya shafi yadda marubuci ya yi amfani da kalmomin da suka tayar da labari ne. Waɗansu labaran kan zo da kalmomi masu tsauri, wasu kuma masu sauƙi. To ya dace sabon marubuci ya yi amfani da kalmomi masu sauƙi wajen fitar da labarinsa ta yadda mai karatu zai iya fahimta a sauƙaƙe. A nan, marubuci ya fara sarrafa labari a ƙwaƙwalwarsa kafin ya fara rubutawa. Sannan marubuci ya yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin masu karatu sun yarda da labarinsa ta hanyar kawo misalai irin waɗanda masu karatu za su iya aminta da su. Ka da sabon marubuci ya ɗauko gingimemen al’amarin da zai yi wa masu karatu wuyar fahimta ko aminta da shi. Kuma ka da ya cika cikurkuɗa abubuwa da yawa ta yadda mai karatu zai ruɗe.

7. Salo mai armashi

Shi salo wani ɓangare ne da ya shafi yadda marubuci ke amfani da shi wajen jawo hankalin masu karatu da burgewa ko ƙarfafa sha’awarsu. A nan, sabon marubuci na iya amfani da karin magana, siffance da makamantansu wajen bayyana abubuwan da ke cikin labarinsa ta yadda zai cimma wannan manufar. Bai kamata sabon marubuci ya yi amfani da harshen da ba za a iya fahimtarsa ba a cikin littafinsa.

8. Gajarce labari

A matsayinka na sabon marubuci, kome daɗin labarinka, idan har ya ya yi tsawo da yawa sosai ba lallai ne mafi yawan masu karatu su karanta shi har ƙarshe ba. Daga cikin dalilan da suka jawo haka kuwa har da irin yadda masu karatun na yanzu suke. Sau da dama yanzu ba kowa ya cika yin karatu ba. Sau da dama za ka taras da masu karatun kuma, ba kowa ke iya zama ya karanta littafi daga farko har zuwa ƙarshe ba. Wannan kuma na iya zama saboda ƙarancin lokaci, yawan buƙatu da uzuri da ya yi wa mutane yawa da sauransu. Sannan yana kuma iya zama saboda girman littafi ko kuma ƙarancin daɗin labarin da zai iya riƙe mai karatu. Wani babban dalili kuma shi ne, ba kowa ke karanta littafin sabon marubuci ba, kuma daga cikin masu karantawar ma ba kowa ne zai ɗauki ƙaton littafi ba, domin zai ba shi tsoron karantawa saboda dalilan da na ambata a baya. Saboda haka, sabon marubuci ya kamata ya gajarce labarin sa, ka da ya yi tsawo sosai. Kuma gajarce labarin zai ba ka damar saka abubuwa masu yawa da za su ja hankalin mai karatu sosai, saɓanin in ya yi yawa wanda har tunaninka ya ƙare a kai.

9. Bango da suna

Bango da sunan Littafi na ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo hankalin mai karatu zuwa ga littafi. Sau da dama za ka ji masu karatu na bayyana irin yadda sunan littafi ya ja ra’ayinsu har suka fara karanta shi. Saboda haka, lallai yana da matuƙar amfani ga sabon marubuci ya zaɓi suna mai matuƙar ma’ana da jan hankali ya saka wa littafinsa. Shi kuwa bangon littafi, kai tsaye a iya cewa muhimmancinsa ɗaya yake da na suna. Domin sau tari wasu masu karatun bangon littafi ne ke jan ra’ayinsu. To a nan, ya kamata sabon marubuci ya sani cewa, ba lallai sai ka sa hoton mutum a bangon littafinka sannan zai samu kasuwa ba. Babban abin nufi shi ne, ya zama yana isar da saƙon da ke cikin littafin. Da za ka bincika manyan litattafan Hausa, mafi yawancinsu za ka taras zane ne kawai a jikinsu. Duba bangon litattafai irin su Ruwan Bagaja, Iliya Danmaikarfi, Jiki Magayi, Magana Jari Ce d.s. Sannan, wani muhimmin abu da sabbin marubuta ya dace su fahimta shi ne, saka hoton Turawa ko Indiyawa a jikin bangon littafinsu, matuƙar littafin bai shafi wani abu na waɗannan mutanen ba tamkar koma baya ne ga Hausa da Hausawa. Kenan, ba lallai sai bangon littafinka ya ya zamo yana ɗauke da hoton mutane ba, kuma bai kamata in zai ɗauki hoton mutanen ya ɗauki na ƙetare ba tare da wani muhimmimin dalili ba.

10. Taurari

Taurarin kowane labari su ke jan ragamar labarin har ya kai inda marubuci ke so labarin ya kai. To sai dai kuma, sabon marubuci bai kamata ya dinga amfani da taurari iri ɗaya ba. Ma’ana, ka da marubucin ya yi ta amfani da taurari kyawawa, masu ilimi, masu kuɗi ko masu muƙamai a kodayaushe. Ya zamana yana sako taurari masu yanayi irin na sauran mutanen da ke cikin al’ummarnu. Hakan zai sa kowa ya ji cewa shi ma ba a barshi a baya ba a cikin labarin. Misalin irin taurarin da za a iya saka su a cikin labari akwai makafi, guragu da sauransu.

11. Yawan karatu

Masu karatu a ko’ina su ke zama marubuta a gaba. Wajibi ne marubuci ya zamo mai yawan karatu, musamman game da irin abubuwan da yake sha’awar yin rubutu game da su. Yawan karatun shi ke ƙara sa marubuci ya samu bayanai masu tarin yawa waɗanda zai iya yin amfani da su hatta a cikin nashi rubutun.

12. Bincike

Abu ne mai matuƙar muhimmanci ga kowane marubuci ya zamo mai yawan bincike, musamman a kan abin da yake so ya yi rubutu a kai. Yin bincike wata hanya ce mai tsafta da ke ba wa rubutun marubuci damar samun nagarta ta hanyar faɗin abinda ya dace kuma a yadda yake, ba wai shaci-faɗi ba ko ƙarya. Rashin yin bincike na iya sa marubuci ya yi ƙage wa wasu gungun mutane ko ya muzanta su ko ya yi katoɓara game da addininsu ko ƙabilarsu. Kai rashin bincike ma na iya sa marubuci ya ya yi saɓo ko kuma ya yi gagarumin lahani ga ilimi ko rayuwar al’umma. Don haka, yana da matuƙar muhimmanci ga sabon marubuci ya kasance ya yi bincike mai zurfi game da abin da yake so ya yi rubutu a kai kafin ya fara.

13. Maigida

Da yawan marubuta kan yi alfaharin cewa su ba su da wani Maigida ko wani na sama da su da ke ɗora su a hanya game da rubutu. Sai dai wannan ba abin alfahari bane, asali ma dai a iya cewa abin kunya ne na bugawa a jarida. Domin ko a cikin marubutan wannan zamani da za ka duba da kyau, za ka samu masu ubangida ko wasu malamai da ke yi musu jagoranci a tagiyarsu sun fi cin nasara fiye da masu yin gaban kansu. Kuma daga cikin dalilan faruwar hakan shi ne, saboda su ana nusar da su zuwa ga yadda za su gyara kurakuransu tun kafin duniya ta gani, saɓanin waɗancan da sai duniya ta faɗa musu sannan suke ganewa. Don haka yana da matuƙar muhimmanci ga sabon marubuci ya zama yana da wani Maigida ko wanda ya fi shi ilimi da zai dinga duba mishi aiyukansa lokaci bayan lokaci domin yin gyara da tace aikin daga ɓarna.

14. Ƙungiyar marubuta

Yana da kyau sabon marubuci ya kasance a cikin ƙungiyar marubuta. Hakan zai ba shi damar haɗuwa da mutane daban-daban kuma zai ƙaru da su ta inda bai yi tsammani ba. Sannan ƙungiyoyin marubuta da dama suna gabatar da shirye-shirye na ba wa junansu horo da shawarwari a fagen rubutu. Kenan hakan zai taimaka wa sabon marubuci wajen gogewa da kuma yaɗa rubutunsa a sauƙaƙe. Akwai ƙungiyoyi da dama da sabon marubuci zai iya shiga, ga kaɗan daga cikinsu:

Lafazi Writers Association
Kainuwa Writers Association
Zamani Writers Association
Arewa Writers Association
Jarumai Writers Association
Noble Writers Association

15. Ziyartar taruka

Ziyartar tarukan gani da ido na marubuta da dandalin marubuta na soshiyal midiya wani babban al’amari ne ga sabon marubuci. Daga cikin amfanin yin hakan akwai haɗuwa da marubuta sabbi da tsoffi, haɗa zumunci a tsakanin marubuta da makaranta da dai sauransu. Duk waɗannan abubuwa kuwa na iya ƙarawa marubuci ilimi ta inda bai yi tsammani ba. Akwai taruka da dama da ake yi da sabon marubuci zai iya halarta. Alal misali, akwai Taron Mujallar Zauren marubuta da ake yi a duk shekara. Akwai bikin ranar marubuta ta duniya, akwai taron Makon Adabi da sauransu da dama. Kuma ƙungiyoyin marubuta da dama su ma kan yi irin nasu taruka.

16. Farawa ta online

Yanzu muna wani zamani ne da karatu ta online ya fi samun karɓuwa fiye da na bugun hannu. Kuma wani ikon Allah, sai ya zamana ya fi sauƙi ga makaranta da marubutan baki ɗaya. A matsayinka na sabon marubuci lallai zai fi kyau ka fara da sakin littafinka a online tukunna kafin ka fara tunanin buga na hannu. Kuma in za ka sake shi ɗin, to ya zama kyauta ne. Hakan zai ba wa masu karatu da yawa damar karanta shi ba tare da sun yi tunanin kashe kuɗin su a kan marubucin da ba su sani ba. Da zarar sun ji daɗin karanta labarin, wata rana don ka sa na kuɗi ba za su ji ƙyashin biya ba. Akwai kafofin yanar Gizo irin su Bakandamiya Hikaya, Okada Books, Arewa Books da Wattpad da marubuta za su iya ɗora litattafansu a kai.

17. Yin rubutu akai-akai

Yawan yin rubutu akai-akai zai sa marubuci ya goge sosai. Amma wasu sai ka ga sun yi rubutu kuma ya karɓu, amma ba za su ƙara yin wani ba sai bayan shekaru uku ko biyar. Ko da ba za ka yi rubutun littafi cikakke ba, lokaci bayan lokaci ka ke yin gajerun labarai ko muƙaloli kana fitarwa.

18. Shiga gasar rubutu

Shiga gasar rubutu dama ce ga sabon marubuci ke samu domin yin gogayya da ‘yan’uwansa marubuta. Sannan tana ba shi damar yin rubutu a kan abubuwa masu yawa wanda zai ba shi damar fito da ainahin basirarsa da kuma hikimar da Allah ya yi masa. Kadan daga cikin irin wadannan gasar akwai gasar Hikayata ta BBC, da gasar Arch. Ahmad Musa Ɗangiwa, da gasar gajerun labaran Aminiya da sauransu.

19. Haƙuri

Duk waɗannan shawarwari, ko da ka bi su gaba ɗaya, to dole sai ka haɗa da haƙuri. Saboda nasara ba ta samuwa dare ɗaya haka kawai. Dole sai ka jajirce, ka nace kuma ka dage da yin rubutun har zuwa lokacin da za ka fito kai ma ka shana.

20. Addu’a

Daɗin labarinka da kuma ƙwarewa a fagen iya tsara shi na iya sa a karanta, amma addu’a ita ce asalin abin da zai kai ka ga nasara. Ka dage ka bi waɗannan shawarwari, kuma ka dage da addu’a, za ka sami nasara da yardar Allah.

4 thoughts on “Shawarwari 20 ga sabbin marubuta”

  1. Avatar

    Ma sha Allah..Gsky shawarwarin abun dauka ne gamu masu sha’awar fara rubutu
    Ni na fara rubutu but ban taba posting har na bude Kungiya na marubuta but members din duk yanzu suka fara rubutu ina fuskanta matsala rashin qualifed members da marubuta masu bani shawari

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page